Ticker

Mijina Ya Bani Dama Na Saki Kaina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mun sami saɓani da mijina sai nace da saki a hannu na yake da na dade da rabuwa da shi, sai ya ce yanzu ma ya bani dama na saki kaina, sai nace na saki kaina saki 1. Yaya matsayin sakin yake?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh Ibnu Ƙudama ya tattauna wannan matsalar dakyau cikin Almugni harma yakawo zantukan malamai da fatawowin sahabbai akai, wanda ya ce ijma'ine tsakanin malamai cewa idan miji ya cewa mace nabaki damar ki saki kanki, sekuwa ta saki kanta anan take awajanda aka yi maganar bata bari sun rabuba setace ta saki kanta toh duk malamai sunce ta saku. Amma idan se bayan sun rabu kila mijin yaje masallaci yadawo misali se kawai ta ce yanzu na saki kaina toh jumhur na malamai suka ce bata saku ba domin damar da aka bata tariga ta yi sanyi. Amma Imam shafi'i dasu Sayyidina Aliyu suka ce tasaku domin dama ai mijin bece kisaki kanki anan wajan ba kawai cewa ya yi ta saki kanta. Kuma Ibnu Ƙuduma ya ce ba a samu wani sahabi ya taɓa cewa inba anan take ta saki kantaba sakin beyiba babu wannan maganar daga wajan wani sahabi.

Dan haka dai a dunkule kawai wannan sakin yasaku in sha Allahu. Kuduba Almugni juzu'i na 7 shafi na 308. Ibnul Usaimin shima ya tattauna wannan matsalar acikin littafinsa Ashsharhul Mumti

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments