Tafi da ruwa malle
Dansarki duka laya ne
Amma Tafida Quranin yan sarki ne
Tafi da bar su su sa swace
Tafid a bar su su sa saki
Kai dai saka shudiyar ka ka shuda su
In kun ce Tafida yaro ne, to da Mista Cara yake zance
In kun ce Tafida maraya ne, A
llah da ya yi maraya,
Ai baya ki maraya ba.
Wasu baituka na mabushi Lagwada ke nan, da yake yiwa Tafidan Kano, kuma Wamban Kano Mamudu, mahaifin Sarkin Ringim Sayyadi, dan Sarkin Kano Usman kenan. A taken sa na, Daga Bayero sai Malle, ba zan bi wani kato ba. Allah ya jikan su
Daga Zauren:
Makaɗa da Mawaƙa
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.