Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, Nijeriya – Oktober, 2023.
Kwatancin Ra'in Newman (2000)
Da Na Parsons (1960) Game Da Azuzuwan Aikatau Na Hausa
NA
SHITU
MUHAMMAD LAWAL
Email: ibnshitu1220@gamil
Phone: +2349065119946
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan
kundi nawa ga mahaifina Alhaji Shitu Balarabe Murai, wanda babban burinsa shi
ne, ya ga na yi karatu. Allah ya gafarta masa da rahma. Tare da mahaifiyata
Mal. Halima Lawal, wacce kullum take ɗawainiya da ni ba ta gajiyawa. Allah ya saka
mata da alkairi. Ameen.
SHAFIN AMINCEWA
Wannan Kundin da aka
gudanar mai suna,"Kwatancin Ra'in Newman (2000) Da Na Parsons (1960)
Game Da Azuzuwan Aikatau Na Hausa". Ya sama amincewa ne a matsayin
wani ɓangare na cika ƙa'idar samun
digirin farko a harshen Hausa (B.A Hausa). Sashen Harsuna da
Al'adu Afirka, Tsangayar fasaha, jami'ar Ahmad Bello, Zaria. A ƙarƙashin jagorancin
Prof. Salisu Garba Kargi.
GODIYA
Alhamdulillahi,
dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (S.W.T), wanda Ya ba ni ikon kammala
wannan aiki. Ina salati ga fiyayyen halitta shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W)
da ahalinsa wandanda suka bi shi baki ɗaya.
Da farko zan fara miƙa godiya ta ta musamman
ga mahaifina Alh. Shitu Balarabe Murai, Allah ya gafarta masa da rahama. Sannan
mahaifiyata Mal. Halima Lawal tare da abokiyar zamanta Khadijat Muhammad da
irin gudummuwar da suka ba ni a rayuwata
baki daya.
Ƙyaƙƙyawar godiya ta
musamman ga fafesa Salisu Garba Kargi, wanda shi ne ya duba wannan aiki nawa,
kuma ya yi bakin ƙoƙarinsa na ganin wannan aiki ya yi nasaran kammaluwa,
Allah ya saka masa da alhairi Amin.
Godiya ta musamman
ga malamaina dake wannan sashe mai
albarka, domin dukkansu sun bayar da
irin tasu gudummuwar ko ta kai-tsaye ko a kaikaice, wanda hakan ya taimaka wajen cin nasaran gamuwar
wannan aiki. Waɗannan malamai sun
koyar da ni ilimi da tarbiya da kuma rayuwa. Hakan ya sa ya zama wajibi na miƙa godiyata ga:
Farfesa Salisu Garba Kargi da Farfesa Magaji Tsaho Yakawada da Farfesa M.L Amin
da kuma Farfesa Balarabe Abdullahi. Haka kuma ba zan manta da Dr. B.S.Y
Alhassan da Dr. Shu’aibu Hassan da Dr. Abubakar Ayuba da Dr. Abdulmalik Aminu da Dr. Adamu Ibrahim
Malumfashi da Dr. R.M Tahir da Dr. Hauwa Muhammad Bugaje da Dr. Halima Kabir
Daura da Dr. Sarɓi da Dr. A.S
Abdulmumin da Dr. Adamu Ago Saleh da kuma Dr. Jibril Dambo.
Ban manta da ku ba,
Mal. Abubaka Muhammad Sarki da Mal. Usman Muhammad da Mal. A.S Fulani da Malama
Harira. Allahn ya saka muku da alheri.
Haka kuma ina miƙa godiya ta ga ɗaukacin jami’an ɗakin karatu, domin
sun ba ni gudummuwa mai tarin yawa, Allah ya saka da alheri, amin.
Daga ƙarshe ina godiya ga
‘yan uwa da abokan arziki kamar: Kabaru da Shafi’u da Aliyu da Umar Me gemu
(mutumina) da Ma’awiyya da Zarahaddin. Sannan ina godiya ga ‘yan uwa abokan
karatuna irin su: Ramalan Sani da
Junaidu B. Aliyu da Idris Nura da Aminu Lawal da Aliyu Ahmad da Sadiƙ Zakariyya Jibril da
kuma abokin faɗana Ibrahim (Ɗanmakaranta) da
sauran dukkan abokan karatuna wanda ba
zai yuwu na iya lissafo su ba. Ina fatan Allah ya bar zumunci.
ƘUMSHIYA
Shafin Farko -- i
Sadaukarwa -- ii
Shafin Amincewa -- iii
Godiya -- iv
Ƙumshiya -- ɓ
BABI NA ƊAYA
Shimfiɗa
1.0
Gabatarwa -- --
1
1.1 Dalilin
Bincike
-- 2
1.1
Manufar Bincike -- 3
1.3 Hasashen Bincike -- 3
1.4 Farfajiyar
Bincike
-- 4
1. 5
Muhimmancin Bincike -- 5
1.6 Hanyar
Gudanar da Bincike -- 6
1.7 Kammalawa -- 7
BABI NA BIYU
Waiwayen
Gabata Ayyukan da Suka
2.0 Gabatarwa -- 8
2.1 Ma'anar Aikatau -- 9
2.2 Ayyukan da Suka Gabata
Dangabe da Aikatau -- -11
2.3 Ra'ayoyin Wasu Masana A Kan
Aikatau -- 12
2.4 Sigogin Aikatau Na Hausa -- 19
2.5 Ra'in F.W Parsons (1960) -- 24
2.6 Ra'in Newman (2000) Game Da
Aikatau Na Hausa -- 33
2.7 Kammalawa -- 43
BABI NA UKU
Kamanci
3.0 Gabatarwa -- 44
3.1 Kwatancin Ra'in Parsons
(1960) da Newman (2000)
Game da
Azuzuwan
Aikatau Na Hausa -- 44
3.1.0 Karin
Sauti Da Wasalin Ƙarshen Kalma -- 45
3.1.1 Ginin
Jumla A Azuzuwan Aikatau Na Hausa -- -49
3.1.2 Ginin
Kalma A Aikatau Na Hausa -- -55
3.1.3 Ma'ana A
Azuzuwan Aikatau Na Hausa -- 56
3.2 Kammalawa -- 59
BABI NA HUƊU
Bambancin
4.0 Gabatarwa -- 60
4.1 Bambanci Ra'in Newman (2000)
Da Na Parsons (1960)
Game Da Azuzuwa Aikatau an Hausa -- 60
4.1.0 Adadin
Azuzuwan Aikatau Na Hausa -- -61
4.1.1 Aikatau
Fa nɗararru (Irregular Verbs) -- 65
4.2 Kammmalawa -- 67
BABI NA BIYAR
Kammalawa
5.0 Gabatarwa -- 68
5.1 Nadewa
-- 68
5.2 Kammalawa -- 70
5.3 Shawarwar -- 71
Manazarta
-- 74
BABI NA ƊAYA
Shimfiɗa
2.0
Gabatarwa
Wannan kundi zai yi nazari ne a kan kwatancin
ra’in F.W Parsons (1960) da na Paul Newman (2000) game da azuzuwan aikatau na
Hausa. Kowanne aiki yana bukatar gabatarwa domin fito da abun da aikin zai ƙunsa. A wannan kuwa,
za a yi bayani ne a kan aikatau na Hausa tare da nazarin da waiwayen
nazarce-nazaarce da aka gudanar a kan aikatau na Hausa. Bayan haka, bincike zai
yi kokarin bayyana ra’o’in biyu fitattu waɗanda suka shahara don kwatanata su, domin
fito da kamanci da kuma bambancinsu.
Sannan kuma, binciken zai yi ƙoƙarin fito da abin da
wasu masana suka yi tsokaci game da aikatau tare da fito da mabambantan
ra’ayoyi na masana dangane da aikatau na Hausa.
Bugu da ƙari, binciken zai waiwayi
nazarce-nazarce da aka gudanar a kan aikatau ɗin kafin Parsons. Domin ganin yadda
abun ya fara. Dga ƙarshe kuwa, wannan bincike zai fi maya da hankali ne
wajen fito da kamanci da kuma bambaancin da ke tsakanin waɗannan masana biyu
game da azuzuwan aikatau na Hausa, don tatance aya da tsakuwa.
1.1 Dalilin Bincike
Masu iya Magana kan ce, “Ruwa baya tsami
banza”. Wannan zance haka yake, domin komai ka ga ya faru akwai dalili
faruwansa. Kenan wannan aiki yana da dalilai da suka sa za a gudanar da shi. Ga
su kamar haka:
1. Babban dalilin wannan
aiki shi ne nuna irin bambanci da kamancin da ke tsakanin waɗannan ra’o’i biyu,
wato ra’in Parsons (1960) da Newman (2000) game da aikatau na Hausa.
2. Dalili na gaba shi ne
a iya cewa wannan aiki ne wanda zai cike giɓin da aka bari a wannan ɓangare, musamman ma a
wannan mataki na digiri. Domin a iya binciken da aka yi, shi ne aiki na farko
da zai kwatanta ayyukan biyu a fagen aikatau na Hausa, domin ganin kamancinsu
da kuma bambancinsu.
3. Haka kuma yana daga
cikin dalilin wannan bincike shi ne, tattara irin gudummuwar da da masanan suka
bayar a wannan sashin na nahawun Hausa dangane da Aikatau. Wanda hakan zai
taimaka wa masu bincike da nazari ganin irin gudummuwar da masanan suka bayar.
2.1
Manufar Bincike
Babban manufar wannan
binciken ita ce, kwatanta ra’o’i biyu wato, Parsons (1960) da Newman (2000)
domin fayyace ko fito da tsarin aikatau na Hausa. Haka kuma wannan bincike yana
da manufar fito da tsarin aikatau na Hausa da sigogin aikatau na Hausa. Bayan
haka, wata manufar wannan bincike ita ce, fito da ayyakan aikatau da aka
gudanar cikin ra’o’i mabambanta domin nuna irin fahimtar kowanne masani a wannnan fage na aikatau na Hausa
1.3 Hasashen
Bincike
Kasancewar wannan
bincike kwatanci zai yi a kan ra’o’i biyu wannan Newman (2000) da na Parsons
(1960) game da azuzuwan aikatau ɗin hausa Hausa. Akwai hasashen kamar
haka:
Ana hasashen wannan bincike ya iya fayyace
irin bambance-bambance dake tsakanin waɗannan masana biyu, domin ganin inda suka haɗu da kuma inda suka
rabu.
Haka kuma ana
hasashen wannann bincike zai kawo kowane ra’i tare da bayyana irin fahimtar
masanin. Wanda hakan zai taimaka wajen sanin ra’o’in masan aga masu nazari a
wannan fagen aikatau na Hausa. Bayan haka ana sa ran wannan bincike ya bayyana
wasu nazarce-nazarce da aka gudanar game da aikatau na Hausa. Domin fahimtar masana
daban-daban game da yadda suka rarraba aikatau ta fuskoki mabambanta.
1.4 Farfajiyar Bincike
Wannan bincike kamar
yadda kanun ya nuna, bincike ne da ya faɗa cikin fagen ilimin nahawun harshe. Wannan
fage na ilimin harshe fage ne mai faɗin gaske tunda ya haɗa da: Ilimin Ma’ana (Semantics) da Ilimin Ginin
Jumla(Syntas) da Ilimi Ginin Kalma
(Morphology) da Ilimin Tsarin Sauti da
Furuci (Phonitics and Phonology) da
gundarin kalmomi da sauransu.
Saboda haka wannan aiki
zai fi karkata ne wajen fito da bambanci da kamanci na mazhabobin biyu a
bangaren nahawun harshe game da aikatau na Hausa.
Wannan bincike zai yi
ƙoƙirin na kwatanta waɗannan ra’o’i biyu ta
fuskoki kamar haka:
a. Tsarin sauti da
waslin ƙarshen kalma.
b. Ginin jumla a
azuzuwan aikatau aikau na Hausa
c. Ginin kalma a
azuzuwan aikatau na Hausa
d. Ma'ana a azuzuwan
aikatau na Hausa.
e. Adadin azuzuwan
aikatau na Hausa.
f. Fanɗararrun aikatau (irregular
Verbs)
Ana ganin bincike ba
zai wuce waɗannan iyakokin ba, za a
takaita shi ne a iya abubuwan da
aka ambata a sama.
1. 5 Muhimmancin Bincike
Wannan bincike yana
da muhimmanci musamman ga ɗalibai masu sha’awar yin bincike a kan nahawun harshen
Hausa. Ana sa ran zai kara musu ƙaimi da ƙwarin gwuiwa wajen sa
su a kan hanya wajen fahimtar azuzuwan aikatau ma Hausa. Bayan haka, wannnan
binciken zai ƙara sauƙaƙa wa manazarta
harshen Hausa su ƙara fahimtar ra'o'in biyu. Domin kasancewar an yi su ne a
harshen Ingilishi. Wannan bincike zai yi ƙoƙari wajen sauƙaƙa aikin zuwa harshen
Hausa. Har ila yau, binciken zai zama tamkar taska ce ta adana harshen Hausa.
Bayan haka binciken zai yi amfani ga malamai da masu nazari wajen zama
amintaccen madogara tare da ba su damar sanin wannan fage na aikatau.
1.6 Hanyar Gudanar da Bincike
A yayin gudanar da
bincike tilas ne a bi hanyoyi da dama domin cin nasara. Wannan bincike zai bi
hanyoyi da dama domin tattaro bayanai masu alaƙa dawannan kanun
bincike. Waɗanda suka haɗa da:
Ɗaya daga cikin hanyar
da za a bi ita ce, tuntuɓar malamai a kƙn abin da ba a
fahinta ba ko ake neman karin bayan, domin dacewa da bincike yadda ya kamata.
Wata hanyar kuma ita
ce, ziyarar ɗakunan karatu a cikin
gida nan A.B.U da wajen makaranta in hakan ya kama. Domin binciko ayyukan da
aka gudanar masu alaƙa da wannan bincike.
Nazartar littattafai
bugaggu da kundayen bincike waɗanda suka haɗa da: B. A da B.Ed. da M.A da kuma Ph.D da
sauransu kamar mujallu da takardu da a gabatar a wurare daban -daban da sauran
makamantansu.
Sannan bincike zai yi
amfani da ilimin fassara wanda zai taimaka ga binckiken wajen fassara littafai
da mujallu da kundaye masu alaƙa da wannnan bincike, waɗanda ba da harshen
Hausa ake yi su ba.
1.7 Kammalawa
Wannan babi a iya
cewa shimfiɗa ce ga wannan
bincike baki-ɗaya wato yadda
binciken zai gudana tun daga farko har ƙarshe. A wannan babi
an kawo gabatarwa da kuma dalilan da suka sa ake gudanar da bincike da manufar
binciken tare da hasashen bincike. Haka kuma akwai farfajiyar bincike da
muhimmancin bincike ga manazarta harshen Hausa. Daga ƙarshe babin zai sake
kawo hanyoyun da za a bi domin tattaro bayanai da za su taomaka waken samun
nasarar binciken.
BABI NA BIYU
Waiwayen
Gabata Ayyukan da Suka
2.0 Gabatarwa
Babi na farko
shimfida ce ga wannan bincike, babin ya gabatar mana da dalilai da mafufin daa
hasashen da farfajiyar binciken. Sannan mahimmanci da hanyoyin gudanar da
binciken sai kuma kammalawa.
Wannan babi na biyu
zai yi waiwaye ne a kan wasu ma'anoni da wasu masana suka ba fa a kan Aikatau
na Hausa. Haka kuma a wannan babi za a kawo ayyukan da suka gabata dangane da
Aikatau na Hausa.
Sannan za a waiwayi
wasu ayyuka da suka rigaya suka bayar da ra'ayoyi mabambanta a kan Aikatau na
Hausa. Kamar su Bargery da Robinson da Schön da kuma Abraham da sauransu. Bayan
haka babin zai kawo mana sigogin Aikatau na Hausa.
Daga ƙarshe babin zai kawo
mana manyan ra'o'in masanan biyu, wato na F.W Parsons (1960) da Paul Newman (2000)
game da Aikatau na Hausa. Bayan haka sai kammalawa.
2.1 Ma'anar Aikatau
Skinner (1977) ya ce, Aikatau su ne duk wata
kalma da take biyo bayan lamiran suna da sauran lokaci waɗanda ba waɗannan ba (-naa da
-kee). Haka ma Ahmad B.Z (1981) ya ce, "wannan kalma an aro ta ne daga
Larabci, kuma ma'anarta ɗaya take da 'Verb' da aro daga
Ingilishi"
Ya ƙara da cewa: To,
fi'ili dai kusan koyaushe yana zuwa cikin waɗannan abubuwa guda uku:
a) Yana nuna irin abun da
wani abu /wata/ wani / wasu ke aikatawa. Misali: Musa ya fasa dutse.
b) Fi'ili na iya nuna
abin da wani ko wani abu ko wata ko wasu ke ciki. Misali: Ƙyanwa ta maƙale a tarko.
c) Fi'ili na iya nuna
abun da ke faruwa a kan wani ko wani abu ko kuma wasu : Mangoro ya ruɓe
Bagari (1986) ya ce, "Ajin aikatau shi ne
ajin kalmomi masu nuna aiki. Misali 'kama' da 'duba' da 'ci' da ' sha ' da ' tafi' da kuma
'gaji'. Kalmomin wannan aji suna zuwa ne
bayan lamirai masu nuna lokaci (Aspect /tense markers) kamar su: "Sun da
Suna" da sauransu. Shi ma, Zarruk (1996) ya ce, ma'anar aikatau kalma ce
mai nuna aiki ko aukuwa ko wakana. Kullum tana bin wakilan suna dangin
"sun da zai" da sauransu. Misali.
(a) Na sauka. (b) Za na karanta.
Sun sauka. Zai karanta.
Yaa sauka. Za ta karanta.
Taa sauka. Za ka karanta.
Kaa sauka. Za mu karanta.
Kun sauka. Za ku karanta.
Mun sauka. Za su karanta.
An sauka. Za a karanta.
Da sauransu.
Bunza (2002:14) ya ce,
ma'anar aikatau wasu kalmomi ne masu nuna aukuwar wani aiki ga mai magana ko
wanda ake magana kansa ko aiki na faruwƙa da shi. Kalmomin
aikatau suna faruwa ne daga faɓa ɗaya har zuwa iyakar
gaɓoɓi Hausa.
2.2 Ayyukan da Suka Gabata Dangabe da Aikatau.
Wannan bincike ya ci
karo da ayyukan masu alaƙa da shi, kuma ya yi amfani da su don ganin aikin ya
cimma burinsa.
Zaria (1981). A cikin littafinsa mai suna
'Nahawun Hausa' ya rarraba nahawun Hausa gida-gada tun daga kan aikatau da irin
rawar da suke takawa a cikin jumlar, ta hanyar caccanzawa ta fuskoki
daban-daban dangane da abun da ya biyo bayanta.
Garba A (2011), a kundinsa mai taken "Kwatancin
Harɗaɗɗun Kalmomi Na
Hausa Inglishi ". A cikin
aikin nasa ya nuna yadda kalamomin Hausa ke harɗewa domin haifar da wata ma'ana.
Wannan aiki suna da alaƙa ta fuskar nahawun harshe kasancewa duk fagen ɗaya ne wajen nazarin
harshe.
Abdullahi I.S (2012)
a cikin kundin digirinsa na biyu "Sauye-sauye a Wasulan Ƙarshen Na Aikatau
'Yan Aji Biyu".
Ya bayyana yadda ake samun sauye -sauye a wasula a ajin aikatau na biyu.
Ƙyambo (2012) a cikin
aikinsa mai taken "Kwatacin Wasun Bayanau (Rukunin Nahawu Dangin Suna)
A Hausa da Fulfulde.
Tanimu (2012) a kundin na digiri na biyu mai
taken"Ideophonic Verb in Hausa". Ya yi cikaken
bayani wajen fito da aikatau masu ɓurɓushin ad9n harshen wanda a iya cewa da yawan
masana ba su ce konai a game da irin waɗannan aikatau ba. Misali: kantsamaa da gabzaa
da ɓulɓula da sauransu. Muhammadu
(2016) a cikin kundinsa mai suna"Gudummuwar F.W Parsons A Aikatau Na
Hausa". Ya yi sharhin tare da kawo yadda Parsons ya rarraba azuzuwan
aikatau na Hausa zuwa har gida bakwai wanda ya kira su da 'Grades'.
Wannan bincike suna
da alaƙa ta ƙud-da-ƙud da wannan aiki
domin kusancin da suke da shi, domin yana magana ne akan aikatau na Hausa ne.
2.3 Ra'ayoyin Wasu Masana A Kan Aikatau
Masana da dama sun ta
kai kawo dangane da aikatau tun kafin aikin da ake ganin shi ne ginshikina
wannan fage na Aikatau na Hausa.
Schön (1862) da
Robinson (1925) sun yi nazarce-nazarce a kan aikatau na Hausa. Ga Shön (1862)
da Robinson (1925) ƙarshen aikataukan canza in ana buƙatar aikatau so-karɓau ya koma aikatau ƙi-karɓau. Misali.
·
Yaa
kaɗa (S-ƙ) madara
·
Ɗalibai sun kaɗu (S-ƙ)
Ana kuma juya aikatau
ya ƙare
da waslin -oo in ana buƙatar karɓau ya amfana. Sai dai Schö (1862) da Robinson (1925) ɗin, sun sha bamban
dangane da yadda suka fahimci aikatau da ya ƙare da wasalin -ee. A
wajen Schön (1802) in aikatau ya ƙare da waslin -ee, ƙerarre ne da aka kumburo
daga wani aikatau. Misali. Ana ƙera 'zubee' (S-Ƙ) daga 'zubaa' (S-Ƙ) ko' zuba (Ƙ-S). Shi kuwa
Robinson (1925) Aikatau da ya ƙare da wasalin -ee saiwa ne. Misali:
Tambayee su (S-Ƙ-S).
Bargery (1934: ɗɗiɗ) A wani babban ƙamusun Hausa kuma a
shafukan farko na jagoran ga mai amfani da shi. A nan ya raba aikatau na asali
Hausa har sai zuwa ga gida biyu kamar hka:
(1) Aikatau so-karɓau
Aikatau so-karɓau wannana asali
aikatau ne wanda kai tsaye karbau zai bi bayansa kafin ma'ana ta cika. Misali:
·
Yaa
gyaaraa motaa. (S-Ƙ)
·
Yaa
gyaaraa ta. (S-Ƙ)
(2) Aikatau ƙi- karɓau.
Aikatau ƙi-karɓau, aikatau ne wanda
kai tsaye karɓau ba ya biyo bayansa
kafin ma'ana ta cika a jumla. Misali:
·
Balaa
yaa zaunaa. (S-Ƙ)
·
Ɗalibai sun karantu (Ƙ-Ƙ-S)
Bargery (1934) ya yi
amfani fa aikatau a cikin jumla ya sake raba aikau so-karɓau zuwa gida biyu:
(1) Mutable (wanda gaɓar kashe ta jirkice).
(2) Unmatable (marar jirkita).
(1) Mutable:
Wannan shi ne aikatau
mai jirkitacciyar gaɓar ƙarshen kalma yayin da
wanip karɓau ya bi bayansa.
Misalm:
Aikatau so-karɓau (Transitiɓe Verb)
-aa / - ee/ -i / ko
-as / - ar / ad
Misali:
a. Yaa barbi karee (Ƙ-S) ko Karee ya
harbaa
b. Saaƙaa ya kooyaa. (Ƙ-S)
c. Yaa kooyee ta (S-Ƙ)
d. Yaa kooyi saaƙaa. (Ƙ-S)
e. Ruwa ya zubar / zubas
/ zubda (S-Ƙ)
Yaa zubar /-as. / zubda
da ruwa.
(2) Unmutable:
Aikatau so- karɓau.
Waɗannan su ne waɗanda suke ƙarewa da -aa. / - ee.
/-oo
Misali:
(a) Yaa ƙeera zoobee
Yaa ƙeeraa shi.
Zoobee ya ƙeeraa.
(b)Yaa kurbi/ karbe kunuu
Yaa kurbee shi.
Kunuu ya kurbee.
(c) Yaa sayoo kayaa.
Yaa sayoo shi.
Kaayaa ya sayoo.
Aikatau ƙi-karɓau
Waɗanda ba su buƙatar karɓau ya biyo bayansa
kafin ma’ana ta cika a jumla sukan ƙare ne da: - a. / -aa. / - oo/ ko-u kamar yadda ake ɓa misalai da suka
gabata.
A takaice Bargary
(1934) ya raba aikatauoi ɗin Hausa biyu (2)
wato so-karɓau da ƙi-karɓau. Ya yi la'akari da
yadda ake amfani da aikatau a cikin jumla, ya sake raba aikatau so-karɓau zuwa gida biyu:
Mutable da Immutable.
Abraham (1946) aiki
ne da aka yi a kan aikatau kafin bayyanar na Parsons. Abraham ya raba aikatau ɗin Hausa zuwa ɓida uku:
(i)
Aikatau so-karbau
(ii)
Aikatau ƙi-karɓau.
(iii)
Aikatau Haddasau.
Abraham ya sake raba
aikatau so-karɓau gida biyu:
changing da. Changing su ne waɗanda karshen kalmar yakan jirkice in wani karɓau daban ya biyo
bayansu.Misali.
(a) Binta Balaa yaa auraa (Ƙ-S)
(b) Binta kam Balaa yaa auree ta.
(c) Bala yaa auri Binta.
Unchanging su ne
aikatau waɗanda ƙarshen su ba ya
canzawa, sukan kare da: -aa / - ee / -oo misali: (a) Yaa gasaa masara (S-Ƙ)
Yaa gasaa ta.
Masaraa yaa gasaa.
(b) Yaa kurɓee kunuu (S-Ƙ)
Yaa kurɓee shi.
Kunuu ya kurɓee.
A takaice Abraham (1946)
ya taba aikatau na Hausa gida uku: Aikatau so-karɓau. Aikatau Ƙi-karɓau. Aikatau haddasau.
Sai kuma ya raba so-karɓau zuwa gida biyu
changing da unchanging.
Junju (1980) ya kira
aiki nasa da sigogin aikatau na Hausana fi'ili.
Sigogin A, B, C, D na
fi'ili mai gaɓa biyu cikin Hausa
yana da Hausa bakwai. Kowanne Hausa yana da sigogi kashi-kashi.
A: Ana amfani da ita ina bayan fi'ili babu
maf'ulli.
B: Ana amfani da ita
ce idan bayan fi'ili akwai lamirin maf'ulli.
C: Ana
amfani da ita idan bayan fi'ili akwai maf'uli maƙasudi.
Bayan haka ya nuna
cewa zai kawo jadawali sigogin aikatau. Kuma a cikinsa za a nuna karin sauti.Ya
nuna cewa wasu wasulan akwai dogaye da gajeru. Sannan ya raba Aikatau daga (1)
zuwa (7) kamar yadda Parsons (1960) ya raba. Sai dai nasan kason, aikatau ɗan aji shida (6) shi
ne, ɗan aji biyar (5).
Sannan dan aji shida (7) shi ne dan aji shida (6), bisa yadda ya raba ajin
aikatau din nasa.
Bagari (1986) shi ne kamar sauran ra'ayoyin
ne, ya ce, ajin aikatau shi ne ajin kalmomi masu nuna aiki kamar: ci, sha,
duba, tafi da gaji. Kalmomin wannan aji suna zuwa ne daga bayan lamirai masu
nuna lokaci (aspect/tense markers) kamar: sun, ko sukan da suna da sauransu.
Ya kuma kasa kalmomin aikatau gida biyu:
Masu ɗaukar karɓau (Transitiɓe Verb): ci,
sha, gani
Marasa daukar karɓau (Intransitiɓe Verb): tafi, gaji,
zaunaa.
Ya kuma nuna cewa, ba kowanne suna ba ne yake
biyo bayan aikatau ya zama ya sami karɓau.Misali:
Audu ya tafi kasuwa.
A nan kasuwa ba karɓa, tunda ba za mu iya
cewa, Audu ya tafi ba? Sai dai mu ce, Ina Audu ya tafi?
Bayan haka kuma ya bayyana cewa, ana iya
karkasa aikatau dangane da tsarin karin sauti (tone pattern) da yanayin ƙarshensu (ending)
kamar yadda F.W Parsons ya yi, inda ya raba zuwa gida (7) wanda ya kira da
'Darajojin aikatau na Hausa ' (Hausa Verbal grade).
Ya kuma nuna cewa, ƙarshen aikatau yana
canzawa dangane da irin karɓau ɗin da ya biyo bayan
aikatau ɗin.
2.4 Sigogin Aikatau Na Hausa.
Aikatau na Hausa yana
da sigogin da ake gane shi da su. Iri waɗannan sigogin su ne suke ba da daamar gane
rukunin da matsayin aikatau ɗin. Bayan haka, sigogin suna tafiya ne da abu biyu, wato
karin sauti da wasulan ƙarshe kalma na aikatau ɗin.
Sigogin sun kasu gida hudu:
(a) Sigar A
(b) Sigar B
(c) Sigar C
(d) Sigar D.
Sigar A
A sigar A, wannan
sigar aikatau in karɓau bai zo bayansa ba
saboda aikatau ɗin ya kasance
ki-karbau ko an mayar da karɓau ɗin farkon jumla a ƙarfafa shi. Ko kuma
kawai dai an shafe karɓau ko an yi tambaya.
A sigar B kuwa,
wannan sigar aikatau in ya zo kafin karɓau kai-tsaye wakilin suna (ni, k a, ki, shi,
ita, mu, ku, su) misali:
Talle ya kaamaa
su
A sigar C, aikatau in
ya zo kafin karɓau kai-tsayw suna.
Musali:
Binta ta kashee ɓeera
A sigar D, aikatau
sigar Da in ya zo kafin karɓau jakada suna ko wakilin suna (mani, maka maki, masa,
mata, mana, maku, masu) d.s Misali:
Audu ya sayaa mana keke.
A irin waɗannan sigogin a kan
iya gane ko wane aji ko rukuni A da kan iya shiga cikin, misali. Aikatau so-karɓau, kawai akan samu a
rukunin ki aji (0) sifili da aji biyu (2) da aji biyar (5). Don haka za su ɗauki dukkan sigogin
guda hudu. (A, B, C, D).
Aikatau ki-karɓau kuwa, akan samu a
aji (3) da (7). Saboda haka sigar (A da D) za a samu………………
Amma a aikatau so-karɓau da ki-karɓau akan samu a aji
(1) da (4) da kuma (6). Dangane da sigogin A da D, aikatau da suke so-karɓau za su ɗauki sigogin hudu
duka. Sannan ki-karɓau za zu ɗauki sigar A da D ne
kaɗai.
Ga sigogin aikatau ɗin a jadawali:
|
S/N |
A |
B |
C |
D |
|
|
1 |
S-Ƙ -aa (S)
S-Ƙ-S |
S-Ƙ -aa (S)
S-Ƙ-S |
S-Ƙ -a (S) S-Ƙ-Ƙ |
S-Ƙ -aa (S) S-Ƙ-S |
|
|
2 |
Ƙ-S -aa (Ƙ) Ƙ-S-Ƙ
|
Ƙ-S -I (Ƙ) Ƙ-Ƙ-S
|
Ƙ-S -e (Ƙ) Ƙ-Ƙ-S
|
Ƙ-S -aa (Ƙ) Ƙ-S-Ƙ
|
|
|
3 |
Ƙ-S -a (Ƙ) Ƙ-S-Ƙ
|
|
|
Ƙ-S -a (Ƙ) Ƙ-S-Ƙ
|
|
|
4 |
S-Ƙ -ee (S) S-Ƙ-S |
S-Ƙ -ee (S) S-Ƙ-S |
S-Ƙ -e (S) S-Ƙ-Ƙ
|
S-Ƙ -ee (S) S-Ƙ-S |
|
|
5 |
S-S
-ar (S) S-S-S |
S-S
ar+ da (S) S-S-S |
S-S
-ar+ da (S) S-S-S |
S-S
-ar (S) S-S-S |
|
|
|
|
|
|
|
|
|
6 |
S-S
-oo (S)
S-S-S |
S-S
-oo (S) S-S-S |
S-S
-oo (S) S-S-S |
S-S
-oo (S) S-S-S |
|
|
7 |
Ƙ-S -u Ƙ)
Ƙ-Ƙ-S |
|
|
Ƙ-S -u (Ƙ) Ƙ-Ƙ-S
|
|
Sigogin cikin
azuzuwan aikatau a jumlar Hausa.
Ajin farko:
A. Yaa taraa (S-Ƙ)
B. Yaa taaraa mu.
C. Yaa taaraa kuɗi.
D. Yaa taaraa mata kasaa
Aji na biyu:
A. Yaa sayaa (Ƙ-S)
B. Yaa sayee shi.
C. Yaa sayi doki.
D. Yaa sayaa musu keke.
Aji na uku:
A. Yaa tafi (Ƙ-S)
Ajin na hudu:
A. Yaa budee (S-Ƙ)
B. Yaa budee ta.
C. Yaa budee ƙofa.
D. Yaa budee mini koofa.
Aji biyar:
A. Yaa kwantar (S-S)
B. Yaa kwantar da shi.
C. Yaa kwantar da yaroo.
D. Ya kwantar mini da yaroo.
Aji shida:
A. Yaa aikoo (S-S)
B. Yaa aikoo shi.
C. Yaa aikoo Binta.
D. Yaa aikoo mini yaroo.
Ajin bakwai:
A Yaa daku (Ƙ-S)
2.5 Ra'in F.W Parsons (1960)
Parsons (1960) ya
raba aikatau na Hausa zuwa azuzuwa. Wanda haka ya zama madogara ga saura masana
a wannan fage na aikatau. Parsons ya raba aikatau ɗin zuwa gida bakwai,
wanda ya kira su da 'Verbal
Grades' ta yin la'akari da karin sauti da wasulan ƙarshen kalma da
aikatau ɗin ke ɗauke da shi.
Parsons ya kasa aikatau
ɗin kamar haka:
(1) Aikatau Aji Ɗaya:
Aikatau ɗan aji ɗaya yana da karin
sauti sama-ƙasa a kalma mai gaɓa biyu. A mai uku kuwa, yana da S-Ƙ-S. A aikatau mai gaɓa fiye da uku, ana
kara mai katin sauti sama (S) a farkon gaɓar kalmar. Bayan haka yana da dogon waslin
-aa a ƙarshen kalma. Sannan wasun kalmomin aikatau na wannan
gida so-karɓau ne, wssu kuma
ki-karɓau ne.Misali:
Gaɓa |
Gaɓa 2 |
Gaɓa 3 |
Gaɓa 4 |
Kalma |
Jiƙaa,
bugaa |
Taakuraa |
Jagalgalaa |
Karin sauti |
S-Ƙ |
S-Ƙ-S |
S-S-Ƙ-S |
Aikatau Ɗan Aji biyu:
Aikatau ɗan aji biyu, yana
zuwa da dogo wasali -aa a karshen gaɓar kalma. Sannan yana da Karin sauti (Ƙ-S) a aikatau mai gaɓa biyu (2). A mai uku
kuwa (Ƙ-S-Ƙ). A gaɓar da ta wuce uku, ana ƙara karin sauti (Ƙ) a farkon gaɓar kalma. Bayan haka,
dukkan aikatau da yake aji biyu so-karɓau ne. Misali.
Gaɓa |
Gaɓa (2) |
Gaɓa (3) |
Gaɓa(4) |
Kalma |
Kwaasaa, sayaa |
Mallakaa |
Shugabantaa |
Karin sauti |
Ƙ-S |
Ƙ-S-Ƙ
|
Ƙ-Ƙ-S-Ƙ |
Aikatau Ɗan Aji Uku:
Aikatau ɗan aji uku, yana ƙarewa ne da jageran
wasli na -a. Sannan da karin sauti (Ƙ-S) a mai gaɓa biyu, a mai uku
kuwa karin sauti kan zama Ƙ-S-Ƙ. A aikatau ɗan aji uku wanda gabarsa ta wuce uku kuwa,
ana ƙara karin sauti (Ƙ) a farkon gabar
kalmar. Sannan dukan aikatau ɗan aji uku ƙi-karɓau ne. Misali:
Gaɓa |
Gaɓa (2) |
Gaɓa (3) |
Gaɓa (4) |
Kalma |
Ɗiga
, cika |
Tsoorata, sulala |
Galabaita,
rikirkita |
Karin sauti |
Ƙ-S |
Ƙ-S-Ƙ
|
Ƙ-Ƙ-S-Ƙ
|
Aikatau Ɗan Aji Hudu:
Aikatau ɗan aji hudu yana ƙarewa da dogon wasali
na -ee a ƙarshen gaɓar kalma. Sannan
da Karin sautin (S-Ƙ) a mai gaɓa biyu. A gaɓa mai uku kuwa S-Ƙ-S. A mai hudu kuwa,
S-S-Ƙ-S. Dukkan aikatau
wannan aji, so-karɓau ne. Misali:
Gaɓa |
Gaɓa (2) |
Gaɓa (3) |
Gaɓa (4) |
Kalma |
Kwalfee, kwashee |
Tsallakee |
Dabaibayee |
Karin sauti |
S-Ƙ |
S-Ƙ-S |
S-S-Ƙ-S
|
Aikatau Dan Aji Biyar:
Aikatau ɗan aji biyar, yana ƙarewa da -ar a gabar ƙarshen kalma. Sannan da karin sauti (S) a duk kalmomin ajin aikatau ɗin. Misali:
Gaɓa |
Gaɓa (2) |
Gaɓa (3) |
Gaɓa (4) |
Kalma |
Kifar , tayar |
Fuskantar |
Sadaukantar |
Karin sauti |
S-S |
S-S-S |
S-S-S-S |
Aikatau Dan Aji
Shida:
Aikatau ɗan aji shida, yana ƙarewa ne da wasli -oo
a ƙarshen
gaɓar kalma. Sannan yana
da karin sauti sama a dukkan gaɓoɓin daga biyu har
hudu. Aikatau ɗan wannan gida
aikatau ne so-karɓau wasu kuma ki-karɓau ne. Misali:
Gaɓa |
Gaɓa (2) |
Gaɓa (3) |
Gaɓa (4) |
Kalma |
Ɓallo,
karboo |
Zagayoo, karantoo |
Rikirkitoo |
Karin sauti |
S-S |
S-S-S |
S-S-S-S |
Aikatau Dan Aji
Bakwai:
Aikatau ɗan aji bakwai yana ƙarewa ne da gajeran
wasalin -u a karshen gaɓar kalmar da Karin
sauti (Ƙ-S) a gaɓa biyu. A uku kuwa (Ƙ-Ƙ-S). Haka a mai gaɓa hudu yana da karin
sauti (Ƙ-Ƙ-S-Ƙ). Dukkan aikatau
wannan aji, aikatau ne ki-karɓau. Misali
Gaɓa |
Gaɓa (2) |
Gaɓa (3) |
Gaɓa (4) |
Kalma |
Dafu, bugu |
Karantu, rubutubu |
Burburkitu, shugabantu |
Karin sauti |
Ƙ-S
|
Ƙ-Ƙ-S
|
Ƙ-Ƙ-S-Ƙ
|
Parsons ya sake kawo wata
muhimmyar fuskar da za iya rarraba azuzuwan aikatau ɗin ta hanya wasu
sigogi hudu: A, B, C, da D.
Parsons ya kawo waɗannan sigogi ne domin
iya gane irin karɓau ɗin da azuzuwan ke iya
ɗauak da kuma waɗanda ba su daukaar
karbau din. Sanna da gane sauye-sauye da ake samu a azuzuwan dangane da wasalin
gaɓar ƙarshe da karin sauti.
Misali: A rukunin:
A: Aikatau wanda karɓau bai zo ba ko babu.
B: Aikatau wanda karɓau ya zo a wakilin
suna.
C: Aikatau wanda karɓau ya zo a suna.
D: Aikatau wanda ya yake da karɓau kaikaitau ko karɓau na guda biyu.
Misali:
Aikatau Dan Aji ɗaya: (S-Ƙ)
A:
taa jiƙaa.
B:
taa jiƙaa shi.
C:
taa jiƙaa magani.
D:
taa jiƙaa mata magani.
Aikatau Ɗan Aji Biyu: (Ƙ-S)
A: yaa sayaa.
B: yaa sayee ta.
C: yaa sayi saniya.
D yaa sayaa musu kwai.
Aikatau Ɗan Aji Uku: (Ƙ-S)
A:
yaa jiƙa.
B:
yaa fita.
C:
yaa sauka.
Aikatau Ɗan Aji Hudu: (S-Ƙ)
A: yaa budee.
B: yaa buudee ta
C: yaa buudee ƙoofa
D: yaa buudee mani ƙoofa.
Aikatau Ɗan Aji Biyar: (S-S)
A: yaa kwantar.
B: yaa kwanatar da ita.
C: yaa kwantar da yaroo.
D: yaa kwanatr mini da yaroo.
Aikatau Ɗan Aji Shida: (S-S)
A: yaa kaamoo.
B: yaa kaamoo shi.
C: yaa kaamoo Biri.
D: yaa kaamoo mata Biri.
Aikatau Ɗan Aji Bakwai. (Ƙ-S).
A: yaa dafu.
B: yaa kaɗu.
C: yaa gyaaru.
Parsons (1960) ya
bambance tsakanin aikatau da ya kira da 'Yan aslin (primary) Aji ɗaya zuwa uku (1-3),
da wanda aka haifar wato (secondry & tertiary) daga na hudu zuwa na bakwai.
Wannan rabe-raben
yana tafiya ne a cikin rukuni amma kai tsaye a ma'ana. Aikatau daga aji (1-3)
ta ma'anarsu a kan sama damar gane wani aji za su fada. Kenana akwai aikatau ɗan aji ɗaya wanda yake so-karɓau ne . Haka kuma aikatau ɗan aji biyu shi ma
so-karɓau. Sannan akwai aikatau
ɗan aji ɗaya
wanda yake ki-karɓau ne da suke da kamancin ma'ana da aikatau ɗan aji uku wanda
dukkansu ki-karɓau ne . Misali:
gayaa (S-Ƙ 1), fadaa(Ƙ-S 2) da yankaa (S-Ƙ 1) da saaraa(Ƙ-S 2) da tsayaa (S-Ƙ 1) inda sauka (Ƙ-S 3).
Haka kuma Parsons ya
gane aikatau ɗan aji (4) sun samo
asali ne a rarraba ƙananan rukunin da aka yi. Akwai wasu aikatau 'yan aji huɗu da suke da ma’ana
ta asali, wanda ba za a iya bambance su ko ta wacce hanya ba. Daga aikatau ɗan aji 1-3.
a. Ajiyee aikatau aji
(4), inda sakaa aikatau ɗan aji ɗaya.
b. Ganee aikatau aji
(4), fahimtaa aikatau (2)
c. Goodee aikatau aji
(4), yarda aikatau (3).
Ko da yake abu ne mai
yuwuwa a canza aikatau ɗan aji 1-3 zuwa
aikatau aji (4) domin samar da kumburarru shi ne, a yain da aka ga saiwar
aikatau ɗin a ɗaya daga kumburarrun ajin. Akan sama kusancin
ma'ana wanda babu shi a azuzuwan 'yan asalin. Haka kuma ga shi nan ƙarara a aikatau ɗan aji biyar (5) da
(7) kamar yadda aka tabbatar. Aikatau ɗan aji (4) ya samu ne a tsakanin azuzuwa 'yan
asali da kumburarru.
Ga tsarin aikin Parsons (1960), a cikin jadawali:
Aji |
A |
B |
C |
D |
1 |
-aa S-Ƙ -S |
-aa S-Ƙ - S |
-a S-Ƙ -Ƙ |
-aa S-Ƙ -S |
2 |
-aa Ƙ-S -Ƙ |
-ee Ƙ-S -S |
-i Ƙ-Ƙ-S |
-aa Ƙ-Ƙ-S-Ƙ
|
3 |
-a Ƙ-S -Ƙ |
|
|
|
4 |
-ee S-Ƙ -S |
-ee S-Ƙ -S |
-e S-Ƙ -Ƙ |
-ee S-Ƙ -S |
5 |
-ar S-S -S |
-ar +da S-S -S |
-ar +da S-S -S |
ar S-S
-S |
6 |
-oo S-S
-S |
-oo S-S
-S |
-oo S-S
-S |
-oo S-S
-S |
7 |
-u (Ƙ)
Ƙ-S
|
|
|
-u (Ƙ) Ƙ-S |
2.6 Ra'in Newman (2000) Game Da Aikatau Na
Hausa.
Newman (2000) aikatau
ɗin Hausa yana faruwa
ne ciki wani tsarin rukunin ginin kalma, wanda akai wa laƙabi da 'grades'
darajoji ko azuzuwan. Kowanne daga ciki
akwai tsayayyen tsarin daya bambanta shi da sauran azuzuwan. Newman ya yi la'akari ne da karin sauti
aikatau ɗin wato (Tone
pattern) da kuma gaɓar ƙarshe (Termination)
Akasarin aikatau na
Hausa suna da alaƙa idan aka duba saiwar
kalmar sai dai a kan sama
bambanci na ma'ana da guraren da
kowannensu ke aiki a tsari nahawu. Misali: sayaa (S-Ƙ 2), sayar(S-S 5) da
sayoo(S-S 6) da kuma sayu(Ƙ-S
7).
Bayan haka, Newman ya
nuna cewa kowanne aji na aikatau ɗin Hausa akwai wasu rukuni da suke shigan
kalmomin domin tantance abun da
ke biye da kalmomin wanda akan
gane mai amsar karɓau da wanda ba ya amsar karɓau ɗin da yadda yake sassauyawa dangane da karin
sauti da kuma gaɓar karshe. Wanɗannan rukunin su ne:
A, B, C, D Waɗanda suke bambance
azuzuwan a kowanne a jumla. Rukunin (A) aikatau ne zuwa ne ba tare da karbau
ba, ko dai aikatau ɗin ki-karɓau ne ko ba a sa masa
karɓau ɗin ba. (B) wannan yana zuwa ne tare da karɓau kai-tsaye na wakilin suna. (C) Shi kuwa aikatau ɗin wanan gida yana
zuwa da karɓau na suna. (D) wannan rukuni aikatau kan sama karbau ne
kaikaitau (indirect object).
Newman ya kasa
azuzuwan aikatau ɗin gida biyu Primary
grade da Secondary grades. A 'primary grades ' su ne ake ganin aikatau ne 'yan
asali. Su kuwa Secondary grades, kuwa su
ne ake ganin samammu ko kumburarru daga gidan 'yan asali. Sannan ya kawo fanɗararrun aikatau wanda
ba su shiga cikin tsarin kowanne aji ba. Kamar ' gani da sanii da barii da kusa
da zama da hau dai kai da baa/bai da jee da zoo.
Ga azuzuwan kamar
yadda Newman (2000) ya raba:
Aikatau Ɗan Ajin Sifili (0)
Aikatau ɗan ajin sifili (0)
Newman (2000) ya kira su ne da sifili, waɗannan aikatau sun yi tarayya ne ta fuskar
tsarin sauti da kuma uadda ake samar da suna ɗan aikatau ta tsawaita waslon da karin
sautin faɗau maimakon waa (Ƙ-S). Aikatau ɗan ajin sifili
akwaibmasu gaɓa ɗaya da karin sautin
sama(S). Shida daga cikinsu sun ƙare da wasalin -i,
biyu da dogon wasalin -aa. A yayin da biyu kuwa suka ƙare da wasalin
-oo.sannan akwai wasu guda hudu da suke da gaɓa biyu karin sautin (S-S) da dogon wasalin
(BiBaa): Misali. biyaa, jiraa, kiraa
rigaa
Miisal:
(1) Wasalin (-i), Karin sautin sama (S).
bi da ci da fi da ji da ƙi da kuma yi.
(2) waslin (-aa), karin sautin sama (S)
Jaa da shaa
(3)
Waslin -oo, karin sautin sam(S)
Soa da zoo.
A |
B |
C |
D |
-i |
-ii |
-i |
-i |
S |
S |
S |
S |
-aa /-oo S |
-aa/-oo S |
-aa/-oo S |
- aa/-oo S |
Aikatau Aji Ɗaya (1)
Aikatau ɗan aji ɗaya, yana ƙarewa ne da dogon
wasalin -aa. Sannan yana da karin sauti (S-Ƙ) a gaɓa biyu, a gaɓa uku kuwa, karin
sautin (S-Ƙ-S). Aikatau ɗan aji ɗaya so-karɓau ne kuma ki-karɓau karɓau ne. Sannan aikatau
ne ɗan asali.
Misali:
kamaa da raazanaa da tumurmusaa.
A |
B |
C |
D |
-aa |
-aa |
-a |
-aa |
S-Ƙ -S |
S-Ƙ -S |
S-Ƙ -Ƙ |
S-Ƙ -S |
Aikatau Ɗan Aji Biyu (2)
Aikatau ɗan aji biyu,
Newman ya kira shi aikatau
mai canzawa (changing Verb) , yana da dofon
wasalin -aa a rukunin A.
Rukunin B kuwa wasalin -ee ne , sai a rukunin C yana da wasalin -i da karin sautin (Ƙ-S). Aikatau so-karɓau. Misali: maaraa da tsoorataa da tattambayaa.
A |
B |
C |
D |
-aa |
-ee |
-i |
- aa |
Ƙ-S Ƙ |
Ƙ-S Ƙ |
Ƙ-Ƙ -S |
Ƙ-S Ƙ |
Aikatau Ɗan Aji Uku (3)
Aikatau ɗan aji uku, yana ƙarewa ne da gajeren
-a, aikatau 'yan wannan aji duk ƙi-karɓau ne. Sannan yana da
Karin sautin (Ƙ-S). Misali.
A |
B |
C |
D |
-a |
|
|
|
Ƙ-S -Ƙ |
|
|
|
Aikatau Ɗan Aji
Uku (3A)
Newman ya ƙirƙiri wanann aji ne
domin wasu kalmomin aikatau
wanda Parsons bai kawo su ba .
Wannan aikatau yana da karin sautin (S-S) da gajeren wasalin
-a, yakan fara ne da
nannauyar gaɓa a farkon gaɓar kalma. Misali. Ƙaura da tuuba da
caara da kuuka da kuma tsuufa.
A |
B |
C |
D |
-a |
-a |
-a |
-a |
S-S |
S-S |
S-S |
S-S
|
Aikatau Ɗan Aji Uku B (3B)
Aikatau ɗan aji uku (b), suna ƙarewa ne da gajeren
waslin -i da - u da -a. Sannan suna da karin sautin (S-Ƙ). Dukkan aikatau ɗan wannan gida gaɓa biyu ne kuma so-karɓau ne. Misali:
Ɓaci da fadi taashi da
wuni/yini da haifu da mutu da kuma ɓata.
A |
B |
C |
D |
-i/-u/-a |
-i/-u/-a |
-i/-u/-a |
-i/-u/-a |
S-Ƙ |
S-Ƙ |
S-Ƙ |
S-Ƙ
|
Aikatau Ɗan Aji Huɗu.
Aikatau ɗan aji huɗu, yana ƙarewa ne da dogon
waslin -ee a ƙarshen kalmar aikatau ɗin. Amma a rukunin C yana ɗaukar gajern
wasalin-e, sannan yana da karin sauti sama-ƙasa (S-Ƙ) a gaɓa biyu, a mai uku
kuwa yana da karin sautin (S-Ƙ-S). Haka a mai gaɓa hudu (S-S-Ƙ-S. Aikatau ɗan wannan gida so-karɓau kuma ki-karɓau ne.
Sanann a wannan aji
akan sama wasu aikatau da suke ƙarewa da ɗafin kwayar ma'ana ta
nyee musamman waɗanda suke da tushen
aji sifili (0) Misali:
Feree da karkadee da ragargajee da kuma shanyee (F- S).
A |
B |
C |
D |
-ee |
-ee |
-e |
-ee |
S-Ƙ -S |
S-Ƙ -S |
S-Ƙ -Ƙ |
S-Ƙ -S |
|
|
-ee
S-Ƙ-S |
-nyee S-Ƙ-S |
-nyee
S-Ƙ S |
-nyee S-Ƙ -S |
-nye S-Ƙ -Ƙ |
|
|
|
-nyee S-Ƙ -S |
|
Aikatau Ɗan Aji Biyar.
Aikatau ɗan aji biyar, yana ƙarewane da harafin
baki a ƙarshen gaɓar kalma aikatau ɗin. Sannan
yana da karin sauti sama(S) a dukkan gaɓoɓin aikatau ɗin.
Haka kuma aikatau ne so-karɓau. A
kan sama sauyi a ƙarshen kalmar rukunin (B), a yayin da wakilin suna ya
biyoa matsayin karɓau. Akan sama -shee karin sautin (S) da 'da'karin
sauti (Ƙ) kafin karɓau.
Misali:
Kooyar da tsooratar da wulakantar.
A |
B |
C |
D |
-ar
(S) |
-ar (S)+ da (Ƙ) |
-ar
+da (S) |
-ar
+ da (S) |
|
-shee (S) |
|
|
|
- - da (S) |
- -
da (S) |
|
Aikatau Ɗan Aji Biyar: (5d)
Aikatauɗan wannan aji, yana ƙarewa ne da ɗafa goshi -daa.
Sanann yana da Karin sautin (S-Ƙ) kamar aikatau ɗan aji ɗaya. Bayan haka
aikatau ne so-karɓau. Misali:
Gaidaa da wahaddaa da
karantadda.
A |
B |
C |
D |
-daa
S-Ƙ |
-daa
S-Ƙ |
-da S-Ƙ |
-daa S-Ƙ |
Aikatau
Ɗan Aji Shida. (6)
Aikatau ɗan aji shida, aikatau
ne mai dogon wasalin-oo a ƙarshen gaɓar kalma. Sannan yana
da Karin sauti (S-S) a duk kalmomin aikatau ɗin. Aikatau
ne so-karɓau.
Misali:
Harboo da karantoo da ratattakoo.
A |
B |
C |
D |
-oo (S) |
-oo (S) |
-oo
(S) |
-oo (S) |
Aikatau Ɗan Aji Bakwai: (7)
Aikatau ɗan aji bakwai yana ƙarewa ɗafa ƙeyar -u, ko da
gajeren wasalin -u. Sannan yana da karin sautin (Ƙ-S). Wannanaikatau ƙi-karɓau ne.
Misali:
Ɗauru da
gajiyu da kanannaɗu.
A |
B |
C |
D |
-u Ƙ-S
|
|
|
|
Newman (2000), ga
yadda abun yake a jadawali:
Rukuni /Aji |
A |
B |
C |
D |
0 |
-i
(S) |
-ii
(S) |
-i
(S) |
-ii (-i)
(S) |
|
-aa /-oo (S) |
-aa/-oo (S) |
-aa/-oo (S) |
-aa / -oo (S) |
1 |
-aa
S-Ƙ
(S) |
-aa
S-Ƙ (S
) |
-a
S-Ƙ (Ƙ
) |
-aa
S-Ƙ
(S ) |
2 |
-aa Ƙ-S (Ƙ) |
-ee Ƙ-S (Ƙ ) |
-i Ƙ-Ƙ-S |
-aa Ƙ-S (S) |
3 |
-a Ƙ-S (Ƙ) |
------------ |
------------- |
-------------- |
3a |
-a
S-S |
------------- |
-------------- |
-------------- |
3b |
-i /-u /-a
S-Ƙ |
------------- |
------------- |
-------------- |
4 |
-ee S-Ƙ (S) |
-ee
S-Ƙ
(S) |
-e
S-Ƙ (Ƙ) |
-ee
S-Ƙ
(S) |
|
-nyee S-Ƙ (S) |
-nyee
S-Ƙ
(S) |
-nye
S-Ƙ (Ƙ) |
|
|
|
|
-nyee
S-Ƙ
(S) |
|
5 |
- ar
S-S |
-ar
(da Ƙ)
(S) |
-ar (da)
(S) |
-ar (da) (S) |
|
|
-shee
(S) |
|
|
|
|
--
(da) (S) |
--
(da) (S) |
|
5d |
-daa
S-Ƙ |
-daa
S-Ƙ |
-da
S-Ƙ |
-daa
S-Ƙ |
6 |
-oo
S-S |
-oo
S |
-oo
S |
-oo
S |
7 |
-u
Ƙ-S |
------------- |
--------------- |
------------ |
2.7 Kammalawa
Kamar yadda aka gani
wannnan babi ya yi waiwaye ne a kan ma'anar aiķatau. Sannan ya
waiwayi ayyukan da aka gudanar masu alaƙa da aikatau. Bayan
hakan, babin ya waiwayi ra'ayoyin masana a kan aikatau domin ganin irin
gudummuwar da kowa ya bayar a wannan fage. Babin ya sake tantance mana sigogin
da aikatau n Hausa ke tafiya da su.
Daga ƙarshe kuwa, babin ya
kawo mana manyan ra'o'in masan biyu wato Parsons (1960) da Newman (2000) a
takaice.
BABI NA UKU
Kamanci
3.0 Gabatarwa
A babin da ya gabata,
babi na biyu ya yi
waiwaye wasu ayyuka na na
aikatau ɗin
Hausa. Inda babin ya kawo
ra'o'in mabambanta dangane
da aikatau na Hausa
da yadda kowanne masani ke kallon aikatau na Hausan.
Wannan babin kuwa , zai yi la'akari ne da muhimmanci
ra'in nan biyu na Parsons (1960)
da Newman (2000), domin kwatanta su a
fito da kamancinsu da kuma bambancin ta
fuskokin mabambanta tare da
kawo misalai waɗanda za su nuna
kamancin ayyukan biyu ƙarara.
3.1 Kwatancin Ra'in Parsons (1960) da Newman (2000)
Game da Azuzuwan
Aikatau Na Hausa
Tun lokacin mai tsawo
masan ilimin harsuna sun yi ƙoƙari wajen
nazarce-nazarce game da aikatau na Hausa. Irin waɗannan masana sun haɗa da: Schon (1862) da
Rabinson (1925) da Bargery (1934) da kuma Abraham (1946). Daga baya ne ka sami
wani masani wanda ya nazarce aikatau ne Hausa ta wata fuskar wanda aka gani shi
ne ya firo da aikatau na Hausa cikinwasu Azuzuwa wanda ya kira da 'Grade'
Wannanmasani kuwashi ne F.W Parsons, wanda ya gudanar da nazarin nasaa (1960).
Wannannazari da ya yi sai ya gama wa
sauran manazarta madogara, wanda
haka ya sa wasu
manazartan suke gani akwai wasu
yan gyare-gyare da ya kamata a yi.
Daga cikin waɗanda suke ganin aikin
Parsons ɗin ya haifar da gibi
game da wasu kalmomin, akwai: Pual Newmaninda ya waiwaiyi ra'in Parsons na (2000),
domin bayar da tasa irin gudummuwar a wannan fage na aikatau a Hausa.
Wannan ya sa za a
kamanta ayyukan ta fuskokn nazarin harshe domin ganin kamancin ra'o'in guda biyu.
3.1.0 Karin Sauti Da
Wasalin Ƙarshen Kalma
Sani (2013) ya ce,
karin sauti nau'i ne na amon murya a lokacin da ake furta lafazin gaɓar kalma. Kowacce gaɓar kalma tana da
karin sauti ɗaya.
Sani ya ƙara da cewa a Hausa
muna da karin sauti irin uku: katin sautin sama (S) da kari saukin ƙasa (Ƙ) da kuma faɗau (F). Haka ma, Parsons
(1960) ya yi amfani da karin sautin wajen raba azuzuwan azuzuwa na aikatau ta
yin la 'akari da karin sauti da waslin ƙarshen gaɓar kalma ta aikatau a
matsayin kwayar ma'ana. Kowanne aji da karin sautin gaɓoɓin kalmominsa wanda
ya kira su da: (Grades markers).
Wannan tsarin Parsons
ya bi wajen raba azuzuwan aikatau har zuwa aji bakwai, inda ya nuna duk aikatau
mai gaɓa biyu in dai ya fito
da karin sautin (S-Ƙ), sannan ya ƙare da dogon waslin
-aa yana aji na (1) ne. Misali: koosaa, rainaa, zaunaa. In aikatauyana da karin
sautinm (Ƙ-S) sannan ya ƙare da dogon wasalin
-aa, aikatau ne ɗan aji biyu. Misali:
Kooyaa, sayaa, aunaa, zubaa. Idan aikatau yana da karin sautin (Ƙ-S) da gajern waslin
-a yana aji uku (3) ne. Misali: rika, fita, shiga, ɗiga.
Aikatau da yake da
Karin sautin (S-Ƙ), sannan yana ƙarewa dogon wasalin –ee,
aikatau ne ɗan aji hudu (4).
Misali: sayee, zubee, shigee. Haka kuma
aikatau da yake da karin sautin (S-S) sannan da gaɓar karshe na -ar, aikatau
ɗan aji biyar (5).
Misali: sayar, koyar kawar zubar,
shigar. In aikatau yana da karin sautin (S-S)
sannan ya ƙare da dogon wasalin -oo, aikatau ne ɗan aji shida (6).
Misali: sayoo, shigoo, kooyoo. Aikatau mai Karin sautin (Ƙ-S) sannan ya ƙare da gajeren wasalin
-u, aikatau ne ɗan ajin bakwai (7).
Misali: zaunu, sayu, bugu, dafu riku.
Waɗannan alamun Parsons (1960)
ya kira su da (Grade Markers) masu ɗauke da kwayar ma'anar kowane aji. Ya kuma ƙaddara waɗannan alama za su iya
tafiya da kowacce tushen kalmar aikatau don tayar da aji n aikatau.
Misali:
Aji |
Karin Sauti |
Waslin ƙarshe |
Kalmar aikatau |
1 |
S-Ƙ |
-aa |
Zaunaa, kamaa |
2 |
Ƙ-S |
- aa |
Sayaa
, zubaa |
3 |
Ƙ-S |
- a |
Fita,
ɗiga |
4 |
S-Ƙ |
- ee |
Sayee , zubee |
5 |
S-S |
- ar |
Shigar kooyar |
6 |
S-S |
-oo |
Fitoo,
shigoo |
7 |
Ƙ-S |
- u |
Shigu , bugu |
Haka kuma, idan muka
duba Ra'in Newman (200) ya nazarci aikatau na Hausa, ya nuna yana da azuzuwa wanda shi ma ya kira
su da 'Grades '. Inda kowannensu yake da tsari na musamman da ake gane shi.
Abubuwan da ake gane kowanne ajin kuwa da su: karin sautin (tone pattern) da ƙarshen gaɓar kalma(termination)
wanda yakan iya ƙarewa da
wasali sai dai akan sama wanda yake
ƙarewa da aB (Baki).
Newman (2000) shi ma
ya yi amfani da karin sautin da wasalin ƙarshewajen
rabaazuzuwan aikatau, inda kowanne yana da irin nasa tsarin. Aikatau ɗan ajin (0) sifili
yana da karin sautin (S) da wasalin -i/-aa /- oo. Aikatau ɗan aji ɗay yana da kari sautin (S-Ƙ) a gaɓa biyu, a uku kuwa (S-Ƙ-S) da wasalin gaɓar ƙarshe na -aa. Aikatau
ɗan aji 3) kuwa yana
da Karin sautin ƙasa-sama: (Ƙ-S-Ƙ) sannan da dogon
wasalin ƙarshe na -aa. A aji uku kuwa, yana da karin sautin ƙasa-sama: (Ƙ-S-Ƙ) sannan da gajeren
wasalin ƙarshe na -a.
Aikatau ɗan aji uku A (3A)
yana da karin sautin (s) sannan yana ƙarewa ne da gajeren
waslin -a. Aikatau ɗan aji uku .B(3B),
yana da karin sautin sama -ƙasa (S-Ƙ), sannan yana ƙarewa ne da wasalin-i
/-u /- a.
Aikatau ɗan aji hudu (4) yana
da karin sautin sama-kasa: (S-Ƙ-S) da wasalin gaɓar ƙarshe na -ee. Aikatau
ɗan aji biyu (5) yana
da karin sautin sama-sama da gaɓar ƙarshe na -ar. A aikatau ɗan aji biyar (5D) yana da karin sautin
sama -ƙasa da gaɓar ƙarshe na -daa. Sai a aikatau ɗan aji shida (6) yana
da katin sautin sama-sama a duka gaɓoɓinsa da wasalin ƙarshe na -oo. Aikatau
ɗan aji bakwai (7)
kuwa, yana da karin sautin Ƙasa-sama ne, sannan yana zuwa da
wasalin gaɓar ƙarshe na -u, kamar
yadda (Newman 2000) ya gabatar.
Ke nan Parsons (1960)
da Newman (2000) suna da kamanci na yi la'akari da karin sautin da wasalin gaɓar ƙarshe kalma, wajen rarraba
azuzuwan aikatau na Hausa.
Haka kuma, idan aka
sake dubawa za a ga an sake samun kamanci a tsakanin azuzuwan kamar a aji na ɗaya da biyu da uku da
hudu da biyar da shida da bakwai, wato babu wanda ya saɓa wa wani ta fuskar
karin sautin ko wasalin gaɓar ƙarshe kalma, duk suna tafiya da tsarin iri ɗaya ne .kamar yadda
suke a wajen wasali ƙarshe a azuzuwan.
3.1.1 Ginin Jumla A Azuzuwan Aikatau Na Hausa.
Parsons (1960) da
Newman (2000) sun yi tarayya wajen yin amfani da kalmar aikatau a ginin Jumla
wajen nazartar kalmomin aikatau na Hausa wato (Morphosyntaɗ). A wajen nazarin
sun duba aikatau ne da dangantakarsa da karɓau ɗin da ya biyo bayan aikatau ɗin in har akwai.
Parsons (1960 da
Newman (2000) sun yi amfani da ginin jumla wajen samar da sigogi hudu kamar yadda
kowannensu ya samar: A, B C, D. Da kuma
gane waɗanne azuzuwan ne ke
amsar karɓau da waɗanda ba sa amsa.
Masannan sun yi tarayya wajen samar da waɗannan \sigogi wanda suka su da (Form). In da
suke nuni da idan karɓau yabiyo bayan
aikatau wacce siga ce aikatau ɗin zai faɗa?
Misali:
Sigar A.
Aikatau sigar A (zubin
A, kan samu ne in karɓau bai zo ba bayan
aikatau ba, ko saboda aikatau ɗin ya kasance ƙi-karɓau ko an mayar da karbau farkon jumla don karfafawa, ko dau an share
karɓau ɗin ne kawai. Misali
(a) Yaa shiga (aikatau ƙi-karɓau) Ƙ-S
(b) Hauwa taa rooƙaa. (an share karɓau) Ƙ-S
(c) Gishiri Hauwa taa
rookaa (an ƙarfafa karɓau) Ƙ-S
(d) Mee Hauwa taa daafaa
?(tambaya) S-Ƙ
Aikatau sigar B
Aikatau Sigar B (zubin B), aikatau ne da yake amsar
karɓau na kai-tsaye a
matsayin wakilin suna kamar: ni, kai ke, shi, ita, mu, ku, da su. A wannan siga
aikatau ɗan aji yakana sauya
wasalin ƙarshe daga -aa zuwa -ee idan ya fado a wannan siga. Misali
(a) Yaa dafaa ta S-Ƙ
(b) Audu yaa auree ta. (-aa zuwa -ee) Ƙ-S
(c) Bukar yaa wankee
ta. S-Ƙ
(d)Bello yaa watsar da
ita, S-S
Aikatau Sigar C.
Aikatau sigar C (Zubin
C), wannan sigar na aikatau ana samun sa ne idan aikatau ya zo kafin karɓau na kai-tsaya na
suna. A wannan siga wasulan karshen
kalmar aikatau kan gajarce a aikatau ɗan aji: ɗaya da hudu. A aji biyu kuwa, wasalin kan
sauya ne daga -aa zawa -i ne. Misali
(a) Ta rubuta wasiikaa. S-Ƙ-S
(b) Taa rooƙi gishiri. (-aa zuwa
-i) Ƙ-S
(c) Yaa wanke
mootaa. S-Ƙ
Aikatau Sigar D
Aikatau Sigar D (Zubin D), kan samu ne in karɓau jakada /kaikaitau
ya gabaci aikatau. Irin jakadar da ake
samu su ne, na wakilin suna ne kamar: ma+ ni, ka da ki da ku da su da sauransu, da
kuma jakadan ‘wa /ma”.
Misali.
(a) Auda yaa daafaa masa
moota. S-Ƙ
(b) Shitu yaa kooyaa wa ɗalibai Hausa. Ƙ-S
(c) Yaa shiga masa gida. Ƙ-S (3)
(d)Yaaroo yaa wankee
mini hula. S-Ƙ (4)
(e) Audu yaa sayar wa
Binta fiilii. S-S
(f) Su taaru mana a gida.
Ƙ-S
Ga wasu misalai na
yadda suke a azuzuwan aikatau na Hausa:
Akatau Aji Ɗaya.
Sigar A. Yaa taaraa. (S-Ƙ)
B. Yaa taaraa mu.
C. Yaa taaraa kudi.
D. Yaa taaraa mata ƙasa.
Aikatau Aji Biyu.
Sigar A. Yaa
sayaa. (Ƙ-S)
B. Yaa sayee shi.
C. Yaa sayi doki.
D yaa sayaa mini keke.
Aikatau
Aji Uku.
Sigar A. Yaa tafi. (Ƙ-S)
B --------------------
C --------------------
D Yaa shiga musu gona
Aikatau Aji Hudu.
Sigar A. Yaa budee. (S-Ƙ)
B.
Yaa budee ta.
C. Yaa bude koofa.
D. Yaa budee mata koofa.
Aikatau Aji Biyar.
Sigar A. Yaa kwantar. (S-S)
B. Yaa kwantar da ita.
C. Ya kwantar da yarinyaa
D yaa kwantar maku da Binta.
Aikatau Aji Shida.
Sigar A. Yaa aikoo. (S-S)
B. Yaa aikoo shi.
C yaa aikoo Bintaa.
D. Yaa aikoo mana shi.
Aikatau Aji Bakwai.
Sigar A. Yaa daku. (Ƙ-S)
B. ------------
C. ------------------
D. Sun taaru mana a ɗaki.
Ke naan kowanne aji
yana da da sigogin hudu sai dai akwai waɗanda ba su ɗauka hudu sai dai A da D. Parsons da
Newman sun yi la'akari ne da aikatau a julma wajen gane waɗanne azuzuwa ne
so-karɓau da ki-karɓau. A nan ma akwai
kamanci wajen masanan yadda suka aikatau na azuzuwan gida uku: aji 1 da 4 da 6, aikatau ne so-karɓau kuma ƙi-karɓau. Aji 2 da 5, aikatau ne so-karɓau. Aji 3 da 7 aikatau ne ƙi-karɓau.
A takaice Parsons
(1960) da Newman (2000) suna da kamanci a wannan fuskar ta aikatau
a gini jumla , inda suka yi
tarayya ta wajen gane irin aikatau
so-karɓau ko kuma ƙi-karɓau ne , kamar yadda aka ga misalai a sama.
3.1.2 Ginin Kalma A
Aikatau Na Hausa
Parsons (1960) da
Newman (2000) sun yi la'akari da tasrifin kalma wajen rarraba aikatau na Hausa zuwa
azuzuwa. Wannan fage ne na nazarin kalma da ka'idojin da suka shafi ƙera kalma, wanda ke
nuna ko fayyace ko kalma saiwa ce ko
kuma Kumburarriya ce ko kuma dai tsirarriya.
Parsons da Newman sun
raba aikatau ta irin wannan fuskar , inda suka kira aji 1-3 da ( ‘Yan Asali)
wanda suke zuma zubin boye na kowanne aikatau,
wato su ne a matsayin saiwar
sauran azuzuwan na aikatau.(Tsirarrau).
Irin waɗannan aikatau na 1-3 daga su ne ake samun saura azuzuwa
bayan an kumbura ko an tsirar da su ta
hanyar mayar da Kalmar saiwa sai a ɗafa masu kwayar ma'anar (Grades markers) na
azuzuwada ake so a ƙera. Misali.
Sayaa = say (Saiwa)
Say = say + ee sayee (S-Ƙ 4)
Say + oo sayoo
(S-S 6)
Say + ar sayar (S-S 5)
Say + u sayu
(Ƙ-S
7)
Parsons (1960) da
Newman (2000) sun yi la'akari da tasrifin kalmomin aikatau inda suka kira su da
saiwar aikatau (Ajin na asali) da (Ajin tsirarru) wanda aka tsirar ke nan ta
hanyar ɗafa ƙeyar karin sauti da
wasalin ƙarshe na ajin da ake so. Misali:
·
Koonaa
(S-Ƙ
1) zuwa
koonee (S-Ƙ 4)
·
Kirɓaa (S-Ƙ 1) zuwa
kirbu (Ƙ-S 7)
·
Sayaa (S-S
2) zuwa sayoo
(S-S 6)
·
Zuba (Ƙ-S 3) zuwa
zubar (S-S 5)
A takaice da Parsons
da Newman suna da kamanci ta fuskar tsirar da wasu azuzuwa daga azuzuwa na
asali, ta hanyar tasrifin kalma.
3.1.3 Ma'ana A
Azuzuwan Aikatau Na Hausa.
Ilimin ma'anar (Semantic)
wani ɓangare ne na ilimin
harshe wanda ya shafi ire-iren ma'ana da kalma kan iya ɗauka. Parsons (1960)
da Newman (2000) sun yi la'akari da wannan ɓangare wajen rarraba aikatau na Hausa. A iya
cewa sun yi tarayya wajen fito da kalmomin aikatau ta fuskar ma'ana. A inda kowannensu ya yarda azuzuwan 1 da 2 da
3 suke dauke da ma'ana ta asali (basic meaning) na aikatau ɗin, sannan ɗaga aji na 4 zuwa 7 kowannensu na da tsirarriyar
ma'ana ce daga ta asali.
Misali. (1)
Aikatau |
Aji |
Karin Sauti |
Kooraa |
1 |
S-Ƙ
|
Kooraa |
2 |
Ƙ-S |
Kooree |
4 |
S-Ƙ |
Kooroo |
5 |
S-S |
Kooru |
7 |
Ƙ-S |
Misali: (2)
Sayaa |
2 |
Ƙ-S |
Sayee |
4 |
S-S |
Sayar |
5 |
S-S |
Sayoo |
6 |
S-S |
Sayu |
7 |
Ƙ-S |
Misali: 3
Zuba |
3 |
Ƙ-S |
Zubee |
4 |
S-Ƙ |
Zubar |
|
S-S |
Zuboo |
6 |
S-S |
Zubu |
7 |
Ƙ-S |
Abun lura a nan shi
ne, masanan suna ƙaddara cewa waɗannan aikatau daga saiwa guda kamar: koor ->
kooraa, da say -> sayaa da zub-> zuba. Daga nan ne za a tsirarda dukkan
sauran azuzuwan da ma'anoni makusanta juna. Bayan haka suna ganin aikatau na
asali (basic meaning) sukan ƙare ne da -aa ko -a, za a iya jingina
wa tsirarrun azuzuwan (Deriɓatiɓe grades) wanann ma'ana.
Misali:
Ajin Aikatau |
Ma'anar Ajin
aikatau |
0-3 (A da B) |
Ma'anata asali (basic meaning) |
4 |
Cikar ma'ana. |
5 |
Haddasau. |
6 |
Halartau / Aikin ya fukanto aikau. |
7 |
Kammalau/ Kyautatu. |
A nan kamar yadda aka
gani a sama, akwai kamanci ta fuskar ma'ana a azuzuwan kamar yadda masanan biyu
suka kira kowanne aji da ma'anar da ajin yake ɗauka a ra’o’in nasu.
3.2 Kammalawa
Wannan babi kamar
yadda aka gani ya duba ayyuka ko ra'o'in biyu na Parsons (196) da na Newman
(2000) ta fuskoki mabambanta, inda ya fito da irin kamancin da ra'o'in suke da
shi tare da ƙoƙarin ba da misalai waɗanda suke nuna hakan a zahiri. A takaice babi
ya kamanta mana ayyukan duk da irin tazarar da ayyukan ke da shi na tsawon
lokaci da kuma Sauye-Sauyen da aka samu kasancewar ayyukan ba mutum ɗaya ya yi su ba.
BABI NA HUƊU
Bambancin
4.0 Gabatarwa
Babin da ya gabata
babi na uku ya fito da kamancin da ra'o'in na masanan biyu
ke da shi , sannan ya yi ƙoƙarin bin hanyoyin na nazarin harshe domin bayyana
irin kamancin ra'o'in wato na Parsons
(1960) da Newman (2000), tare da fito da misalai mabambanta.
A wannan babin kuwa
duk da irin kamancida ayyukan ke d shi, hakanbai hana a sama kuma
bambance-bambance a tsakaninsu b. Wannan babi zai mayar da hankali ne wajen
zakulo irin bambance-bambancenda ayyukan biyuke da shi ta fuskoki mabambanta.
4.1
Bambanci Ra'in Newman (2000) Da Na
Parsons (1960) Game Da Azuzuwa Aikatau an Hausa.
Duk da cewa masana da
dama sun nazarci aikatau na Hausa ta
fuskoki daban-daban, hakan ne ya
haifar da ra'o'in mabambanta game da aikatau na Hausa. Irin waɗannan masana sun haɗa Parsons da Newman, waɗanda ake ganin su ne
suka fi sauran masanan kwankwance aikatau ɗin na Hausa yadda ya dace.
Parsons (1960) ya ya
gabatar da nazari a kan aikatau na Hausa, inda ya yi la'akari da karin sauti da
waslin gaɓar ƙarshen kalma ya raba
aikatau ɗin zuwa hargida
bakwai (7). Daga baya shi ma Newman (2000) ya ga ya dace ya sake nazartar
aikatau na Hausadomin fito da wasu abubuwan da yake ganin ba waiwaye su ba. Newman ya gabatar da nasa aikin, ya raba
aikatau na Hausa daga sifili har zuwa aji bakwai (0-7) tare da wasu Azuzuwan
masu harrufa kamar (3A) da (3B) da kuma (5D), wanda hakan ya bambanta ra’in
biyu. Kenan idan aka lissafa sai a ga azuzuwan sun kai har goma sha daya (11).
4.1.0 Adadin Azuzuwan
Aikatau Na Hausa
Kamar yadda bayani ya
gabata duk da kasancewar Parsons da Newman
sun raba aikatau zuwa azuzuwa ta yin
la'akari da karin sautin da wasalin gaɓar ƙarshe, hakan bai sa ayyukan sun zama ɗaya ba . Shi Parsons (1960) ya raba azuzuwan
daga (1-7). Shi kuwa Newman ya raba ne daga (0-7) tare da wasu azuzuwan masu
harrafi kamar (3A) da (3B) da kuma (5D), wanda hakan kenan ya bambanta ra'o'in
biyu.
Misali:
Newman (2000) ya samar da ajin sifil (0)
Aikatau Ajin sifili (0)
aikatau ne waɗanda suka kasa shiga cikin
azuzuwan Parsons na aikatau, Saboda aikatau ne masu gaɓa ɗaya. Newman ya ware
wasu ya sa su a aji na daban da ya kira da (Grade Zero). Dalilin da shi Newman
ya bayar shi ne , waɗanna aikatau
sun yi tarayya ne ta fuskar
tsarin sautin da kuma yadda suke samar
da suna ɗan Aikatau ta tsawaita wasalin da kuma
karin sautin faɗau maimakon -waa (S). Dukkan aikatau ‘yan ajin sifili so-karɓau ne.
Misal: (a)
Shida daga ciki sun
ware da -i da karin sautin (s)
Bi ji fi
Ci
ƙi yi
(B) Guda biyu sun ƙare da dogon wasalin
-aa
Jaa da
shaa
(C) Guda biyu sun ƙare da dogon wasalin
-oo
Soo da
yoo/woo
(D) Guda huɗu masu gaba biyu ne
da karin sautin (S-Ƙ) wanda gaɓar farko akan sama wasalin -i, a kuma gaɓar ƙarshe -aa (BiBaa)
·
Biyaa Kiraa
·
Jiraa Rigaa.
Aikatau Ɗan Aji Uku (3A)
Shi ma wannan aji
Newman (2000) ya samar da shi ne domin wasu kalmomin aikatau da wanda Parsons
(1960) ba su da gurbi a tsarin azuzuwan na shi. Irin waɗanna aikatau suna da
gaɓa biyu ne da karin
sautin sama-sama da gajeren wasalin a ƙarshe kalma na -a.
Bayana haka suna da nannauyar gaɓa a farko .Misali:
·
Buuya girma saura farga
·
Kwaana suuma
tsiira
·
Ƙaura
kuuka tsuufa tuuba.
Aikatau Ɗan
AjiUkuB (3B).
Wannan ajin yana daga
cikin azuzuwan da Newman (2000) ya samar wa wasu kalmomin gurbi wanda ba su da
gurbi a tsarin Parsons. Saboda suna da
karin sautin sama-ƙasa da gajerun wasalin gaɓar ƙarshe na -i/ -u / -
a. Sannan dukkansu aikatau ne masau gaɓa biyu kuma ƙi-karɓau ne. Misali:
·
baaci gudu ɓata
·
yini
/wuni haifu/
hu mutu
·
faadi taashi .
Aikatau Ɗan Aji Biyar D (5D)
Newman (2000) ya
samar da wanann azi ne don akwai kalmomin aikatau na karin harshe wandanda ake
ake amfani da su a daudaitacciyar Hausa.
Aikatau ne da suke da karin sautin (S-Ƙ) sannan suna ƙarewa da gaɓar -daa wanda suke da
ma'ana daidai da aikatau ɗan aji biyar (5).
Misali.
·
Gaidaa maidaa
·
Fiddaa zubdaa
·
Badaa. tadda
A takaice waɗanann azuzuwan sun
bambanta ayyukan guda biyu, domin a aikin Parsons (1960) babu azuzuwa masu
tsarin irin na waɗanan kalmomin aikatau,
waɗanda Newman ya yi
musu gurbi a nasan azuzuwan.
4.1.1 Aikatau Fa nɗararru (Irregular Verbs)
Ta fuskar irin waɗannan aikatau da
kowannensu ya kira da (irregular Verbs) wato aikatau da
suka ƙi shiga cikin tsarin azuzuwa da kowannensu ya samar.
Parsons (1960) ya
kira irin waɗannan aikatau ne da
fanɗararru saboda ba su
shiga cikin tsarin azuzuwa nasa ba. Iri waɗannan aikatau shi kuwa Newman (2000) ya samar
musu da gurbi ko a cikin azuzuwan nasa na aikatau na Hausa. Misali.
A wajen Parsons
aikatau ɗin da Newman ya kira
da 'yan ajin sifili (0) kamar:
Yi
ji
shaa
kiraa
fi
bi jaa
jiraa
Ƙi soo
rigaa
ci yoo/woo
biyaa
Duk waɗannan aikatau ne 'yan
ajin sifili (0). Haka kuma aikatau da Newman (2000) ya kira da aji uku (3A da
3B), duk fanɗararru ne a wajen
Parsons (1960). Misali:
Newman (2000) Aikatau
(3A). Parsons (1960) Fanɗararru Aikatau (irregular
Verbs)
·
buuya
girma saura
·
Kwaana suuma farga
tsiira.
·
Ƙaura kuuka
tsuufa tuuba.
Aikatau ajin (3B):
·
baaci faadi
gudu
·
Haihu taashi
mutu
·
Yini ɓata.
Da sauran kalmomin
aikatau da suka saɓa wa tsarin azuzuwan
nasa, su ne ya kira da 'yan togiya (Irregular Verbs).
Shi kuwa Newman
(2000) cewa ya yi, aikatau yan togiya su ne waɗanda ba su da tsarin irin na saura
kalmomin da suke tafiya da tsari ɗaya. Sannan irin waɗannan aikatau duka-duka
guda goma ne (10). Ga su kamar yadda ya kawo.
·
Ganii kusa kau 'yan/ 'yam. (S)
·
Barii
(S-Ƙ) zama
baa/ bai
·
Sanii
(S-Ƙ) hau
zoo.
Ke nan wannan ya
bayyana man irin bambancin da ra'o'in biyuke da shi a kn irin waɗannan aikatau waɗanda kowannensu ya
kira su da (Fanɗararru).
4.2 Kammmalawa
Kamar yadda aka gani wannan babi ya yi ƙoƙari ya Kwatanta ra'o'in biyu na Parsons (1960) da na Newman (2000), domin fito da kamanci da kuma bambance-bambance da yake tsakanin ra'o'in. Sannan ya sake duba aikatau da masanan suka kira su da fanɗararru, inda ya fito da bambancin ra'ayi da masana ke da shi ta wanannan fuskar.
BABI NA BIYAR
Kammalawa
5.0 Gabatarwa
Babin da ya gabata ya
yi ƙoƙarin fitowa da iri
bambance-bambance da ayyukan biyu ke da shi duk da cewa a kan abu guda suka yi nazarin.
Wannan babi zai yi ƙoƙarin takaita ko naɗe dukkan abun da aka gudunar ne a sauran
babukan da suka gabata. Sannan a wannan babin akwai kammalawa wanda zai yi
takaitaccen bayani a kan aikatauda azuzuwan aikatau. Haka kuma zai kawo shawarwari da za su
amfanar da sauran masu sha'awar fagen da sauran masu ruwa da tsaki.
5.1 Nadewa
An gudanar da
wannan bincike ne a kan Kwatancin ra'o'in biyu na Parsons (1960) da na Newman (2000), binciken ya yi nazarin ayyukan biyu domin
gano kamanci da bambancin da yake tsakanin
masanan biyu ta fuskar nazarin
azuzuwan aikatau na Hausa.
A babi na farko,
binciken ya yi ƙoƙarin gabatarwa da kawo dalilan wannan aiki da
muhimmancinsa da manufar gudunar da binciken.
Haka kuma ya kawo hasashen binciken da hanyoyin da za a bi wajen gudanar
da binciken.
A babi na biyu kuwa,
ya yi waiwaya ne a kan ayyukan da suka gabata a wannan fage na aikatau daga
masana da sauran masu nazari. Inda ya kawo ra’o’in masana game da kalmar aikatau
na Hausa da kumar yadda suka kalli kalmomin aikatau ɗin suka raba su.
Babi na uk aikin ya
yi ƙoƙarin fito da kamanci
da yake tsakanin ra'o'in biyu na Parsons (1960) da Newman (200), kamar yadda
taken binciken ya nuna. Babin ya yi ƙoƙaribin wasu matakai
na harshe wajen nuna irin kamancin da suke da shi ta waɗannan fuskokin, Domin
ganin an fitar da lauje cikin naɗi.
Babi na
hudu kuwa, ya yi bayani ne dangane da irin bambance-bambancen da ra’o’in biyu ke da shi, ta fuskoki
mabambanta. Babin ya bambance su ta yawan azuzuwan aikatau da kuma aikatau da
suka fanɗare tare da misalai
ga kowanne ra’i daga ciki.
A
wannan babi kuwa, wato babi na biyar, ya naɗe duk saura babin ne da suka gabata, domin
takaitawa da tattaro abun da sauran babin suka ƙunsa. Bayan haka
babin ya y iƙoƙari ya fito da abun da binciken ya gano. Sannan kuma ya
ba da shawarwarin da ya ga ya dace a bayar musamman ga masu sha’awar gudanar da
Nazari a wannan fage na aikatau na Hausa.
5.2 Kammalawa
Wannnan aikin da aka
gudanar ya yi ƙoƙarin nazartar ayyukan biyu ne. Domin fito da iri kamanci da bambancin da
suke da shi. Aikin ya yi ƙoƙari wajen yi kyakkyawan nazari a kan ra'in Parsons (1960)
na aikatau. Haka kuma aikin ya sake
nazartar aikin Newman (2000). Bayan haka aikin ya yi ƙoƙarin bayar da misalai
wanda za su sauƙaƙa fahimtar masu nazarin aikatau.
Wannan aiki ya yi ƙoƙarin ya kwatanta
ayyukan biyu, a inda ya fito da kamanci da yake tsakanin ra'o'in biyu a zahiri.
Sannan aikinya sake fito da bambance-bambance da ra'o'insuke da shi a
tsakaninsu. A takaice wannan aiki ya gano cewa aikatau na Haus, masana sun yin
amfani da ilimin rassan nazarin harshe wajen raba aikatau zuwa azuzuwa. Bayan haka
kuma ya gao irin kamanci da bambancin da yake tsakanin ra’o’in biyu ta fuskar
yawan azuzuwa aikatau da Karin sauti da ma’ana da tasrifin kalma da ginin kalma
da gini jumla.sannan kuma ya gano aikatau waɗanda suke fanɗararru da masanan suka sama saɓani a kansu kamar
yadda aka gani.
Bayan
haka, aikatau ya rabu zuwa gida biyu, da yan asali wato ajin (0-3) a matsayin
ma’ana ta asali. A aji na (4-7) su ne rukunin tsirarru, masu dauke da tsirarrun
ma ‘ana. Ta fuskar karɓau kuwa akwai so-karɓau da ƙi-karɓau. Inda akan sama
so-karɓau ne a ajin (0, 2 da
5), wanda hakan ke sa a sama sigogin (A,B,C,D). Aikatau ƙi-karɓau kuwa akan same su
ne a ajin (3, 3A, 3B DA 7), saboda haka ake samunsigar (A da D). Ta fusaka
ma’ana kuwa, bincike ya gano kowanne tsirarren aji yana da ma’anata musamman da
ya keɓanta da shi.
5.3 Shawarwar
Masu iya magana kan
ce, 'Mai shawara aikinsa ba ya ɓaci.' Lallai wanna zanɓe haka yake. Wannan dalilin ne ya sa aka ga
ya dace a bayar da Shawarwari kamar haka:
Akwai buƙatar ɗalibai masu naɗari da su riƙa zage dantse wajen
gudanar da bincike da ya shafin wannan fage na Harshe, musamman ma wannan fage
na Nahawun harshen Hausa. Domin kuwa har yanzu akwai ɗinbin ayyuka wanda ya
kamata a ce an nazarce su, amma har yanzu suna nan ba yi ba su ba.Misali
:kwayar ma’ana a azuzuwan aikatau na Hausa,
ko samuwar suna ɗan aikatau daga wasu azuzuwan aikatau na Hausa. Ko kuma
ma’ana a azuzuwan aikatau, da dai sauran su.
Akwai buƙatar malamai musamman
na manyan makarantu su sake waiwayan wannan fanni na harshe fagen aikatau na Hausa, don gudanar
da nazarce-nazarce da za su sa a samar da isassun kayan karatu ga masu
sha'awar fannin. A gaskiya akwai ƙarancin litattafai na
wannan fage musamman ma waɗanda ka yi su cikin harshen Hausa.
Haka kuma yana da
kyau malamai su riƙa ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa da kwadaitar da su game da
nazari wannan fanni na harshe. Domin a yau ɗalibai da yawa suna gudun wannan fage na
harshe, duk da mahimmancinsa. Ko da yake an ce, "A rashin tayi, akan bar
arha".
Daga ƙarshe ina bai wa 'yan
uwana ɗalibai shawara
musamman masu nazarin harshen Hausaa manyan makarantu mutum damar gudanar da
bincike a fagen harsuna, kasancewar ilimi ne na baki-ɗaya.
MANAZARTA
Abdullahi
I.S. (2012) Sauye-SauyeA Wasulan Ƙarshe Na Kalmar
Aikatau 'Yan Ajin Biyu A Zazzaganci. Kundin digiri na farko, Sashin Harsuna da
Al'adun Afirka, Tsangayar Fasaha, Jami'ar Ahmad Bello, Zaria.
Abraham
R.C (1958) Dictionary of the Hausa
Languages. London Hodder and Slaoughton Limited.
Bargery G. P (1934) A Hausa -English Dictionary Sand English-Hausa Vocabulary: Classification of
Verbs. Londa Oɗford University Press.
Galadanci
M.KM (1976) An Introduction to Hausa
Grammar. Ibadan; Longman Nigerian Limited.
Mcintyre
J.A. (2008) Regular and Irregular Verb in Hausa an Alternatiɓe to the Grade System. Afrika
and Ubersee, Band pg. 88.
Muhammad
(2016) Gudummuwar F.W Parsons A
Aikatau Na Huasa. Kudin Digiri na Farko, Sashin Harsuna da Al'adun
Afirka, Jami'ar Ahmad Bello Zaria.
Muhammane
L.A (1992) Aspectsof Hausa
Morphosyntaɗ In Role and
Reference Grammar. Ph.D Thesis.
Newman
Paul (2000) The Hausa Language 'An
Encyclopedic Reference Grammar. New Heaven Yall.
Parsons
F.W (1960) The Verbal System In Hausa.
Und
ubersee 44:36, Journal.
Salisu
N. (2011) Hausa da na Inglishi.
Kundin Digiri na Farko, Sashin Harsunan Kwatancin Ɗafi da Saiwar Harsheen da Al'adun Afirka, Tsangayar Fasaha, Jami'ar
Ahmad Bello, Zaria.
Skinner
N (1977) A Gramma of Hausa. Norther
Nigerian Publishing Company.
Tanimu
D (2012)) Ideophonic Verb in Hausa. Kundin Digiri na
biyu, Sashin Harsuna da Al'adun Afirka,
Jami'ar Ahmad Bello Zaria.
Zaruuk
(2005) Aikatau A Nahawun. (Unpub.
book). ISBN 9782528. 04-8.
Zaruuk
R.M (1996) Aikatau A Nahawun Hausa.
Institute of Education Ahmadu Bello University press Zaria.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.