TAMBAYA (31)❓
Dan Allah
malam adaure a amsa man tambayoyina inata tambaya ba amsa wanan babbar damuwace
Fassarar mafarki
Assalamu
alaikum malam barka da wanan lokaci malam ni na kasance me yawan mafarkai amman
ingari yawaye bana iya tuna mafarkin Danai, to Allah yataimaki malam kwanannan
ina yawan mafarki gani awani gida babba mata sun fi ashirin acikin gidan kowace
mace tana mashaa da yar uwarta anata kamo mata takarfi ana maɗugo dasu ina kallo har
abun yakan ban shaawa inji daman ni akemawa sai inga anyo kaina ankama ni sai
susakan suce banda wanan,wayenda suka ki yarda agabana zanga ana fiddo wani abu
aka sansu nace miye wanan aka ce beli ne akacire masu wasu nata ihun basuso da
anfara masu sai suita nishi alamun suna jin dadi to malam saikuma inganni
acikin wani daki kamar kwanar makaranta inata Sallah ina neman tsari ga mutanen
sai suzo kame su tsallakeni dan Allah malam inason fassarar mafarkinnan dan
abun nadamuna.
AMSA❗
A cikin
littafinsa mai suna Fassarar Mafarki, Imam Muhammad Ibn Seerin (Tabi'i kuma
dalibin Imam Malik) ya ce:
Yin fasiqanci
da yaro a mafarki na nufin wahala da dogon bakin ciki. Mafarkin kwanciya da
macen da za ka iya tunowa na nufin za ka samu ci gaba a harkar nemanka.
Mafarkin fasiqanci da tsohuwar macen da baka sani ba na nufin faduwa a
kasuwanci. Kwanciya da matar wani a mafarki na nufin za ka samu ribar kasuwanci
daga wajen mijinta. Mara lafiya ya yi mafarkin yana fasiqanci da mahaifiyarsa
hakan na nufin mutuwarsa saboda anan mahaifiyar tana nufin duniya
Idan mace ta
yi mafarkin tana fasiqanci da yar uwarta mace wadda ta sani to hakan na nufin
za ta sanar da ita sirrikanta, za ta zamo qawarta, ko mabiyarta, sannan kuma za
ta dinga kwaikwayon halayyarta
Idan batasan
ta ba kuma to hakan yana nufin za ta fada cikin tarkon zunubi. Idan matar aure
ta yi mafarkin tana fasiqanci da wata matar hakan na nufin mijinta zai saketa
ko kuma za ta zamo bazawara
Haka kuma
mafarkin fasiqanci na nufin biyan ba shi ko kuma samun nutsuwa a rayuwa. Yin
zina da karuwa a mafarki na nufin son duniya ko kuma samun ribar kasuwanci.
Mafarkin saduwa da Hurul Ayn na nufin karfin imani a addini
SHARHI:
Da farko dai
yakamata ki godewa Allah SAW da ya baki ikon tsallake tarkon wadancan shaidanun
matan masu neman lalata da mata irin jinsinsu
Saiki dinga
yawaita neman tsari daga sharrin qawaye ta hanyar yawaita adduoi da Annabi SAW
ya koyar
Allah ya
kiyayemu da kiyayewarsa.
Amsawa:
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.