Magajiya (Hausa Novel)

    💎💎💎💎 MAGAJIYA💎💎💎💎

    (Hot love and romantic story)

    Free page 1️&2️

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    A garin Kebbi garin ya yi duhu sosai sakamakon hadarin daya mamaye sararin samaniya, iska ne yake kaɗawa mai sanyi ya yinda ƙafafu suka ɗauki sosai hadari ya mamaye sararin samaniya tsawa ce ke tashi ga cida anatayi, a kuda yaushe ruwa zai iya faccewa,

    GRA yana ɗaya daga cikin jerun shiyoyin masu hannu da shuri, ku kuma babbar shiyace a cikin garin, domin kuwa babu wata shiya da takai kwatan ta.

    Titi ne shimfiɗe a kan hanyar yayinda shiyar ta yi shiru sosai daman shiyar manya ce domin kuwa manya mutanene a cikin ta duk wani ɗan siyasa mai ji da kuɗi mai ji da mulki izza yana zaune a wannan shiyar.

    Wata kyakyawar budurwa na hango sanye take da wani crazy black da wata karamar riga white mai hannun best kayan sun ɗameta sosai duk wani motsinta sai cikin ta ya motsa gashin kanta yasha attachment black & blue har ƙokunta. . .

    Tafiya take mai haɗe da gudu sosai take nishi alamar ta gaji wajen wata black car ta nufa ƙirar benz ɗan tsagaitawa ta yi tare da buɗe back sit ta ɗauki swam water, buɗe marfin ta yi tare da kafa bakinta makut! makut!! shi ne sautin da ke tashi bata ɗauke bottle ɗin ba har saida ta shanye shi tass, ajiye gorar ta yi tare da shiga motar batayi wata tafiya mai tsawo ba ta yi horn a wani babbab gida mai hawa ukku. . .

    Mai gadi ne ya je ya buɗe get ɗin danna hancin motar ta yi sai wajen da aka tanada domin ajiye motoci tana fita ta nufin cikin gidan kamar yadda ta yi tsammani kuwa haka ce ta faru hawa na ɗayan zazzaune suke both maza da mata wasu nashan sigari wasu kuma na shan shosha wa'insu suna tsaye sai juyi suke ansa speaker sai wakokin turanci ke tashi wasu na zaune ana cha cha. . . .

    Direct wajen speaker ta nufa ta na zuwa kuwa ta kashe kiɗan "wani she gen ne ma tsau tsayin " ya yi maganar a rarrabe sakamakon buguwar da yayi, bai ƙarasa maganar da ya yi niyaba saka makon ganin ta da ya yi bashi kaɗai ba dukkansu domin ba suji shigowar ta ba " Allah ya ja zamanin MAGAJIYA " hannu ta ɗaga mishi tare da ɗaure fuska kamar bata taɓa dariya ba magana ta fara cikin jin ta kaicin su duka. . . . .

    "Wannan wane irin rashin mutumce ne iya shegen har yaka haka haba wallahi duk zan gyara muku zama kun sanni ba mutumci ne daniba, kuna ganin hadari ya haɗu shi ne hadda wani cashewa ko tu kubari idan kunfita waje saiku yi ba dai nan gidan ba ne su kuke ayi mana ruwan sufabulu to ba daniba, ke kuma Limcy ki biyoni” ta yi maganar tana wucewa steps. . . . .

    Shi hawa na biyun babu kowa a ciki. Wadda aka kira da Limcy ce ta tashi jiki ba kwari ta bi bayanta tsit sukayi domin duk rashin mutumce su na MAGAJIYA ya fi nasu domin kuwa duk gata ta yi musu duk yadda sukejin bariki ta dannesu ta shanye. . . . .

    Zaune ta saman bed zama ta yi a gefenta batare da ta ce kumai ba sun ɗau tsawon 5mnt bata ce kumai sai da taja wani gwauron numfashi kafin ta fara magana cikin isa da ƙasaita "ki je ki sanar musu cewa gobe kada wanda yafita da safe idan na tashi akwai magana za mu haɗe a meeting rom" daga haka bata ƙara cewa komai ba ta nufi toilet. . . . . .

    Ganin zaman ba zai yi mata ba ya sa ta tashi domin isar da saƙonta tasan yau ko za ta kwana a nan ne basake magana za ta yi ba tana mamakin MAGAJIYA duk barikinta tana riƙe ibada bata wasa da dokokin Ubangiji ku kaɗan da haka har ta isa gunsu sheda musu saƙon ta yi kafin ta je ta zauna babu wanda ya ce ƙala kuwa da abin da yake tunani cikin ransa. . . . . . . .

    Comments and Share fisabililla

    ✍️Alƙalami ya fi Takobi🗡️

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    Free page 3️&4️

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . . Wanka ta yi haɗe da ɗauro a'lwala fitowa ta yi ɗaure da towel iya cinyarta mirror tanufa stole ɗin cikinshi ta jawo ta zauna mayukka tafara shafe laulausar fatarta da su bayan tagama shafa man wadrob ta buɗe wata ƙaramar rigar bacci ta sa pink colour sai wata hula saƙa ita ma pink katun hijab ta jawo tasa sallaya ta shimfiɗa ta kabarta sallah bayan ta idar addu'o'i ta yi sosai sannan ta ɗauki Ƙur'ani mai girma ta fara karantawa saida ta yi hizib biyu sannan ta kulleshi tare da ajiyewa inda yake hijab ɗin ta cira ta maidashi cikin wadrob ta ninke sallayar ta mayar kwanciya ta yi saman bed ɗinta laptop ta jawo cikin ƙaramar duruwar dake gefen bed ɗin sarrafata ta farayi cikin kwarewa saida ta raba dare sannan ta yi addu'a ta kwanta. . .

    💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

    Kano City

    GRA

    Wani babban gida na gani wanda bantaɓa ganin irinshiba a nan Nigeria ba.

    Gida ne wanda yakai gida tree steps ne amma samanshi anyimishi volconi gidan ya haɗu sosai get ɗin gidan ma kawai abin kallo ne da ganin tarin masu tsaron gidan ka san ba ƙananan mutane accikinshiba.

    Daƙer nasamu hanyar shiga cikin gidan domin duk inda na bi securities ne.

    Wow a shema wajen gidan bakomai ba ne ba ku ina na gidan flowers ne wata ƙofa na gani da alama wadda za ta sadaka da parlourn gidan ce ciki na shiga wani sanyayyen ƙamshi ne ya daki hancina ƙarar AC ne ke tashi a cikin parlourn plastima ce ke ƙara masu jajeyen kunnuwa nata shige da fice ƙarar taku na ji da a nan na fahimci somebody is coming ƙofar na ƙurama ido domin ganin wazai fito.

    Wata kyakyawar mata ce ke sakkowa ahankali fara ce daga ganin matar ka san kuɗi mulki haɗe da izza dattijantaka duk atare da ita.

    Daga ganin ta ba za ta wuce 42 ba amma za ka ɗauka yar'shekara ashirin ce domin hutu daya zauna.

    Daining ta nufa kololin wurin ta buɗe komai yarda ta barshi haka yake girgiza kai ta yi tare da faɗin"wato shi son baici abincinba taya rayuwa za ta yi a haka "

    Ta ƙarashe maganar da nufar wata ƙofa da alama wani part ne tana buɗewa kuwa wani part ya bayyana sosai komai na wurin abin burgewa ne komai milk and golden colour ne.

    Kan bed ɗin ta nufa daya ke dunƙule cikin bedsheet " son!son!!son!! katashi mana haba ko abinci ba ka ciba fa please” ta ƙarashe maganar tana yaye bargon da ya rufa.

    Wani kyakyawan saurayi ne ya bayyana tashi ya yi ahankali ya shiga toilet" kayi sauri ka fito " cewar Momy tana fita daga ɗakin.

    Wanka ya yi ya fito sanye da bathroob fara ƙal subhanallah shi ne abin da na iya furtawa da ganin wannan kyakyawar halitta ta ubangiji.

    Fari ne amma farinshi ya yi sirka da ja ga dogon hancin daya ke tsaye a fuskarshi yana da wani tusar jaki a ka san bakin ji yana da gashi da ka ganshi ka san na fulani ne domin yadda ya sauka har ƙeyarshi ga kuma gyara dayake sha.

    Comments and Share fisabililla

    ✍️Alƙalami ya fi Takobi🗡️

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    Page 9&10

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . "yanzu abin da ka aikata dai dai ne sabida Allah katafi kabar matarka haba wallahi idan hakƙin aure ya kamaka ka shiga uku, ba ka gudun ranar da ubangiji zai kamaka a kan haƙƙin matarka”

    Taƙarashe faɗa tana kallon yadda idanunshi suka wani rine, "To yanzu ni mai na aikata da kullum laifi nane ita bata laifi ku ita haƙƙi ba zai kamataba haba ƙafa fa tasa ta yi fatali da abin da na ce " yakarashe maganar jijiyoyin kanshi na miƙewa da alama abun yana mashi zafi, kwantar da kanshi ta yi kan cinyarta tana shafa kwantaccen suman kanshi cikin tausayawa ta ce.

    "Na sani na san kana haƙuri da Safiya amma ka ƙara don't let angry to control you kawai kai kasauke kuwane irin haƙƙin ta dake kanka kaji” murmushi kawai ya yi domin zama a kan cinyarta yana samu wata nustuwa haka ta dinga kwantarmishi da hankali sai azahar yabar part ɗin yanufi sashen iyalinshi.

    Kebbi

    Sai 11am ta tashi wanka ta yi fitowa ta yi sanye da bathrobe fara ƙal hannunta riƙe da ƙaramin towel tana tsani leman kanta gashi ne kwance har ɗuwawunta abin da yaban mamaki ke nan kudai shi ma na doki ne🤔 fuskanta kawai ta gyara batayi wani makeup ba wardrobe tabuɗe wasu set nakaya ta ɗauko Riga da wando pitch colour sai wata sweeter fara bayanta anyi Rubutu da manyan baki aka rubuta "MAGAJIYA” da pitch sosai kayan suka amsheta bell tasama ƙugunta shi ma fari cover shoe's farare tasaka masu ratsin pitch kannan kuwa kamar kullum gyarashi kawai ta yi ta relaxer ya yi wani murɗiya ta zubushi ta yi kyau sosai haka ta fita inda already su Arne sunshirya motoci, mota bakwai suka shirya inda uku sukasa tata tsaka sauran kuma duk yarantane a ciki hakimce ta ke abaya tana duba jarida yayinda Limcy ke zaune a mazaunin mai zaman banza.

    Kumai zaifaru tsakanin Magajiya da controller hmmm bari mu leƙa kano. .

    Kano

    Duk India yabi fadawa zubewa suke haka har ya isa part ɗin kamar kullum abin da ya yi zatu shiyaka sance dan kuwa zaune ta ke kishingiɗe bayi na bautamata kamar wata abin bauta ƙamshin turarenshi da taji ne yasata buɗe yan'idanunta da sauri aiku sai akanshi, tashi ta yi jiki na rawa ta isa inda yake hugging ɗinshi ta yi tana faɗin " haba my heart yanzu shi ne katafi ka shareni yau sati na ɗaya da dawowa fa " tafaɗa cikin shagwaɓa wanin wawan kallo yamata wanda yasata matsawa da sauri tsaki mai suti ya ja kafin yawuce hanyar da za ta sadashi da part ɗinshi .

    Sasai abin da yamata ya baƙanta mata rai gashi ga bayi nan wurin kawai yanke shawarar ta yi bari kawai ta naɗe tabarmar kunya da hauka wani kallo tabisu da shi kafin ta yi musu wata tsawa duk da a ciki akwai sa'ar uwarta " uwarme kuke jira munafukai yan'iska bana gaya muku idan miji na yadawo kubarmin parlour ba shegu"ai kafin ta rufe bakinta duk suka ɓace zama ta yi kafin tafara magana cikin fushi” harni gimbiya Safiya za a walakanta haka wallahi ba kaci bulus ba mtssss " takarashe da dogun tsaki. . . . . . . .

    Comments and Share fisabililla

    ✍️Alƙalami ya fi Takobi🗡️

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    . . . . Motocinsu ba su tsaya ku ina ba sai new prisoo suka nufa already security ɗin wurin sun santa don haka kawai buɗe musu ƙofa aka yi mutane sukayi tsaye wanda suka santa tun ganin motocinta sunganeta kawai jira suke suga wankanta domin tana burgesu ku don yawan taimakonta da na ƙasa da ita da kuma ɗaukar wanka, wanda ba su santaba ko tsaye suke suna jiran ganin fitowar shugaban ƙasa(Na yi nan💃🏽💃🏽).

    Direct bakin office ɗin controller sukayi parkin tuni su Arne sun firfito suna zagaye white car ɗinda ta ke ciki ƙirar Benz7+ da manyan bindigo pitch carpet mai laushi aka shimfiɗa har cikin office ɗin controller yana zaune yaga wani ƙaton basamude aikuwa ya rikice amma da yake namijin duniya sai bayyi ko motsi ba, ta yi five minutes zaune bayan motan kafin taɗauki black gun tasa a ƙugunta cingwam tasa a bakinta kafin ta fito take mata baya sukayi yayinda Limcy ke right hand ɗinta while Arne na left haka har suka shiga office ɗin.

    Ƙaremishi kallo take a walaƙance kafin takai dubanta ga motumin dake zaune har yanzu yana kallon ikon Allah, Baƙine gashi da jiki tumbinan kam ba’a magana sanye yake da uniform ruwan ƙasa ya yi wani balance saman kujera zama sukayi kafin ta yi magana ahankali cikin sanyinta da kuma rashin sabo.

    "Abdullahi Bukar ɗa ga Bukar Adamu da Zulai mai ƙosai miji ga Rashida mai zoɓo uba ga Hakeem and Zulai, Fareda, Maimunatu and others dadiro ga Magajiyar gidan karuwan Bt, na aiko da saƙo kace na zo da kaina to gani na zo su nake kasaki yarana”

    Tun da tafara magana yake kallonta da mamaki domin wannan sirri babu wani wanda yasan da shi abin mamaki saigashi tana faɗa wani murmushi yay kafin ya ce cikin tsageranci " wow beb gaskiya kin haɗu ni Ashe da na yarda da ƙawarki dana yi asara gaskiya kin. . "kafin yaƙarasa yaji wawan mari a gefen fuskanshi na dama before yagama tantance waya mareshi ya sake jin wani a hagunshi magana ta ke cikin fushi " kai harka isa ka san wace ni tabbas zan nunamaka kuni wace ce zanga wanda zai tsayamaka ba dai gwamnati kake taƙama da ita ba kanacin zarafin mutane to yau zan taka gwamnatinka na nunamaka ni izzata tafi ta mulki” tafaɗa ta na hankaɗashi waje.

    Tsakiyar mutanen ta kaishi nan tafara dukanshi baji ba gani saida ta dakeshi son ranta kafin Arne yabata wani abu yana tururi zubamishi ta yi tsakanin cinyoyinshi wata ƙara yafasa ni sumewa ya yi ku ya ohu.

    Already an fidda Ajali kawai suka tafa kafin su shiga motocinsu suna ba za ƙura wasu dadama sunji daɗin wannan aikin wash kuma sun yi Allahwadai da wannan rayuwar, suna gama parking ta FIFA duk mutanen gidan na compound ana jiransu batabi takansuba ta yi ficewarta wanka ta yi kafin ta kwanta ku rigar wankan bata cireba. . . .

    Kano

    Wanka ya yi ya ɗauru Al'wala yarsa jam'i hakan ya sa ya yi a gida abinci Amminshi ta aiko mishi aiko yaci sosai yanagamawa wayarshi ta yi ringin dama yasan wayar aikinahi ce hakan ya sa bai ɓata lokaciba ya ɗauka daga ɗaya ɓangaren akace " hello sir am calling you from S&H company so we have meeting tomorrow please sir we are reƙuesting you to come its very important " ok I will be thare by the grace of god which time " 4:30pm sir "ok" kawai ya ce yakashe wayar dama yanason abin da zaisa yabar garinnan su yake ya yi 1 week kafin yadawo.

    Kafin dare ya yi settling komai har bucking flight ya yi kuma baida matsala da Ammi da kuma Maimartaba yagayamusu aiki ne mai muhimmanci shi ya sa zaije baigayawa Safiya ba saidai idan zaitafi. . . .

    Hmmmm fans koya abun zai kaya tsakanin waɗannan jaruman gadai Magajiya za ta na meeting and Yarima ma kuma desame company koya haɗuwarsu za ta ka sance just follows my pen and see 🥰🥰

    Comments and Share fisabililla

    ✍️Alƙalami ya fi Takobi🗡️

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    Page 13&14

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    KANO

    . . . . . . Tun 10:00am yagama shiryawa domin su yake by 12 ya'isa yahuta before the time of meeting fitowa ya yi sanye yake da wata arniyar shadda gezner ta ya'yan wane da wane ɗinkin zamani blue anyimata aikin black sosai shaddar ta amsheshi black hular ya sa zanna bukar yakarya ta sai wasu black cover shoe's agogon azurfa ne a hannunshi white mai ƙyalli sai ƙamshi yake zubawa part ɗin Safiya ya nufa.

    Zaune ta ke a kan bed ɗinta ta yi wanka ba laifi ta yi kyau ƙamshin turarenshi ne ya'isar da zuwanshi sallama ya yi ciki ciki tamatu a kallonshi harma bata san sanda ya'iso inda take ba hannu ya sa a aljihunshi yaciro kuɗi masu yawa yabata yana cewa.

    "Ni zangi tafiya zantafi Kebbi saina yi one week zandawo" idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta kalleshi ta ce "Haba my heart jiya fa kadawo ku lokaci ba mu samu tareba amma kake cewa za ka sake tafiya kallonta ya yi harzai wuce saikuma yadawo yana murmushi ya ce” to ki yi haƙuri abin ujila ne but i promised you I will call you when I arrived " rungumeshi ta yi cikin jindaɗi tana mishi ardu'a.

    Part ɗin mai Martaba ya nufa dan yasan a can zaisamu Amminshi suna ko zaune suna fira ya shigo da sallama a bakinshi amsawa sukayi suna kallon mafi soyuwa a garesu " har za ka taxi” cewar mai Martaba "eh" addu'a sukayimishi kafin ya wuce mota bakwai ta rakashi airport yana shiga jirgi da wasu security sauran motoci suka kama hanyar kebbi.

    A sauka lafiya Yarima💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽

    Kebbi

    4:30 tafito sanye cikin Gown yar' kanti copee colour iyakarta guiwarta, wadda ta amshi white skin ɗinta tasa hula 👒irin ta good luck lite copee hill shoe's tasa suma lite copee hannunta ɗare da wani diamond which mai ƙalli ta yi kyau sosai haka suka shiga motoci masu rubutun Magajiya a lambarsu.

    Lokaci ɗaya suka shiga hall ɗin mai suna Marshal event tare motocinsu suke shiga ka sancewar get ɗin babbane parking space sukayi parking tun shigowarsu wurin heart beat ɗinsu ya tsananta kusan five minutes da buɗe musu kofar kafin su fito abin kamar haɗin baki tsakiya securities suka sata shi ma haka ta ka sance ahankali yaɗago idanunshi dai dai ita ma ta ɗago nata kallon kallon sukayi kafin ta ɗake kanta saboda wani irin sarawa da kanta ya yi cikin 2second ya ƙare mata kallo ba laifi ta burgeshi amma shigarta sam batayi mishi ba "mtss mace har mace amma batasan mutunci ba kawai saboda iyayenta nada kuɗi sai abarta ta yi yadda taga dama” ya faɗa cikin zuciyarshi kuda yaɗago sunshige.

    Sabanin ganin da yayimata a waje yanzu tasa wata black court mai rubutun "MAGAJIYA” Golden colour mai maita sunan yake ta yi acikin zuciyarahi, meeting ya yi meeting inda manyan baƙi suka gabatar da kansu kamar su Magajiya and Yarima sosai ya yi mamaki ka sancewar wai ita ce mai dukiyar haka kawai yakesun sanin ku ita wace ce, bayan komai ya gudana ne aka sanar anason duk mai share a company gobe around 5pm atafi Sokoto domin ƙarin haske a kan business kowa ya yi na'am haka aka waste bakin parking space rigima tahaɗasu kowa ba zai iya jayewa ɗaya ba a fusace ta fito motar da ta ke hannu tasa ta matsar da motar dayake gefe zaune yake yana kallon abin mamaki mace ɗaya da aikin namiji biyu ko ukku back site tanufa tana knocking kamar za ta fasa glass ɗin fuskewa ya yi ya rage glass ɗin.

    Magana ta ke tana nunashi da yatsa "how dare you block my way who do you think you are this is not Kano is Kebbi my city am a the Ƙueen of here and this is my place don't you there try it again mtssss" juyawa ta yi za ta wuce wani yaronshi ya riƙo mata hannu "ke kin san wayeshi kuwa ke Yar gidan urban waye agarinnan" ya faɗa a fusace mari ta ɗaukeshi da shi kafin ta ce” he don't you their touch me again to hell with who is he and kafin katambayi who is my father ask who iam" tanagama faɗar haka suka ja motocinsu suka wuce, yarima da tun da tafara magana yake tunanin inda yasan wannan fuskar amma yaka sa kawai ya tainki hannun yaronshi riƙe da nata wani irin bugawa zuciyarahi ta yi Wanda bai san dalili ba haka suka wuce abin mamaki area guda suke zaune gidan dake facing nata wanda inkahau balcony za ka iya ganin almost abin da ke gudana a gidan. . . . .

    Free page ya ƙare remain one page kibiya naira dari biyu kacal ki karanta ga number na pls idan baki tashi sayeba karki min magana 07030446917

    Comments and Share fisabililla

    ✍️Alƙalami ya fi Takobi🗡️

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    Page 15&16

    Free page ya ƙare

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . Tana shiga gida tawuce part ɗinta wanka ta yi ta gabatar da salla har isha'i kafin ahankali ta nufi balcony domin tasan duk motanen gidan na can.

    Sanye take da wata sleeping gown iya cinyarta shara shara har pants ɗin jikinta ana gani ta zuba gashinnan har ƙugunta wayarta ce a hannunta ƙirar IPhone 15pro duk suna zaune daga masu shan shisha, cocaine, sigari, dola and other zama ta yi gefen Arne suka tafa wata special shisha ya ɗauku mata tafara zuƙa cikin kwarewa tasha sosai kafin ta kunna wata ƙatuwar sigari kuɗinta kaɗai ya'ishi wani talaka sayan gida.

    Ɗagowar da za ta yi suka haɗa ido da shi wanda yake zaune shi ma a balcony gidanshi sanye yake da T-shirts armless fara sai tree ƙuarter black kanshi sai kyalli mayukka yake shikuma yana operating system yana sipping joes a hankali, tsaf suka Karewa juna kallo kafin a hankali ta harareshi tana busa masa hayaƙin sigari ware idanu ya yi yana nuna ƙirjinshi baki ta murguɗa murmushi ya yi yana mamakin kanshi haka kawai yaji duk wata damuwa tashi tana guduwa a hankali (tab anya).

    Saida suka raba dare kafin kowa ya kwanta washegari around five aka samu matsala jirgin da za su hau yasamu matsala saidai atafi a mota ahanyarsu ta zuwa dayeke ba wanda ya je da mutanenshi mota ɗaya suke irin jeep innan har duhu yafara sauka saura kauye ɗaya sukai sokoto ka sancewar ita ce zaune gidan gaba sanye ta ke da wandon juns sai farar T-shirts falmarat ma ta juns ce ta yi kyau facing Cap ce akanta white mai rubutun Magajiya blue.

    Yana baya zaune sanye cikin court pink colour masu kyau da tsada ƙafarshi na cikin black cover shoes gashin kanshi sai kyalli ya ke.

    A hankali yatsinkayi sanyayyar muryarta tana faɗin" Deriver tsayar da motanna” kowa kallonta ya ke glass ta rage kaɗan ta shaƙi iska warin sigari takeji sosai alamun suna kusantarta " akwaifa matsala " tasake faɗi tana juyuwa suna facing juna wani ne ya ce " wace irin matsala ce "I think its rubber's" zaro idanu sukayi kafin suka fara cewa mukoma kawai taɓa ƙugunshi ya yi yaji ba bindigarshi tsaki ya yi kawai don bashida mafita " yanzu abin da za ayi waya iya halbi yadawo gaba ni zantsaya na yi driving " kowa ya yi shiru " zan yi "kawai ya ce yana dawowa gaba ita kuma ta kuma wurin tuƙi.

    Bindiga taciro a ƙugunta guda biyu ta bashi ɗaya ta riƙe ɗaya kallon bindigan ya ke yana mamakin ina ta samu su domin ba kuwa ake bari ya yi register irin wannan ba muryarta yaji tana cewa” tun da motar ba bulletproof bace kowa ya kwanta " duk kwanciya sukayi "kada kayi harbi daga nesa hakan zai fargar dasu" wuta taba mutar ɓarayin na ganin haka suka fara harbi” bendown and shut " aidasauri ya duƙa yana halbi kwanciya ta yi saman sit ƙafarta ce ke controlling staring while tana shan sigari haka aka yita musayar wuta har suka tsere saida suka shiga cikin sokoto gefe ta yi parking idanunta na lumshewa.

    Mamakin yagama kashe Yarima domin kushi ba zai iya wannan kasadar ba balle mace lallema a mata akwai maza ya faɗa cikin zuciyarahi sauran da suka gama tsorata godiya kawai suke mata juyawar da zai yi ya yi mata faɗa saboda irin gangancin da ta yi da rayuwarta yaga jini a cikinta kuma tana lumshe idanunta " meyasameki miye haka kika aikata "ya faɗa yana rungumota jikinshi wai ashe ana musayar wuta bullet ya shiga cikinta aida sauri yadawo jikinta yana driving sai wani private hospital da sauri aka amsheta emergency aka shiga da ita dakyar aka ceto rayuwarta kowa yatafi amma shi yaka sa tafiya ya bar ta jiyake kamar rayuwarshi tana wannan asibitin ne.  

    Likita ya ce zai iya ganin ta shiga ya yi tanata bacci kaida ganin baccin ka san na dole ne fuskarta ta yi fayau duk taƙara haske zuciyarshi ce ta buga hannunta ya kama ya motsa bakinshi amma ni ma banji komai ba, wani gado dake wurinnan ya kwanta wayarshi ya ɗauka wata lamba ya kira ana ɗagawa ya ce " sunake na san komai gameda "MAGAJIYA” Idan na ce komai to ina nufin komai "kawai yakashe wayarshi yana kwanciya bacci ya ɗauke shi. . .

    A firgice ya tashi sosai ya shiga damuwar rashin mafarkin daya saba hakan na nufin wadda yake nema na kusa da shi dai dai nan tafara buɗe idanunta. . . . .

    End End End

    Free page ya ƙare na san za ku so sanin waɗannan abubuwan

    *Wace ce Magajiya

    *Wace yarinya yarima yake nema

    *Wa yake mafarki da ita

    *Fuskarwa yake gani a fuskan Magajiya

    *Su waye iyayen Magajiya

    *Ya aka yi ta samu wannan Uwar dukiyar

    *Mai zai faru idan ta buɗe idanunta

    Ki biya naira ɗari biyu kacal ki karanta

    Ga mai nema, ya tuntuɓi wannan number

    07030446917

    Comments and Share fisabililla

    ✍️Alƙalami ya fi Takobi🗡️

    Taku har kullum
    Rukee Sauwa

    Magajiya (Hausa Novel)

    Paid book 200 naira only💎

    Mallakar
    Rukayya Buhari Sauwa
    (Rukee Sauwa)💎

    Ga masu buƙatar normal group za ki biya naira ɗari biyu kacal. Idan katin waya ne, za ki turu MTN a wannan number 07030446917. 💎

    Idan kuwa transfer ne za ki tura ta wannan Bank.

    Account number
    3057513094
    Account name
    Rukayya Buhari
    Bank name
    Polaris Bank. 💎

    Sai ki yi screenshot ki tura ga wannan number ta sama👆

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.