Labarina

    1.
    Wasiƙa a baƙar takarda!
    Ta riske ni a can a kanda,
    An tsaro ta kamar jarida,
    Na amshe ta ina sukuni.

    2.
    Ni a zatona in na duba,
    Zan ga kamannin sahiba,
    Cikin fara'a ban ƙaddara ba,
    ZumuÉ—i na shiga kan gani...

    3.
    Ina fara'a nai warwarewa,
    Rubutu maƙil nai ganewa,
    Ta layin farko nai biyawa,
    A zuciya sai na ji na boni!

    4.
    Na shiga halin É—imuwa,
    Hannayena biyu na rawa,
    Hawaye na ta malaluwa,
    Sanadin ƙunshen bayani...

    5.
    Saƙon Bilkisu kamar haka:
    Ka min so zuciya har baka,
    Ka ba ni kulawa don haka,
    I haƙuri yau ba kai babu ni!

    6.
    An ce tsuntsun SO kan fura,
    Yau ya koma ƙwaryar fura,
    To ɗau haƙuri kar kai bara,
    Na sauya don na É—au gwani.

    7.
    Kai É—an makaranta ni karatu,
    Ƙaramin marubuci mai rubutu,
    Ka gagara share min kumatu,
    Yau wanda na kama bai hani.

    8. 
    Ka iya zance babu ƙarya,
    Wasiƙar SO sai dai su koya,
    Kalami ma ka ba su baya,
    Amma in ba harka da muni.

    9.
    Na ya da wasiƙar tata gefe,
    Duniya na juyi kai na dafe,
    Na ji ni a ƙar sai shafe-shafe,
    Duhu ya maye haske ban gani.

    10. 
    Na ba ta gabaÉ—aya zuciyata,
    A raina ta zama gimbiyata,
    Na yi zaton na samu gata,
    Ashe na yo shuka da rani.

    Aminu Lawan Elder...✍️
    07031212623
    Fajaruddeen

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.