𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum. Ina da yaya (wa) wanda muke uwa ɗaya
uba ɗaya da shi, sai
ya auri wata bazawara, kuma ita ma tana da babbar ’ya. Shin ko zan iya auren
wannan ’yar tata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa'alaikumus
Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Da farko: Aure
ba yana cikin babin Fiƙhul-Ibaadaat
ne, wanda ba a iya aikata komai a cikinsa sai da umurnin Allaah ko Manzonsa
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Amma yana cikin babin Fiƙhul-Mu’aamalaat ne wanda
ba a hana komai a cikinsa sai abin da Allaah ko Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya hana. Don haka, kowace mace ya halatta musulmi ya aure
ta in dai ba an samu wani dalili daga Allaah (Sabhaanahu Wa Ta’aala) a cikin Alƙur’ani ko Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin Sahihan Sunnah ko wata ƙa’idar musulunci sun hana ba.
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ مِنَ الرَّضَاعَة
An haramta
muku auren uwayenku, da ’ya’yanku, da ’yan uwanku, da goggoninku, da innoninku
da ’ya’ya mata na ’yan uwanku maza, da ’ya’ya mata na ’yan uwanku mata, da
uwayenku waɗanda
suka shayar da ku nono, da kuma ’yan uwanku mata na shan nono. (Surah
An-Nisaa’: 23).
Manyan malaman
musulunci da suka gama yin nazari a cikin Alƙur’ani
da Sunnah sun fitar da nau’ukan matan da ba su halatta musulmi ya aura ba. Da
farko sun kasa matan gida biyu ne:
WAƊANDA
SUKA HARAMTA HAR ABADA
Akwai guda
bakwai da suka haramta saboda dangantaka:
1. Duk macen
da ta zama mahaifiya gare ka, kamar uwa da mahaifiyarta da kakanninta mata da
mahaifiyar uba da kakanninsa mata.
2. Duk macen
da kake matsayin mahaifi gare ta, kamar ’ya ko ’yar ’ya, ko ’yar da duk yadda
suka yi ƙasa.
Kuma wannan ’yar ko ta aure ne aka same ta ko ba ta aure ba ne.
3. Duk macen
da ta haɗu da kai a
asalin iyayenka, kamar ’yar uwa wacce ka haɗu
da ita ta hanyar uwa da uba gaba ɗaya
ko uwa kaɗai ko kuma
uba kaɗai.
4. Duk macen
da ta haɗu da
mahaifinka ko kakanninka maza a asalin iyayensu: Ta fuskar uwa da uba gaba ɗaya, ko ta uwa kaɗai ko kuma uba kaɗai, kamar: Inna.
5. Duk macen
da ta haɗu da
mahaifiyarka ko kakanninka mata a asalin iyayensu: Ta fuskar uwa da uba gaba ɗaya, ko kuma ta uwa kaɗai ko uba kaɗai, kamar: Goggo.
6. Duk macen
da ɗan’uwanka ya
haife ta, ɗan’uwan
nan ko shaƙiƙi ne
ko wanda kuka haɗa
uwa ce kaɗai, ko
kuma wanda kuka haɗa
uba ne kaɗai.
7. Duk macen da
’yar uwarka ta haife ta, ko ’yar uwarka shaƙiƙiya ce, ko wacce kuka haɗa uwa kaɗai, ko kuma wacce kuka haɗa uba kaɗai.
Akwai kuma
guda uku da suka haramta ta fuskar surukuta:
1. Mahaifiyar
matarka ko kakarta, da zaran an ɗaura
maka aure da matar taka.
2. Matar ɗanka ko matar jikanka, da
zaran an ɗaura musu
aure.
3. Matar
mahaifinka, da zaran an ɗaura
musu aure.
Amma agolarka,
watau ’yar da matarka ta haifa aurenta na zama haram gare ka ne kawai idan ka
riga ka sadu da mahaifiyarta, watau matarka. Amma ba kawai domin an ɗaura muku aure, alhali ba
ku tare da juna ba.
Sai kuma wasu
nau’ukan mata guda bakwai da suka haramta ta dalilin shayarwa:
1. Matar da ta
shayar da kai, da kakarta ta wajen uwa ko ta wajen uba.
2. ’Ya ko
jikar matar da matarka ta shayar da ita.
3. Macen da
mace ɗaya ta shayar
da kai kuma ta shayar da ita.
4. ’Ya ko
jikar matar da wata mace ta shayar da kai kuma ta shayar da ita.
5. ’Ya ko
jikar namijin da wata mace ta shayar da kai kuma ta shayar da shi.
6. ’Yar’uwar
mijin matar da ta shayar da kai.
7. ’Yar’uwar
matar da ta shayar da kai.
Haka kuma duk
matar da miji ya yi mata li’ani¹ a gaban alƙali, ita ma ta haramta gare shi har
abada.
Li’ani wani
nau’in sakin aure ne, inda miji da mata ke rantsuwa a gaban sarkin musulmi ko
na’ibinsa, tare da yi wa junansu addu’ar aukuwar la’ana da fushin Ubangiji a
kan maƙaryaci,
saboda zargin rashin amincewa a tsakaninsu.
MATAN DA SUKA
HARAMTA NA-WANI LOKACI:
Ga su kamar
haka:
1. Haɗa ’yan uwa mata biyu ko
fiye a wurin mijin aure ɗaya
a lokaci guda. Amma idan auren ya mutu ko matar ta rasu, to zai iya auren ’yar
uwarta.
2. Haɗa auren mace da innarta
ko goggonta a wurin mijin aure ɗaya,
sai dai ko in auren ya mutu ko matar ta rasu.
3. Matar auren
wani, har sai ya sake ta kuma ta gama idda, ko ta gama takaba a bayan
rasuwarsa.
4. Matarsa da
ya sake ta saki na-uku, har sai bayan ta auri wani miji na-daban kuma ya sako
ta a bayan ya sadu da ita saduwa ta haƙiƙa, kuma ta gama iddarsa.
5. Mushirika
watau kafirar da ba Ahlul-Kitaab (Yahudu ko Kirista) ba, har sai lokacin da ta
musulunta.
Akwai sharuɗɗa da malamai suka sanya
kafin musulmi ya iya auren macen Ahlul-kitaab, wanda yawanci a yau mutane ba su
cikawa, don haka suke ta samun matsaloli a bayan auren. Haka kuma haram ne mace
musulma ta auri duk wanda ba musulmi ba ko da kuwa daga cikin Ahlul-Kitaab ne.
6. Auren wata
mace ta-biyar a lokacin da yake tare da matan aure guda huɗu, har sai lokacin da ya
rabu da wata ɗaya
daga cikinsu kuma ta gama iddarta.
7. Ɗaura
aure a lokacin da yake cikin harama da aikin hajji ko umurah, har sai lokacin
da ya fita daga haramar.
8. Mazinaciya,
har sai lokacin da ta tuba. Haka ma mazinaci ba za ta aure shi ba har sai ya tuba.
Mazinata ma sai sun tuba.
A ƙarƙashin
wannan bayanin kana iya auren ’yar da matar yayanka ta haifa, tun da ba ta daga
cikin waɗannan matan
da Allaah Ta’aala ya haramta aurensu. Sannan kuma dayake ba mu ga wata ƙa’ida daga cikin ƙa’idojin musulunci da ta hana
hakan ba.
WALLAHU A'ALAM
Muhammad
Abdullaahi Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.