Makauniyar Shari'a [Kashi na 5]

    Ya Allah ina godiya da bisa dukan ni'imominka a gareni. Yanda na fara Lafiya ka ba ni ikon gamawa Lafiya. Alkhairan da ke cikinsa ka ba ni ladansa, sharrin da ke ciki ka yafe min.

    Allah ka dauka Alkalamin marubuta a duk in da suke

    Gaisuwa ta musamman gareku na hannu dama ta.

    • Besty (Sarat Alkasum)
    • Maman Amatullah
    • Ummu shkura
    • Fadila Sani Bakori
    • Maman Sharifa
    • Mamashu
    • ABBA Yakubu
    • Dan Salma
    • Da Autan Jarumai.

    Waɗanda ban samu damar kiran sunansu ba, duk ina mika sakon gaisuwata a gare ku.

    Yayyena abun Alfaharina

    • Hadiza
    • Hussaina
    • Hassana
    • Maryam

    Gaisuwa ta mussaman gareki

    Anty Zulai, mutan Kano, surukar Auta na.

    Jarumai Writers Association, marubuta masu aiki da Jarumta wajen Fadakar da Al'umma

    MAKAUNIYAR SHARI'A

    MAKAUNIYAR SHARI'A

    IKILIMA ADAM (Kyauta daga Allah)

    09069080725 ko +22953726162 (Whatsapp kaɗai ban da kira)

    Marubuciyar da ta nishaɗantar da ku a littattafanta kamar haka:

    1. Kai ka ja wa kanka
    2. Kanwata
    3. RAI DAYA (Jan Za ki)
    4. RUDANI (mai tafiya daukan rai)

    Da sauran su.

    Yanzu ga ni ɗauke da sabon littafina mai suna MAKAUNIYAR SHARI'A

    *****

    SHAFI NA SHA TAKWAS

    Cikin tsananin tashin hankali Yasmin da su Fauziyya su kayi kanta Cikin rudewa, ajijjege suke girgizata dukansu amma ina sam bata numfashi, isowar Jami'an tsaro ne ya sa aka fara jan su baya, kana cikin yan sanda suka ciccibeta tare da yin farfajiyar kotun da ita cikin hanzari, sai a sannan Alhaji Isah ya kai dubansa a kan yanda yan sanda wasu sun rike kafafunta wasu sun tallafeta ta kai da gangar jiki, sosai jikinsa ya yi mugun sanyi, kasa ɗauke idanunsa ya yi ganin anyi cikin motar yan sanda ankwantar da ita, kana su Yasmin duk sun zagaye motar suna ƙoƙarin ganin sun shiga, gani ya yi yan sanda sun hanasu, kanwarta Hajara kaɗai suka bari ta shiga motar amma su kam, sun nuna sai an tashi daga zaman Shari'a za su je asibitin. Ganin cigaba da kallonsu ze tuna masa wani abu ya sa shi ɗauke kallonsa akansu yana mai jero tsaki.

    Bayan motar yan sanda yabar kotun su Yasmin suka dawo suna kuka kamar wayanda aka sanarwa mutuwar Mamy. Suna zama kan kujerar da suka tashi suka kai dubansu a kan Isah Sharifai dashi ɗin ma suke yake kallo, wani uban harara suka watsa masa dukansu lokaci daya, Yasmin da yatsa ta nuna shi tana masa alamun da sai ya gani, fahimtar hakan ya shi kwabe baki yana mamakin tsaurin idanu da rashin tsoro irin na Yasmin.

     

     Basma kuwa kowannensu da mamaki suka kallon réaction din Yasmin a kan Alhaji Isah, gabakidaya kotun jikin kowa ya yi sanyi zuwa yanzu sun fara raba tunaninsu gida biyu in ma kazafi aka mata ko kuma tashin hankali tona mata asiri da ya yi a idon duniya shi ne ya sa ta faduwa.

     Gyaran murya Alkali ne ya sa kowa ya nutsu harda Barister Hadiza da kanta ya yi mugun daukan zafi.

     " korafi be karbu ba, dan haka Barister kina iya cigaba" ya yi shiru yana kallon Barister tana jinjina masa kai alamun godiya.

     Barister Hadiza cikin tafasar zuciya da ɗaukan Alwashin sai ta kwatarwa, A'isha hakkinta.

    " Ya mai Girma mai Shari'a ina son kotu ta yi la'akari da zaman zamanin nan da ake ciki da yanda kishiya ke iya shiga ta fita ganin ta fitar da abokiyar zamanta, a bayanan Isah ya nuna cewa da taimakon Basma ne ya san ana cin Amanarsa, ma'ana dai Basma ce ta sanar masa, ta yi amfani da shirinta wajen tarwatsa auren A'isha da mijinta, idan kotu zata duba lamarinnan da idanun Basira, ya fada mana cewar A'isha tana barci, wannan ze nuna Lallai anyi amfani da magani wajen sumar da ita, sannan in kotu zata yi duba a kan yanda A'isha Muhammad ta fadi a nan kotun, wannan yana nuni da cewar bata san dalilin da ya sa ya kaurace mata ba sai ayau dinnan, duk wanda ya ji mummunan kazafi daga sama tabbas yana iya faduwa, ina son nayi amfani da wannan damar wajen rokon a daga Shari'a domin mu kawo shedu a gaba, Nagode ya mai girma mai shari'a". Tana kai nan ta zauna kusa da abokin aikinta, a sace take kallon Lauyan me kara wanda ya kasance Mijinta ne, harara ya aika mata wanda ya sa ta sauke idanunta kasa tare da mai da hankalinta a kan Alkali da ke magana.

     " Abisa rashin lafiyar wacce ake kara, ya sa za'a dakatar da sauraren wannan Shari'a har sai ta warke, sannan tana samun sauki zata koma ta cigaba da zama Gidan Isah Sharifai har sai ankama sauraren korafe korafe, dan haka kotun ta dage wannan Shari'a har sai nan da sati hudu masu zuwa". Alkali ya ƙarashe zancen cikin dattako da kamalarsa gudumar da ya buga ya sa duk wa'yanda suka taru a kan sharia su Sharifai fara fita daga hall din.

     Barister Hadiza Ibrahim, ita da abokin aikin nata hanzarta fita suka yi dan sun gama nasu, suna fitowa haraban Kotun ta tarar dasu Yasmin suna jiranta cikin tsananin damuwa a fuskokinsu, ahankali ta karaso kusa dasu ita da abokin aikin nata, kana cikin tausayi da kulawa ta ce " kuyi hakuri, in sha Allah Mahaifiyar ku shekaru kusan ashirin da ta yi a kuncin ya zo karshe, kunsan an ce bayan wuya sai dadi, jarabta ce ba wanda ya wuce hakan, sannan nasan kuna son sanin wani asibiti aka kai mamarku, Asibitin Camp Ghuezo nan yan sanda da sojoji suke kai marasa lafiya, dan haka ku je umegency, zuwa gobe ina nan tafe domin duba jikin nata, in kuma da wani abun kuna iya tuntuɓata a waya" ta karshe zancen cikin tausayawa. Abokin aikin nata shi ma cike da kulawa yake ba su hakuri da kuma tabbatar za suyi tsayin daka ganin sunyi nasara a zaman kotun. Yasmin da yan uwanta cikin kuka suke wa Hadiza da abokin aikinta godiya, kana suka hanzarta fita daga farfajiyar kotun, suna fita suka hango motar Isah Sharifai shi da ya'yansa sun fice tare da tada musu kurar hayaki. Yasmin cikin fushi ta ce " Allah ya tsinewa Yar bura ubar da ta tada mana hayakin mota, shegu jikokin fir'auna" ta karashe zancen suna mai kama hanyar zuwa asibitin da yake babu nisa da kotun, a kasa suke tafiya.

    Daga cikin kotun kuwa Hadiza Ibrahim bayan abokin aikinta Mahfouz ya fice, ta fara rarraba idanu inda zata hango Lauyan me kara, watau mijinta, ahankali take taku cikin shigarta na lauyoyi tana mai karasowa wajensa fuska ɗauke da murmushi, tana karasowa ta iske tsaye da dukan alamu waya yake amma idanunsa yana kanta yana mai harararta, sosai ta sha jinin jikinta ganin yanda yake bin ta da banzar kallo mai wuyar fassara, yana gama wayar ya fara jero tsaki akai akai, cikin takaici ya ce.

     " Hadiza daman bakinsa darajar aure ba? ".

     Dan ware idanunta ta yi cikinsanyin murya ta ce.

     " Haba baby wannan furucin be dace dani ba ".

     " Au !! be dace da ke ba, dan tsabar rainin hankali tun a Gida me ya sa baki fadamin ke ce wacce za ki kare Matar Isah sharifai ba sai da nazo kotu na ganki, kuma ban da rashin kunya dani za kiyi jayayya".

     " Hum am sorry baby ai ni kaina bansan case zata hadamu ba sai yau dana zo nagani kuma baka fadamin cewar kanada sharia da yasha shafi Isah Sharifai ba, yanzu de ta faru ta kare kayi hakuri, maganar jayayya aiki ne ya kawo hakan ka daina sako aikinmu acikin tarayyar aurenmu".

     " Hadiza maganar gaskiya bazan boye miki ba ina son ki ajiye wannan case din, Umarni na baki ba shawara ba". Ya karashe zancen tare da shiga motarsa a zafafe.

     Cikin zazzare idanu take juya kalamansa, cike da takaici ta bude murfin motarsa ta shiga gaba ta zauna, tare da rufo kofar hakan ya sa ya tada motar yana tsuki.

    Saida suka dauki hanya babu wanda ke kula dan uwansa.

     

     " Maganar in ajiye case din nan ma, bata taso ba sai de mu ajiye dukanmu shi ne adalci ".

     Da idanu yake kallonta yana dan ciza yatsa, kana ya ci gaba da tukinsa yana girgiza kai.

     Asibiti

    Cirko cirko dukansu su kayi tare da Kanwar Mamy jin likita ya ce musu zuciyarta ya bugu sosai, tana buƙatar taimakon gaggawa, cikin tsananin tashin hankali Yasmin ke fadin " yanzu kudin da za'a kashe ina za mu same shi?".

    Fauziyya ta ce " ai yan sanda sunce sai angama komi za'a biya ta" karashe zancen tana kai dubanta a kan Abdullahi abokin Umar.

    Shi ma Umar cikin juya yi yake fadin " in sha Allah, za'a samu mafita, zanyi iya ƙoƙarina ganin an samu kudin da aka bukata ai Umar ya wuce haka a wajena, a gobe nake son zuwa Abuja amma ya kamata ace munje da wata daga cikinku". ya yi furucin yana jinjina lamarin.

    Cikin kadawar harshe Yasmin ta ce.

     Ni tunda ba nida aure ina iya bin ka mu je su kuma su zauna tare da Mama, sannan ka sanarwa me gidan nasa da ba su hadu ba, yana heatquater na yan sanda ya je cen kafin mu iso " ta yi furucin cikinsanyin murya.

     Fauziyya cikin tausayawa ta ce " a'a Yasmin ba za ki je ba, ke fa macece, kuma yarinya me za ki iya yi kuma bayan babu masaukin sauka, kai ko da akwai ma ba za kije ba, Abdullahi dai ze je mana sai a samu wanda ze masa rakiya shi ne kawai, ai duk halin da ake ciki za mu ringa samun labari ".

     Yasmin cike da sanyin jiki da yanayin ta da babu kuzari, ta ce" babu komai a yi hakan. ".

     Abdullahi kallon yanda Yasmin ta yi mugun rama yake, harda yanda idanunta suka firfito waje kamar wata mayya, wuyanta yake bi da kallo yanda duk kasusuwa yake hanga babu tsoka. Kar kada kai ya yi cike da tausayawa ya musu sallama a kan gobe ze zo masu sallama kafin ya su fice Abujan.

    Kaka Mariya ban da tagumi da jan carbi ba abin da take daga zaune.

    Abuja

    A yau ne Rid ya koma aikinsa na dan sanda, be shirya da wuri ba sai wurin karfe biyu na rana, ya fara kiciniyar fita cikin kakinsa, ya dade adaki yana gyara kansa, yana kallon kansa ta cikin madubin dakin sa, manyan manyan takalminsa na aiki da ya sanya yake kallo in har babu sauran kura akai, ganin tsaf yake ya sa shi daukan wayoyinsa a kan mirror tare da sanyasu a cikin aljihun wandonsa, yana bude kofar dakinsa, da kafafunsa ya tura kofar ya rufe gam, wanda ƙarar bugawar kofar ya sa su Mamy da ke zaune ita da Madina, zabura dan rabon su da su ji ya buga kofa da karfi tun lokacin yana aikinsa na Dan sanda. .

    Tsoro da fargaba ne ya cika Mamy jin takun tafiya daga saman bene, yanda takalminsa yake bada sautin kara.

     Cikin zallan mamaki Mamy ke kallon saukowarsa kasa ita da Madina, ko da ya karaso kallonsu yake su ma shi suke kallo, cikin takun kasaita da tsare gida yake gaishe su.

     Kana ya kara kai dubansa a kan Mamy, murya na rawa ya ce " Mamy na koma aikina dan haka sai na dawo, ki dauki atm dinki na miki transfert, kana drever ze kawo kayan abinci, duk abin da Babu ku sanar masa ze kawo muku" yana kai karshen zancen nasa ya kama hanyar fita cikin tafiyarsa me ban tsoro.

    Madina ba karamin kwarjini ya mata ba yanda kasan yau ne karo na farko da ta fara ganinsa.

    Kallon kallo sukewa juna ita da mamy.

    Mamy ta yi ƙarfin halin fadin" Ridwan yana nufin duk asirin da aka masa sai da ya koma aikinsa? Innalilahi wa'inna ilairajun, Madina ba ni atm dina dan Allah shirya muje wajen malam da ke nan abuja taya akayi hakan ta faru ", ta karashe zancen cikin kuka da sabon tsoron da ya shige ta.

    Cikin zafin nama suka fara shirin fita ita da Madina domin zuwa wurin Malam.

     

    Amatullah har sashin da marayu ke rayuwa, Hasina ta rakata domin kai musu ziyara, suna isa wurin cike da mamaki take kallon yanda marayun wurin suke rayuwa cike da tsafta da kyawawan muhalli, cike da jin dadi ta ga wata yarinya wacce za suyi shekaru daya da ita a cikinsu, kayataccen murmushi ta sakar mata, haka ma Yarinyar ta mai da mata martani tare da bata hannu dan suyi musabaha. Suna hada hannun wani annuri da jin dadi ne ya ratsa Amatullah wannan shi ne karo na farko arayuwar da ta yi mu'amala da yar uwarta mace wacce suke tsara cike da mutuntawa.

    Cikin shauki ta ce " ya sunanki?. ". ta yi mata tambaya idanunta na cikin nata.

     " Suna na Saudat, ina da kannen casa'in da uku " ta yi furucin fuska ɗauke da annuri.

     Amatullah cikin zazzare idanu take kallon Hasina da ita ma din ita take kallo tana murmushi, cike da rudewar tunani Amatullah ta sake kai dubanta a kan yarinyar tare da fadin.

     " kannenki casa'in da uku, taya hakan ta kasance ban taba ji a tarihi ba ".

     

     Daga sama suka ji muryan Karfin Iko yana kusanto inda suke cikin dan daga murya ya ce.

     " Saboda su din Marayu ne sun zama uwa daya Uba daya " ya ƙarashe zancen yana karasowa kusa da su.

     Saudat ganin isowarsa ahanzarce ta durkushe kasa, cike da ban girma ta ce .

     "Barka da zuwa Abbanmu" kokan ta gama rufe baki dukannin yaran suka zagaye shi, cike da so da kauna, suna masa barka da isowa.

     Shafa kawunansu ya yi daya bayan daya kana ya kai dubansa a kan me Kula dasu, ba tare ya amsa mata gaisuwa ba, kai kawai ya gyada mata yana mai dawo da kallonsa a kan Amatullah da ruwan hawaye ya cika kwarmin idanunta, sosai take jin ganin su a haka ya tuno mata wasu abubuwan, yanzu ta kara tabbatar da Karfin Iko wani mutum ne, na musamman duk da kasantuwarsa dan Kidnapping, muryansa ce ta katse mata tunani cikin jin yana fadin.

     " Amatullah taho muje kano mu dawo". ya kai karshen zancen yana mai mika mata nikaf ta sanya.

     Hannu na rawa ta amsa cikin jin dadin za su je ganin Salim, tana amsa daga hannunsa, Hasina ta fara ƙokarin sanya mata bayan ta sanya hijab.

     Be jira cewar su ba ya yi sallama da y Hasina da yaran da kuma me kula dasu.

     Yana yin gaba Amatullah ta bi sahunsa tana kallon yanda ya jefa jakar kuɗi acikin motarsa, tare da shiga cikin, yana shiga ya bude mata kujera mai zaman banza, ahankali take taku kamar bata so har ta sanya fararen kafafunta cikin motar.

     

     Ridwan daga wajen aiki ya fito domin ze je super market yin siyayya, ya kai kusan mintuna talatin yana diban abin da yake so, koda ya gama siyayyan har cikin mota aka kai masa kayan nasa, cike da hanzarinsa yake ƙoƙarin komawa wajen aikinsa domin kayan abinci da kukunsa ze ringa masu girki a wajen aiki ne ya siya, azafafe ya ba motarsa wuta ganin babu motoci masu tahowa.

     Karfin Iko saida ya zo gab da Motar Ridwan hankalinsa ya yi mummunar tashi ganin number motar Ridwan, da baya baya ya fara jan motarsa domin kaucewa Ridwan din. Amatullah cike da mamaki take kallon yanda Motar Rid yake turo motarsu da karfi, cikin tsananin tsoro da fargaba ta ga yana ta kara tura motarsu da tashi Motar, cikin tsananin tashin hankali karfin Iko ya fito daga motarsa ya diba aguje, gudu yake ba kama hannun yaro.

     Ridwan da ke kallon yanda karfin Iko ke gudu, murmushi gefen baki ya yi kana ya sauko daga cikin motar, cikin zafin nama ƙoƙarin bin sahun karfin Iko yake ya ji ihunnn Amatullah tana buga gilashin motar, alamun abude ta. .

     Cak ya tsaya tare da. . . .

    makauniyar Shari'a taku ce

     Comment and share

    [10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat. whatsapp. com/KgIV8gvcWZi7LcGiwtpDPa

    Makauniyar Shari'a

     Sai a Lahira

     Na

    IKILIMA ADAM

     (Kyauta daga Allah)

     09069080725

    Jarumai wait association

    SHAFI NA SHA BAKWAI

    " Alhaji Isah yana neman a raba shi wa'yannan yayan da ba ta hanyar Aure aka haifa masa su ba" ya karashe zancen tare da jan numfashi.

     " Baya ga haka tana zaune masa gida da daurin gindin Mahaifiyarsa, abisa adalcinsa na gudun yiwa Mahaifiyarsa abin da be dace ba ya sa ya yi ƙararsu dan a raba shi da ya'yan a kuma musu iyaka da shi, sannan su daina amfani da sunan Isah sharifai, idan kotu ta nemi shaida muna nan dan gabatar dasu, dan haka ina rokon kotu da ta yi gaggawar bi masa hakkinsa a kan wannan matar dan ya zama iznah ga sauran matan aure da ke gidajen su" yana kai karshen zancen ya koma ya zauna kusa da abokiyar aikinsa.

    A'isha ba karamin gigicewa ta yi ba jin yanda Lauyan me kara ya ringa jifanta da kalamai masu hatsarin gaske ba tare da ta ankare ba, hawaye masu zafi suka fara bin kuncinta, Firdaus da ita ma hawaye ke bin kuncinta jin wai su shegu ne ba ya'yan Sunnah ba, sam a ranta bata jin zata iya yafewa Alhaji Isah sharifai da Matarsa. Kai dubanta ta yi a kan Mamy da ke kuka ahankali tana girgiza kai domin dacin maganganun sun ratsa dukan sassan jikinta, muryan Lauyan me kare su ne, ya sa ta dago kai tare da kai duba a kan ta.

    Lauyan me kare wanda ake kara cike da kasaita da jin izzah ta fara magana ba kakkautawa.

     " Ya mai Girma mai Shari'a, abunda Isah Sharifai yake fade a kan A'isha Muhammad, duk karya ce kazafi ce ya yi ne domin ya bata mata suna a idon duniya, domin bahaushe yana cewa komin nisan dare, gari ze waye, wannan ke nuni da duk inda gaskiya take za ta yi halinta, A'isha Muhammad ita ce matar da su kayi Auren saurayi da budurwa idan kotu taban dama zan so Alhaji Isah Sharifai ya bayyana a gabanta " ta kai karshen zancen tana mai juyo da kallonta a kan Isah Sharifai da ya tashi tsaye cikin farar shaddarsa fuskarsa ba yabo ba fallasa.

     Alkali gyaran murya ya yi tare da fadin " Kotu na son ganin Isah Sharifai ". Ko kan ya gama rufe bakinsa har Alhaji Isah ya bayyana wajen da aka tanada domin amsa tambayoyi.

    Shi kam Alhaji tsaye yake yana mai kai dubansa a kan Basma da ke kar kada masa Kai alamun karfin gwiwa take bashi, fahimtar hakan, lumshe idanunsa ya yi yana mai juyo da kallonsa a kan Barister Hadiza Ibrahim da ta yi tsaye gabansa tana kare masa kallo na tsanake.

    Cikin gyara tsayuwarta da gyra kwalar rigarta cikin yakini da sanin makaman aikinta ta ce.

     " kotu zata so jin sunanka".

     "Suna na Alhaji Isah Muhammad Sharifai.

     "Ko zaka iya gayawa kotu meye alakar ka da A'isha Muhammad".

     " A'isha Muhammad Matata ce ". Ya fada yana rintse idanunsa.

     " Gud da jin wannan amsar, ko zan iya tsanin tun wani lokaci kuka yi aure da ita da kuma. . . . ". Kasa karasa sauran kalamin nata ta yi jin dakatarwa daga Lauyan me kara cikin kakkausar murya.

     Lauyan me kara ne ya tashi cikin dan bacin rai tare da fadin.

     "Objection My Lord, be kamata Lauyan me kare wacce ake kara ba, taringa shiga hurumin da ba nata ba, ma'ana ba dai-dai ba ne ta tsaya bincikar rayuwarsu na baya, domin bashi ne ya tara mu ba ". Yana kai karshen zancen ya zauna yana mai da numfashi.

    Alkali cikin hanzari ya ce " korafi be karbu, Barister kina iya cigaba" ya yi furucin yana mai kallon yanda ta rinsina kai alamun girmamawa.

    Cike da jin dadi Barister ta ce.

     " Alhaji Isah ka sanar da kotu tun yaushe ku kayi aure da kuma lokacin da ta fara haihuwa, shin Auren saurayi da budurwa kuka yi ko a bazawara ka aure ta. "

    Alhaji Isah cike da dan tsoro yake jera tamboyin Barister, da jim ya yi alamun tunani kana ya dan saisaita muryansa cikin kuzari ya ce " munyi Aure da A'isha shekaru talatin da bakwai da suka wuce, kuma tun tana yar shekara sha biyar aka ba ni aurenta, budurwa na aure ta ba bazawara ba ".

     " Alhaji Isah ka ce a budurwa ka aure ta, shin da ta tare agidan naka ta zo da ya'ya ne? ".

     " A'a bata zo dasu ba, kuma a nan gidan ta fara haihuwa in da ta haifi Usman wanda mukewa lakabi da Balarabe".

     "Ya'yanka nawa da A'isha?".

     

    " Babu ko daya domin cin amanata ta yi tana tarayya da wani adakina a kuma kan gadon auren mu na sunnah" ya sa nayi bincike na tabbatar wa'yannan ya'yan dukansu ba nawa ba ne ".

     Barister rintse idanunta ta yi daga ita har Mamy da su Mariya da Fauziyya har ma da yan uwansu.

     

     Ɓangaren su Basma murmushi suke ita da ya'yanta har da yan uwanta, kana suna ta jifan su Yasmin da harara.

     Lauya cikinsanyin da jikinta ya fara dauka ta ce.

     " Matan ka nawa? ".

     " Biyu ".

     " Lokacin da ka fara ganin wani yana shigo maka gida har kan gadon barcinka ka kara aure ko kuwa ita kaɗai ce a lokacin ".

     " Eh na ka Aure lokacin ma Amaryata shekarta uku agidan Sannan na farga".

     "Taya akayi ka farga da kuma da wani lokaci ne ka fara ganin alamun cin amana daga matar ka. "

     " Na kamasu ne da rana tsaka a kan gadona bayan sun gama Alfasha su ".

     

     Shin da ka shigo ka gansu, Matarka A'isha ta san hakan? ko dai bata san ka ganta ba ".

     " A'a ita a lokacin har ma ta yi barci, kwarton dai na gani, ko da ze fice daga dakin nata cikin tsoro yake fadamin dan Allah na yafe masa, wallahi sharrin shedan ne, kuma ya'yan da ta haifa nashi ne domin yana gudun Allah ya kamasa da hakkin cin amanar aure da kuma haihuwa da matar wani " ya karashe zancen cikin kunan rai da damuwa da kuma wasu hawaye masu dumi da ke sassarfo masa a fuska ba tare da ya ankare ba.

     Daga cikin kotun har ma da wa'yanda Shari'a be shafe su ba kowa saida ya rike kansa yana jujjuya kalamansa.

     Mamy kuwa kuka take iya karfinta, kuka take kamar ranta ze fita dan bakin ciki. Hakama su Yasmin kuka suke rerawa tare da yan uwansu.

     Alhaji Isa cikin zubda hawaye masu zafi daga idanunsa ya ce.

     " Ni dan halak ne bana manta halarci amma bazan iya zama da mazinaciya ba, badan Basma ta ankarar dani haka ya'yan nan za su gajeni bayan babu raina, kuma yanda na lura Mahaifiyata tana bayan su hakan ya sa na kaurace mata na daina mata dawainiya na barta dasu dan a ganina Uwa ta fi kowa sanin zafin Danta, amma ni sabanin hakanne, ya !! bazan share lamarinsu ba in rungumi me kaunata ba, Usman da ya fahimci ni ba Mahaifinsa ba ne tun wuri yabar gida ya shiga duniya wanda har yau din nan be waiwayo ba. ". Yana kai karshen zancen ya fashe da kuka me nuni da zallan bakin ciki da yake dannewa aka tono masa sabuwa fil.

    " kuma tun daga wannan lokacin ban kara ganin wannan mutumin ba, Basma ta ban Shawara nayi awon jini domin tabbatar da in dagaske ba ya'yana ba ne, wataran na tara duka yaran nawa nayi muka kaisu asibiti nida Basma, koda akayi awon result ya nu. . . na. . . ba. . . ya. . . ya. . . na . . . ba ne ". Ya ƙarashe zancen cikin kuka mai tsarkewa numfashi.

    " A ganina ba dukan namiji ne ze yarda ya kara barin matarsa da ta ci amanarsa ba kuma ta haifa masa shegu, suci gaba da zama gidansa ba, sanin babu inda zata je yasa, na kyalesu na fita harkansu na rungumi Matata da ya'yana". Yana kai karshen zancen ya dukar da kansa.

     Murmushi kwance a fuskokin Basma da ya'yanta harda yan uwan nata.

     

     Gabakidaya All din wajen sosai da yawa suka tausayawa Alhaji Isah, kana suka fara Allah wadai da halin A'isha da Mahaifiyarsa.

     Barister Hadiza dan jimm ta yi kana cikin rudewar tunani da rashin kuzari ta ce.

     " Alhaji Isah in kotu ta nemi shaida shin zaka bayar? da result din hawan jinin da aka yi a shekarun baya ".

     "Kwarai kuwa, nazo da shaida, in kotu ta nemi zan bayar a duba". ya kai ƙarshen zancen cikin tafasar zuciya.

     Barister Hadiza Ibrahim juyowa ta yi tana kallon Alkali, kana cike da ban girma ta ce.

     " Ya mai girma mai Shari'a ina son kotu mai Alfarma ta yi la'akari da cewar Alhaji Isah sai bayan ya kara Aure ne ya fahimci matarsa tana kawo maza acikin gidansa, ya kara da fadin lokacin da ya gansu tana barci, a bisa Mahanga ta hankali ya tabbatar da cewar sharri ne daga Amayar. . . . . . . . . ". Sake yin shiru ta yi domin jin korafi daga bakin Lauyan me ƙara.

    Lauyan me kara cikin hargitsi ya ce.

     

     Ya mai Girma me Shari'a be kamata Lauyan me kare masu kara ta shigo da kazafi acikin bayananta ba. ". Ya yi furucinsa a zafafe.

     Alkali ta cikin glass din idanunsa yake kallon Lauyer Hadiza Ibrahim, sannan ya kara kai dubansa a kan yanda hankalin kowa ya tattaru akansa, cike da yakini ya ce.

     " Korafi. . . . . . . . . . ". Saurin dakatawa ya yi sakamakon ganin Mamy ta zube kasa sumammiya.

     

    Cikin tsananin tashin Yasmin da su Fauziyya suka yi. . . ., .

    Makauniyar Shari'a

    Kuke karantawa daga Alkalamin (kyauta daga Allah.

    09069089725

    [10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat. whatsapp. com/KgIV8gvcWZi7LcGiwtpDPa

    Makauniyar Shari'a

     Sai a lahira

     NA

    IKILIMA ADAM

     (Kyauta daga Allah )

    09069080725

    Jarumai writ associations

    Shin kin kuwa san illar da infection ke yi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

    Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga  ba suke nan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, za ki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

     Ga mai bukata ya tuntuɓi Wannan number

    09069080725

    SHAFI NA SHA TARA

    Cak ya tsaya tare da kai dubansa a kan yanda take bugun gilashin Motar da iya karfinta, juyowa ya yi inda take yana doso wajen motar a zafafe, ita kuwa ganin isowarsa ya sa ta tsaida buga Gilashin tana kallonsa ta cikin nikaf, shi ma kallonta yake babu ko kiftawa, kusan mintina daya suka dauka idanunsu tsarke cikin na juna, ko wani dakika daya yana tafiya da bugawar zuciyarsa, firgit hankalinsa ya dawo gangar jikinsa, kana ya idasa kai hannunsa kan murfin motar, yana latsa madanni bude murfin idanunsa na kanta yanda take ta zazzare idanu kamar ta ga mala'ika, a tarihin rayuwarta

    tana mugun tsoro ta yi tozali da dan sanda ko soja. Ko da ya bude Motar, gani ya yi ta cire nikaf din, kallo daya ya mata ya murtuke fuska tamau, cikin kakkausar murya mai amo ya ce,

    " Ke!! me kike nema a Motar Karfin Iko" ya yi magana a tsawace.

     Tsabar gigicewa kadan ya rage Amatullah bata saki fitsari a wando ba, tunda ta taso bata taɓa shiga tashin hankali makamancin wannan ba.

     

     " Ina magana !! kin min shiru kinga wasa a cikin kwayar idanuna ne?" ya kai karshen zancen yana mai zazzare mata idanunsa da suka canza launi daga fari zuwa jajir.

    Kar kada kai ta yi tana girgiza kai, ba tare da ta ankare ba, ta saki fitsari mai dumi ajikinta.

     Rike da kungunsa yake sake bin ta da kallo in har hasashen gaskiya ce wannan ita ce yarinyar da ya kusa bugewa da mota a kauye, kuma ita ce yaga hoton mai ɗauke da sunan Amatullah Haruna Karfin Iko, sosai ya ji wani tsananin bacin rai ya kara shigarsa. Da idanu yake bin ta da kallo masu rikitarwa.

     " Zan kai ki heatquater na yan sanda, alamu sun nuna kema babbar yar ta'adda ce har da jakar kudade a gabanki, ki hanzarta fita daga motar tun kafin abinneki babu jam'i " tun kan ya gama rufe bakinsa aguje ta yi wuff ta sauko har jikinta na markakata, tana fitowa babu abin da yake gani tattare da ita sai zallar kuruciya da karancin shekaru dan a iya hasashensa ya san bata wuce shekaru sha biyar zuwa sha shida.

     Ɗauke idanunsa akanta ya yi tare da dannawa kira ga yaransa, sanar musu inda yake ya yi kana ya katse wayar yana mai kallon yanda Amatullah take ƙoƙarin mai da nikaf dinta. Tsaki ya jero cike da takaicinta ya ce. .

    .

     "Yawancin irinku masu sanya nikaf ire ire-irenku babu gaskiya a tattare daku, in kika kuskura kika mana karya aduk abin da za mu tambayeki to wallahi sai kin raina kanki ". Ya ƙarashe zancen yana kallon yanda take rawar dari dari. .

     Kar kada kai ta yi kamar kadangaruwa, shi kuwa dan matsawa daga inda take ya yi yana mai cigaba da amsa kiran da ke shigowa wayarsa.

     Ba'a dau lokuta masu tsawo ba, yaran nasa duk suka iso, saida suka su kayi dube dubensu a cikin motar karfin iko, daya daga cikin dan sandan ne yaja motar zuwa heatquater na yan sanda, Ridwan kallon Amatullah yake yanda duk ta tsorace ban da mazari ba abin da jikinta yake yi, muryansa da sam babu rahma ya ce.

     Za ki shiga kosai na babbala kafafunki ". Kokan ya gama rufe baki har ta danna madanni murfin motar baya tana ƙoƙarin shiga.

    Atsawace ya ce " Au so kike ki zauna bayan mota ki saida Plan dina ko? ".

     Girgiza kai ta yi cike da tsoro, be kara bi ta kanta ba illah shigewarsa a motar da ya yi ya zauna, ganin har ta shige ne ya bashi damar tada motar, cikin hanzarinsa, yana tuki yana kallon motsinta ta madubin mota.

     

    Unguwar Lugwai

    Sun sha tafiya mai dan nisa kafin Motar Madina ta Paka gaban wani tsohon gida, suna jan birki ba su bata lokaci ba wajen saukowa ba, Dukansu suna sanye cikin Habaya dark bleu, ita Mamy hijab bleue ne akanta ita kuwa Madina tana sanye da bleu din gyale ta yi roll dinsa akanta irin ga yan mata nan . Da idanu Mamy ke bin wajen da kallo kasantuwa an dade an dau lokaci mai tsawo ba su zo ba, tsohon gini ne mai tsohuwar kofar karfe wacce take da tsatsa, kallon junansu suka yi kusan a tare da, Madina cikin kasa da murya ta ce " muje daga ciki, amma ki bari in fara shiga dan in sanar masa da zuwa ki".

     Mamy samun kanta ta yi da gyada mata kai, ganin Madina ta yi gaba hakan ya bata damar bin sahunta, suna tura tsohon kofar suka fada tsakar gidan mai cike da yashi da tarin ledo alamu sun nuna sam ba'a sharar gidan, tafiya suka yi har suka iso kusan dakinsa, sannan Madinah ta waigo, cikin kasa da kasa murya ta cewa Mamy ta dan zauna kan dakalin da ke wajen, hade da bata dan kyalle daga jakarta dan ta goge kurar wurin kafun ta zauna, koda ta mika mata shigewa ta yi daga ciki, tana shiga iske shi zaune ta yi yana cin farfesun kaza, yana ganinta, washe mata manyan manyan hakoransa masu tsayi da tsini ya yi wajen fadin "

    Barka da isowa ".

     " Yawwa barkaɗai" tana mai kara gyara zamanta a kan tabarma.

     

     " Yawwa Malam ina tare da Saratu nace ta dan jirani daga waje, kasan dai na gaya maka kar ka bari ta san, ina shiri a kan sai na auri danta kuma abin da bata so sai ta gan shi wlh, ai bata isa ba, tunda ba zeyi aure ba ni kuma ina sonsa sonda ban taba yiwa Mahaifinsa ba tun yana raye ba, dan haka ka sake ba ni sabon hadi dan wlh yaron nan aikin nan da akayi ya karye ".

     Malam da tunda take magana da idanu yake kallonta, cikin mamaki ya ce " wani aikin  ba suke nan ya karye ".

     

     Turo baki gaba ta yi ta ce " Aikinsa na dan sanda wallahi ya dawo aiki ".

     " Ai laifinku ne, na gayamuku in aka saba sharadi ze dawo aikin nan, alamu sun nuna an samu akasi ne, yanzu tashi ki shigo da ita, amma kafin nan ki sani sai kin auri Ridwan mai Nasara sai kin haifa masa tagwayen haihuwar fari ". ya karashe zancen yana turmushewa da mugun dariya.

     Da murmushi kwance a kan fuskarta ta ce.

     "Wallahi ai inna Auri Ridwan, wallahi na maka Alkawarin gida da mota da miliyan goma " tana kai karshen zancen ta fice da dan hanzarinta fuskarta ɗauke da yalwatccen murmushi.

    Tana fitowa bakinta na rawa ta ce " Saratu mu je daga ciki ".

     Da " toh ". Mamy ta amsa mata kana suka shige dukansu a tare. .

     

     Mamy na ƙoƙarin zama kan tabarma wayarta ya fara ring, ahanzarce ta zaro wayar daga jakarta, ganin number Ridwan na yawo kan screen din wayar, cikin tsoro da fargaba ta fara furta.

    " Innalilahi wa'inna ilairajun".

     Madina da Malam hada baki su kayi tare da fadin " Lafiya me yake faruwa ne?".

     Ridwan ne ke kiran wayata, na rasa taya zan daga bayan nasan bana gida ".

     

     Malam cikin hanzarisa ya ce.

     ".

     Daga wayar babu abin da ze faru. "

     Hannunta na rawa ta daga wayar tare da karawa a kunnenta.

     Cikinsanyin murya take aikawa da sallama.

     Dagacen bangaren yana zaune yaransa ma'aikata zagaye dashi idanunsa nakan Umar Faruk da ke durkushe a kasa gabansa, kara tattara nutsuwarsa sa ya yi a kan wayar da yake tare da fadin.

     "Mamy kina ina ne haka". ya yi magana cikin jiran amsa.

     Daga Mamy har Madina da Malam har cikin kunnensu suka ji tambayar da Ridwan ya mata.

     

     Murya na rawa ta ce " ina. . . . . gi. . . da. . . ".

     " Ah wane Gidan  ba suke nan? Muhallin mu kodai na wasu?"

    ya karashe zancen yana jifan Amatullah da ke cen zaune gefe daya da harara, amsar da Mamy ta bashi ne ya sa shi tattaro nutsuwarsa jin tana fadin.

     " Gidan namu muhallin mu mana, kai ma kasan da zan fita ai zan sanar maka ko, Ridwaan ni fa Mahaifiyarka ce ba fa Matarka ba ". Ta idasa zancen murya na rawa cikin tsoro abin da ze je ya dawo.

     

     Ridwan ahanzarce wayar na kunnansa ya matso da Computer tare da fara yin tracin din layinta a gaggauce, karar keyboard din da yake dannawa har cikin dodon kunnen Mamy, hakan ba karamin gigita ya yi ba, ƙoƙarin katse wayar take domin ta kashe wayar ma gabakida taji yana fadin.

     

    "Am sorry Mamy ai nasan Ni danki ne, daman zan fada miki na Daura Aure, ki sanarwa Mama Madina ta fara ƙokarin hado kayan lalle kafun taron bikina.

    Zumbur Mamy ta mike tsaye har jikinta na kadawa kamar mazari nan da nan ta jike shargab da gumi da dayan hannunta take fita fita, daga Madina har Malam tashi su kayi domin jin me yake faruwa.

     Ƙoƙarin yin magana take ta ji ya kara da fadin " Mamy ki cewa Madina. . . . . . . . . . . . . . .

    .

     Ina barar addu'a daga bàkunanku masu Albarka.

    Makauniyar Shari'a taku ce.

    [10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: https://chat. whatsapp. com/KgIV8gvcWZi7LcGiwtpDPa

    Makauniyar Shari'a

     Sai a lahira

     NA

     

     IKILIMA ADAM

     (Kyauta daga Allah)

     09069080725

     

    Jarumai writ associations

    SHAFI NA ASHIRIN

    " Mamy ki cewa Madina ta dan matsa maganar namu ne ni da ke".

     Mamy cikin kidima ta kalli wayar tare da hanzarta kashe wayar gabakidaya, cikin tsoron da ya lullubeta ta kai dubanta a kan Madina da Malam, tare da fada musu abin da Rid ya sanar mata.

    Agigice cikin dariyar ban takaici Madina ta ce.

     " Ke wallahi karya yake, haba!! ke kin yarda wannan yaron ze yi aure a bazata, haba ki daina daukan maganar banzan nan daga bakinsa ya yi ne dan ya gwadaki ". ta karashe zancen cikin tsoro da faduwar gaba.

    Malam zama ya yi kana ya umarce su da su zauna, suna zama ya fara jan carbi yana yi yana buga kasan da ke gabansa, yana yi yana kallon yanda Madina duk ta duburbuce lokaci daya, mai da kallonsa a kan Mamy da ta zabga tagumi ya yi, cigaba da motsa labbansa ya yi kana ya yi gyaran murya.

    Wanda ya sa daga Madina har Mamy tattaro nutsuwarsu wajen sauraren abin da ze fada.

    " Watau dai maganar Ridwan karya yake beyi aure ba amma kuma a zuciyarsa akwai niya na yin hakan, ko alama kar ku daga hankalinku, ku barsa ya yi auren dan kwata kwata beda sha'awa ajikinsa tuntuni mun ɗauke masa, kuma ko ya yi auren ma na wucin gadi ne, na fa gayamuku baze taba kusantar wata ya mace ba, saidai akwai hanya daya da za mu bi wajen kauda hankalinsa na har abada". ya yi shiru yana kallonsu.

    Cikin hanzari suka hada baki wajen fadin.

     " Wani hanya  ba suke nan".

     " Madina duk da kin haifi Ridwaan kece za ki taimaka kuyi aure na wucin gadi".

     

     Daga Mamy har Madina kallon juna suka yi suna zazzare idanu.

    Bakin Mamy na rawa ta ce.

     " Malam aure fa ka ce tsakanin kawata da dan cikina?".

     " Kwarai kuwa hakan nake nufi, dan Aljani Kul'usu yace inhar ana son ahana shi yin aure dole sai ya yi na wucin gadi, kema kinsan ba iya kusantar ta zeyi ba, ita ma Madina nasan ba yarda za ta yi ba amma in daga waje ne ya auro yarinya kinga dole ne zata damu a kan dole sai ya yi tarayya da ita, to taga tsayayyen namiji babu amfani kinsan ba zata yarda ba ". ya ƙarashe zancen yana kallon Madina.

    Madina tabe baki ta yi cikin iya bariki da kisisina ta ce " Haba Malam aikuwa sai de anemo wata Ridwan fa mune muka raine sa taya zanyi amai na lashe ". ta yi furucin cikin tsantsar ɓacin rai a fili.

     

     Mamy na ganin hakan jikinta sanyi ya yi cikin rage damuwarta ta ce.

    Madina ke din ce za ki taimaka kiyi hakan babu yarinyar daze aura ta yarda suyi auren wucin Gadi ke ma kin sani, kinsan bana son a rabe shi, ballatana wata shegiya yarinya ta yi tunanin ta zo gidan hutu zata baje ta zuba ya'ya, ta kuma. . . . . ".

     Malam ne ya dakatar da ita, ta hanyar daga hannu tare da fadin.

     

     " Saratu basai kin ce komi ba ai andade ana aiki ko, duk abin da muka sanya a gaba muna samun nasara, kuma nasan ya koma aiki tunda na gani acikin duban da nayi dan haka ki kwantar da hankalinki nan da sati daya me zuwa ze kara ajiye aikin nan, kuma duk wannan tambayoyin da yake miki wallahi bugun ruwan cikinki yake besan inda kike ba amma da yake shi ɗan sanda ne sun iya wayau da dabara wajen kamo gaskiyar abin da suke son sani, ku tashi ku tafi, in kun je gida ki ba Madina kuɗi ta turo mun dan zan yanka raguna biyu da manyan turaruka ". Ya kai karshen zancen yana tattara kasar da ke gabansa.

    Babu bata Lokaci suka mike daga Madina har Mamy kana cikin ban girma suka masa sallama tare da fita daga Dakin.

     

    Cen bangaren Ridwan ganin Mamy ta katse wayar, mai da kallonsa a kan Umar ya yi, cikin tsare gida ya ce.

    " Ya sunanka?".

    " Suna na Umar Faruk ".

     " Sunan Mahaifinka fa?".

     "Ni dai a Gidan Isah Sharifai na taso ata kaice dai na zama kamar dan gidansa".

     Zazzare idanu Ridwan ya yi cikin rawar murya ya ce.

    " Isah Sharifai, kana nufin kun zauna inuwa daya".

    " Eh hakane " cewar Umar.

    " Gud, kaji zargin da ake maka a kan kisan kai, gayamin gaskiya dan gaskiyarka shi ne abin da ze fitar da kai ". Ya karashe zancen yana bude wayarsa tare da fito da wani hoto daga galeri din wayarsa, fuskar wayar ya ke nuna wa Umar.

     " Kasan wannan da ke cikin hoton nan?. "

     Cikin zazzare idanu Umar ke kallon na cikin hoton bakinsa na rawa ya ce " wanna ai Balarabe ne?". ya ƙarashe zancen muryansa na rawa.

     Ridwan cikin takunsa mai ban tsoro ya ce.

    " Taya za mu banbance tsakanin Umar da Balarabe kasan Balarabe inkiya ce, kai da na cikin hoton nan bakuda maraba, so kake kayi wasa da hankalin hukuma? ". ya ƙarashe zancen hoton fuskar Balarabe na yawo kwanyar kansa, shekara na dukan Shekaru yake neman yin tozali da Balarabe da matarsa. . dawowa hayyacinsa ya yi jin.

    Umar na fadin " wallahi bansan na hoton nan ba yadai yi min kama da dan uwana Balarabe wanda uwa daya ta haife mu amma tabbas in an kalli hoton nan za'a dauka nine amma wallahi nasan ba ni ba ne a hoton nan ". Ya kar kashe zancen cikin muryan kuka.

     Ridwan kallonsa yake, yatsarta daya a baki kana ya fesar da numfahi tare da kai dubansa a kan ma'aikatan da ke tsaye a bayansa, " kuna iya shigar da shi a cell har sai ya shirya amsa min tambayoyi, amma ban da horo kudai ku je da shi ". Yana ƙarashe zancen ya fara ƙoƙarin tashi tsaye.

    Babu bata lokaci jami'an tsaro suka mikar da Umar tare da tasa keyarsa agaba za su fitar dashi daga dakin, dai-dai fita daga kofar dakin ne, Umar ya sauke idanunsa a kan Amatullah da ita ma shi din take kallo azabure suke kallon juna bakin sa na rawa ya ce.

     " badan nasan Yasmin na Cotonou ba da sai in ce ita ce, amma kuma yasmin dita ta girmi wannan yarinyar "ya yi furuci murya na rawa.

    Ma'aikatan da Ridwaan dukansu tattaro nutsuwarsu suka yi a kan furucinsa, ita kuwa Amatullah bakinta na rawa ta ce " Malam laifin me kayi aka kawo ka nan, duk tsoron Allah ka da koyar da dalibai be hana sun kamaka ba ". ta yi furucin iya gaskiyarta. Ta kara da fadin" ni bansan wata Yasmin ba suna na Amatullah Papy " ta karashe zancen murya a raunace, kukan zuci take dan har ga Allah, tsoro ya kamata laifin me Malam ya yi aka kamasa.

    Jami'ansa tsaron ba su bar Umar ya faɗi abin da yake shirin fade ba, aka fitar dashi daga dakin.

    Ridwan da ke tsaye sosai yake nazartan dan kalaman musayar yawu da Amatullah ta yi da Umar.

    Ƙoƙarin fita yake dan shirin tafiya office din Mansur, har ya kusa kai wajen Amatullah ya ji daya daga cikin ma'aikatan ya ce.

    " wannan Yarinyar akai ta cell ne?".

     

     Cak ya tsaya yana jujjuya kalamansa, ita kanta Amatullah sosai ta razana jin zancen cell.

     Kamar me tunani ya yi shiru, koda ya iso gab da Amatullah kallo me cike da tsana ya ke bin ta dashi, kana cikin ransa yana ayyana yanda yake jin haushin yarinyar, cikin maganar da sam be san ze iya furtawa ba ya ce.

     " Taya za'a saka yarinyar karama a cell, ba tare da babban laifi ba, akwai inda zan ajiye ta ". kai dubansa a kan Amatullah da ta rintsinar da kanta kasa ya yi.

    " Za ki tashi mu tafi ko sai. . . . ".

     Tun kan ya gama rufe baki a tsorace ta tashi furr jikinta har kadawa yake dan tsananin tsoron da take masa.

     Yin gaba ya yi, cikin hanzari ta take masa baya, tana kallon yanda yake taka kafafunsa yana tafiya cikin izza da takama.

     Suna ƙoƙarin fitowa tsakar gidan ma'aikata cikin harara ya buga uban tsaki tare da fadin.

    " Ai da yawon ta'addanci zaku je da kin sanya nikaf, amma cikin jama'a abude kike yawo babu aji". ya yi furucin kamar ba shi ya yi tare da yin gaba yana mai musabaha da ma'aikatan da suka zagaye shi.

    Amatullah ban da " "Innalilahi wa'inna ilairajun " ba abin da take maimaitawa domin ta san ta fada hannun wanda ze azabtar da ita, cikin hanzari ta sanya nikaf din, tare da bin inda yake ganin har yana ƙoƙarin shiga motarsa.

     Wuff ta isa wajen ta fara sanya hannu domin bude murfin motar zata shiga, ahanzarce jami'in dan sanda ya bude motar domin Ridwan ya musu magana akanta.

     

    Bayan kwana biyu

    Garin Cotonou.

    Sosai jikin Mamy har an ba su sallama mijin Fauziyya da abokin Umar ne suka dauki nauyin komi na asibitin.

    Koda suka dawo gida Mai Gadi sai da ya kawo matarsa domin gaishe da Mamy da jiki.

    Alhaji Isah Sharifai cikin tsanani ɓacin rai yake sauraren Basma na fadin.

    " Wallahi Alhaji ina me tabbatar maka Mariya ba ita ce ta haifeka ba, a iya binciken da nayi an ce a gidan marayu ta karbo ka bayan likita ya tabbatar mata da ba zata haihu ba ". . .

     Alhaji Isah Sharifai cikin damuwa da rashin sanin ciwon kansa ya ce.

    .

    " Ya ce Basma biri ya yi kama da mutum, duba ki gani fa yanda duk ta koma bayan su, kwata kwata ko nemana bata yi tunda na ɗauke kafana da zuwa wajenta, mikawa tsaye ya yi tare da goya hannayensa a baya cikin dodewar basira ya ce.

    " Wallahi Basma ke Rahma ce gareni na yarda da ke dari bisa dari kamar yanda na yarda da Manzon Allah (saw) shi ne manzon mu, kuma Wallahi Mariya bata dau Amanar da ta amso ba gidan marayu, yanzu tana nufin Muhammad Sharifai ba Mahaifina ba ne 😪 Basma anya Shari'a nan, ba kara shigar da wani zanyi ba, saidai abu daya ze hana nayi hakan ".

     Ahanzarce Basma ta ce

    "Meye hakan  ba suke nan Alhaji" tana taune lip dinta.

    " Basma zan ji kunya da bakin ciki ya yin da duniya suke min kallon dan Sharifai azo ce ashe ba dansa ba ne, kinga  ba suke nan dukiyata dana amso a hannun yan uwansa dole ne kotu ta amsar musu kuma kudin dana hana Mariya tunda bata tare da dani shima duka za su amsa ". ya karashe zancen cikin duhun kai.

     Kasaitaccen murmushi Basma ta yi tare da yin taku mai girgiza mazaunanta, hannunta ta sanya ta dafa shi ta baya hakan ya sa kai dubansa a kan hannunta da ke kafadarsa yana sakin ajiyar zuciya.

     " ka manta da maganar Mariya ba sai anje kotu ba, kawai ka yafe mata amma kasani babu kai babu ita har abada kar ka nuna kasanta dan wallahi indai uwa bata haifi da ba to babu shakkah ze ga tsana bayan girmansa ". Ta karshe zancen tana kai masa runguma ta baya.

     

    Shi kuwa ɓacin ran da yake ciki ya sa ko alama be, saurareta ba, illah ɗauke hannunta ya yi daga jikinsa tare da yin hanyar dakinsa azafafe babu abin da yafi bukata illah kaɗaici.

    Ita kuwa ganin ya fice, a yiririr nanaye ta rangada guda tare da fadin.

     " Isah Sharifai kana wasa da Basma ai da hannunka zaka fitar da Mariya daga gidan nan, algungumar mata. Ta karashe zancen tana bushewa da dariya.

    Bangaren Mamy kuwa zaune suke jugum suna ta kiran abokin Umar domin jin labarin ya ake ciki, abokin Umar sanar musu ya yi har yanzu ba su samu ganin Umar ba, amma in sha Allah za su gansa. . da wannan ne suka samu dan sassauci suna addu'a da neman agaji awurin Allah.

    Fauziyya cikin jin dadi ta ce " Mamy kinga har wani kiba kikayi dan zaman Asibitin nan, dan kin samu hutu kin sha barci sosai, kuma barister Hadiza ta zo gida dazun kina barci".

    Murmushi yake Mamy ta yi tare da faɗin.

    " Allah ya fitar min da Umar, ita kuma Hadiza Allah yasaka mata da Alkhairi, dan wallahi ta yi ƙoƙari zaman kotun nan, kuma aikin da take mana badan kudin data amsa ba ne, dan abin da muka bata be iya daukar kwararra lauya irinta ".

    " Hakane kam" cewar Fauziyya ta yi saurin taran numfashin Mamy.

     Safiyya da Firdaus cike da jin dadi suke dan taba hira da Mamy duk da sama sama take amsa musu.

    Bayan sallah Isha'i Basma ce zaune gaban malamin ta.

    . cikin rawar murya ta ce Malam aiki nake son kamin a kan Fauziyya Isah sharifai, domin alamu sun nuna ita ce take daukan nauyin mahaifiyarta, abu daya nakeso shi kasa mijinta ya dankaro mata kishiya, ƙishiyar ma yar makotarsu da ke suke mutunci nake son ka hada, sannan fa kar ka manta ina son ya tsaneta ta zama abun kwatance kamar mahaifiyarta ". ta karashe zancen cikin tsananin bukatuwa.

    Malam cikin babban muryansa ya ce " Basma sha kuruminki ai yanzu tana gaban Mahaifiyarta ". Kwarya ya zubawa ruwa cikin hanzari ya kara da fadin " dan leko kwaryan nan kika mamaki ".

     Ahanzarce ta sako kai tana lekawa, cikin tsananin kaduwa ta ce.

     " Malam ga Fauziyya nan ina gani ". ta yi shiru tana kallon yanda Mamy ke lumshe idanu tana kallon yanda Fauziyya ke mata fifita.

     " Ai yanzu za mu sanya mata cutar wari, da kuma kanzuwa dukan sassan jikinta, shi ne farkon abun da Jibril ke fara tsananta, ke ma kinsa dole ne ya fara tunanin karo aure ko?".

     Ahanzarce ta girgiza kai tana fadin.

    " Amma fa Malam kai mugun shu'umi ne ji fa yanda tunaninka ya je inda bankai ba, gaskiya a yi hakan shegiya zanga ta inda zata kara taimakon Uwarta.

    Malam bushewa da dariya ya yi kana ya jefa karamin laya cikin kwaryan.

    Daga cen Bangaren ahanzarce Fauziyya ta saki abun fifita, cikin gigita da fitar hayyaci ta fara. . . . . . . . . . . . . . .

    ****** 

    Littafin nan, na kuɗi ne. Da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. Hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

    Kibiya dari biyar kacal domin samun shiga group na musamman.

    Domin Karin bayani a tuntuɓe ni ta wannan lambar 09069080725 ko + 22953726162.

    Siyen nagari mai da kuɗi gida.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.