Ticker

Kallon Bidiyoyin Batsa Ko Bidiyoyin Mata Tsirara Ko Hotunan Batsa (Hotunan Mata Tsirara)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, mene ne hukuncin mijin da yake buɗe wa matarsa ‘blue film’ don su kalla tare?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Musulmin gaskiya shi ne wanda ya miƙa wuya gaba-ɗaya, watau ya jawu ga bin dokokin Ubangijinsa (Tabaaraka Wa Ta’aala) cikin imani da tsoro da neman lada a koyaushe kuma a cikin komai na rayuwarsa, tun daga farkawarsa daga barcin safe har zuwa komawarsa barci da dare. Yana yin iyakan ƙoƙarinsa wurin kaucewa bin zugar shaiɗaninsa ko sha’awar ransa wurin aikata saɓo matuƙar iyawarsa. A kullum yana tsoron Ranar Tsayuwarsa a gaban Mahaliccinsa wanda zai tambaye shi a kan yadda ya yi da gaɓoɓin jikinsa da Allaah ya ba shi amanarsu, kamar ta irin waɗannan kalle-kallen da ya yi, ko ya nuna aka kalla. Allaah ya ce:

 إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولࣰا

Haƙiƙa ji da gani da zuciya kowanne daga waɗannan abin tambaya ne a kansa. (Surah Al-Israa’i: 36)

Sannan kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi tsawa a kan wannan mummunan aikin kamar inda ya ke cewa:

« لاَ يَنْظُرُ الرَّجُلُ إِلَى عَوْرَةِ الرَّجُلِ ، وَلاَ الْمَرْأَةُ إِلَى عَوْرَةِ الْمَرْأَةِ ، وَلاَ يُفْضِى الرَّجُلُ إِلَى الرَّجُلِ فِى ثَوْبٍ وَاحِدٍ ، وَلاَ تُفْضِى الْمَرْأَةُ إِلَى الْمَرْأَةِ فِى الثَّوْبِ الْوَاحِدِ ».

Kar wani namiji ya kalli al'aurar wani namiji, kuma kar wata mace ta kalli al'aurar wata mace. Kuma kar wani namiji ya lulluɓa da wani namiji a cikin maya fi guda, kar kuma wata mace ta lulluɓa da wata mace a cikin maya fi guda. (Sahih Muslim: 794).

Idan har ya hana wannan a tsakanin namiji da namiji ko a tsakanin mace da mace, ashe ya hana shi a tsakanin namiji da mace a wurin kallon tsiraici ko lulluɓar shi ya fi cancanta, don shi ya fi tsanani.

Kuma ko ba komai wannan kallon yana daga cikin hanyar kusantar zinar da Allaah ya hana a cikin maganarsa cewa:

وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا

Kuma kar ku kusanci zina, haƙiƙa ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israai: 32).

Domin kuma a cikin hadisin Muslim (6925), Annabin Rahama (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« الْعَيْنَانِ زِنَاهُمَا النَّظَرُ ، وَالأُذُنَانِ زِنَاهُمَا الاِسْتِمَاعُ ، وَاللِّسَانُ زِنَاهُ الْكَلاَمُ ، وَالْيَدُ زِنَاهَا الْبَطْشُ ، وَالرِّجْلُ زِنَاهَا الْخُطَا ، وَالْقَلْبُ يَهْوَى وَيَتَمَنَّى»

Idanu zinarsu ita ce: Kallo, kunnuwa kuma zinarsu ita ce: Saurare; harshe kuma zinarsa ita ce: Magana; hannu kuma zinarsa ita ce: Kamawa; shi kuwa ƙafa zinarsa ita ce: Tafiya; sannan kuma zuciya ita ke shaawar hakan kuma take nemansa.

Bayan duk waɗannan, akwai waɗansu munanan ta’adi da wannan kallon ke haifarwa ga masu yinsa, kamar haka:

(1) Zunubi ne, wanda yake ƙeƙasar da zuciya, ya nisanta bawa daga Allaah Ubangijinsa, ya afkar da shi a cikin fushinsa da azabarsa tun daga nan duniya kafin makoma lahira.

(2) Aikata wannan laifin yana nisantar da Mala’iku daga bawa, ya kusantar da shaiɗanu gare shi, masu ƙara zuga shi da tura shi ga dukkan hanyoyin hallaka.

(3) Kallon tsiraicin waɗanda ba su ba, yakan sanya ma’aurata su fara kushe wani abu na halittar tsiraicin da Allaah ya yi wa junansu, wanda kuma hakan ke iya kai wa ga ƙiyayya da ƙyamar juna.

(4) Bayan kallo fima-fiman babu abin da ke biyo baya sai ƙoƙarin kwatanta irin abin da aka gani. Don haka ba abin mamaki ba ne su fara ƙoƙarin saduwa ta dubura ko ma ta baki, kamar yadda suka gani!

(5) Rashin iya aiwatar da saduwa daidai da abin da suka gani a fim, wannan kan kai su ga da’awar rashin gamsuwa da juna, mai kai wa ga rashin jituwa da yawan faɗa, kuma mai kai wa ga rabuwa.

(6) Ƙoƙarin aikata yadda suka gani a cikin fim kan kai ga cutar da jikkunansu ko ma hallakarsu, domin sukan manta da cewa abin da suka kalla shirya shi kawai aka yi, ba haƙiƙa ba ne.

(7) Yaɗuwar waɗannan fima-fiman a yau na daga cikin dalilan yawaitar zinace-zinace da fyaɗe da sauran ayyukan assha a tsakanin jama’a manya da yara, maza da mata, har ma da dangi da ’yan uwa.

(8) Masu irin wannan aikin sukan zama abin koyi ga wasu ma’aurata irinsu, ko kuma ma ga yaransu, waɗanda kan fara koyon wannan ɓarnar tun suna ƙanana.

ƙarshe dai abin da yake wajibi a kan duk wanda ya faɗa a cikin irin wannan masifar ita ce:

(i) Ya yi saurin nadama da tuba ya daina wannan aikin, ya nemi gafarar Ubangiji Ta’aala tun kafin zuwan mutuwarsa.

(ii) Ya lalata duk wani abu na waɗannan fima-fiman da ke tare da shi, ya daina kallonsu, ya daina nuna wa wani daga cikin mutane, ko da kuwa matarsa ce.

(iii) Ya ƙara ƙoƙari wurin janyo hankalin duk wanda ya san shi ne ya koya masa kallon waɗannan fima-fiman, don shi ma ya tuba kamar yadda shi kansa ya tuba.

Allaah ya tsare mu daga dukkan zunubai na fili da ɓoye, ya gafarta mana gaba-ɗaya.

WALLAHU A'ALAM

Shiekh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments