𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Na kasance mai
yawan mafarkin tashin alqiyama kuma acikin mafarkin saida naga na tsira, dan
Allah kokasan fassarar abun da mafarkin ke nufi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Gaskiya abin
da fassarar wannan mafarkin ba, nidai ban iya fassarar mafarki ba kowanne iri
domin bankoyi yanda akeba.
Tabbas akwai
fassarar mafarki acikin shari'ar musulunci saidai ba haka kawai mutum zai goge
fuska ya ce yanada kansa amatsayin mai fassarar mafarki ba, Saidai yanda zamani
yagurbace kuma galibi mun ɗauki
mafarki kamar wata al'amara shi ne ya sa kwata-kwata babu mutanen kirki afannin
fassarar mafarki, yawanci saidai madamfara masu cin dukiyar mutane batareda
hakkiba da masu ci da addinine suke riqe da fannin ayanzu awannan zamanin.
Amma tabbas
akwai fassarar mafarki a musulunci kus-kurene kai mafarki kabarshi haka kawai
baka samu malamin Allah wanda ya iya fassarar mafarki yafassara maka wannan
mafarkinba.
Shaik usmanu
Bin fodio rahimahullahu acikin littafinsa ihya'ussunnah ya ce: yana daka cikin
bidi'ar da mutane suka auka cikinta shi ne insunyi mafarki ba sa zuwa afassara
musu mafarkinsu.
Shawara kawai
da za mu iya baki Shi ne: Kilazimci yin Addu'ar da Manzan Allah sallallahu
Alaihi wasallam yakarantar damu dangane da mafarki Maikyau ko mara kyau, domin
Inkikace zaki a fassara miki tabbas zaki wahalar dakankine kawai, addu'ar ita
ce:
Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: idan mutum yaimafarki yaga abun da ya
burgeshi mafarkin yagodewa Allah, sai ya ce: ( Ya Allah ina rokonka Alkhairin
wannan mafarki da Alkhairin da ke cikinsa) Idan kuma mummunan mafarkine saiya
ce: *(Ya Allah ina neman tsarinka daka sharrin wannan mafarkin dasharrin abun
dake cikinsa) Bayan yai tofi abarin hagunsa na hagu. kuma karya bawa kowa
labari.
Sannan lallai
kada kibiyewa rudin Shaiɗan
dangane dagani dakikai amafarkin cewa kin tsira ki godewa Allah akan hakan,
kuma kada yasaki ki saurara wajan biyar Allah dakiyaye dokokinsa saidai kiqara
kaimi da himmah darike dokokin Allah, Allah yaimiki tsari daka sharrin Shaiɗan dakuma sawa kicika da
imani.
Inkika ɗauka keɓance cikin mutane, babu
shakka Shaiɗan ne
zaici nasara akanki yalalata miki imaninki.
kiyi koyi da
Annabawa da salihan bayi da magabata nakwarai, duk da sun san cewa Allah
yaimusu alkawarin su 'yan aljannane hakan baisa sunyi rauniba sunshantake ba,
A'a kara kaimi da himma suke akan biyar Allah, Allah maɗaukakin sarki ya ce:
كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبًا وَرَهَبًا ۖ وَكَانُوا لَنَا
خَاشِعِينَ
Sun kasance
suna rige-rige wajan ayyukan Alkhairi, kuma suna rokonmu dare darana suna masu
saka rai daka rahamar Allah dakuma tsoran Azabarsa, Sun kasance masu tsoran
mune. (Suratul Anbiya: 90)
Tare dacewa Su
Annabawane, Sahabbbaine Allah yaimusu Alkawarin Aljannah tun suna aduniya, Amma
hakan baisa Sun nade kafaba.
Ina kuma gamu
nakusa dakarshen duniya, kuma tare da hakan bamu dayakini ko tabbas akan abun
da muka gani cikin mafarkin.
Ga wasu kadan
daka cikin litattafai na fassarar mafarki kina iya samun malamin Sunnah mai
tsoran Allah tsayayye yabincika yafassara miki mafarkin ki.
Littafin
fassarar mafarki na muhammad Ibnu sireen. Saidai shi malamin zai fada miki cewa
ba a dogara da abun da yake ciki na fassarar mafarkin da ke cikin wannan
littafin da sauran litattafan fassarar mafarkin sai abun da dalili nashari'a ya
nunar ko wani abu dayake nuna hakan amma kada mutum yadogara da fadin wani akan
fassarar mafarki.
Atakaice dai
idan mutum yai mafarki mai kyau yana aikata alkhairi koya kubuta daka wani
bala'i ko macen dabata hai-huwa tai mafarkin Samun haihuwa kota haihu duk wani
mafarki dai na alkhairi mutum zai godewa Allah a kansa yakuma fadawa wanda yaso
cikin mutane.
Amma idan na
sharri ne kamar yanda muka fada mutum zai nemi tsarin Allah daka Shaiɗan dakuma tsarin munin
mafarkin yatofa ahagunsa sau uku, Sannan kada yabaiwa kowa labarinsa wallahu
A'alamu.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.