Ticker

Masanan Farko ga Tsara Ka’idojin Rubutun Hausa

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

733. Sai mu yi godiya ga Durugu  manyanmu,

 Su suka yo ɗawainiya ga Hausar bokonmu,

 Dukkan tsare-tsare su nai tsarinmu,

 Turawan ga sun yi ƙwazo harshenmu,

Shi da Abega manya-manyan Hausawa.

 

734. Su suka fara yin tunani ga rubutu,

 Su suka yo aron haruffa na rubutu,

 Sun tsara su don mu mu masu karatu,

 Sun yi ɗawainiya ga tsari na rubutu,

  Har aka fara zana harshen Hausawa.

 

735. Su suka fara tsara harshen Hausawa,

 Kuma sun nuna yadda za a karantawa,

 Sun share waje suna ta faman koyarwa,

 Sun yi alama ta zan wakilin furtawa,

  Bisa harufan Nasara harshen Turawa.

 

736. Sannu a hankali abin yab bunƙasu,

 Har yay yaɗu, ko’ina kuma yaw watsu,

 Hausa suna da sautuka ga rubutun su,

 Sautin Hausa yanzu mun san ya watsu,

  Yay yi kane-kane ga bokon Turawa.

 

737. J.F. Schon ya zo ya inganta haruffa,

 Ya gyara waɗansu, kyau tamkar tuffa,

 Ya ware waɗansu, ga su sun ɗau wata siffa,

 Yai ƙwazo, ya zo da tsari na haruffa,

  Duk mai ƙugiya ɗigo yake sanyawa.

 

738. Shi ko Abraham ya zo yas share su,

 Ya yi gwagwarmaya don gyara su,

 Ya shirya su ya yi ƙwazo aikin su,

 Turawan da sun gabatai aikinsu,

  Yas sa lanƙwasa haruffan Hausawa.

 

739. Haka dai sannu har abin yab bazu sosai,

 Aikin nasu ko’ina ya shiga sosai,

 Masu kari sai su nemi kokonsu da ƙosai,

 Haka ƙwazonsu ƙaida ta tsayu sosai,

  Boko yat tsaya haruffan Hausawa.

Post a Comment

0 Comments