Me Ya Sa Ake Kiran Abubakar "Garba"?

    Na ga bayanan mutane da dama akan kalmar Garba da kuma dalilin da ya sa ake wa Sayyadi Abubakar a Siddique (Abdullahi bin Abi Quhafa) Allah ya kara yadda da shi, laqabi da sunan. Bari in dan tunatar da mu cewa, shi kan sa sunan Abubakar din, suna ne na alkunya kamar yadda ake wa mai gayya mai aik, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) lakabi da Abul Qasim, ko Sayyadi Aliyu bin Abi Talib (KarramalLahu Wajahahu) lakabi da Abu Turab. To shi ma Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) ya yi masa alkunya da sunan Abubakar wato ubanbudurwa. Saboda aura masa Nana Aisha da yayi, wacce ita ce budurwar.

    To amma me ya sa bahaushe ya kirkirar masa wani sunan? Domin mu fahimci dalilin, ya kamata mu fara sanin, me kalmar Garba take nufi a hausa.  Na ga wani anan ya ce kalmar Garba ta samo asali ne daga kalmar larabci ta "Qurba", wato makusanta kamar yadda tarjamar Malam Nasiru Kabara da ta Malam Abubakar Gumi suka fassara ta. To amma a dan karamin fahimtar da na yi wa nahwun larabci, kalmar Qurba bata hau kan irin alakar dake tsakanin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) da Sayyadi Abubakar ba a magana ta gaskiya, alakar da ke tsakanin su ta sahabbantaka ce, kamar wacce ke tsakanin sa da su Sayyadi Umar, Usman da sauran su. Kalmar Qurba na manzon Allah a yar karamar fahimta ta in za a danganta ta ga Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) to za ta hau kan irin su Sayyadi Hamza, Aliyu, Abbas, Akilu da su Fadhalu ne da sauran yayan sa, kamar Nana Fatima (Allah ya kara musu yadda). Amma aboki ba zai shiga cikin Qurba ba. Duk kuwa da cewa, nasan ta can sama in an tafi, za a iya samun alaka ta jini, tsakanin su biyun, amma kusanci jini bai kai a kebe Sayyadi Abubakar da kalmar ba.

    Wani abin lura, Bahaushe kan wa shahararrun mutane lakabi ne da abinda suka kebantu da shi, misali, Maryam Daso, an samu Daso daga kalmar dashe, saboda dashen da Allah yayi wa Sayyada Maryama (Alaiha salam) na cikin Annabi Isa (Alaihi Salama) ba tare da ta kwanta da wani namiji ba. Anyi amfani da shudadden lamari (past tense) na dashe ne, saboda labarin yazo ne a matsayin abinda ya riga ya faru, wato (narrated), tunda sai bayan an samu cikin aka san da shi. Dan haka ake kiran Maryam da Daso, saboda ta kebanta da wannan lamari. Haka ma akan kira Asmau da  sunan Yar shehu ko fara, saboda tafi kowacce ya da Shehu Usman Danfodio ya haifa shahara. Ko kuma in an cewa mutum Maikano an san Abdullahi ne, saboda Sarkin Kano Abdullahi Majekarofi, ko kuma a kira mutum da,  Maidaura, to an san Abdurrahman ne saboda Sarkin Daura Abdurrahman.

    To mu koma batun Garba. Kalmar ba balarabiyar kalma ba ce, kuma tana da nau'o'i da dama, akwai Garb'a, wata rawa ta fitsara da mata kan yi in ana kidan Saran Marke ko Duman Girke. Wacce da musulunci yayi karfi aka hana. Akwai Garb'a na barzajjen hatsi. Amma ita kalmar Garba ta samo asali ne daga kalmar Garbali, wato dangali kenan. Kalmar na nufin shinge ko matara da aka kafa domin kare wani abu daga cutarwar wani abu. Akan kira kyauren da aka sanya a kofar gari da sunan Garbali ko dangali, haka kuma akan kira shingen da aka yi wa lambu da wannan kalma dai. To amma meye alakar wannan kalma ta Garbali ko Garbati (kamar yadda ta zo a wani wasan karya harshe da ake cewa "Garba Garbati gwanin gyaran gwangwanin gwamnatin jihar Gwangola)?

    Abinda ya sa a ganina wasu ke ganin kalmar daga Larabci ce, saboda sun san harshen Hausa ya shahara da aro, amma ya kamata a lura ba duk kalmar hausa ba ce dan tayi kama da ta larabci ko wani yare take ta aro. A da, da yawa sun dauka kalmar "Boko" ta samo asali ne daga turanci wato "Book", amma daga baya suka fuskanci cewa bahaushiyar kalma ce da ke nufin, "jabu" wato abinda ba orijina ba, ko kuma a turance a ce (fake). Domin har akwai wasan yara da ake kira da amaryar boko, inda yara kan shirya wata daga cikin su, su yi mata kwalliya a goyo ta, a yi layi kamar an dauko amarya, amma kuma amaryar boko ce, wato amaryar jabu ce. Haka ma bahaushe yana amfani da kalmar "biri boko", wato abin da yake na jabu ko yaudara. To shine. Bahaushe ke kallon tsarin ilmin da bature ya zo da shi, a matsayin ilmin jabu, don haka ya kira shi da ilmin boko. Har ma ya kara da bokoko a wuta.

    An wa Sayyadi Abubakat lakabi da wannan kalma ne, saboda tarihin hijira. Kowa ya san shi kadai ne suka yi hijira tare da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) daga Makka zuwa Madina. Akwai abubuwa biyu da suka shahara a tarihin hijira a kasar Hausa, wanda suka nuna Sayyadi Abubakar ya zamarwa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) shinge a wannan tafiyar. Kodai ya inganta sun faru, ko bai inganta ba, wannan wani abu ne na daban, amma dai bahaushe ya ankare da wannan namijin kokari da aka gaya masa ya faru.

    Na daya, zaman su a kogo, inda aka ce Sayyadi Abubakar ya ringa yaga suturar sa  yana toshe duk wani rami, saboda gudun kar wani abu ya fito ta ciki ya cutar da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam). Inda aka ce akwai daya da ya rage, sai ya saka dunduniyar sa ya toshe.... wata yayi Garbali da kafarsa. Wannan kan iya zama dalili na kiran sa da wannan suna.

    Na biyu, shi ne batun da aka ce, a tafiyar ta su. Sayyadi Abubakar ya ringa wata irin tafiya, sai ya shiga gaban Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) sai kuma yayi sauri ya koma bayan sa. Da ya tambaye shi, me ya sa yake haka, sai ya ce "saboda in har wani abu zai same shi ta baya ko ta gaba, ya zamana ya kare shi ta nan". Wato dai ya zamar masa garkuwa.

    Wannan dalilai ni ina ganin shi ya sa bahaushe ya kira Sayyadi Abubakar da Garba.

    Allahu a'alamu

    Daga:

    Malam Muhammad Fatuhu
    Zauren Hikima

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.