𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum
da fatan MALAM yana cikin koshin lafiya, Allah yasa haka. Bayan haka inada
tambaya ce, MALAM Dan Allah mijina yaki ya biya mun kuɗi nayi karatun sanin addinina kuma shi ba
zai iya koya mun ba amma ya yadda nayi, Toh ya halatta in dinga cire wa a kuɗin cafane da yake ban Dan
na tara har yakai nabiya kuɗin
karatun, Hakan ya halatta akaramakallahu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Sata tana daga
cikin manyan Zunubai a Musulunci. To amma akwai keɓantattu Hukunci dangane da zamantakewar
Ma'aurata.
Misali :
Ciyarwa, Shayarwa, Ilimantarwa, samar da sutura, da kuma matsuguni duk Waɗannan suna daga cikin
hakkokin da kowacce yarinya take da shi akan iyayenta. Amma daga ranar da aka
daura aurenta to hakkokin nan sun koma kan Mijinta.
Wajibi ne
akansa ya rika koyar dake addini, ko kuma ya dauko Miki wacce za ta koyar dake,
ko kuma ya kaiki wajen da zaki koya.
Idan kuma ya
gaza wajen sauke wannan hakkin, to kina da Zaɓi
guda biyu anan:
1. Ko dai ki
sanar ma Waliyyansa kai tsaye, ko kuma Mahaifanki su sanar dasu domin azauna
ayi masa nasiha a tunasar da shi akan haka.
2. Ko kuma ki
rika rage ɗan wani
abu daga cikin kuɗin
cefane ɗin. Ki ɗauka bisa Gwargwadon
yadda zai isheki ki biya kuɗin
Islamiyyar. Amma Kar ki sanya almubazzaranci aciki.
Hujjah anan
ita ce hadisin da Imamul Bukhariy ya
ruwaito daga Nana A'isha (ra) ta ce: "HINDU BINTU UTBAH (RA) TAZO WAJEN
MANZON ALLAH ﷺ ta ce
"YA RASULALLAHI HAKIKA ABU SUFYAN (MIJINTA) MUTUM NE MAI KWAURO (ROWA) BA
YA BANI ISASHEN ABINDA ZANCI NI DA YARANA. SAI DAI ƊAN ABINDA NA ƊAUKA
BA TARE DA SANINSA BA". Sai Manzon Allah ﷺ
ya ce "KI ƊAUKI ABINDA ZAI ISHEKI KE DA YARANKI TARE DA ADALCI".
Aduba Sahihul
Bukhariy hadisi na 5364).
To anan kin ga
Ilimantarwa shima hakki ne na Wajibci kamar yadda Ciyarwa da shayarwa suke.
Acikin
Littafinsa mai suna "NAILUL AUTAR" Juzu'i na 6 shafi na 383, Imamush
Shaukaniy ya yi shigen irin wannan maganar dangane da halascin cirar wani abu
daga dukiyar Miji domin riskar da wani hakkin da ya wajabta akansa amma bai
sauke ba.
Sai dai
Malamai sun ce irin wannan yana halatta ne agun Matar da ba'a tsoron lalacewar
tarbiyyarta ta dalilin haka. Don haka idan kin san zaki iya samun matsalar
lalacewar tarbiyyah, wato zuciyarki za ta zarme to bai halatta gareki ba.
Yana halatta
ne kaɗai ga matan da
suke da tsantseni da tsoron Allah. Idan kin san kina cikinsu to shikenan.
Kuma ilimin
addini muke magana akai. Ba wai Ilimin boko ba. Domin karatun boko ba wajibi ba
ne. Kuma ba ya cikin hakkin mace akan mijinta.
Kuma idan Mace
ta rage wani abu domin yin buki, ko sayen kayan kwalliya, ko wasu bukatun
kanta, to wannan kai tsaye haramun ne.
WALLAHU
A'ALAM.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.