Jinin Al'ada Yana Min Wasa, Idan Ta Ɗauke Yau Gobe Ta Dawo

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, na kasance ina jinin al'ada kwana shida 6, to amma innayi kwana huɗu 4 sai ya ɗauke, Rana ta biyar zan wuni har dare bakomai, sai Rana ta shida zai dawo da asuba,

    To Mallam ranar da baizoba Zanyi wanka ne in cigaba da sallah ne ko zan dakata ?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    An tambayi Sheikh muhammad bin swalih al'uthaimeen-(rh) irin wannan tambaya, sai ya ce: Abinda ya fi bayyana shi ne wannan tsarki da take gani kokuma bushewan farji wanda yake zuwa mata acikin kwanakin hailanta, shima hailane ba tsarkiba. Saboda haka za ta cigaba da barin duk abinda mai haila za ta bari.

    Wasu daga cikin malamai suka ce: Wanda take ganin yau jini gobe babu jini. To jinin, jinin hailane. Rashin jinin kuma tsarkine. Matukar bai wuce kwana sha biyarba (15days). Wannan shi ne fahimtan mafi yawa daga cikin malaman mazhaban hanabila.

    Sai dai bisa ga wannan bayanai guda biyu zance tsaka-tsaki shi ne: Awayannan kwanaki idan jinin ya yanke sai taga alaman tsarkinta, (wato taga wannan farin ruwa) lokacin tsaya wan jinin, to wajibine ta yi wanka ta yi sallah. Idan jinjn ya dawo sai ta bar yin sallan. Idan kuma bataga alaman tsarkiba, to za ta zauna ciki wannan halin harsai taga alaman tsarki. Wannan shi ne abinda shekhul islam ibnu taimiyyah ya tafi akai. 

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.