Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
474. Doka ce ta gwama kalma biyu tare,
Wani sa’in sukan
fi biyu ga su a jere,
In aka sa shi an
haɗe su suna cure,
Don haka za a zo
da shi tsakiya tsare,
Don su haɗe wuri guda ba a rabawa.
475. In aka sa shi babu sauran kirdado,
Ba sauran a zo a
yo muna gadodo,
Ma’ana ta fito,
karanta muna Lado,
Sharaɗi ya cike a harshenmu na gado,
Kalma ta zamo guda
ga hukuntawa.
476. Wani ɗan lokaci yakan shiga sunaye,
Sai a kula shi in
ya zo daɗa kai waye,
Ɗan layi yake zuwa
tsakiya jaye,
Doka ta aminta sa su a jeranye,
Su biyu ko fiye
da su za a haɗewa.
477. In aka zo faɗar sa domin nunkawa,
Sunayen gaba ɗaya ga rubutawa,
Za ka saka su, sai
alamar ɗorawa,
Ka ga gari-gari a gun mai furtawa,
Dubi gida-gida misalin ganewa.
478. In ga sifa ya zo idan aka nunka ta,
Ita ma za a sa shi
in za a rubuta,
Shi zai warware ma
kowa ya karanta,
Shi ke nuna za a nunka
ga faɗinta,
Za a yi ɗan karan tsakani na rabewa.
479. Ɗauki misali ga masu yin kiwon dabba,
In har za ka zaɓi dabba don riba,
Za ka rubuta dogo-dogon
nan babba,
Ko kuma mai baƙi-baƙin nan na duba,
Ya ɗara wake-wake ƙoshin turkewa.
580. Har a bayanau akwai ta nan ta wanzu,
Dubi misali da za
a bayar tun yanzu
Wanki sannu-sannu, amma sun darzu,
Zabura yanzu-yanzu
don ya fita ɗazu,
Sai ka yi sauri-sauri don ba a sakewa.
481. Ka ga fa ɗanya-ɗanya ce wannan gwanda,
Sa mana wada-wada gun kalmar wada,
Haka ma sanda-sanda
gun kalmar sanda,
In ka kula halin karan-ɗori sada,[1]
Dat tsaka zai shiga ga dokar nunkawa.
482. Wasar doki-doki
sai gun ‘yan yara,
Haka nan lambe-lambe su ne na lura,
Ko wargi na ɓoyo-ɓoyo in sun tara,
Wasar langa-langa ma ta zama sara,
Sai a yi goyo-goyo domin sheƙawa.
483. Duk kalmar da mun ka nunka ka kiyaye,
Mun mata ‘yar
alama haka gindaye,
Nan tsaka mun ka
zo da dokar kai waye,
Kowace kalma
gabanta ɗan layi jaye,
Za mu sako karan
da zai zo ɗorawa.
484. Ɗan layin da an ka zana tsakiyarsu,
Ai shi ne ya ɗora kalmar jimlarsu,
Sun ka zamo guda ga tsarin aikinsu,
Wato dai ya nuna
aikin nunkasu,
To shi ne kara ga
dokar ɗorawa.
485. Ƙiuyar sa shi kuskure ne munana,
Dole a sa shi in
ana neman ma’ana,
Ai ƙin sa shi ya zamo
yankan ƙauna,
Ga karatunsa nan
ake faman ɓarna,
Jimla za ta yamutse
ba ganewa.
486. Lura da su dukan misalan ka fahimtu,
Don kar ka ɓata hankalin masu karatu,
In aka sa shi sai ya zam ya daidaitu,
Kalma duk da an ka katse ga rubutu,
Kan a cika ta to
kara za a sakawa.
487. Matuƙar dai ka fara kalma ƙarshe ja,
Ɗan layi ka sauka
sannan ka cika ja,
Shi ka nuna isuwar
kalmar ba ja,
Ga misali ka ce fararen daj jaja-.
Ye sun hana babbaƙun budare lelawa.
[1] Kalmar “sada” tana nufin “koyaushe.”
Wannan kalma an fi amfani da ita a yankin Sakkwato da Kebbi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.