Riga-Kafi Ya Fi Magani: Riga-Kafin Ciwon Shan Inna A Ma’aunin Bahaushe

    Published in Himma Journal of Contemporary Hausa Studies, Vol. 1 No. 1 June, 2009, Department of Nigerian Languages, Umaru Musa Yar’adua University, Katsina, Page 106 – 121

    Riga-Kafi Ya Fi Magani: Riga-Kafin Ciwon Shan Inna A Ma’aunin Bahaushe 

    English Rendition as “Preɓention is better than Cure: Poliomyelitis as Measured by a Typical Hausa man” 

    BASHIR ALIYU SALLAU
    Department of Nigerian Languages
    Umaru Musa Yar’adua University, Katsina – Nigeria 

    Tsakure

    Rayuwar kowace al’umma tana tafiya tare da tunaninsu da yardarsu da imaninsu kan abubuwan da ka iya faruwa gare su da ma waɗanda suka rigaya suka faru a gare su. Wannan dalili ne ya sa kowace al’umma takan alaƙanta dukkan abin da ya faru ga ‘ya’yan wurin wani abin da suka amince da shi. Misali, kafin al’ummar Hausawa su karɓi addinin Musulunci da kuma shigowar sabuwar rayuwa wadda Turawa suka kawo, idan wata cuta ta kama mutum, a mafi yawancin lokaci ana alaƙanta wannan cuta da iskoki ko mutanen ɓoye, ko kuwa a danganta ta da sammu ko makaru. Misali, cutar Shan Inna cuta ce wadda wasu Hausawa suka ɗauka, iska Inna ce take haddasa ta. Karɓar addinin Musulunci da shigowar Turawa ƙasar Hausa ya kawo sauye-sauye dangane da wannan tunani aka fahimci cewa, akwai cututtuka waɗanda iskoki kan haddasa, akwai kuma waɗanda ake kamuwa da su ta hanyar shigar wasu ƙwayoyin cuta cikin jikin mutum, ana kuma iya yin riga-kafin kamuwa da su. 

    1. 0 Gabatarwa

    A haƙiƙa yana da matuƙar wuya a ce ga lokacin da ɗan Adam ya fara tunanin warkar da cututtukan da kan matsa wa rayuwarsa ko bin wasu hanyoyi domin kare kansa daga kamuwa da su. Saboda haka a iya cewa, asalin magani domin warkar da cututtuka ko domin kariya daga kamuwa da su a wannan duniya al’amari ne wanda ya daɗe ƙwarai. Wannan dalili ne ya sa wasu masana da manazarta da ɗaliban nazarin magani da al’adu suka kawo hasashensu kan asalin magani a wannan duniya kamar haka:

    Hanya ta farko wadda aka bayyana a matsayin wadda ɗan Adam ya sami wannan hikima, ita ce ta jarraba abubuwan da Allah Maɗaukaki ya yalwata a kusa da shi. An ƙara da bayyana cewa, akwai abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da itatuwa da tsirrai da sinadarai a ko’ina, kuma a yalwace cikin wannan duniya tamu, waɗanda ta hanyar gwada su ne a lokacin da aka fuskanci wata matsala ta rashin lafiya ɗan Adam ya sami hanyar warkar da cututtuka iri daban-daban da suke damunsa. Masu irin wannan ra’ayi na ganin cewa, ta wannan hanya ce magani ya samo asali har ya kai matsayin da yake a yau (Musa, 1986:7).

    Hasashe na biyu ya bayyana cewa, magani ya samo asali daga tsuntsaye da dabbobi da ƙwari na gida da na daji. A wannan ra’ayi ana ganin cewa, magani ya samo asali ne a sakamakon ire-iren hakukuwa da tsirrai waɗanda tsuntsaye da dabbobi ke ci. Wai a lokacin da waɗannan halittu suke lafiya akwai nau’o’in abincin da suke ci, haka kuma a lokacin da ba su da lafiya akwai ire-iren hakukuwa da itatuwan da suke ci. Waɗanda suka kawo wannan ra’ayi sun bayyana cewa, ta wannan hanya ce ɗan Adam ya gano ire-iren hakukuwa da tsirrai waɗanda idan aka yi amfani da su za a sami waraka daga wasu cututtuka (Musa, 1986:8).

    Wani hasashen kuma yana bayyana cewa, magani dai ya samo asali ne a sakamakon baiwa da Allah Maɗaukaki yake ba wasu mutane a kan sanin magungunan cututtuka iri daban-daban. Masu irin wannan ra’ayi suna bayyana cewa, ire-iren waɗannan mutane kan sami irin wannan baiwa ce a lokacin da wani ciwo ya kama su. A irin wannan lokaci ne Allah Maɗaukaki, cikin ikonsa yake sanar da su ire-iren hakukuwa da tsirran da suka dace su yi amfani da su da kuma yadda za su yi amfani da su domin samun waraka daga wannan cuta (Musa, 1986:8).

    Idan muka nazarci waɗannan hasashe na asalin magani, a iya cewa ra’ayi na uku ya fi ɗaukar hankali, don kuwa tun farko an yarda da cewa, Allah Shi ya halicci mutum, ya kuma halicci magani da cuta, sannan ya sanar da mutum magungunan cututtuka iri daban-daban, amma waraka a hannunsa take.

    Ta irin sanin da Allah Maɗaukaki ya ba ɗan Adam ne aka sami wasu mutane a wannan zamani waɗanda suka gudanar da nazarce-nazarce na kimiyya wanda ya haifar da samuwar nau’o’in magunguna daban-daban. Ire-iren waɗannan magunguna ana amfani da su domin warkar da cututtuka masu yawa ko kuwa don yin kariya ga jiki yadda ba zai fuskanci barazanar kamuwa da wasu cututtuka ba. Haka kuma a wasu lokuta wasu daga cikin manazarta kan zuba wasu abubuwa cikin waɗannan magunguna da suka ƙirƙiro domin cim ma wani buri wanda ka iya yin aibi ko kasha wanda ya yi amfani da wannan magani.

    A saboda haka, bayanan wannan takarda an gabatar da su ne, domin a fito da bayani kan ciwon Shan Inna da yadda Hausawa suka ɗauke da kuma ire-iren magunguna da alluran riga-kafin wannan ciwo a wannan zamani. 

    1. 1 Tarihin Magungunan Riga-Kafi

    Hanyar yin riga-kafi ko kare jiki daga kamuwa da wasu cututtuka daɗaɗɗiya ce a tsakanin al’ummomin wannan duniya. Tun kafin shigowar Turawa ƙasar Hausa, akwai hanyoyin da ake amfani da su domin a kare yaɗuwar wasu cututtuka a tsakanin wannan al’umma. Misali, mutanen ƙasar suna amfani da ‘ya’yan iccen gawo domin riga-kafin ciwon ƙyanda. Ana yin ‘yar ƙofa a wurin ‘ya’yan a saka zare a rataya wa yara a wuya kamar laya. Haka kuma, suna amfani da baƙin tukunya wanda ake shafa wa yara a idanunsu domin riga-kafin ciwon ƙyanda nau’in da yake sanadiyyar makanta yaran day a kama. Bayan wannan akwai cututtuka iri daban-daban waɗanda Hausawa suke yin riga-kafin kamuwa da su. A tunaninsu waɗannan hanyoyi suna taimaka masu wajen rage yaɗuwar waɗannan cututtuka da makamantansu. Wannan dalili ne ya sa Hausawa suke da wata faɗa da suke cewa, “Riga-kafi ya fi magani”, watau a yi riga-kafin cuta kafin abkuwarta.

    A lokacin da Turawa suka shigo ƙasar Hausa sun kawo sabuwar rayuwa wadda ta ƙunshi amfani da magungunan zamani naƙwarori da na ruwa na shad a allurai da sauransu. Haka kuma, sun tarar cututtuka irin su ‘yan rani da agana sun addabi mazauna wannan ƙasa. Saboda haka, alluran riga-kafi na farko da aka fara shigowa da su cikin ƙasar Hausa, sun e na yaƙi da ciwon ‘yan rani da agana waɗanda a wancan lokaci aka riƙa kiransu ‘lamba’. Sannu a hankali ana ƙara samun wayewa da fahimtar muhimmancin magungunan asibiti har aka kawo wannan zamani wanda aka ƙirƙiro magungunan riga-kafin cututtuka iri daban-daban waɗanda a wasu lokuta suke nakasa wanda ya kamu da cutar ko su kasha shi.  

     

    2. 0 Alluran Riga-Kafi

    Alluran riga-kafi hanya ce wadda ake bi a wannan zamani domin kula da lafiyar jarirai da yara ƙanana don kare jikinsu daga kamuwa da wasu cututtuka waɗanda kan yi barazana ga lafiyarsu. Ire-iren waɗannan cututtuka sun haɗa da ciwon Shan Inna da tarin-huka da tarin maƙarau da tarin shiƙa da tsinkau-tsinkau da ciwon hanta da ciwon ƙyanda da ciwon shawara. Haka kuma ana yi ba jarirai da yara ƙanana sinadarin Ɓitamin ‘A’ domin ƙarin gani da ƙarfin garkuwar jiki.  Wannan takarda za ta yi bayani ne a kan ciwon Shan Inna a idon Hausawa jiya da yau.

     

    2. 1 Ciwon Shan Inna

    Shan Inna cuta ce wadda kan yin dalilin mutum ya rasa ɗayan hannuwansa ko ƙafa ko wani sashe na jikinsa ya shanye, ya kuma daina yin cikakken amfani. A wasu lokuta wasu daga cikin waɗanda suka kamu da wannan ciwo kan samun taɓuwar ƙwaƙwalwa, haka kuma yakan haddasa wasu cututtuka iri daban-dabam kamar sanyewar magana, da fitar da yawu ba da sani ba, da rawar kai da kyarmar hannu da ciwon farfaɗiya da sauransu (Bunza, 1995:543).

     

    2. 2 Ciwon Shan Inna a Idanun Hausawa

    Ita wannan cuta ta Shan Inna, Hausawa sun ɗauka cewar iska Inna ce take haifar da ita. Wannan dalili ne ya sa idan ciwon ya kama mutum ake kai shi wurin bokaye ko ‘yanbori’ ko wanzamai domin neman magani.

    Haka kuma an ɗauka cewa, ita wannan aljana Inna ce take shanye jinin mutum daga nan sai ya kamu da ciwon Shan Inna. Wasu Hausawa kuma, sun yarda da cewa, kowane mutum yana tare da iskoki, kuma dukkan abin ya yi ko ya faɗa suna jin sa. Wannan dalili ne ya sa har a wannan zamani ake tsoron faɗar wata Magana ko yin wani aiki wanda zai zama marar daɗi wurin iskokin, don suna da tunanin yin haka zai sa iskokin su cuci wanda ya yi ire-iren waɗannan maganganu ko ya aikata irin wannan aiki. A saboda haka ne, mafi yawancin mutanen da aka tattauna da su dangane da wannan bincike day a shafi ciwon Shan Inna a al’adar Hausawa, a farko da ƙarshen bayaninsu, sai sun yi roƙo da yin tuba ga iska Inna, don ta san ba zagin ta ake yi ba. A tunaninsu yin haka ne zai sa ba za ta cuce sub a. Ga irin roƙon da ake yi mata:

    “Amma Allah shi ba ki haƙuri,

    Yabonki ake yi ba zagin ki ba,

    Sha’ani ne na amana da haihuwa,

    Ka da ki bi ko ɗaya,

    Ka da ki bi mai tambaya,

    Ka da kuma ki bi mai ba da bayani,

    Kuma ka da ki cuci kowa,

    Mu nan duk iyalinki ne Inna,

          Sai amana a tsakanin mu,

                Allah Shi ba ki haƙuri”.

    Alamomin da suke nuna cewa mutum ya kamu da ciwon Shan Inna a gargajiyance sun haɗa da, yaron da ciwon ya kama zai fara da yin zazzaɓi wanda za a yi magani ya ƙi sauka. Daga nan sai a ga alamar wani ɓangare na jikinsa kamar hannu ko ƙafa ya bar yin amfani. Daga baya sai a ga wannan hannu ko kafa ko sashen jikin ya shanye. Ganin waɗannan alamomi, sai a yanke hukuncin cewa aljana Inna ce ta yi masa wannan aiki, sai neman magani.

    Daga ana sai a kai wannan marar lafiya wurin boka ko ‘yan bori domin neman magani. A lokacin da aka je wurin boka, sai ya hau bori don yin magana da aljana Inna. Bokan zai tambayi aljana Inna ko ita ce ta kama wannan majiyaci? Idan ita ce, sai Bokan ya roƙe ta don ta yi haƙuri, ta saki wannnan majiyaci don ya samu lafiya. Idan ta yi haƙuri, sai ta sanar da bokan ire-iren abubuwan da za a deɓo don yin magani. Ana kuma zuwa wurin wanzamai don neman maganin Shan Inna.         

     

    2. 3 Magungunan Gargajiya na Ciwon Shan Inna

    Akwai magungunan ciwon Shan Inna waɗanda Hausawa suke amfani da su kafin zuwan na Turawa. Ire-iren waɗannan magunguna akwai waɗanda ake dafawa da ruwa a sha, akwai kuma wanda ake yin hayaƙi da kuma wanda ake shafawa a wurin da ciwon ya kama.

    Maganin da ake amfani da shi don sha shi ne, sai a sami sassaƙen iccen gauɗe da sauyoyinsa a haɗa su, sai a sanya su cikin tukunya da ruwa a dafa. Idan ruwan ya huce sai marar lafiyar ya riƙa sha. Zai yi ta sha har sai ya warke.

    Wanda kuma ake amfani da shi don yin hayaƙi shi ne, sai a samu hakin da ake kira karfatoci da kashin tunku da na baƙin jaki da ƙaron itacen faru da kitsen baƙar akuya, sai a haɗa su a dake. Daga nan sai a samu ɗan kasko wanda za a riƙa zuba garwasin wuta a cikinsa, ana ɗan ɗibar wannan maganin ana zubawa a ciki. Daga nan sai a ɗauko wannan kasko a ajiye shi gaban wannan marar lafiya a lulluɓe shi da mayafi tare da kaskon maganin yadda hayaƙin zai game jikinsa. Za a yi ta yi masa hayaƙi a kullum har zuwa tsawon kwanaki bakwai.

    Shi kuma maganin da ake amfani da shi don shafa wa shi ne, sai a sassaƙen itacen sansani da sauyoyin geza a haɗa su a daka. Garinsu ne za a riƙa kwaɓawa da ruwa ana shafawa wuraren da ciwon ya kama har zuwa tsawon kwana bakwai.

    An bayyana cewa idan an yi ire- iren waɗannan magunguna za a warke daga cutar, amma wurin da ciwon ya kama ba zai koma kamar yadda yake a da ba. Gaɓuɓɓan da cutar ta kama za su shanye su zama naka sassu.

     

     

    2. 4 Ciwon Shan Inna a Wannan Zamani

    A sakamakon shigowar Turawa ƙasar Hausa an gano cewa ciwon Shan Inna ba Aljana Inna ce ke kawo shi ba. Wannan ciwo na kama mutane ne a sakamakon shigar wasu ƙwayoyin cuta cikin jikin mutum. Ana kiransu da suna ƙwayoyin cutar Shan Inna “poliomylitis ɓirus”. Idan ƙwayoyin cutar suka shiga jikin mutum, matuƙar ba a yi gaggawar yi masa magani ba, za su nakasa wani sashe na jikinsa.

    Wannan cuta na yaɗuwa cikin mutane ta hanyoyi da dama waɗanda suka haɗa da:-

    Tana shiga cikin jikin mutum ta baki a lokacin da mutane suka ci abinci ko shan ruwa wanda ya gurɓace da bayan-gida (kashi).

    Haka kuma wannan cuta na saurin yaɗuwa a wuraren da ba su da tsafta.

    Ta fi saurin shiga cikin jikin jarirai da yara ƙanana saboda rashin cikakkiyar garkuwar jiki. Abin nufi a nan shi ne, jarirai da yara ƙanana ba su da cikkakkar kariyar jiki wadda za ta iya yaƙar ƙwayoyin cutar Shan Inna. Ƙwayoyin cutar Shan Inna na shiga hanyar jini, daga nan, sai su kai farmaki ga jijiyoyi da ƙwaƙwalwa, wanɗanda suke yi wa aibi ko su lalata su.

    An bayyana cewa a mafi yawancin lokaci idan yaro ɗaya ya kamu da wannan cuta a cikin unguwa, yana iya harbin sauran yaran da ke a wannan unguwar.

    Yaran da suka kamu da wannan cuta na iya yaɗa ta da sauri daga kwana bakwai zuwa goma kafin alamomin cutar su fara bayyana a jikinsu. Haka kuma suna iya yaɗa ta ga ‘yan uwansu daga kwana bakwai zuwa kwana goma bayan alamomin cutar sun fara bayyana a jikinsu.

    Waɗanda suka kamu da wannan cuta, amma saboda wasu dalilai, sai alamominta ba su fara bayyana ba na iya yaɗa ta.

    Wasu mutane a lokacin da suka kamu da ƙwayoyin cutar Shan Inna, ba su faye kamuwa da waɗansu cututtuka ba.

    Cutar Shan Inna ta kasu zuwa iri uku kamar haka:-

     

    i) Mataki na Ɗaya

    Wannan mataki na Shan Inna ya fi shafar yara ƙanana. Wannan kuwa ya faru ne a saboda ba su da wadatacciyar kariyar jiki, kuma ana haihuwar wasu yaran da shi. Wannan mataki ya rabu zuwa iri uku kamar haka:-

    Nau’i na Ɗaya – Irin wannan ciwo idan ya shiga cikin jikin yaro, yana sa masa matsananciyar rashin lafiya wadda za ta iya nakasa wasu daga cikin gaɓoɓin jikinsa ko kuma dukkan jikinsa.

    Nau’i na Biyu – Shi kuma irin wannan ciwon Shan Inna bai faye nakasa yaron da ya kama ba, amma yana sakar masa yawan zazzaɓi.

    Nau’i na Uku – Irin wannan ciwon Shan Inna yakan sakar wa yaro da ciwon sanƙarau, kuma yakan shafi ƙwaƙwalwar yaron. A wani lokaci yakan iya kaiwa ga nakasa wani sashe na jiki ya shanye kamar hannu ko ƙafa.

    Abin la’akari a nan shi ne, idan aka nazarci waɗannan ire-iren ciwon Shan Inna, za a ga cewar Nau’i na Farko ya fi dukkan sauran haɗari, domin idan ƙwayoyin cutar suka shiga cikin jikin yaron, cikin ɗan ƙanƙanen lokaci, sai a tarar hannun yaro ko ƙafarsa sun shanye ba tare da an lura ba. Amma Nau’i na Biyu da na Uku ba su faye shanye hannu ko ƙafar yaro ba.  

     

    ii) Mataki na Biyu

    Irin wannan ciwon Shan Inna an fi samunsa wurin manyan mutane, amma a wasu lokuta yakan kama yara ƙanana. Wannan kuwa ya faru ne a saboda cutar da ke haddasa shi ba iri ɗaya ce da ta ciwon Shan Inna Mataki na Farko ba. Akwai cututtuka iri daban-dabam waɗanda ke haifar da irin wannan ciwo na Shan Inna. Ire-irensu sun haɗa da ciwon hawan – jini da yin allura a wurin da bai dace ba, misali a tsira allura a bisa jijiyar da ke sarrafa motsin jikin mutum, ko kuwa a yi rauni a cikin lakka wadda ke kai wa ƙwaƙwalwa bayanai da sauransu. Idan aka samu ɗaya daga cikin waɗannan cututtuka wani ɓangare ko dukkan sassan jiki na iya nakasa ya shanye.

     

    iii) Mataki na Uku

    Wannan mataki shi ma ya yi kamanni da wanda ya gabace shi, domin kuwa shi ma ba ƙwayoyin cutar Shan Inna ke haifar da shi ba. Yana kama mutum a sakamakon shigar wasu ƙwayoyin cuta a cikin jiki. Ire-irensu sun haɗa da cutar ƙari a cikin ƙwaƙwalwa da ciwon tarin-fuka wanda ya shafi lakka da kuma ciwon ƙari wanda ya kama ƙoda da sauransu. Ire-iren waɗannan cututtuka idan suka kama mutum, wani sashe na jikinsa na iya nakasa ya shanye.

    A binciken da aka gudanar an gano cewar, a sakamakon kama mutum da waɗannan cuta waɗanda aka yi bayani a kansu a Mataki na Biyu da Mataki na Uku, suna iya haifar da nakasa ɗaya daga cikin waɗannan, shanyewar rabin jiki ko ƙasan jiki ya mutu ko kuma dukkan jiki ya mutu.  

    2. 5 Riga-Kafin Ciwon Shan Inna a Wannan Zamani

    A wannan zamani ana amfani da hanyoyi uku domin yin riga- kafin ciwon Shan Inna. Waɗannan hanyoyin su ne: Matakin kariya na ɗaya da na biyu da na uku:

    Matakin Kariya na Ɗaya – A wannan mataki ana yi wa jama’a cikakken bayani dangane da ciwon Shan Inna. Ana faɗakar da su ire-iren illoli da hanyoyin da ciwon ke yaɗuwa a cikin al’umma. Haka kuma ana bayyana cewa wannan ciwo ba aljana Inna ce ke haifar da shi ba, ƙwayar cuta ce ke haifar da shi. Ita wannan ƙwayar cuta an fi samunta a cikin najasa kamar bayan gida. A saboda haka ne ake yi wa iyaye gargaɗin su daina barin ya’yansu taɓa bayan gida. Idan sun taɓa a wanke masu hannuwa kafin da bayan sun ci abinci. Idan ana barin yaran da suka taɓa bayan gida cin abinci ba a wanke masu hannuwa ba, akwai yiwuwar su kamu da ciwon Shan Inna.

    Matakin Kariya na Biyu – Hanya ta biyu wadda ake bi a wannan mataki domin yin riga-kafin kamuwa da ciwon Shan Inna, ita ce ta yin allurar riga-kafin wannan cuta. Ana ɗiga wa yara sinadarin maganin riga- kafin ciwon Shan Inna wanda ake kira da suna (OPƁ) a cikin baki ɗigo biyu a lokaci ɗaya. Ana fara ɗiga wannan magani a lokacin da aka haifi yaro. A kuma maimaitawa bayan mako shida da ɗiga na farko. Daga nan kuma za a sake ɗigawa bayan mako huɗu, a kuma ƙara bayan wasu mako huɗu. Ana buƙatar lokacin da yaro zai kai mako goma sha huɗu da haihuwa a ɗiga masa sinadarin maganin riga- kafin ciwon Shan Inna sau huɗu, lokaci bayan lokacin kamar yadda aka yi bayani a sama.

    Bayan wannan kuma a lokaci zuwa lokaci ana bi gida-gida don ɗiga wa jarirrai da yara ƙanana waɗanda ba su wuce shekara biyar da haihuwa ba wannan sinadari na riga-kafin ciwon Shan Inna.

    A nan Nijeriya akwai hukumomi na gwamnati da waɗanda ba na Gwamnati ba da ke ɗaukar ɗawainiyar rarrabawa da ɗiga sinadarin riga-kafi ciwon Shan Inna. Waɗannan hukumomi sun haɗa da:

    ·         Hukumar kula da riga-kafin cututtukan da ke kashe yara ƙanana ta Gwamnatin Tarayya Nijeriya (NPI/ FGN).

    ·         Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

    ·         Hukumar Ci-gaban Ƙasashe ta Amurka (USAID).

    ·         Hukumar Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF).

    ·         Ƙungiyar Rotary ta Ƙasa da Ƙasa.

    Matakin Kariya na Biyu – A wannan mataki ne ake ƙoƙarin binciko wanda wannan ciwon ya kama a farkon kwanaki uku zuwa goma sha huɗu da kamuwa. Daga nan sai a ɗauki bayan-gidansa a kai ɗakin awo don a bincika a gano a cikinsa akwai ire-iren ƙwayoyin cuta waɗanda ke haifar da cutar Shan Inna? Idan aka tabbatar da cewa ya kamu da ciwon Shan Inna, sai a ɗora shi akan hanyar da zai samu magani. Idan da can an yi allurar riga-kafi a unguwar da wannan wanda ya kamu da cutar ya fito, alama ce wadda ke nuna cewa, har wannan lokaci akwai ƙwayoyin cutar Shan Inna a wannan Unguwa. Wannan dalili ne zai tilasta a sake yin allurar riga-kafi a wannan unguwa da kewayenta. An bayyana cewa abin da ke kawo haka shi ne, wani baƙo mai ɗauke da wannan cuta ya shigo unguwar. Hukumar Lafiya ta Najeriya tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin da ke yaƙi da ciwon Shan Inna a Nijeriya, sun ware kuɗi masu yawa don bayarwa ga duk wani jami’in kiwon lafiya wanda ya kawo labarin yaron da ke ɗauke da ƙwayoyin cutar Shan Inna, wanda kuma bai wuce kwana goma shan huɗu da kamuwa ba. Ana yin haka ne domin a yi wa yaron magani yadda ba zai nakasa ba, amma idan ya wuce wannan lokaci yana iya nakasa wani ɓangaren na jikinsa ya shanye.

    Matakin Kariya na Uku – Ana amfani da wannan matakin kariya ne  lokacin da cutar Shan Inna ta rigaya ta kama mutum, har ta kai ga matakin nakasa wani sashen jikinsa ya shanye. Dukkan sashen da ya nakasa ba wani magani da za a yi amfani da shi ya mayar da shi yadda yake kafin kamuwa da ciwon. Abin da ake yi kawai shi ne, sai a yi ƙoƙarin kula da shi ta hanyar ba shi wadataccen abinci da sutura da muhalli mai kyau. A kuma riƙa cuɗanya da shi ba tare da nuna masa ƙyama ba. Yana da kyau kuma a riƙa koya masa yin amfani da sashen jikinsa. Wannan ne zai sa ɓangaren da ya nakasa samun ƙarfi ba kamar idan an sanya masa ido ba. Yana da matuƙar muhimmanci a yi ƙoƙarin koya masa wata sana’a wadda zai riƙa yin wasu abubuwa waɗanda za a sayar a kawo masa kuɗin da za su taimaka masa ya riƙa dogaro da kansa, ba a bar shi ya riƙa yin bara ko ya dogara ga wani wanda a yau da kullum yana iya gajiya daga ƙarshe ya bar shi ya tagayyara.

     

    2. 6 Ra’o’in Mutane Dangane da Riga-Kafin Ciwon Shan Inna

    A saboda yadda hukumomi na Gwamnati da ma waɗanda ba na Gwamnati ba suke ba yin allrar ruga-kafi ciwon Shan Inna muhimmanci da kuma yadda ake yawan yin wannan allura, ya kawo shakku a cikin zukatan mutane. Wannan dalili ne ya sa aka fara tunani kan amfani ko rashinsa ko aibi dangane da yin wannan allura.

    A lokacin da aka fara wannan tunani an ɗauka cewar akwai wata manufa ta ɓoye da ta sa aka ba allurar riga-kafin ciwon Shan Inna muhimmanci da bai dace a ba ta ba. Masu irin wannan ra’ayi sun kafa hujjarsu da cewa, akwai cututtuka masu kisan yara waɗanda ya kamata a ba muhimmanci fiye da irin wanda aka ba cutar Shan Inna wadda ita nakasa yaro kawai take yi. Waɗannan cututtuka masu kisa sun haɗa da ciwon ƙyanda da amai da gudawa da zazzaɓin cizon sauro. An bayyana cewa daga cikin mutane Miliyan Ɗari Biyar waɗanda waɗannan cututtuka ke kashewa, Miliyan Ɗari Huɗu da Hamsin, kimanin kashi casa’in bisa ɗari (90%) sun fito daga ƙasashen Africa. Daga cikinsa kuma kashi Arba’in bisa Ɗari (40%) sun fito daga Nijeriya (Kaita, Ba Shekarar Bugu:1).

    Wannan al’amari ya jawo hankalin matasa da masu sharhi kan al’amuran rayuwar yau da kullum da ƙungiyoyin addinai don gudanar da bincike a gano gaskiyar wannan al’amari. Misali, Gidan Radiyon Tarayyar Nijerya na Kaduna (FRCN Kaduna) ya gabatar da sharhin bayan labarai, wanda a cikinsa an bayyana cewa, babban gidan Talabijin mai watsa labarai a duk duniya na ƙasar Amurka (CNN), a wani shiri mai taken lafiyarku “Your Health, ” masana ilimin kiwon lafiya, a cikin tattaunawar da suke yi a wannan sharhi, sun gargaɗi mutane dangane da aibin da ke tattare da alluran riga-kafin ciwon Shan Inna. Waɗannan masana sun bayyana cewa, ruwan maganin riga-kafin ciwon Shan Inna (OPƁ) wanda ake ɗiga wa biliyoyin yara a wannan zamani, zai iya haifar da wata cuta bayan shekaru da yawa da ɗiga masu sinadarin. Sun kira wannan cutar da sunan Bi-Bayan Maganin Riga-kafin Shan Inna (Post-Polio Syndrome PPS). Sun ƙara bayyana cewa, a lokacin da ire-iren yaran da aka ɗiga wa wannan riga-kafi suka kai shekara ashirin da ɗiga masu wannan sinadari, za a tarar sun kamu da wasu irin munanan cututtuka waɗanda suka haɗa da fitowar ƙari a ƙwalwa, kuma za su kamu da wasu cututtuka waɗanda ba ire-iren su a wannan zamani, don haka za su yi wuyar magani (Bello, 2001: 3).

    Duk da ire-iren waɗannan ƙorafe-ƙorafe da koke-koke da ake yi dangane da illoli da shakkun da ake nunawa akan maganin riga-kafin ciwon Shan Inna, hukumomin da suke bayar da shi, watau Gwamnatin Tarayya da Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗunkin Duniya da Ƙungiyar Rotary ta Ƙasa da Ƙasa da Hukumar Ci-gaban Ƙasashe ta Amurka da Hukumar Yara ta Majalisar Dunkin Duniya, sun ci gaba da bayyana cewa, wannan magani na riga-kafin ciwon Shan Inna, ba shi da wata matsala ko illa, kuma yana maganin riga-kafin kamuwa da ciwon Shan Inna (Kaita, Ba Shekarar Bugu: 3).

    Waɗannan hujjoji da waɗannan hukumomi suke bayarwa, ba su gamsar da mutane ba. Wannan dalili ne ya tilasta wa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya kafa kwamitin ƙwararru don binciko sahihancin maganin riga-kafin ciwon Shan Inna. Wannan kwamiti ya ƙunshi ƙwararrun masana kan kimiyyar haɗa magunguna da kuma sarakunan gargajiya. Waɗannan ‘yan kwamiti sun ziyarci shahararrun ɗakunan bincike da haɗa magunguna a ƙasashen Afriƙa ta Kudu da Indonesiya da Indiya a cikin watan Fabrairu na 2004. Sakamakon binciken wannan kwamiti bai zama karɓaɓɓe ba wurin al’ummar Nijeriya. Dalili kuwa shi ne, ana zargin sun sanya sakamakon yadda zai wanke waɗanda suka tura su, don a yarda da cewa maganin riga-kafin ciwon Shan Inna ba shi da wata illa, kuma yana da amfani wajen riga-kafin kamuwa da ciwon Shan Inna (Kaita, 2004:1-2).

    Wannan sakamako na Kwamitin Gwanatin Tarayya, ya haifar da tsegunguma da ka-ce-na-ce. Wannan dalili ne ya sa Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta kafa wani kwamiti, don ya binciko mata, ya kuma kawo mata ingantaccen bayani a kan sahihancin maganin riga-kafi ciwon Shan Inna inna. ‘Ya’yan wannan kwamiti sun ɗauki ɗaya daga cikinsu mai suna Farfesa Haruna Abdu Kaita, wanda a yanzu shahararren Farfesa ne a kan Kimiyyar haɗa magunguna, kuma a wancan lokaci, shi ne Shugaban Tsangayar Kimiyyar Haɗa Magunguna a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. An ɗora wa wannan masani nauyin ya tafi ƙasar Indiya don ya gudanar da bincike kan wannan magani. Kafin ya tafi ya tattara samfur na ire-iren kwalebanin ruwan maganin riga-kafin ciwon Shan Inna daga jihohin Kaduna da Sakkwato da Zamfara. Ya saka su a cikin kuloli waɗanda ke ɗauke da wadatacciyar ƙanƙara wadda za ta sanyaya su yadda ba za su lalace ba har zuwa wuri da lokacin da zai ɗauka na aiwatar da bincikensa. Ya samo waɗannan samfur ne a Ofishin Riga-kafin cututtuka na ƙasa a waɗannan jahohi, kuma waɗannan magunguna an yi su a ƙasashen Faransa da Indiya da Belguim (Kaita, Ba Shekarar Bugu:1-2).

    A Indiya ya yi kwanaki ashirin da uku. Mafi yawancin waɗannan kwanaki ya yi su ne, a mashahurar ɗakunan kimiyyar bincike da haɗa magunguna waɗanda masana ilimin kimiyyar bincike da haɗa magunguna na duniya suke aminta da su. Bayan ya kammala bincikensa, ya fito da sakamako kamar haka:

    Ya gano cewa daga cikin sinadaran da aka yi amfani da su cikin ruwan maganin riga-kafin ciwon Shan Inna, akwai abubuwa waɗanda ke da aibi ga mutane kuma suna iya hana haihuwa.

    Haka kuma ruwan maganin gurɓatacce ne, don kuwa yana ɗauke da abubuwa waɗanda suke da mummunan lahani ga rayuwar mutane (Kaita, 2004: 1- 2 of 5, Kaita, Ba Shekarar Bugu, 3-10).

    Wannan sakamako ya ɗaure masa kai da sauran manyan masana ilimin kimiyyar haɗa magunguna ‘yan ƙasar Indiya waɗanda ya gudanar da wannan gwaji a kan idanunsu. A saboda haka sun yi matuƙar mamakin samun wannan sakamako wanda ke nuna cewa, maganin riga-kafin ciwon Shan Inna na ɗauke da waɗannan mugayen abubuwa waɗanda bai dace a same su a cikinsa ba. Wannan dalili ne ya tilasta ma shi maimaita wannan gwaji. Amma da ya kammala sakamakon bai canza ba. Ya sake yi, ya ƙara maimaitawa, ya kuma maimaitawa sau da dama, amma duk lokacin da ya kamala, sai sakamakon ya bayyana masa cewa, wannan magani na ɗauke da waɗannan abubuwa waɗanda ya gano tun farko. Daga ƙarshe ya yanke hukuncin cewa, wannan sakamako dai haka yake, ya kuma amince da cewa wannan magani gurɓatacce ne, kuma ba shi da kyau (Kaita, 2004:1-2).

    Farfesa Kaita ya gabatar da rahoton bincikensa a gaban kwamitin ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam wanda ya ƙunshi masana da manazarta kimiyyar haɗa magunguna. Bayan su kuma akwai wakilai daga Hukumar Riga-Kafin Cututtuka ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Hukumar Lafiya ta Duniya da Hukumar Ci- gaban Ƙasashe ta Amurka da Ƙungiyar Rotary ta Ƙasa da Ƙasa da Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Dunkin Duniya. A lokacin da ya gabatar da wannan rahoto, an yi masa tambayoyi masu tarin yawa waɗanda suka shafi wannan rahoto. Ya kuma ba su gamsassun amshoshi waɗanda suka kare wannan rahoto da abubuwan da aka gano. Daga ƙarshe waɗannan hukumomi suka yarda da cewa, wannan ruwan magani da aka riƙa ɗiga wa yaro tun daga shekara ta 2000 zuwa ta 2004 gurɓatacce ne, wanda suka ce a wannan shekara ta 2004 zai ƙare. Waɗannan Hukumomi sun bayyana cewa, suna gayyatar dukkan wani masani ko manazarci ko wata ƙungiya da ke da sha’awar gwada wannan sabon magani, don ya zo a ba shi samfur don yin gwaji (Kaita, 2004: 2-4 of 5).

    Idan aka yi la’akari da sakamakon binciken da Farfesa Haruna Kaita ya bayar, da kuma irin halin ko-in-kula da Hukuma mai kula da riga-kafin cututtuka ta Gwamnatin Tarayya (NPI/FGN) da Hukumar mai kula da ingancin abinci da magunguna ta Tarayyar Nijeriya (NAFDAC) suka nuna a lokacin da ake ta yin wannan ka-ce-na-ce, kuma ba su ɗauki wani mataki ba, sai mutum ya yanke hukuncin cewa akwai wata manufa ta ɓoye. Wasu na danganta wannan da cewar, waɗannan hukumomi da ita kanta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya wakilai ne na Amurka da Turawa waɗanda ke yaƙi da yawan haihuwa a ƙarshen Afrika da Asiya da Latin Amurka. A irin tunaninsu, wai yawan haihuwa a waɗannan Nahiyoyi da kuma ƙasancewarsu matalautan ƙasashe, zai ƙara yawan kwararrar baƙin haure zuwa ƙarshen Turai da Amurka. Domin su yi maganin haka ya sanya suka ƙirƙiro yin allurar riga-kafin Shan Inna wadda aka gurɓata da sinadarin da zai hana haihuwa. A tunaninsu ta wannan hanya ce za su rage yawan haihuwa a waɗannan ƙasashe.

    Wasu kuwa na danganta goyon bayan da jami’an kiwon lafiya waɗanda ke ba da wannan riga-kafi ke bayar wa, ya samo asali ne, a sakamakon maƙudan kuɗin da waɗannan hukumomi na Turawa da Amurka suke bayarwa a duk lokacin da za a yi alluran riga-kafin ciwon Shan Inna. A duk lokacin da za a yi allurar riga-kafin ciwon Shan Inna, waɗannan hukumomi na turo kuɗi masu tarin yawa, waɗanda daga ƙarshe jami’an da ke gudanar da wannan aiki, tun daga Gwamnatin Tarayya da Jihohi da Ƙananan Hukumomi da sarakunan gargajiya a wani lokaci ma har da shugabannin addinai suke rarraba waɗannan kuɗi a tsakaninsu. Idan aka yarda da cewa waɗannan magunguna gurbatattu ne ba su da amfani, kuma suna cutar da yara a saboda haka a daina yin su, zai sanya waɗannan Hukumomi na Turawa da Amurka su dakatar da ba da kuɗin da suke bayarwa. Yin haka zai sanya waɗannan manyan mutane na wannan ƙasa su bar samun waɗannan kuɗi. A saboda haka ne suke ta yin bakin ƙoƙarinsu ta hanyoyi iri daban-dabam don jawo hankalin talakawa su ba da goyon baya a riƙa yi wa ’ya’yansu allurar riga-kafin ciwon Shan Inna. Daga  cikin ire-iren matakan da aka riƙa ɗauke don tilasta wa iyayen yara yarda a ɗiga wa ’ya’yansu maganin riga-kafin ciwon Shan Inna, ana ɗaurewa da muzantawa da cin mutuncin iyayen da suka hana a ɗiga wa ya’yansu wannan magani. Haka kuma suna amfani da dabarun jawo hankalin yara ta hanyar ba su kyaututtukan abubuwa irin su alawa da biskit da makamantansu da kuma magunguna irin su panadol da ɓitamin c na ruwa don su zo a ɗiga masu wannan sinadari.

    Duk da cewa hukumomin da suke gudanar da yin allurar riga-kafin ciwon Shan Inna, sun bayyana cewa sindarin da ake amfani da shi a yanzu an tabbatar da cewa ba shi da wani aibi kuma lafiyayye ne, kuma yana yin riga-kafin kamuwa da ciwon Shan Inna, har yanzu akwai mutane masu yawa waɗanda ba su aminta da shi ba, kuma ba a yi wa ‘ya’yansu riga-kafin da ake yi wa yara.

     

    3. 0 Kammalawa

    Ta yin la’akari da yadda wasu cututtuka suke yin barazana ga lafiyar al’ummomin wannan duniya musamman jarirai da yara ƙanana a wannan zamani, ya zama dole a sami ingantattun magungunan riga-kafi domin yin kariya ga jiki yadda ba zai fuskanci barazanar kamuwa da su ba. Wannan dalili ne ya sa hukumomi na gwamnati da ma waɗanda ba na gwamnati ba suka duƙufa wajen gudanar da bincike don samo ingantattun magungunan riga-kafin wasu cututtuka waɗanda suke nakasa ko kashe jarirai da yara ƙanana a wasu lokuta ma har da manya. Kamar yadda aka gani, wannan takarda an yi bayani ne a kan cutar Shan Inna dangane da yadda al’ummar Hausawa suke ɗauke ta da yadda suke yin maganinta, daga nan kuma aka kawo matsayin wannan cuta a wannan zamani da yadda ake yin riga-kafin kamuwa da ita da kuma irin ka-ce-na-ce da ake ta faman yi a kan wannan riga-kafi da kuma irin yadda Hausawa suka yarda ko ƙin yarda a yi wa ‘ya’yansu wannan riga-kafi a yau.

    A haƙiƙa yin riga-kafi don kare jiki daga kamuwa da wasu cututtuka al’amari ne mai matuƙar alfanu ga al’ummar wannan zamani a ko’ina suke cikin wannan duniya, amma abin da yake ɗaure wa wasu mutane kai ya kuma sanya su cikin tunanin da ya tilasta su ɗaukar matakin ƙin yarda a yi wa ‘ya’yansu wani nau’i na alluran riga-kafi shi ne, irin yadda waɗanda suka ɗauki nauyin yin alluran riga-kafi suka bayar da muhimmanci fiye da kima kan yin alluran riga-kafin ciwon Shan Inna maimakon a mayar da hankali kan cututtukan da suka fi shi barazana ga lafiyar jarirai da yara ƙanana. Misali, ciwon Shan Inna nakasa yara kawai yake yi, amma cututtuka irin su ƙyanda da zazzaɓin cizon sauro da sauransu suna kashe jarirai da yara ƙanana har ma da manya a wasu lokuta. A nan ire-iren waɗannan cututtuka ne kamata a ba su cikakkar kulawa ta musamman don a ceto rayuwar al’umma. Yin haka ne zai sa al’umma ta san cewa abubuwan da ake yi, ana yin su ne domin ci-gabansu ba da wata ɓoyayyar manufa ba, kuma zuciyarsu ta amince taimaka masu ake yi ba tare da sun kawo wata shakka ba.

    Bisa la’akari da bayanan da suka gabata da kuma muhimmancin alluran riga-kafi a wannan zamani, ya zama dole ga gwamnatocinmu a duk lokacin da aka shigo da wasu sababbin allurai ko magunguna, a riƙa sanya masana ilimin kimiyyar haɗa magunguna ‘yan ƙasa gudanar da bincike mai zurfi domin gano alfanu ko rashinsa da aibin da yake tattare da waɗannan magunguna. Yin haka da kyakkyawar niyya, zai taimaka matuƙa ainun waje rage ire-iren kurakuran da aka aikata a Kano inda kamfanin ‘pfizer’ ya yi gwajin maganin ciwon sanƙarau mai suna ‘troɓan’ wanda ya yi dalilin mutuwa da nakasa yara masu yawa.

     Manazarta

    Bello, A. I. M. (2001) “The Meaning of Globalisation”, Part I and II, In Focus. Kaduna: Current Affairs Unit, Federal Radio Corporation of Nigeria.

     

    Besmer, F. E. (1073) “Praise Epithets and Song Teɗt for Some Bori Spirits in Kano”. Journal Article. Kano: Harsunan Nijeriya, Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University.

     

    Bunza, A. M. (1988) “Hayaƙi fid da na Kogo”, Maƙala. Kano: Bikin Makon Hausa na 18, Ƙungiyar Hausa, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

     

    Bunza, A. M. (1990) “Hayaƙi Fid da na Kogo: Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Bunza, A. M. (2000) “Gurbin Laya a Magungunan Bahaushe”, cikin Ɗegel Journal.

    Ibrahim, M. S. (1982)”Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Jinju, M. H (1982) “Hanyoyin Warkarwa a Ƙasar Hausa”. Zariya: Sashen Harsunan Nijeriya da na Afirika, Jami’ar Ahmadu Bello.

    Kaita, H. A (Year of Publication not Aɓailable) “Facts on Polio Ɓaccine”, Seminar. Zaria: Faculty of Phamaceutical Sciences, Ahmadu Bello University.

    Kaita, H. A. (2004) “Our Polio Test Was Conclusiɓe”, Interɓiew. Kaduna: Weekly Trust, Posted on the web on March 8, 2004.

    Kaita, H. A. (Year of Publication not Aɓailable) “Why Polio Ɓaccinations should be Suspended”, Seminar. Zaria. Faculty of Phamaceutical Sciences, Ahmadu Bello University.

    Kaita, H. A. (2004) “Polio Immunisation and Child Survival”, Seminar. Kuru-Jos: National Institute of Policy and Strategic Studies.

    Musa, I. L. (1986) “Rayuwar Amina Fanteka, Tarihinta da Shahararta a Fagen Magungunan Gargajiya”. Kundin Digiri na Farko. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    National Programme on Immunization (NPI), (2004). Basic Guide for Routine Immunization Service Providers, Federal Government of Nigeria. Abuja: USM Press.

    Sallau, B. A. S. (2000). ”Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

     

    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.