Labarin Tafiyar Alhaji Audi Howeidy Kasar Italiya

    Labarin Tafiyar Alhaji Audi Howeidy Kasar Italiya
    Wata shekara lokacin yana Sakataren gwamnatin Jihar Kano, sai Alhaji Audi Howeidy ya ziyarci London don hutu da aiki. Kodayake a tikitinsa an hada da ziyarar Rum, babban birnin Italiya, amma sai ya janye wannan É“angare na tafiyar saboda rashin guzuri.
    Rannan sai wani tajiri dan kasuwa a Kano, ya kai masa ziyarar ban girma a Otel dinsa, suna hira, sai tajirin ya ce ai jiyan nan ya dawo daga Rum. Alhaji Howeidy ya ce, 'Mhm! wallahi ni ma ba don rashin guzuri ba, da na je. Har tikiti na sayo tun daga Kano.' Da jin wannan, sai tajirin ya ce, 'Kash! Ina ma na zo da canji mai yawa ai da na ba ka ranka ya dade, ka je ka gano wannan birni mai tsohon tarihi.' Howeidy ya ce, 'A a, babu komai kada ka damu wallahi, domin na riga na janye tafiyar daga shirye-shiryena'. Duk da haka, sai tajiri ya sa hannu a jakarsa, ya dauko kudin Italiya yana kirgawa. Da ya gama, sai ya mikawa Howeidy ya ce, 'Wallahi, ranka ya dade ragowarsu kenan. Dubu tamanin ne da kadan ba yawa'.
    'Dubu nawa?!' Howeidy ya tashi zaune. 'Aaaa!, ai sun isa yaro. Kai! amma fa na gode. Allah Ya yi maka albarka. Haka fa.' Tajiri zai yi magana, Howeidy ya sake yanke shi da godiya da shi-albarka. Bayan dan Iokaci kadan, sai suka yi sallama, Howeidy ya raka shi har kasa, ya ce kuma da sun koma gida Kano, lallai ya zo ya same shi a Ofis. Tajiri dai ya yi bankwana ya tafi yana mamaki da fatan ba dauka ya yi masu yawa ne ba.
    Da dawowar Howeidy daki, sai ya buga waya kamfanin Jirgin Italiya, ya kama kujera zuwa Rum washegari da safe, gari na wayewa, ya kama hanya ya tafi ya shiga jirgi, sai Rum, da Lira dubu Tamanin a aljihunsa, yana ta busar iska da dokin zai je ya yiwa Rum kaca-kaca. Da isarsu, sai ya umarci direban Taksi ya kai shi babbar Otel a tsakiyar birnin Rum. Haka kuwa, aka kai shi wata kasaitaceiyar Otel, irin ta sarakuna da manyan tajirai. Saboda kasaitar wannan Otel, su ne suke biyan kudin Taksi, sannan su sa a cikin hisabin karshe.
    Saboda haka Howeidi bai san ma abinda aka biya taksi ba. Shi dai kawai ya cike takarda an kai shi wani kasaitaceen daki, wanda aka ajiye shaye-shaye da 'ya'yan itatuwa da na kwalama masu dadi a cikinsa, don kawai maraba da babban bako. Howeidi ya ga duk wadannan, ya ce, 'Haba malam! A nan ake cin duniya, in dai da kudinka.' Ya cire kayansa ya yi wanka, ya fito ya tasamma kayan kwalamar nan, ya cika cikinsa tam, ya kishingida. Alhaji bai farka ba sai bayan Magriba. Ya tashi ya rama sallolinsa ya shirya ya fita don ganin gari da kuma 'yan saye-saye, irin nasu na masu kuru. Ya fita yana takama, ya nufi kantuna.
    Dama wannan Otel a tsakiyar kantuna take, saboda haka sai Howeidy ya taka da kafa ya fara zagayawa. Yana tafiya a hankali, irin tafiyar masu kuru, yana leka tagogin kantuna yana kallo. A hankali, sai ya fara Iura da yawan kudaden da suke rubutawa kayansu, amma saboda yawan ya faskara, sai zuciyarsa ta raya masa a wasu kwabbai suke lissafinsu, alhali shi famfamai yake dauke da su, can sai ya shiga wani kanti ya fara duba wani takalmi. Da ya juya wajen farashin, sai ya ga an rubuta Lira 220,000. Sai ya kirawo mai kanti ya ce, 'Me aka rubuta a nan?' Mai kanti ya ce Lira dubu metan da shirin'. Howeidi ya ee, 'Lira?!!!' Ya sa hannu a aljihunsa ya dauko takarda guda wadda aka rubuta Lira 10,000 ya nunawa Mai kanti ya ee, 'Irin wannan?' Mai kanti ya ce, 'Irin wannan ashirin da biyu ce za ta sai maka wannan takalmin'. Howeidy hannu da baki na rawa, ya sake tambaya, 'Lira nawa ce a fam dayar Ingila?' Mai kanti ya ce, 'Lira dubu da dari Shida'.
    'Lahaula wala Kuwati! Amma wannan shegen yaro ya cuce ni.' Inji Howeidy da Hausa. 'Me ka ce?' Mai Kanti ya tarnbuya. Howeidy bai tsaya ba shi amsa ba, sai kawai ya ajiye takalmi ya fita da saurin gaske ya doshi Otel dinsa, yana salati yana cewa, 'yau na shiga uku. Takalmi ma kenan mai araha ya ninka kudin aljihu na gida uku, ballee kudin Otel irin wannan? Lahaula wala Kuwati! Ina zan sa kai na a wannan Kasa ta Mafiya?'
    Ya iso Otel, nan da nan ya zarce teburin masu karɓar baki, jikinsa na rawa. Wata yarinya ta gaishe shi tana tambayarsa, ko yana son a shirya masa zuwa wani Kulob ne da daddare. Ya ce, 'A a. Nemo min gidan ambasadan Nigeria a nan Kasar'. Ta ce, 'Ai mu ma za mu iya nuna maka gari', tana zaton abinda yake so kenan. A fusace da Hausa, 'Don ubanki ki nemo min ambasadan Nigeria na ce. Yau ga 'yar banza.' Da ya fahimei ashe Hausa ya yi mata, sai ya maimata mata da turanci, amma ba zagin. Da ta ga ransa a ɓace yake, sai nan da nan ta dauko littafin waya ta nemo lambar gidan ambasador. Aka ei sa' a kuwa aka same shi.
    Howeidy ya fara bayanin ko waye shi da kuma halin da ya ke ciki. Kodayake ba su san juna ba, amma yanzu Ambasadan ya san Howeidy babban mutum ne. Saboda haka nan da nan ya yarda zai zo ya same shi a Otel. Howeidy ya yi ajiyar zuciya, ya ajiye waya ya tafi ya sami kujera ya zauna ya fara jira. Yana zama sai yaron Otel ya zo ya tambayi ko yana son shayi. Howeidi ya kore shi da isharar hannu; 'Tafi ka bani gu. Shayin banza!' Sannan ya mai da hannu kuncinsa cikin tagumi yana ta danasanin wannan abin takaici da ya sa kansa ciki. Can sai ga Ambasada ya zo yana duddubawa, sai ya hango shi a zaune cikin tagumi. Ya hanzarto ya zo Suka gaisa suka zauna, suka fara maganar matsalar. Ambasada ya kyalkyale da dariya, ya cewa Howeidy, 'Ai ba komai, ranka ya dade, sai ka karasa hutunka ko da kwana uku ne, za mu biya'.
    Howeidi ya ce, 'Na gode. Amma wallahi gobe da jirgin sassafe zan koma London. Ku biya kwanan daya ya isa. Da na je Kano za mu aiko maka da kudinku.' (Allah ya jikan Alhaji Audi Howeidy)

    Daga:
    Malam Mustapha Aliyu Jos
    Filin Alh Mamman Shata Katsina

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.