Likita Ba Zai Fifita Tsakanin Marasa Lafiya Ba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh, Allah ya karawa malam imani, tambaya zan yi game da ma'aikata musamman na asibiti. Idan abokin aiki ya zo da Mara lafiya sai ayi anfani da sanayya a sallame shi da wuri alhali akwai waɗanda suka Daɗe a layi, sannan kuma suna cewa wai alfarma ce ta tsakanin abokan aiki, shin ya hukuncin yin hakan, kuma an Shiga hakkin waɗanda suke layi idan har ba a nemi izinin su ba? Allah ya bawa malam damar amsa mana.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam.

    Mutukar yanayin ciwonsu iri ɗaya ne, babu bambancin tsanani ko hauhawar ciwon bai halatta a gabatar da wani Mara lafiya akan wani, saboda kusancinsa da likita, ya wajaba a jera su gwargwadon zuwansu.

    Hukuma ta ɗauki ma'aikaci ne don ya yiwa jama'a aiki, ba tare da nuna Bambanci ba a tsakaninsu.

    Ana biyan Likita ne da kuɗin al'umar da yake yiwa aiki, don haka zalunci ne ya fifita wani sashe akan wani sashen na jama'a, saboda dukkansu matsayinsu iri ɗaya ne.

    Rikon amana yana jawo ci gaban rayuwa.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄��𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.