Ticker

    Loading......

Muslim-Muslim

1. Mun faɗa muku yaudara ce,
 Kuka ce mana kun amince.

2. Mun faɗa muku kar ku zaɓa,
 Kuka ce mana mun makance.

3. Babu Allah a nufinsu,
 Kuka ce mana hassada ce.

4. Yadda Manjo yai yi za sui, 
 Kuka ce ba wanga zance.

5. Kul! Gidan jiya za mu koma,
 Kuka ce mini karkatacce.

6. Muslim biyu damfara ce,
 Kuka ce mana wai mu kauce.

7. Malamai suka ingiza ku,
 Da faɗa muku tabbatace.

8. Yanzu ga shi ana daka mu,
 Sun yi gum tamƙar itace.

9. Ba batun gyara muke ba,
 Ta abinci muke ta zance.

10. Ga kisar ba a daina yi ba,
 Magidanci sai a sace.

11. Ga Dala tashi take yi,
 Ga su naira a sukurce.

12. Duk da wai an buɗe boda,
 Ga farashin ya ƙi kwance.

13. Arziki na ƙasa a ha'u,
 In ka ganmu kamar a mace.

14. Ga shi fetur na ta tashi,
 Ga shi ba mai ba mu rance.

15. Ga matasa babu aiki,
 Ga ƙasar duk a rikice.

16. Ga shi tafiyar na da nisa,
 Ga jiki namu duk a karce.

17. Rabbana tuba muke yi,
 Kar ka bar mu da masu ƙwace.

18. Ba su san mai za su yo ba,
 Don su seta ƙasar ta kauce.

19. Daga rugujewa su ceci,
 'Yan ƙasar kar su talauce.

20. Rabbana mun zo gare ka,
 Ga ƙasarmu tana a goce.

21. Ban da kai ba mai iyawa,
 Wanda ke shakka ɓatacce.

22. Ya Azizu ka gyara komai,
 Don Rasulu abin kwatance.

23. Mun sani za kayi Allah,
 Shi ya sa muka zo mu dace.

24. Rabbi Sallu ala Nabiyi,
 Alu, Sahabu da sun yi ficce.

25. Ɗanbala ya rubuta waƙar,
 Daga Borno gidan zumunce.

©
Mohammed Bala Garba.
7:11am
27 Oktoba, 2023.

Post a Comment

0 Comments