TAMBAYA (42)❓
aslm malan barka da warhaka. da fatan maln yana cikin koshin lfy. mln dan
allah ina da tamba ya akwai abun da ya kullemin kai. dan allah inason awar
waremin. a kan mijin mune inada abokiyar zama
amman malm dan ace yau girkina ne sai yadau lokacina yakai mata kokuma ya
je gidan ta da janaba ya yi wanka acan kuma ya ce dan ya sadu da ita baharamun
ba ne saiyace mun ni ma in inason hakan zai kwanta dani ni akullun ina ce mishi
ahaka ake haifar shege amman ayau na ce barina ji tabakin malam kohakan kuskure
ne
AMSA❗
Waalaikumus, Warahmatullahi, Wabarakatuhum
Tabbas ba haramun ba ne ba idan ya sadu da ita tun da ai matarsa ce ta
sunnah, saidai kuma idan kun yi alƙawari da shi cewar zaku dinga raba kwana ita 1
kema 1 to a nan ya saba alƙawarin kuma ya zamo munafuki domin kuwa saba alƙawari
yana daya daga cikin suffofin munafukai kamar yanda Annabi SAW ya fada
(Sahih al-Bukhari 33, Sahih Muslim 59)
Batun a haka ake haifar shege kuma ai bai taso ba ma, domin kuwa shege shi
ne wanda aka haifa ba ta alaƙar auratayya (auren sunnah) ba, kin ga kuwa ai ita
kishiyar taki ai yar uwarki ce musulma kuma matarsa ce halak malak to me ya
kawo batun shegantaka a nan ?
Idan har ranar girkinki ita ce ranar da zai kwana a gidanki to bai kamata
ya dinga dan waken zagaye yana bullawa gidan abokiyar zaman ki ba harma yana
bata aron lokacinki na kebantuwa, hakan yana nuna ba zai iya adalci a
tsakaninku ba
Idan kuma har ba zai iya adalci din ba to bai kamata ma ya auri mace sama
da 1 ba
Allah SWT ya ce:
( وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَىٰ فَانكِحُوا مَا طَابَ لَكُم مِّنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا )
النساء (3) An-Nisaa
Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, (akwai
yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci
ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan
shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba
Shawara a nan ita ce: Ki bashi shawara a ilimance cewar abin da yake baya
kyautawa a addinance, domin kuwa duk wanda baya adalci tsakanin iyalansa to a
ranar lahira zai tashi ne tsagin jikinsa a shanye (paralyzed) kamar yanda
hadisin ya tabbatar
(Sahih Muslim)
Amsawa:
✍Usman
Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.