Ticker

Kalmomin Tambaya

 Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

272. Ba a tambaya ya zan babu bayani,

 Ko amsa ta yanzu sai in da sukuni,

 In an tambaye ka sai ka yi tunani,

 Kana ka karkata kana mai yi nuni,

  In aka yi ta duk bayani ka biyowa.

 

273.  Kalmomi na tambaya na nan shirye,

 Sai ku biyo mu sannu don ba ma tauye,

 In ka lura ba abin da yaz zama na ɓoye,

Matuƙar tambaya a kai sai ka kiyaye,

  Kalmomi na tambaya za su biyowa.

 

274. Kalmomin wane, wace, koko mene?

 Za su biyo cikin misalin kowanne,

 Wane ne yake ɓira[1] nan ga tukane?

 Wace ce take biɗa ta? Wai mene?

  Ko ka ce waɗanne jam’in tarawa.

 

275. Ka ga su su huɗun ga tsarin sigarsu,

 Sharuɗa ne na tambaya yo nazarin su,

 Harhaɗe za a gan su nan ga rubuta su,

 Ba a raba su ko alama! Tilas a haɗe su,

  In aka gan su tambaya za ta biyowa.

 

276. Ga rubuta su ba a ware su ka lura,

 Masana sun ka tsara komai na lura,

 Ba a raba su, sa dabara ka yi kara,

 Ba su zama kamar rubutun ‘yan yara,

  Tare ake saka su ba a warewa.

 

277. In suka zo da ne da ce kar a haɗe su,

 Nan kan dirka ce, a tilas a rabe su,

 ‘Ne’ ɗin nan da ‘ce’ sukan ci gashin kansu,

 A rubutunsu wajibi ne a raba su,

  Wace ce ake faɗa da rubutawa.

 

278. ‘Wane ne’ gami da ‘mene ne’ lura,

 In sun zo hakan ga ja ‘ne’ ɗan wara,

 Kar ka haɗe da ‘wane’, ‘mene’, ka lura,

 ‘Ne’, nan dirka ce da ‘yancinta ka lura,

  Ba a haɗe su ka ga yadda nake sawa.

 

279. In ka ce waɗanne ne an ka aje min?

Koko ka ce, su ‘wane’ na ka taɓa min?

Shin ‘wace’ ce ta take daɗa shirya min?

A waɗan ne wurin ga nan an saɓa min.

  Ka ga waɗanne sun haɗe ba a rabawa.

 

280. Kalmomi na tambaya had da misalai,

 Mun kawo su mun saka had da dalilai,

 In aka tambaye ka ƙara da misalai,

Daɗa na bar ka ƙarasawa da misalai,

Don ka fahimta kar ka zan mai ruɗewa.



[1] Wannan kalma ta ɓira tana nufin faɗuwa. Amma a nan za a ga hoton mutum yana faɗuwa cikin tukane (jam’in tukunya) yana tashi. Kuma wannan na nuna ba shi kaɗai yake faɗuwa ba har da tukanen.

Post a Comment

0 Comments