Ticker

Matsalolin da Rubutun Hausa ke Fuskanta

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

655. Hausa saboda ƙoƙarin bunƙasarta,

 Ta mamaye harsuna da dama na maƙwabta,

 Wasu manyan ƙasar ga kullum kushe ta,

 Sun saka ta a zaɓi saboda mu ‘yan kishinta

  Ta sha yunƙuri ana daɗa dannewa.

 

656. Matsalolin da sun ka tauye ta dukansu,

 Bai wuce ɓangaren karatu da rubutu,

 Kowa yai biris ga tauye ta waɗansu,

 Kuma sun lura matsalolinta dukansu,

  Ba su da waibuwa wajen magancewa.

 

657. Na’uran da za su daidaita rubutu,

 Su ma dai da nasu laifi na rubutu,

 Domin dole ne a idan za a rubutu,

 Sai an neme su, sannan ku sani su,

Sun ka ƙaranta sun hana mata walawa.

 

658. Na’uran da an ka ƙago na rubutu,

 Duk an yi su don a daidaita rubutu,

 Amma ku sani fa ku masu karatu,

 Na’uran da an ka yo duk na rubutu,

  Manufofinsu yaɗa harshen Turawa.

 

659. Hausa a dole dai aro za ta yi ke nan,

 Ba zaɓi gare ta tilas ga aron nan,

 Sautin Arbiya haɗa da na Turawan nan,

 Na’uran da za a zana rubutun nan,

Ba ta da nata wanda zai yi na Hausawa.

 

660. Bayan tsegumin aro ga na kurarra,

Can ga rubutunmu ga shi mun shaƙu da kara,

 Ga kure yanzu ai kusan ba mu da tsara,

 Mun samo sautuka na harshenmu ku lura,

  Can gun sautuka na harshen Turawa.

 

661. Harufa masu lanƙwasa ba su a keken,

 Ƙ, ɓ, ɗ, da ‘y ku san babu su keken,

 Haka ma ƙa’ida ta tsari na fataken

 Ba a saka su can ga tsarinmu na keken,

  Dole da hannuwa muke daidaitawa.

 

662. Wai ɗan ci gaban da an ka ga ya samu,

 Kowa na ganin kamar mun yi na kammu,

 Sai a rubuta shafuka na buƙatarmu,

 Wannan ci gaban da Hausarmu ta samu,

  Kwamfuta ta zo da su don gyarawa.

 

663. Ko ita ba tagwan baƙi, ba na wasulla,

 Sannan babu ‘y a duba don a kula,

 Sai dai kai da kanka ka ɗauki ka ƙulla,

 Tilas ai hakan ga don babu maɓulla,

  Ba ƙamus cikinta mai daidaitawa.

 

664. Wata matsala akwai ƙarancin malammai,

 Ga wasu sun tsufa yanzu ba sa iya komai,

 Wasu na gab da yin ritaya, shin sai mai?

 In an lura Hausa babu yawan malammai,

Masu sanar da yara harshen Hausawa.

 

665. Ko an ce akwai su ce babu ƙwararru,

 Wasu bakin sakandare, ga shekarru,

 Wasu koyarwa kawai suke babu dabaru,

 Wani ko ya ƙware wajen yara ku taru,

  Ɗan koyo ina yake iya koyarwa.

 

666. Wata matsala ta ukku kishin harshe ne,

 Ba kishi na Hausa nan ni sheda ne,

 Wasu ma su da kansu ai ‘yan shirme ne,

 Ƙyama sun ka sa gaba ko kun gane?

Gun masanan ga namu wato Hausawa.

 

667. Sun ƙi jinin a ce da Hausa suke koyo,

 Balle ma a ce da shi Hausa ya koyo,

 Ba kishi gare su kullum yo-yo-yo,

 Yaya za su yi da Hausa, sai dai su amayo,

  Ba sha’awa suke ba can gun koyarwa,

 

668. Kullum sai su ce amso musu kwabbai,

 Ba kishinta, ba na kai, su dai dubbai,

 Sun ka fi so a ba su, sun ɗauki zunubbai

 Sun muzanta Hausa can gun ɗalibbai,

  Wai su Ingilishi shi ke birgewa.

 

669. Sun lalata ɗalibai sun dabirce,

 Ba su Gabas a Yamma sun ɓalɓalce,

 Ba su faɗa a ji su balle a rubuce,

Ba komai a kan su duk sun takkwalce,

Ba su ga Hausa, babu harshen Turawa.

670. Masana sun ka ce waɗannan malammai,

 Ba amfanin a sa su aiki na kalamai,

Sun dace a sa su layin azzalummai,

Ba ilmi gare su, kan su na kullummai,

  Gara a bar saka su aikin koyarwa.

 

671. Cikas babba ga ƙarancin littaffai,

 Ba a da damuwa da su sai aljifai,

 Kowa ba ya damuwa kan littafai,

 Na roƙa a yo gudummuwar littattafai,

  Gun masana da ɗalibai don koyarwa.

 

672. Ba laifi a ce a shekara a yi taro,

 Sai a yi gangami a ba kowa goro,

 Masana duk su hallara gun taro,

 Manazarta su zo, a ɓarje muna gero

  Don daidaituwar rubutun Hausawa.

 

673. Wata matsalar batun karin harshe na nan,

 Don mun san ƙasar mu na da faɗi ke nan,

 Sai mun tattaro mutane na ƙasar nan,

A ji bakinsu sai a shirya mata sannan,

  A yi mata gangami batun daidaitawa.

Post a Comment

0 Comments