Kibiyar Ƙauna

Ƙosai da waina ba su yin juyi kamar-

So mai kamar Soso na wankin zuciya.


Kullum idanuna idan na cira sama,

Zan hangi tsuntsun so cikin farfajiya.


ko ba faɗi na san abun da kamar wuya ,

Farɗar furannin so cikin sarkakiya.


So ne kaɗai ke canja launin ɗan adam,

Gun yara har manya ya kanyi tsumagiya.


Ya saka maza mata su zauce tuntuni,

Zafinsa in ka ji sai ka ce bulaliya.


Nima cikin rami na faɗa ba kula,

Kaciɓus na hango ƴar fara falleliya.


Ko ban faɗa ba kana ganina ka sani,

Kallon abinso nai ƙurii da idaniya.


Na gaza wajen sauke maganai na a kan-

Fuskarta gun kallo na taka ƙarangiya.


Kai sai ka ce soɓo ta yo wasa da shi,

Da idon ta tarwai mai kama da samaniya.


Na kasa ɗauke kai bare na yi waiwaye,

Na tsuke baki na kamar shan tsamiya.


Na gazawa numfashin da zai gamsar da ni,

Kibiya ta so ta soki ƙoƙon zauciya.


Na kawar da kai don kar ta gane wai ashe,

Ta ankare harma tanai mani dariya.


Na ɗaga kaɗan na faɗi cikin ƙarfin hali,

"Sannunki ƴanmata" ta ɗan yo dariya.


Na matsa na ce sunanki ya kama da ke,

Maryama ne sunanta ba ta shariya.


Ta faɗa cikin sanyi "samari yakake,

Layin da ke bayanku zan ɗan zagaya".


Wayyo kamar na mace da jin sautin ta don-

Kibiya ta ƙauna ta taɓa mini zuciya.


Na ƙure ta har ta wuce da kallo bai ɗaya,

Tafiyarta ɗaf-ɗaf-ɗaf kamar ta wahainiya.


Har yau ina kewarta tare da addu'a,

Allah ya ban wannan farar tumfafiya.


Maisugar Ringim ✍️✍️

ringimmaisugar@gmail.com

09123098967

29/9/2023

Post a Comment

0 Comments