Ticker

Kalmomin Jam’u (Gama-Gari)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

281. Kalmomi na tambaya mun ƙare su,

 Mun kuma bayyana su ga tsarin su,

 Yanzu na jam’u su muke son aikinsu,

Kalmomi na jam’u can ga bayaninsu,

  Sun haɗe kowane iri ba warewa.

 

282. Hausawa suna da dokokin kan su,

 Na rubutu da sun ka tsaro dukkan su,

 Kalmomin jam’u in ka gane su,

Tare ake haɗe su ba a ware su,

  Bi ni da sannu yanzu su zan kawowa.

 

283. Kalmar kowace da kowane, koyaushe,

 Ba a rubuta ‘kowa’ sa ‘ce’ can ƙarshe,

 Haka kowa a je da gefe ƙarshe,

 Ba a rubuta ‘ko’ daban ‘yaushe’ a ƙarshe,

  Kowanne mutan Kano ke furtawa.

 

284. Kowannensu, kowancensu da dukkansu,

 ‘kowannen su’ shi kure ne a raba su,

 Bai dace ba in ka sa ‘kowancen su’,

 Ba daidai ba ne rubutun dukkan su’,

  Tarsashinsu har jimillarsu haɗewa.

 

285. Kalmar kowaɗanne ma sa su a zance,

 Dukkanninsu duk rubuta su rubuce,

 Kar a raba su sai ka jera su rubuce,

 Kar a rabe su yin hakanga dabara ce,

  Bisa nahawunsu ba faragar togewa.

 

286. Kowane lokaci idan za ka rubutu,

 Sai a haɗe su, sai a tsara su, su saitu,

 Shi zai taimaka rubutun ya karantu,

 Dokokin da an ka tsara na rubutu,

  In aka zo gare su ba a warewa.

 

287. Dokokin da ke saman nan je kwashe,

 Kar ka yi dambala ka gane koyaushe,

Ruɗanin gaɓa ta farko ko ƙarshe,

 Shi ke sa rabe su ni nawa hasashe,

Kar ya shige ka can ga zancen furtawa.

 

288. Tabbata ka rubuta kominsu a tare,

 Ba a rabe su ko’ina sa su a jere,

 Kalmomi na jam’u sam ba su a ware,

 Doka ce ta yin rubutun mu a tsare,

Haka masananmu sun ka ce ba mu musawa.

 

289. Komai, na wurin akwai kowa, ƙara,

 Ba a rubuta ‘ko’ daban ‘mai’ ta wara,

 Haka ko wa tsakanta ba tazara lura,

 A haɗe kar a ware ko ɗai maza tara,

Tabbata ka haɗe su duk ba ka rabawa.

 

290. Ai komai da lokaci nai lamunce,

 Kowa na da nasa haƙƙi a rubuce,

 Kowane taliki da aikinsa rubuce,

Ga misali a nan ka ce kowace macce-

  Kowane lokaci miji taka renawa.

 

291. Kowannenmu na ta faman dagewa,

 Kowanmu ba shi son nuna gazawa,

 Kowa ya sani ƙwarai ba ya musawa-

Kowane taliki yana son hutawa,

  Komai ƙoƙarinsa zai kai ga gazawa.

 

292. Kowa ke da ilmu shi ke morewa,

 Kowannenku yai shirin fafatawa,

 Rarrabu ko’ina, ku lura da toshewa,

Kowannensu yai shuru ya ƙi muɗawa,

Kuma dukkansu sun ga ya kasa wucewa.

 

293. Masu faɗan ga sun gangara rafi,

 Rafin ga ruwa ciki nai ga zurfi,

 Shi mai kucce-kucce shi ne mai ƙarfi,

Lallai ko’ina ake aikata laifi,

  ‘Yan sanda da ke wurin na ganewa. 

Post a Comment

0 Comments