Ma'anonin Bara Da Roƙo Da Raraka Da Tumasanci Da Bambaɗanci

    Bara: neman abinci ko dai wani kayan masarufi domin rashin wadata ta hanyar bi gida-gida ana  magiya da Allah, Annabi. Mafi akasarin mabarata, to ana alaƙanta su ne da almajirci.

    Roƙo: tambayar wani abu daga wajen wani daban. Ba lallai sai abinci ba, ana roƙo don neman kowane irin abin duniya. Wasu ma sun ɗauki roƙo sana'a, tun da har gadonta ake, ana kiran masu sana'ar da sunan “Maroƙon baka; Ɗiyan ma'abba; Masarta; Bambaɗawa ko kuma Ɗiyan durbai.” Suna gudanar da sana'arsu ne musamman a wuraren aiwatar da bukukuwa, ta hanyar koɗa duk wanda suka ga yana da alamar maiƙo a wurin bikin.

    Raraka: roƙon abu, amma ba kai tsaye ba. Ana dai saka ‘yan dabaru domin samun abin da ake nema cikin hikima.

    Tumasanci: an samo kalmar daga ‘Tumasa’ ne, wato mutumin da ke samun wata fa'ida ta hanyar yin tsegumin wani zuwa ga wani daban. Misali, idan mutum ya san Alhaji wane da Alhaji wane ba su ga-maciji, to sai ya lallaɓo wajen ɗaya daga cikinsu yana aibanta wancan da ba shi nan, duk don wannan Alhaji ya ji daɗi, har ta dalilin hakan ya ɗauki kyauta ya ba shi.

    Bambaɗanci: roƙo ne ta hanyar zuga mutum da zuguguta shi. Ba-banbaɗe (bambaɗawa; jam'i) su ke aiwatar da bambaɗanci. Suna kambama mutum tare da hura mishi kai ta hanyar tula mishi ƙasa (sarar ’yan zamani), har ya tumbatsa ya yi masu kyauta. Kamar dai yadda bayani ya zo a wajen roƙo, bambaɗanci na da alaƙa mafi kusa ne da shi roƙo.
    .
    © Hafiz Koza, 2016
    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.