Ticker

Mafarkin Haihuwar Jariri

TAMBAYA (32)

TAMBAYA 2 na kwanta barchi sai nai mafarkin nahaifi jariri namiji sainaganni agidan iyayena mahaifiyata tamikoman jaririya mace ta ce anban nace wayaban ta ce itama ba ta saniba wata kil kowaye yason kinason diya macen ne saina ansa inata murna nazauna nafara shayar da ita harta koshi naajeta nadau namijin shikuma yaki shan nonon sainikecema mahaifirtawa innakoma gidana yazancema dangin mijina bachin sunga da daya nahaifa,kuma lokacin akwai jinin haihuwa jikina ruwan nono kuma nata zubarman duk yabata man kaya sainaga bayaran ahannuna sai wani abu guda biyu ban iya tantance miye amman naganshi shiba dutaiba shiba tsokaba abudai medan baki jikinshi saina nafarka kuma na kasa mantawa shi ne nace bari nai tambaya. Don girman Allah malam ka amsaman tambayoyina

AMSA

A cikin littafinsa mai suna Fassarar Mafarki, Imam Muhammad Ibn Seerin (Tabi'i kuma dalibin Imam Malik) ya ce:

Mafarkin haihuwa na nufin samun sauqi daga wahala, samun waraka, ko kuma tashi daga gida ko maqota. Haka kuma haihuwa na nufin nutsuwa, hutu, biyan kudin ba shi da kuma tuba ga Allah. Idan mace ta yi mafarkin haihuwar namiji na nufin karshen wahalarta, albishir, biyan ba shi, ko kuma tuba ga Allah

Idan kuma ta haifi ya mace na nufin daraja, daukaka da sauqi. Idan mabuqaci ya yi mafarkin haihuwa hakan na nufin sauqin rayuwa. Mafarkin dan kasuwa ya haihu na nufin asara a kasuwanci

SHARHI:

Na biyu kuma. A fahimtata akwai hakkin wasu akanki. Idan kinsan ana binki ba shi to ki gaggauta biya tun kafin ki koma kabari da hakkin ba shi akanki

Allah ya kiyayemu da kiyayewarsa.

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments