Ticker

Makauniyar Shari'a [Kashi na 2]

Ya Allah ina godiya da bisa dukan ni'imominka a gareni. Yanda na fara Lafiya ka ba ni ikon gamawa Lafiya. Alkhairan da ke cikinsa ka ba ni ladansa, sharrin da ke ciki ka yafe min.

Allah ka dauka Alkalamin marubuta a duk in da suke

Gaisuwa ta musamman gareku na hannu dama ta.

  • Besty (Sarat Alkasum)
  • Maman Amatullah
  • Ummu shkura
  • Fadila Sani Bakori
  • Maman Sharifa
  • Mamashu
  • ABBA Yakubu
  • Dan Salma
  • Da Autan Jarumai.

Waɗanda ban samu damar kiran sunansu ba, duk ina mika sakon gaisuwata a gare ku.

Yayyena abun Alfaharina

  • Hadiza
  • Hussaina
  • Hassana
  • Maryam

Gaisuwa ta mussaman gareki

Anty Zulai, mutan Kano, surukar Auta na.

Jarumai Writers Association, marubuta masu aiki da Jarumta wajen Fadakar da Al'umma

MAKAUNIYAR SHARI'A

MAKAUNIYAR SHARI'A

IKILIMA ADAM (Kyauta daga Allah)

09069080725 ko +22953726162 (Whatsapp kaɗai ban da kira)

Marubuciyar da ta nishaɗantar da ku a littattafanta kamar haka:

  1. Kai ka ja wa kanka
  2. Kanwata
  3. RAI DAYA (Jan Za ki)
  4. RUDANI (mai tafiya daukan rai)

Da sauran su.

Yanzu ga ni ɗauke da sabon littafina mai suna MAKAUNIYAR SHARI'A

SHAFI NA BIYAR

TALLA! TALLA!

Marubuciyar nan taku Sarat Alƙasum wacce kuka fi sani da (Maman Nusaiba) wadda ta baje basirarta ta nishaɗantar da ku a cikin littafanta kamar su : Amir da Amira, Aljanar Jarumai, Hafsat, Ƙaddara ce, Tani da Manu, Rayuwar ma'aurata, Sumaiya baiwar Allah, Aljanar Gidanmu, A maƙabarta ne, ABBA NE, Fa'ima.  Yau ma ga ta ɗauke da sabo zazzafa mai suna A HAKA NAKE SON SHI Littafin da ya ƙunshi abubuwa daban-daban zalunci, makirci, cin amana, zallar tsagwaron soyayya mai ratsa zuciyar mai karatu, da sauran su. Ka ku bari a baku labarin wannan kayataccan littafin.

Littafin A HAKA NAKE SON Na kuɗi ne normal ~N~ 300 vip ~N~ 500 ne.

Za ki tura kuɗin ku kai tsaye ta wannan banki.

Account number 0003187186

Name account, khadija Salisu

Name Bank, JAIZ Bank

Domin Ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan number +966577675904

Cikin tsananin mamaki take kallon Matar da ta bata magani tasha a Kauyen Daguzau, lumshe idanunta tayi, sannan ta kara bude su ahankali, stil dai itadin dai take gani da murmushi a kan fuskarta.

Bude murfin motar matar ta yi ta fito cikin shigarta na doguwar riga habaya baki mai adon tsone ta yi ronlin kanta da bakin gyale. Numfashi ta fesar cikin rawar murya da zallan mamaki ta ce, " Amatullah kece a nan gun wa kuka zo a nan Garin?. " shiru ta yi tana sauraren amsar daga bakin Amatullah da ta tsura mata idanu.

Amatullah dukar da kanta kasa tayi, idanunta na kallon kasar da ke kasa, sannan ta kallon gefen titi yanda motoci ke safa da marwa, kamar ba za ta yi magana ba ta ce, " yau mu ka zo kuma anjima za mu koma, zan tafi inda aka aikeni. " ta yi maganar tana ƙoƙarin wuce ta.

 Jin an kamo hannunta ya sa ta saurin waigowa suna face din juna, ahanzarce ta sauke idanunta akasa, gabanta tsananta bugawa ya ke yi gab-gab da karfin tsiya.

 Tsinkayar muryan Matar ta yi tana fadin " Me ya sa kike tsorona, na ga haduwarmu ta farko haka ki kayi, ko nayi miki kama da muguwa ne ".

 Saurin Girgiza kai Amatullah ta yi alamun ba haka ba ne. Cikin rashin son magana kamar an mata dole ta fara fadin " Hajiya kiyi hakuri, kawai ban damu da yawan magana ba ne, kuma nagode da kulawarki gareni aranar farko, kamar yanda nace miki munzo ne yau za mu kuma hakanne babu karya. " tana kai karshen zancen ta gimtse bakinta ta yi shiru.

 Matar kallonta take tare saka hannu cikin jakarta zaro wayarta ta yi tare da duba time, kana takara mai da shi acikin jaka, again idanunta yana kan Amatullah wacce take karewa kallo tun daga sama har kasa, dan yau ta ganta cikin sutura ta mutunci ba kamar haduwarsu ta farko ba.

 " Daman kunada yan uwa a ghetto ne?. " ta jefo mata tambaya tana kara tsura mata idanu.

 Amatullah kalmar ghetto sosai ya shige cikin kunnenta, cikin zuciyarta take maimaita daman sunan unguwar da muke zaune ghetto, tsoron kada Matar tagane karya take mata ne ya sa ta fadin " Nima bansan munada yan uwaba saida Papy ya kawoni nan kuma kinga anjima kadan za mu bar garin nan ". tana kai karshen zancen ta fara ƙoƙarin barin wajen.

 Daga sama taji muryan Matar tana fadin " Amatullah kai ni in gaishe da Papynki ".

 Firgit ta waigo kamar saukar aradu taji maganar ta doki dodon kunnenta. Shiga duniyar tunani ta yi tuno da lokacin da hirarsu da Papy inda yake fada mata kada ta kuskura ta kawo wani ko wata da sunan azo gansa ko ataimaka musu in ta yi gangancin yin haka, zata rasa shi na har abada, wani gumi me zafi ne ya fara karyo mata a fuskarta. Murya na rawa ta ce", Papy ya je kasuwa baya nan, kuma sauri nake kada ace na dade ban dawo ba. " bata jira cewar ta ba ta diba aguje tana gudu tana waige waige.

 Da zallan Mamaki Matar take kallonta har ta ba ce mata da gani, ta dade nan tsaye tana ta jiran ganin dawowarta. Abin da bata luraba shi ne, Amatullah ta labe c'en gefe daya tana kallonta.

 Ganin kamar ba dawowa zatayi ba, hakanan ta hakura tashige motarta ta yi tafiyar ta

 Amatullah ganin ta tafi ne ya sa ta fara sauke boyyayen ajiyar zuciya. sannan ta samu wuri ta dan zauna tana hutawa, kusan mintina talatin ta dauka kafin ta ci gaba da tafiyarta tana yi tana waiwaye adon tafiya kada matar nan tana bayanta. Daidai kusan masu siyar da lemun za ki ta karaso, har gaban me saida lemun ta tsaya, shikuwa yana ganinta a hanzarce ya karaso tare da tambayar me take bukata, itakuwa nan da nan ta kankance murya cikin roko da magiya ta ce " Don Allah ka ba ni sadaka ko da ta abincine, wallahi ba mu da abin da za mu ci ". ta kai karshen zance tareda yin kasa da kanta, duk firar da suke wani matashin saurayi da baze wuce shekaru talatin ba yana kallonsu daga c'en gefe abin shisha ne agabansa yana zuka sai tada hayaki ya ke yi a gabansa.

 Me saida lemun, abun fifita ya dauka yana korar kuda da suka cika mishi farantin lemu, kana ya kara kallonta da jajayen idanunsa kamar gauta, bakinsa mai ɗauke da dattin haƙora ya bude ya fara magana.

 " Kin san dai bazan baki sadaka ba, bayan ni baki ba ni komai ba, in kina son kudi, kinga dakina a nan kusa yake sai in kwatanta miki kije c'en ki jirani, Kinga har dubu daya ma zan iya baki yanda kike me kyaun din nan ". ya karashe zancen yana washe mata haƙora.

 Duk da bata fahimci me yake nufi amma tabbas ta san, inda abun arzikine baze ce ta je dakinsa ba, cunno baki gaba ta yi tare da fadin " a nan zaka ban abin da zaka ban in kuma babu kacemin na tafiya ta kawai basai kasa nayi tafiyar wahala ba". ta karashe zancen cikin tsiwar da bata san ta iya.

 Ƙoƙarin yin magana yake ya ji an nausa masa wawan mari a fuskarsa, cikin razana yake kallon Karfin Iko hannunsa rike da kuncinsa ya ce, " me nayi maka ne?. " ya kai karshen zancen cikin tsananin tsoro da fargaba, da baya baya ya fara yi domin kauce masa.

 Amatullah tunda Karfin Iko ya yi mari rintse idanunta ta yi ji take kamar ita ce, ze kai wa mari sakamakon yanda taga jijiyoyin hannayen sa murmudaddu su ka mike. Khausassen Muryan Karfin Iko ne ya katse mata tunaninta jin yana fadin " Kai ban da dan iska ne, iskancin naka harda yan Yara matasa wannan Yarinyar duka nawa take da kake son yin lalata da ita a kan abinci". ya karashe zancen cikin daga babban muryansa.

 Jama'ar da ke wajen sosai suka shiga fadin " Amma kai dai Hamisu mai lemu ba zaka iya canza halinka ba. Wani gurgu da ke kan keken guragu karasowa wajen ya yi tare da soma zagin Hamisu mai lemu, hakuri ya shiga bawa Karfin Iko ya san sarai yanzu sai yahau dukan mai lemu inda dakyar za su iya kwatarshi.

 Karfin Iko huci yake sama- sama kana ya dawo da kallonsa kan Amatullah da ta rintse idanunta dan tsananin tsoro da fargaba, ahankali ta fara yunkurin bude idanunta, tana budewa idanunsu suka tsarke cikin na juna ita da Karfin Iko, aguje ta sake rufe idanunta. Sautin muryansa ta ji yana fadin " Yan mata kamar nawa kike bukata kudin cin abincinku? ". ya yi shiru yana busa sigari kamar ba shi ya yi magana ba. Gurgu da ke kan kekensa, cikin tausayawa ya ce, " Yan mata Karfin Iko yana magana ba a kyaleshi babu amsa kinji ko. " gyada masa kai ta yi ba tare da ta kalleshi ba, shikuwa Gurgu da sauran jama'ar da ke kallon abin da ya faru duk sun koma mazauninsu suna Allah wadai da halin mai lemu, Hamisu mai Lemu zama ya yi rike da kuncinsa yana satar kallonsu.

Ganin ba za ta yi magana ba ya sa Karfin Iko zaro dubu goma daga Aljihun wandonsa, kamo hannunta ya yi ya saka mata a hannu cikin yin kasa da murya ya ce, " ni yayanki ne, dan haka da kinzo nan wajen, in baki ganni ba kice a nuna miki Karfin Iko duk inda nake za su nemo ni kinji ko?. " gyada masa kai ta yi ba tare da ta dago kanta ba. Shikuwa sata gaba ya yi tare da mata rakiya saida ya tabbatar ta fice sannan ya dawowarsa.

 Itakuwa tafiya take cikinsauri saurinta tana tafiya tana waige waige, saida ta kusa hanyar Gidan nasu sannan ta daidaita nutsuwarta direct wani shago ta nufa, inda a nan ne ta samu tasiye gawayi da kayan abincinsu na kwana biyu, nan take dubu goman yakare Nigeria ana fama da tsadar Rayuwa. Harda ledan pure water tasai musu tana jin dadi yau zata sha ruwan pure water dan a kundin tarihin rayuwarta sau daya ta taba sha tun awannan kauyen da wata mata ta sai mata hade da magani sai yanzu da zata kara sha. tana isa Gidan iske Papy ta yi zaune ya tasa Rediyo agabansa, ganinta ya sa ya sakar mata murmushi ganin yanda ta shigo da kayan abinci alamun yau za su ci su koshi. nan ta zayyana masa duk abin da yafaru tun daga kan matar data tsaida ita a kan titi har kalaman mai lemu da taimakon da Karfin Iko ya yi mata. Papy kuwa maimakon ya yi murmushi sai taga ya rintse idanunsa yana girgiza kansa alamun tarin damuwa, cikinsassaita nutsuwarsa ya ce " Amatullah kar ki bari wani ya zo inda muke kinji harsai inni da kaina na baki izini, ko kinason ki rasani ne?". Ahanzarce ta girgiza kai alamun a'a.

 " to kada ki sake yarda ki kula wannan Matar tunda har takeson sai taga Papynki, sannan kuma duk Namijin da zece kuje dakinsa yabaki kuɗi ko wani abu kada kiyarda dashi kice bakyaso kin Yarda?. " nan ma gyada masa kai tayi.

 Murmushi ya sakar mata yana mai jin nutsuwa tattare da ita tare da shafa kanta yana mata addu'a. Cikin jin dadi Amatullah ta fara ƙoƙarin yi masu Girki duk da ba iyawa ta yi ba Papy ke koya mata yanda ake girkin.

 Unguwar Asokoro

 Ridwan Zaune a office dinsa shi da Mansur suna shawara a kan sabbin ma'aikata da za su dauka, wayarsa ce ta fara ruri yana dubawa yaga Anisa ce, be bata lokaci ba wajen daga wayar, daga cen bangaren ta ce, " Yaya Rid, Mamy ta ce, kaba drever izini ya kaita asibiti bata jin dadi, kuma tace babu kuɗi ahannunta ".

" zan kira shi, kuɗi kuma saina dawo ai nasan akwai ragowar kudade a hannunta, ko tana nufin har sun kare ne? ".

 A zafafe Mamy ta Karɓe wayar daga hannun Anisa cikin tsananin bacin rai ta ce, " Ridwan har ni zaka ringa fadin maganganun akaina kullum kaine kyautar Gida da mota da kudade kai ne bada zakka, wajen bada taimako kullum kaine sahun gaba, Amma Rid. . . . . . . ".

 " Dakata". Shi ne farkon kalmar da ya samu damar fitowa daga bakinsa.

 " Mamy shin k. . . . . . . . . . . . . .

 SHAFI NA SHIDA

TALLA! TALLA!

Marubuciyar nan taku Sarat Alƙasum wacce kuka fi sani da (Maman Nusaiba) wadda ta baje basirarta ta nishaɗantar da ku a cikin littafanta kamar su : Amir da Amira, Aljanar Jarumai, Hafsat, Ƙaddara ce, Tani da Manu, Rayuwar ma'aurata, Sumaiya baiwar Allah, Aljanar Gidanmu, A maƙabarta ne, ABBA NE, Fa'ima.  Yau ma ga ta ɗauke da sabo zazzafa mai suna A HAKA NAKE SON SHI Littafin da ya ƙunshi abubuwa daban-daban zalunci, makirci, cin amana, zallar tsagwaron soyayya mai ratsa zuciyar mai karatu, da sauran su. Ka ku bari a baku labarin wannan kayataccan littafin.

Littafin A HAKA NAKE SON Na kuɗi ne nomal ~N~ 300 vip ~N~ 500 ne.

Za ki tura kuɗin ku kai tsaye ta wannan banki.

Account number 0003187186

Name account, khadija Salisu

Name Bank, Ja'iz Bank

Domin Ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan number +966577675904

" Dakata. " shi ne farkon kalmar da ya samu damar fitowa daga bakinsa.

 "Mamy shin kin san maganganun da kike fade kuwa, nasan girman Allah, kuma ina tsoron haduwata da shi, abubuwan da nake miki na farillah ne bana kawo sunnah acikin al'amaruna da ke Mamy, taimakon da nake yi dafatan dai ba sokike in daina yi wa addini hidima ba? in ko hakane babu biyayya ga abokin halitta wajen sabawa Allah. "yana kai karshen zancen ya katse wayar, tare da ajiye wayar kan tabur din gabansa, hannayensa duka biyun ya sa dafe da kansa, nan take wasu hawaye masu zafi kebin kyakkyawar fuskarsa, kuka yake kamar karamin yaro, Mansur cikin kidima ya karaso gabansa hade da dafashi ta baya yana bubbuga masa baya Alamun rarrashi, hannunsa ya sa ya kauda tarin file da ke gaban Ridwan, kana ya dawo ta gabansa ya zauna kan tebur din, cikin muryansa me nuni alamun wanda ke shirin yin kuka ya ce, " Rid tun muna Yara muka taso sau da dama na kan ganin kamar baka jituwa da Mamynka, amma kullum inna tambayeka dalili baka gayamin, kuma na lura kuka baya maka wahala muddin Mamy ta yi maka magana a kan matsalarta, shin ban canci ka gayamin damuwarka ba ne? ko dai abun naka sirrine da baze iya faduwa, amma kar ka manta Rid, kai sirrina ne, ni kuma sirrikane, dan Allah kar ka bari abotanmu ya samu rauni da rashin aminci. " Ya kai karshen zancen yana mai tura yatsarsa daya abakinsa. Ridwan dagowa ya yi tare da kai dubansa a kan Mansur dinsa, cikin azababben kuka da ya kara zuwa masa, yanda yake kuka kai ka ce sakon mutuwa aka aiko masa, kukan yake sosai sannan yana fesar da numfashi tare da daukan tissu ya fara goge hawayensa, hannunsa ya sa still ya sa tissu ze gogewa Mansur hawayensa, ga mamakinsa sai ganin Mansur ya yi ya kauda kansa gefe hade da sauka daga kan tebur din, tafiya yake goye da hannayensa abaya har ya karaso wajen window din office din, idanunsa na kan farfajiyar ma'aikatar mai cike da haduwa, inda jerin motocin ma'aikata suke yake kallo, idanunsa na kan Motar Rid kirar Mercendenz 2022, murmushi mai kama da ciwo ya yi jin Ridwan ya dafa shi ta baya, be waigo ba amma duk hankalinsa da nutsuwarsa ya dawo a kan Ridwan da ya ji ya fara magana.

 " Mansur kafi Mamy daraja da kima a wajena".

 Firgit Mansur ya waigo kamar an tsinkaye shi da allura, cikin rawar baki ya ce, " Ri. . . . d. . . w. . . a. . . . . n. . . . . ka ko. . . . san abin da ka. . ke. . fa. . de. . . kuwa. . . . . ". sauran kalamansa samun makalewa su kayi jin Ridwan yana magana kamar haka.

 " Eh nasan abunda nake fada kuma kai ma kasan ban da Mahaifiya data wuce Mamy, kar kaga laifina domin na tsani !! mata, natsani mata !!, banason Hulda da mata !! Wannan dalilin ya sa ko Aure ni Ridwan bazanyi ba, ahaka zan kare rayuwata, amma ina kaunar kannena mata, mahaifiyata ban tsaneta tunda ta kawoni Duniya har nake shan iskan cikinsa, kuma abin da kake son sani a kan abubuwan dana fada a kan Mamy zan fada maka amma ba irin wannan lokacin ba, Mamy bata min komi ba a rayuwata ba, ni Ridwan zan baka labarin zuciyata kila muzo ra'ayi daya ni dakai. " Ya kai karshen zancen yana mai share kwallan daya zubo masa.

 Mansur hannayensa masu taushi ya sa ya soma goge masa kwallah, cikin murmushinsa wanda ta zama dabi'arsa ya ce, " Rid bansan meye dalilin da ya sa ka tsani Mata ba, amma babu Dalilin da ze sanya ka ce babu kai babu Aure arayuwarka wannan kuskurene, in sha Allah Ridwan sai kayi Aure harda ya'ya. ". ya karashe zancen da guntun murmushi a fuskarsa.

 Ridwan ba tare da ya bashi amsa ba, ya koma kan kujerar office dinsa mai lilo, yana zaune yana juya kujerar. " cikin yin kasa da muryansa in ba ka kasa kunne ba, bazaka taba jin me yake fade ba, file a hannunsa ɗauke da biro ya ce, " ai Mansur ya'yanka nawa ne in ka haifa sai ka ba ni su amma ban da ya'ya Mata. " ya kai karshen zancen yana mai yan rubu-rubucensa kamar bashi ya yi magana ba.

 Murmushi mai sanyi, Mansur ya yi tare da tsurawa Ridwan idanu yana kallon kyakyawan fuskarsa mai ɗauke da yalwataccen saje da aka taje su suna sheki da walwali, kallonsa yake yanda baka iya banbance shi in har ya shiga cikin labaraba domin fari ne tass, kyakyawan matashi ajin farko, jajayen labbansa yake kallo yana, kara kallon sumar kansa masu tsantsin da sheki, nan ma murmushi ya yi yana magana a zuci, tare da daukan alwashin canza masa duk kudirinsa, maye masa gurbin kuka da dariya, murmushi yake sakarwa shi kaɗai, wanda hakan ya jawo hankalin Ridwan tare dan dago kansa yana fadin " Mansur wai me ka ke wa dariya ne?, gulma dai babu kyau ". ya yi magana yana mai harhada takardun da ke gabansa.

Mansur cikinsanyin murya ya ce " ni bazan baka ya'yan da zan haifa ba saidai ka haifi naka da kanka, har fadi kake kada na baka ya'ya Mata, yanda kasan na hannun yarjejeniya ni dakai, duk abin da kake fade in sha Allah saina canza shi ". Ya kai karshen zancen da guntun hawaye a fuskarsa. Ridwan kwabe baki ya yi tare da cigaba da abin da ke gabansa.

 Kano

 Asibitin Murtala.

Salim kwance agadon asibiti sam be san wanda yake kansa ba, domin tunda aka kawo shi, baya iya magana, saidai ya yi ta zuba idanu yana kallonka babu kiftawa, Mahaifiyarsa sanye cikin atamfar roba, me ɗauke da dinki buba, cikin mutuwar jiki da rashin kuzari take masa fifita da abun fifita, shikuwa Salim da idanu yake bin ta da kallo. Mahaifinsa da kannensa da ke c'en gefe daya suna kallon halin da Salim yake cikin, cikin rawar murya mamansa ta ce, " kana jin docto ya ce sai anfitar dashi waje za'a masa aiki domin ya samu matsala a cikin cikinsa, wannan abun duk kune kuka ja da tun farko kun saurare shi da hakan bata faru ba, to in har shi ne ya fitar dasu tunda dai ba'a gansu ba, basai a hakura ba, yanzu ina yaran da kasa su masa duka suke? Kaga kafarsu a asibitin nan, ya kamata in ranmu ya ba ce kada hankalinmu ya gushe, duk dangi mu babu mai arziki ina za mu samu kudaden da za'ayiwa Salim aiki, kuma shi ne kaɗai ke fadi tashi wajen nemo mana abin da za mu ci, yau gashi a kwance be iya tabuka komai, kai kuma ba wani ƙoƙari gareka ba ". ta yi furucin cikin fada tana mai hararan Mahaifinsa da kannensa.

 Abban Salim gaza magana ya yi ban da " Uhmmm. " Babu abin da yake maimaitawa.

 Tunaninsa ta ina za su samu kudade masu yawa har miliyan biyar !! Kara shiga matsananci damuwa ya yi a karo na biyu tareda zabga uban tagumi.

 ABUJA CITY

 Ghetto

Bayan kwana biyu misalin karfe goma na safe Papy kwance a kan katifarsa, yana mai sauraron rediyo yaji Muryan Amatullah tana fadin " Papy zanje ko zan samu bara domin yanzu kayan abinci gare mu babu na siyen biredi da kayan miya. " ta yi magana tana mai dauko hijab dinta da ke makale kan kofar dakin, kar kada mata kai ya yi alamun sai ta dawo, kana yakara mai da hankalinsa a kan Rediyo da yake saurare.

 Ahanzarce ta fice tana tafiya tana fadin Allah ya sa ta samo sadaka, cikin tsananin tsoro da Fargaba taga Karfin Iko zaune a kan wata katuwar dutse da dukan Alamu waya yake yi mai muhimmanci. Ba jinsa take sosai ba, amma kunneta ya jiyo mata inda yake fadin " Haba Mandula ka hanzarta kuje Kafachan da ke jahar Kaduna, ku bincika gidan Alhaji Ado mai kaji, in sha Allah za'a nuna muku. Dan Allah ku tabbatar kunyi garkuwa dashi, kuma in kun cika aiki ku sanar dani zan gyara muku muhallin da za mu ajiyeshi ". yakarashe zancen cikin babban muryansa.

 

 Zazzare idanu Amatullah ta soma tare da sa hannayenta ta toshe bakinta, da baya baya ta fara tafiya tana ƙoƙarin sanya gudu, ganin kamar ze waigo ne ya sa ta gyara tsayuwarta hade da kakalo murmushin dole ta fara taku ahankali kamar wacce ruwa ya cita ƙoƙarin wuce shi take, taji Muryansa me ban tsoro yana fadin" ke!!!. ". nan da nan hantar cikinta ya kada bata san sanda ta saki fitsari awando ba.

 Tasowa daga zaune da yake ya yi karaso kusa da ita kafafunta yake kallo yanda ruwan fitsari ke bin ta, cikin Mamaki ya ce " daga ina kike !? Kuma me kike nema a nan ko a nan Gidanku yake?. " cikin hanzari ta girgiza masa kai tare da masa alamun A'a ba a nan suke ba.

 " Me kike nema a nan wurin?. " Ya yi magana cikin tsareta da idanu yana hura hanci.

 Bata bashi amsa ba illah kawai kara yin kasa da kanta ta yi ban da harbawa babu abin da Zuciyarta take yi.

 " Nasan bara za kiye, kuma nasan har dakin ku, zuwana nan saboda ke ne, waya na tsaya yi da tuntuni kin ganni kofar dakinku ". Nan da nan hantar cikinta ya kada jikinta ya hau rawa kamar mazari, cikin rawar murya ta ce " dan Allah kar ka zo Gidanmu Papy bayaso kowa ya zo inda muke banason na rasa shi ɗan Allah kar ka zo". Ta kai ayar zancen cikin kukanta mai tsuma zuciya.

 Papy da ke cikin dakin sa jin kamar muryan Amatullah da wani ya sa ya juyo ta bayan Gidan yana kallonsu ba tare da sun gansa ba, yana sanya idanu a kan Karfin Iko nan da nan hantar cikinsa ya kada, jikinsa ya hau rawa kamar mazari, hango wani kango ya yi daga c'en gefensa cikinsanda sanda ya tafi c'en ya boye tare da tattare kansa waje daya.

 Karfin Iko kama hannun Amatullah ya yi suka karaso har Gidan nasu. Kana yashiga dakin nasu, daga ita har shi kallon juna suke. Cikin mamaki take fadi a zuciyarta kardai Papy ya gudune kamar yanda yanda yasha furta mata, muryan Karfin Iko ne ya dawo da ita cikin hayyacinta, jin yana fadin " daman Papyn naki yafita ne? ". Girgiza kai ta yi tare da fadin " eh ya ce min ze je unguwa sai bayan la'asar ze dawo ". ta idasa zancen cikin tashin hankali da ba'a sanya masa rana.

 Karfin Iko sosai ya shiga nazartan yanayinta ganin duk a tsorace take dashi ya sa shi fadin " ni fa ba mugu ba ne babu abunda zan miki sai Alkhairi, zan baki dubu ashirin kije ku siya duk abun da kuke bukata ". ya karashe zancen yana mai zaro bandir din kudin daga aljihun wandonsa.  

 Da murmushin yake a fuskarta ta karba tana masa godiya, shikuwa ganin wayarsa ta fara ring ne, ya fito cikinsauri takalman ƙafarsa manya manyan irin na masu shiga ruwa take bi da kallo, kana ta kai dubanta a kan gashin kansa mai ɗauke da kitso irin na Bob maley sanyayan ajiyar zuciya ta sauke ganin ya fice yana waya, sannan wani karin tashin hankali ya kara zuwar mata ganin babu Papy a wajen harta daura hannunta akai zata kurma ihuu ne, ta ji an dafata da baya, afirgice cikin tsoro ta waiga, ganin Papy na mata dariya ya sa sauke nauyayyen ajiyar zuciya tare da fadawa jikinsa aguje, wani marayan kuka ta saki stil cikin narke murya ta ce, " Dan Allah Papy kar ka gujeni". yanda ta yi magana saida ta karya masa zuciya, hannayensa ya sanya domin share mata hawayenta, cikin tsananin mamaki da fargaba suka ji takun tafiya alamun anzo gab dasu, atare itada papy suka kai dubansu akan. . . . . . . . . . .

 Makauniyar Shari'a taku ce.

 

 Domin son magana dani 09069080725

 Share and comment pls

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 

NA

IKILIMA ADAM

 (kyauta daga Allah)

Littafin nan, na kuɗi ne da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Dari biyar kacal

3115484026 Ikilima Adam firts bank

Tura shaidar biya a kan wannan lambar (09069080725) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.

Siyen Nagari mai da kuɗi Gida

Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma. 📚📚

SHAFI NA BAKWAI

Cikin tsananin mamaki suka ji takun tafiya alamun an zo gab dasu, atare ita da Papy suka kai dubansu a kan Matar nan. Ajiyar zuciya mai karfi suka sauke dukansu,

suka kai dubansu akanta, cikin zallan mamaki da nacin Matar, Amatullah take kallonta cikin idanu nan da nan ranta ya soma ɓaci, cikin muryan kamar wacce ke gab da shirin sakin kuka ta ce, " Baiwar Allah me ya sa kike ta bibiyata ne? In akwai abin da na miki ki sanar min dan Allah". ta kai karshen zancen tana kallon yanda Matar ta tsura mata idanu. Fesar da numfashi mai zafi, Matar ta yi ita ma fuskarta babu annuri ko walwala ta ce, " Amatullah kwantar da hankalinki, ban biyoki nan dan cutarwa ba amma shi Papy naki me ya sa baya bude fuskarsa? Ba wannan ba, bari in dauko miki wani hoto a wayata za ki gasgata abin da nake son nuna miki". Tana ƙoƙarin ciro hoto daga jakarta.

 Papy kuwa kallon kallo suke yi shi da matar, kana ya kai dubansa a kan hoton data fiddo acikin jakarta, tana ƙoƙarin nunawa Amatullah.

 " Dakata ". Shi ne kalmar da Papy ya furta murya a khausashe.

 " Ni za ki bawa na duba in ya cancanta ta gani sai in bata in kuma babu cancanta dan Allah ki koma da kayanki kuma ki kyalemu ". Ya kai karshen zancen yana mai mika mata hannun alamun ta bashi.

 Mika masa ta yi tana kallon kwayar idanunsa, so take ta gane ko ta taɓa ganinsa sauke idanunsa da ya yi be bata damar hakan ba.

 Agigice yake kallon Hoton nan da nan ya fara zazzare idanu, yana kallon hoton yana kallon Amatullah, muryansa da harshensa na rawa ya ce, " Hajiya ya sunanki? Inason ganinki na minti biyar ya yi magana tare dan janta gefe daya.

 Amatullah da mamaki take kallon sun raba c'en gefe, fuskokinsu take kallo dukansu cike da tsananin damuwa, da mamakinta ganin Papy ta yi yana ma Matar magana yana mata nuni da hannayensa, alamu sun nuna kamar kwatance yake mata, kanacen baya yagama maganar, sai taga matar ita ma magana take tana rintse idanunta alamun maganganunsa masu tsauri ne".

 Cikin damuwa ta ce, " Me ya sa Papy ya hana in ga hoton nan, shin me yake faruwa ne ". Take tambayar kanta, ganin babu mai bata amsa sai shi, ya sa ta nemi wuri ta zauna.

 Mintina kusan arba'in suka dauka suna magana, kafun su dawo inda Amatullah take, Matar kuwa kallon Amatullah ta yi tare da fadin " Yar Gidan Papy zan tafi ki kula da kanki in sha Allah, zan kara waiwayo ku ".

 Murmushin yake kwance a kan fuskar Papa ya ce, babu matsala sai ta dawo din, kana ya dan mata rakiya, ganin ta fice ne ya dawo tare da shigewa dakin nasa. Yana ciki, jingina da bangon dakin ya yi yana mai tunanin maganganunsa da matar kana yakara gyara zamansa dakyau, yana kallon kasan dakinsu, katifar kwanciyarsu yake bi da idanu. Batareda ya ankare ba wani barci mai daɗin gaske ya yi awon gaba dashi, cikin barcinsa ya fara mafarki.

Zaune yake a kan babban kujera na Alfarma, wani babban daki na Alfarma yake zaune acikinsa. Daki ne wanda yaji kayan alatu na more rayuwa, fankan saman dakin kalar zinariya akayi goldin, kujerun dakin har ma da carpet din dakin, dîner table duk kalarsu daya, ga tarin takarduna a gaban sa yana sanye da hula irin na Alkalai akansa, dattijone shi ba Fari ba kuma ba'a sakashi sahun bakake ba, kyakyawa daidai gwargwado, cikin aikinsa yake yaji kamar ana tunkaro shi daga bayansa wanda ya sa aguje ya waigo ga mamakin wata mata ya gani rike da wuta, wanda ya nuna da dukan alamu matarsa ce, zumbur ya tashi ya soma ja da baya baya, bakin sa na rawa ya fara ƙoƙarin magana. . . . . . . . . . . . Bubbuga shi da karfi da Amatullah ta yi ne ya sa shi farkawa arude, nan da nan ya jike shargab da gumi kana, cikin rawar jiki ya fara karanta innalillah wa'inna ilairajun.

 Cikin rudu Amatullah ta ce, " Papy Lafiya kuwa kake ta muzurai acikin barci, wallahi duk na rikice Papy anya kayi aduar da kake koyamin in za mu shiga barci kuwa?. ". Sai yanzu hankalinsa yadawo jikinsa, murya na rawa ya ce, " kawai mafarkin ban tsoro nayi dan haka alwala zanyi, kuma yau mu hada kayanmu za mu canza unguwa". Ya yi magana babu wasa acikinta.

 Amatullah kallonsa take yanda yadan rame na lokaci daya, tana son sanin me yake damunsa amma ganin be bata fuska ba ya sa ta yin shiru tareda lulawa duniyar tunani.

Asokoro

Sai kusan karfe shida na yamma, Ridwan ya kama hanyar Gidan nasu, tafiya suke a mota suna hira shida Mansur, Tik tok Mansur ya kunna yana kallon Video Murja Ibrahim kunya yanda take tikan rawa, murmushi yake cike da zolaya ya ce, " Ridwan wannan yar Tik tok din in ka sameta ka huta wallahi, yarinya ga farin jini, kuma ma an ce Abba Gida-Gida gwanar Kano ya ce, ta fito da miji ze mata Aure, dan Allah malam kafito ka aure ta kawai awuce wajen ". ya karashen zancen yana dariya iya gaskiyarsa. Ridwan ta gefen idanu yake kallon video da murja ke rawan kana ya tabe baki hade da yin siririn tsaki, cikin takaici ya ce, " ai wannan ko a Aljanna Allah ya mallaka min ita nasan banyi abun kwarai ba, kaga ita ga fitsara a fili, sannan wannan kazamar yar kauyen nan da mukaso bigewa, da kuma haukanta ya motsa ta biyomu har cikin taro, ko akafa aka dauraminsu, cire kafafun zanyi na wurgar in huta da kuda, gwamma ta Tik tok din ko bakomai tana wanka, kai nace maka ka daina min hiran mata yau ma bansan dalilin dayasa na biye maka ba ". Ya idasa zancen cikin takaicin tuno da Amatullah.

 ban da Dariya babu abin da Mansur ya ke yi cikin, tsokanar muryan Ridwan ya ce, " ta kauyen nan bata shige maka zuciya ba kuwa na ga meye na tuno ta daga ana hiran Murja, kodai kauyen za mu koma ". ya kai karshen zancen yana mai kallon yanda Ridwan ya yi shiru kamar baya jinsa. .

 Ridwan kam kasa magana ya yi yana jinjina kalaman sa, tare kara mai da hankalinsa ga tukinsa.

Tare suka karasa Gida shi da Mansur, suna fitowa daga cikin Motar su na Alfarma nan da nan Bodyguard da ma'aikata suka zagayesu, cike da bangirma suke masu barka da dawowa, fuska asake suka amsa musu, Ridwan cikin dabi'arsa da sam baka gane yanayinsa da kunci ko na walwala ne ya kai dubansa a kan su, ahankali kamar ana masa dole ya daga jajayen labbansa masu sheki da burgewa ya ce, " ina fatan babu wata matsala ko? sannan inason daga gobe Bodyguard dina su dawo aiki, akarshe kuma inason ku sani duk wanda ya kara Gulmata a gidan nan zan dau kwakwaran mataki akansa. " Yana kai karshen zancen ya kama hannun Mansur da ke kallon yanda ya ke magana babu wasa ko daukan raini aciki, binsa ya yi inda suka shige daga ciki.

Ma'aikata da Bodyguard sosai suka razana jin furucin da ya yi, to su wani irin gulmarsa suke yi, kuma ma waye ya f'ada masa hakan, Lallai acikinsu akwai munafukai cewar daya daga cikin ma'aikatan, gudun karsu kara sakin baki ya sa suka bar wajen tare da yin gum da bakin su.

 Ridwan kallon Mamy ya ke yanda take zaune a falon da dukan alamu kamar tana cikin bacin rai, make kafada ya yi alamun ko ajikinsa. Kana suka karaso falon hannunsu cikin juna shi da Mansur, dukansu durkushewa suka yi suna mika gaisuwa ga Mamy, cikin fushi ta amsa musu gaisuwar tasu. Atare suka mike, Ridwan cikin kosawa yake shirin su bar falon shi da Aminiyansa, ya ji sautin muryan Mamy tana fadin " dan Allah Mansur zo ina son ganinka ".

 Cak suka tsaya dukansu daga shi har Mansur din, sakin hannun Mansur din ya yi tare da yin gaba, shikuwa Mansur cike da fargaba ya dawo falon, yana isowa wajenta ya fara ƙoƙarin durkushewa gabanta ahanzarce ta hana shi tare da nuna masa wajen zama, kana ita ma ta dawo kusa da inda ya zauna din.

" Mansur kai fa Aminin Ridwan ne, me ya sa bazaka fada masa ya ji tsoron Allah ba, ya fidda hakkin iyayensa musamman Mahaifiyarsa, ko ya manta girman Uwa ne a wajen Allah, Manzon Sallallahu alaihi Wasallam saida yace abi Uwa sau uku sannan ya ambaci Uba sau daya, yanzu saboda Allah jibi arzikin Ridwan ace ko Makkah ban taba zuwa ba, ko Humra kuma bayan kullum saidai inji yabiyawa mutane hamsin kujerar Hajji duk shekara, me na tsare mishi ban da abincin da yake ba mu babu abin da yake sinana mun, kullum saidai inga abu a wani Gida amma ban da Gidana, hatta wayar hannuna dakyar ya siyamin ka ganta nan airtel ". ta karashe zancen tana mai nuna masa wayar.

 Shi ma wayar yake bi da kallo yanda aka manne ta da robe dan kada murfinta ya cire.

" Yanzu ya dace ace Ni Mahaifiyar Ridwan Muhammad Mai nasara, ni ce awannan yanayin babu kyaun gani, fuskata duk kuraje, wallahi tallahi inajin bakin cikinsa, kuma ya san inna tsine masa ze bisa, kayi masa fada tun ban kai shi kara kotu ba. ". takarashe zancen cikin muryan kuka da takaici.

 Jikin Mansur ya yi mugun sanyi babu abunda ya gigita masa tunani jin furucin wai zata makashi a kotu, hannayensa ya daura akai alamun tunani, kana ya dawo ya dago kansa da ke sarawa da tsananin ciwon kai na lokaci daya, idanunsa da suka kada jajir ne yake kallonta dasu, cikin rawar baki da disashewar murya ya ce, " Mamy da farko dai hakuri zan baki, kuma duk wanda ya yi hakuri yana tare da nasara, kinsan dai Ridwan ba jahili ba ne yana da ilimi daidai sanin da Allah yabashi kuma yana da tausayi da jin kai, amma bansan me ya sa duk wannan halayen nasa ba, baya ji kwata kwata akanki, maganar kotu kar ki fara saboda Ridwan D'an da ki ka haifa da cikin ki ne, ni ban da ya nuna min ya tsani Mata ba ina ganin kamata ya yi a masa aure kila a dalilin ganin yanada iyali ze bar wasu abubuwan ".

 

 Cikin tsananin tashin hankali Mamy ke juya kalaman aure kuma a ranta, a fili kuma ta ce, " Please abar zancen auren nan banaso .

 

 Cikin zallan mamaki Mansur ke kallonta, kana ya mike cikin rashin kuzari tare da fadin ze tafi gun abokinsa kuma ze iyakar ƙoƙarinsa ganin ya dawo dashi kan hanya da wannan kalaman ya samu damar barin falon ransa fal da tunanin me Mamy take nufi? batason Ridwan ya yi aure ne da wannan tunanin ya hau matakalan step.

 Itakuwa rike da baki take juya kalamansa har Anisa ta zo gabanta bata sani ba, sai magana take ma ta shiru, Anisa murmushi ta yi tare da dafa Mamy, wanda ya sa a firgice ta dawo hayyacinta, cikin subutar baki ta ce, " nace maka Ridwan bazeyi aure Please abar zancen nan. ". da mamaki Anisa ke kallonta hade da taba ta, tana fadin " Mamy lafiya kike sambatu, kuma a kan yaya Ridwan ".

 Mamy dafe da kanta ta nuna mata bama ta san ta yi furucin ba.

 

 Ghetto

 Tun adaren Papy ya haɗa musu kayansu, za su bar unguwar, in ta kama Garin za su bari.

 Asuba tana yi suna idar da sallah suka kamo hanya fita daga unguwar riki riki da kayansu ahannunsu Papy ya rike wasu Amatullah ma haka, yana sanye cikin shigarsa ta buzaye kamar yanda ya saba, sun kusa isa bakin titi, suka ga ansha gabansu antare gabansu da bayansu, babban cikinsu sanye yake cikin bakaken kayan sanyi masu kauri rigarsa mai haɗe da hula ne akansa ya juya musu baya, bayan rigarsa suke kallo, inda Papy yaga an rubuta. . . . . . . . . . . . . .

Makauniyar Shari'a taku ce.

 Domin son magana dani 09069080725

Share and comment pls

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 

NA

IKILIMA ADAM

 (kyauta daga Allah)

Littafin nan, na kuɗi ne da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Dari biyar kacal

3115484026 Ikilima Adam firts bank

Tura shaidar biya a kan wannan lambar (09069080725) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.

Siyen Nagari mai da kuɗi Gida

Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma. 📚📚

SHAFI NA TARA

Cikin zallan mamaki da rudewar tunani yaga Mansur a tsakiyar su yana ƙoƙarin ficewa suna shan gabansa da lasifunku su, da idanu yake bin fuskar Mansur da yaga tsantsar bacin rai tattare dashi ganin sun hana shi hanya, janye glass din window ya yi ya dawo cikin a hanzarce, cikin hanzarinsa ya hau canza kaya zuwa wandon jeans da riga dark bleu wanda su kayi masa masifar kyau, tsadaddan flat din takalmansa ya sanya a uzurce, dauka wayoyinsa ya yi, kana ya yi hanyar fita daga dakin cikin da sauri saurinsa.

Mamy da su Anisa kowannensu ya yi cirko cirko yana magana a kan me yake faruwa ne?. Jin takun tafiyar Rid cikin hanzari ya sa dukansu kai duba akansa har Faisal da ya fito daga dakinsa don zuwa ganin me ke faruwa. Kallo daya ya musu ya kauda kansa tare da wuce su be musu magana ba. Mamy ta san Rid duk miskilancinsa in har ze ganta tabbas ze mata magana ko da ta gaisuwace, ƙoƙarin bin sahunsa take Anisa ta dakatar da ita dan ta san yayansu yana ganin ta fito ransa zeyi matukar ɓaci. Mansur na ƙoƙarin bude gate din Gidan domin shiga suka ci karo da Ridwan yana ƙoƙarin fita a ujajan, Mansur hannayensa ya rike domin dakatar da shi. Cikin bacin rai Mansur ya ce, " pls kar ka fita yan jaridu ne fa, kai ma kasan babu abin da za su sanya maka sai bacin rai ". Narkakkun idanunsa ya zuba masa masu eyelash, be tankawa Mansir ba illah kawai cigaba da tafiyarsa ya yi gun karasawa wajen Gidan, hakan ya sa Mansur take masa baya. Koda fitarsa habawa yan jaridu kewaye shi suka da lasifuku, cikinsu harda Gidan television na Arewa 24, kallonsu yake da sam baka gane bacin ransa ko farin cikinsa, Dan jaridar bangaren Arewa 24 ne ya samu damar saka lasifika agabansa tare da fadin.

" Mai girma Ridwan Muhammad Mai nasara, labari ya karade dukan jahohi a kan wai kaje Kauyen Daguzau ka Auri wata yar yarinya wacce bazata zarce sha biyar zuwa sha shida ba, kuma ana ta rade radin an nemesu an rasa daga kauyen har dimbin jama'a suna ta rade radin cewar anya ba Kidnapping din Yarinyar da babanta kayi ba ma'ana ko asiri zakayi da ita ku kuma dodon tsafi zakaba ita?". Ya karashe zancen yana mai kara saita lasifika daidai bakin Ridwan din.

 Ridwan tunda dan Jaridar ya kai karshen zancensa ya ji kansa ya fara sarawa ji yake tsananin tashin hankali ya maye gurbi da farin cikin daya kwana dashi, nan da nan ya ji notice din kansa ya fara kwancewa, cikin dabi'arsa da sam baka ba a gane bacin ransa ko akasin hakan sai shi in ya bayyana a kalamansa, kallon Mansur yi kana ya kai dubansa a kan Faisal da ke tsaye rungume da hannayensa yana jinjina sabon al'amari. Daddazon mutane da ke kewaye da kofar gidan yake bi da kallo daya bayan daya, matasa da datijawa har ma da yara, be san lokacin da yaja tsiririn tsaki ba, cikin zazzafan martani ya ce " ni Ridwan ba zanyi mamakin tsareni da kukayi kuna min tambayoyin banza da rainin hankali, kuma na karfin yaro sai de baban yaro, eh na Auri Yar kauyen kuma na bayar da ita gun yan mafiya sai akayi yaya, hausawa sun ce da kai da kaya mallakar wuya ce, tunda Aurenta kuka ce nayi banga abun damun kai dan bakusan yanda nayi dasu ba, Mahaifinta shi ma duk guri daya na bayar dasu, bazan bayar da daya in bar daya ba shiyasa nayi jam'i, to in ban da dabbanci da rainin hankali ku rasa wanda zaku sako a wasan ku sai ni Dan Muhammad Mai nasara, kuma. . . . . . . ". Kalaman da yake shirin furtawa me zafi ne ya samu makalewa sakamakon tashinsa daga Mafarkin da yake yi.

Azabure ya bude idanunsa ganin su Mamy harda Mansur da su Faisal da kannensa mata sun cika dakin fuskokinsu cike da damuwa suke fadin", sannu yaya ". cikin shock rashin kuzari kasala yake jin sautin muryan Mansur na fadin " In zaka kwanta barci ka ringa addu'a ji bi har falo akejin sautin muryanka ". Ya karashe zancen yana mai karasowa kusa dashi.

Ridwan kasa magana ya yi ban da dafa saitin kansa ba abin da yake yi, cikin takaici da rasa dalilin wannan Mafarkin nashi ya sa shi ƙara dago kansa a karo na biyu yana kallon kannensa da Mamy da damuwa ke kwance kan fuskarta, bakinsa na rawa ya ce " Mamy kar ki damu kawai mafarki nayi ". Nan ya shiga ba su labarin mafarkinsa ya kara da bata labarin kauyen da suka je shida Mansur har bige Amatullah da suka so yi da motarsu. Nan da nan Mamy ta rikice mummunan tashin hankali ya bayyana a fuskarta, cikin rawar murya ta ce " Aure kuma? haba ba wannan zancen saidai a mafarki ". Firgit gabakidaya dakin suka kai dubansu akanta. Surutai ta soma bata san tana yi, cikin damuwa ta ce " Ridwan ya yi Aure Hummm". Ahanzarce Anisa ta karbi zancen daga bakinta tana fadin haba Mamy kin ko san me kike fada kuwa?".

Ajiyar zuciya ta sauke kana cikin muryanta da sam babu nutsuwa da sukuni ta ce " kuyi hakuri Wallahi ban san nayi magana ba, Allah yakyauta ". Ta karashe zancen tare da barin dakin cikin hanzarinta. Da idanu suka bita da kallo, Ridwan kallon Kannesa da suke masa sannu da Allah yakyauta ya yi, ganin su ma sun fice daga Dakin da dukan alamu jikinsu a sanyaye yake.

 

 Dawo da kallonsa a kan Mansur ya yi dafe da kansa da ke sarawa kana cikin rashin walwala ya ce, " yau nayi latti dan jirani inje inyi wanka ". Ya karashe zancen tare da barin dakin sam be son Mansur ya fahimci sabuwar damuwar da ta tunkaro shi. Yana shiga ban daki saka yatsarsa daya ya yi abakinsa yana mai kallon kansa acikin madubin da ke makale jikin bangon ban daki, fararen idanunsa da suka kada izuwa ja yake kallo, gaban mirror ya kara kusanto daf da mirror yana mai matse bakinsa domin hana kansa yin kuka, hawayen da yake dannewa ne suka samu damar silalowa daga kwarmin idanunsa, ji kake shar shar kamar bakin fanfo, nan da nan fuskarsa ta dawo kalan kuka, sakin marayan kuka ya yi yana kallon kansa ta cikin mirror, kuka yake wacce ke nuni da zallan bakin ciki, kuka mai nuna tarin ma'anoni da neman agaji a wajen Allah, cigaba da rera kukan yake har sheshekarsa yana fita waje . Mansur da ke danna system cikin tsoro da fargaba da tashin hankali yake kallon kofar ban dakin, hanzarta tashi ya yi tare da zuwa kasa kunnennsa jikin kofar banɗakin domin tabbatar da abin da yake ji, cikin mamaki yake jiyo tabbas kuka ne daga cikin ban dakin. Nan da nan launinsa ya canza zuwa kukan duk da besan kukan me Ridwan yake ba amma zuciyarsa ta bashi a kan kalaman Mamy ne,

, makalewa jikin kofar ya yi, yaringa jan jikinsa har ya gangaro kasa zaune dirshan dafe da kansa. Daga cen cikin ban dakin saida ya yi kukan mai isarsa sannan ya tsagaita tare da fara yunkurin cire kayan jikinsa. Ya dauki mintuna ashirin kafin ya gama wanka, ƙoƙarin fitowa banɗakin yake, ahankali ya sa hannayensa masu taushi domin bude hadadden kofar, mamaki ne ya cika sa jin yana tura kofar domin budewa, ya ji kamar antare wajen, hakan ya sa ya tura da karfinsa. Mansur jin anturo kofar da karfi ne, hankalinsa ya dawo jikinsa, hanzarta tashi ya yi domin ba shi daman fitowa. Ridwan na fitowa hannunsa ɗauke da kayan da ya cire, tawul mai taushi ne ajikinsa. Dawo da ganinsa ya yi a kan Mansur da ke masa kallon tuhuma cikin damuwa, har cikin ransa yake jin sam be shirya yin magana adaidai Lokacin ba, yin hakan ze baiwa Mansur sanin hakikanin damuwar da yake boyewa, kauda kansa gefe ya yi dan baze iya jurar kallon ƙwayar idanun amininsa ba, cikinsu babu wanda ya yi magana kowannensu sakon idanu yake aikawa dan uwansa har Ridwan ya gama shirinsa cikin shigar boyel maroo ba karamin kyau ya yi da shigar ba, takalmansa mai dan karan tsada da agogon diamond da hularsa duk ya sanyasu a uzurce tare da karasawa gaban mirro, daddan turarensa mai sanyi kamshi da tsuma jiki oud collection ya diba tare a tafin hannunsa tare da shafa jikinsa dashi, kallo Mansur ya yi ganin yanda yake binsa da idanu babu kiftawa, hakan ya sa cikin muryansa da sam babu hayani fadin " Dan Allah tashi mu je ko? ". Ya kai ƙarshen zancen yana ƙoƙarin fita daga dakin. Mansur ma tashi ya yi ba tare da ya bashi amsa ba, keyarsa yake bi da kallo yana girgiza kai.

 Bangaren Mamy tana shiga dakinta ta fara safa da marwa yatsarta daya a baki, ta dade tana a wannan yanayin kafin ta yi tunanin kirar kawarta Madina, cikin hanzarinta dannawa Madina kira har sai da ta kusa katsewa, sannan aka daga, cikin murya mai ɗauke da damuwa tabawa Madina labarin damuwarta, daga cen bangaren ta ce, " haba Hajiya Sarah a kan mafarkin Ridwan duk za ki bi, ki daga hankalinki, haba kar ki kuma damuwa ai mafarki ba gaskiya ba ce, ayanda Ridwan yake kwata kwata Mata basa birgesa ke kanki shaidace, dan ke kanki tunda ya girma ya san kansa ba za ki ce ga ranar da Ridwan ya nuna miki kulawa irin yanda d'a yake nunawa Mahaifansa ba, kisha kurumin indai a kan wannan matsalar ne ki shirya nan da kwana uku zan rakaki wajen malamina acen kauyen tsakuwa da ke jahar Kano. "

 

 

 " kema kinsan Ridwan baze taba barina naje har Garin Kano ba, kuma a kanon ma har kauyen Tsakuwa, ina laifi kije a madadina zefi kam, sai ki fada min kamar nawa zan tura miki". Cewar Mamy cikin kasa kasa da muryanta.

 Nan da nan Hajiya Madina ta fada mata tana buƙatar dubu dari biyu ze isa a yi aikin da ya dace. Cikin damuwa Mamy ke jinjina kudin kaf Dakinta ta san ko dubu ashirin babu na kanta bare har ta samu dubu dari biyu, nesawa a tunani ta yi hakan ya sa ta mance waya take yi muryan Madina ne ya dawo da ita hayyacinta tare da jan tsiririn tsaki, nan ta tabbatar mata ta bata sati daya zata san yanda za ta yi ganin ta samu kudaden, domin tashi alwashin in har tana raye Ridwan ba zeyi Aure ba. Zama bakin gado ta yi tana ciza labbanta, maganganun Mafarkin Ridwan ne suke yawo a kwanyar kanta sabuwa ful.

Ghetto

Kashe Gari wunin talata.

Rana ya bude sosai hakan ya sa har cikin dakinsu Amatullah zafi ya damesu sai gumi suke fitarwa dukansu, abun fifita ne hannun Amatullah tana yiwa Papy fifita shi kuwa sai lumshe idanunsa yake alamun sosai yake jin dadin ƙoƙarinta akansa. Gyara zamansa ya yi yana mai kallon ta cikin idanunsa masu tattare da kamala da dattako, a nutse tattare da kamalarsa ya ce, " Amatullah wannan takardan da ke hannuna naki ne, nasan kin iya karatu daidai gwargwadon yanda na koyar da ke, banason ki karanta wannan wasikar har sai ta kankama, ina nufin bayan babu ni ". Ya kai karshen zancen, yana maganar zuci inda yake fadin " Amatullah ki gafarceni, ki yafe min ban da mafita da ya wuce in kama next level.

Abun fifitar ne ya samu damar faduwa daga hannun Amatullah, tashin hankali ya bayyana a fuskarta, murya na rawa ta ce " Papy ka daina maganar mutuwa, ba yanzu ba dan Allah kaɗaina bana jin dadi, ka ce min Allah Swt ya kaddara mana rayuwa da mutuwa, ka ce Allah ne ya hallicemu ya tura Manzon sa Muhammad Rasulillah, ka karantar dani hadisai ka karantar dani karatun boko dai-dai iya karfinka, Papy ni a arayuwata ban taba kwana daki ba sai wannan da muke ciki tun zuwanmu Abuja, Papy kai Mahaifina ne, kaɗaina sare min gwuiwowina, ban da Uwa kaine ya maye gurbinta kuma ka ce ana Aure tsakanin mace da namiji amma Papy kaki yin Aure, naso ace na samu Uwa wacce zata taimaka mana wajen rage kaɗaici amma sam Papy tunda nayi wayau nasan kaina ko fita zakayi saidai ka barni ni kaɗai kaje inda zaka kuma sam baka barin yan gari suga ainahin fuskar ka, bayan ni bana tunanin akwai wa'yanda za su tantance kamannin ka ". Ta kai karshen zancen hannunta cikin nasa, idanunta har sun fara hako ruwan hawaye.

 

 Shi kuwa da idanu ya bita har ta kai karshen zancenta, jikinsa a mace ya kama hannunta tare da sanya mata takarda mai ɗauke da envelope, cikinsanyin murya ya ce " My Friday kar ki damu, ina miki tuni ne bawai zan rabu da ke ba ne, dan haka tashi mu fita kofar daki mu sha iska domin zafin ya yi yawa ". Ya karashen zancen domin son kawar da hankalinta a kan tunaninta. Stil dai kallonsa take amma sam ta kasa gasgata maganganun da ke fita daga harshen bakin sa, suna fita, da idanu take binsa duba ga yanda yake jan hannunta izuwa wata dakali da ke dan gefe da bukkansu

 Kasar Benin Cotonou

 Bayan kwana biyu ta kama Alhamis wajen azhar, Umar Faruk ya shirya tsaf cikin shirinsa na wanda ze yi tafiya, zaune yake gaban Mahaifiyarsa A'isha wacce ta dan fara samun sauki gefenta Yasmin ce da ke mata fifita dan hatta wutar lantarki sashin nasu yankeshi mai Gidan ya yi. Cikin tausayawa yake sanar mata tafiyar da zeyi ta zo har Abuja ze je wani abokinsa ya gayyacesa yin aiki tare dashi, Mama cikin jin dadi yau Danta ze dan samu abun da zai kara rikesu ta ce " Allah Ubangiji ya kai ka lfy ya sa asamu abin da akaje nema, ya kare ka da sharri mutum da Aljan ".

 Da Ameen ya amsa yana mai lumshe idanunsa, domin ba karamin tasiri da kuzari addu'ar Mahafiyarsa ta sashi ba, kallon Yasmin yake yanda ta dawo kalan tausayi, cikinsanyin murya ta ce " Yaya Please kayi zamanka banson tafiyarka ka, ka zauna kacigaba da kanikancin ka tinda ana dan samu babu laifi". ta yi furuncinta da iyakar gaskiyarta.

 Mama da ke zaune kallon ta take ban da murmushi ba abin da take, cikinsanyin murya take nunawa Yasmin cancartar tafiyarsa domin nauyinsu ya rataya a wuyarsa ga kakarsa ga ita, badan rai yaso ba hakanan Yasmin ta fara kukan rabuwa dashi, shima hakan ba karamin tada masa hankali ya yi ba, ganin Mama itama ta biyewa Yasmin suna kukan atare, jikin asanyaye ya ce " Mama ku daina min kuka, Please addu'a kawai ta isheni zanje nayi sallama da Kakata daga nan mu zarce tasha ".

 Mama da Yasmin share kwalla sukayi inda suka rakashi har sashin kakarsu da ke zaune tana cin kilishin da Umar ya kawo mata adaren jiya, tana ganinsa da jakarsa ta fashe da kuka. Cikin muryanta na tsufa ta ce, " Umar tafiya zakayi dagaske? ". Ta karashe zancen tana kallon Mama da Yasmin da suke goge kwallansu.

" ku min addu'a". Shi ne furucin da yasamu damar fitowa daga bakinsa muryansa na rawa, hawayen da yake dannewa ne yasamu damar silalo daga idanunsa ganin be iya cigaba da kallon yanda kaka ta dafe kai tana kuka ya sa ya fice daga Dakin ba tare da ya musu magana ba.

Yasmin da Mama sam ba su ga fitarsa ba, hakan ya sa su fadin" kai Umar zo kaka ta maka adua ". Wayam da suka gani ya sa jikinsu macewa. Nan da Kakata ta shiga masa adu'oin kariya cikin muryan kuka da hawayen da suka cika kwarmin idanunta.

Abuja Ghetto

Bayan sallah magrib sosai Garin ya hade, ban da tashin iska babu abin da kake ji, iska sai fatali take da abubuwa marasa nauyi robobi ledoji har lemar jama'a tana ta dagawa sama, Amatullah rike da tochla hannunta ganin yanda iska duk ya kada masu robobinsu, kan ka ce mai aka saki tsawa daga sama, wanda ya firgita, ahanzarce ta yi cikin dakinsu jin a kece da ruwa mai karfin Gaske, bakin ta na rawa ta ke fadin " Papy kaga ruwan da ake tsulawa kuwa? ". Firgita ta yi ganin babu shi babu alamun sa, tunani ta fara to ta ina yabi yafita kodai yashiga banɗaki ne, hakan ya sa ta dan zauna tana sauraren yanda ruwan sama ke sauka har cilin din dakin nasu da ke dan yoyon ruwa kadan kadan so take ta dauko roba ta tare domin gujewa jikewar dakin. Har ta tara robar ji take shiru Papy be dawo ba, hakan ya sa cikin ruwan ta fito ta fara ihunn kiran " Papy! Papy ! Papy ! Kana ina !!? ". Shiru takeji babu amsa sai ta karar ruwan sama.

 Tunani ya fado mata ta leka ban dakin tana dubawa nan ma taga wayam, "innnalillahi wa'inna ilairajun". Ta shiga maimaitawa. Bata damuwa da ruwan da ke zuba daga tsakiyar kanta zuwa gangar jikinta ba. Kuka mai gunji take tana ihuu iyakar karfinta, ji ta yi an dafata da baya, arazane ta waiga, wanda ta gani ya sa ta fara ja da baya baya cikin ruwan tana ja da baya yana kara kusanto inda take har ta kai da ya. . . . . . . . . . . .

***** 

Littafin nan, na kuɗi ne. Da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. Hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Kibiya dari biyar kacal domin samun shiga group na musamman.

Domin Karin bayani a tuntuɓe ni ta wannan lambar 09069080725 ko + 22953726162.

Siyen nagari mai da kuɗi gida.


Post a Comment

0 Comments