Dukkan godiya su tabbata ga Allah tsira da aminci su kara tabbata ga annabi Muhammad (SAW)
Sumayyah Abdallah Khalil sunana ni hafaffaffiyar garin Gwarzo ce, da ta ke karamar hukuma ce dake ƙarƙashin jahar Kano da sana'a ta maida mahaifina cikin birnin Kano bayan haihuwata da muke yanzu zaune a cikin birnin Kanon unguwar Gandun Albasa mahaifina Malam Abdallah Khalil da mahaifiyata Hauwa'u ni ce diyar fari a gurinsu sai kannena Ahmad shi ne mai bina daganan Rumaisa, Khadija, Sadiƙ, Khalil da a yanzu shi ne ƙaraminmu, mahaifina ƙaramin karfi gareshi yadika yake saidawa ficis a kasuwar kantin kwari a gefen kasuwa da runfarsu take wani lokacin kuma zagayawa yake cikin kasuwar, tun tasowata da na soma fahimtar yanayin yadda rayuwarmu take na fara janye jiki ga duk wanda ya fimu karfi, haka burina na zama ma'aikaciyar jarida duk na ajiyesa gefe, burina yau ace na kammala secondary da nake yanzu SS1a government Girls Gadun Albasa na cikin garin Kano ba dan komai ba saidan hidimomi su fara sauki daga kaina, Mamarmu macace mai zurfin ciki ko da garinmu mu kaje sam ba za kaji ta fadawa 'yan uwanta babu ba haka za mu yi kwanakinmu mu dawo duk da ka sancewar danginta ba masu kudi ba ne haka suke ƙoƙarin hadomu da kayan abinci da na sawa idan mu kaje, a gurin mahaifiyata na koyi boye sirrina zai wuya maganganuna masu muhimmanci na fadawa wasu musamman rayuwar da muke ciki a gidanmu, danginsu Abba kuwa babu laifi duk masu kudine sai dai suda Abban sam babu taimako idan muka je gidajensu ko da mun je Gwarzo ko gidajen waɗanda suke a nan cikin Kanon babu kyauta tsakaninmu sai jifanmu da maganganu marasa dadi, na sani tun ina karama Abbanmu mai zuciyar neman nakanshi ne sai dai har yau Allah bai kaddara zai yi arziki mai yawa ba, duk da ka sancewar ya yi karatu aikin ne garesa ya yi wuyar samu, ba zance Abba bai da sa'ar rayuwa ba, tun da yanada lafiyar fita ya samo na kansa harma ya ishi iyalansa mu shida da shi da Mama suka ka sance na takwas kawai abin da na sawa raina arziki ne Allah bai kaddara zai tara ba, irin yanayin da muka tsinci kanmu na hantarar dangi ya sa muke zaune guri guda babu mai sha'awar zuwa dangi da gani har kannena, duk da ka sancewar mu din talakawane amma sam ba muda kwadayi irin na wasu daga cikin talakawa kamarmu, kai idan ba kazo gidanmu ka gani ba dan ka gan mu waje tunaninka ba zai ba ka mu talakawa ba ne sosai duk da bawai kaya ba ne masu tsada jikinmu amma kullum za ka gan mu kayan jikinmu wanke goge, da ya ka sance aikin Mama tun ina yarinya har na girma na dora da yiwa kannena, haka batun abinci babu maiwa Mama korafin abinci a gidanmu musamman idan mun yi baki ko da muna jin yunwar har sai sun tafi, duk da saimuyi watanni ba mu ga bakin ba domin dai da masu kudi akafi harka a yanzu mu kam idan an zo kudin mota ma ba za ka samu ba, masu kudi kuwa sam indai ba haihuwa ba Mama ta yi ba ba mai zuwa gurinmu shi ma haihuwar ba za a zo suna da wuri ba da duk dangin Abba ke hakan to mai za suci daga garemu, dan sanin kowane irin rayuwar da talaka yake cikin dangi ba ma sai an fada ba, Mama idan ta yi maganar ba’a zuwa gurinta mamarsu takance
"Hauwa'u idan an zo nauyi za
a dora muku, kin san 'yan uwanki suma ba karfi garesu ba wata da kyar za ta hada
kudin zuwa, kuma tana zuwa daga gareki keda Abdullahi zatace tana jiran nadawowa”
Jin maganar Gwaggo da Mama taji
gaskiyace ya sa ta hakura da batun son 'yan uwanta suzo gurinta, batun gidan da
muke na haya ne ina tausayin Abba da yadda yake biyan kudin hayar da sai Mama
ta hada da nata kudin da take sana'ar cikin gida gishiri, ashana, maggi, Omo da
sauransu duk da ka sancewar cinikin kayan jefi jefi akeyi dan yawanci unguwar
tamu mazajensu ajiyemusu kayan abinci suke komai sunadashi idan ba abun ya kare
ba kafin a siyo a nan ale cinikin, wasu kuma da su siya gurinka gwara su tafi
bakin titi su siyo
Batun kawa sam ni ba maison tara
kawaye bace dan kawata daya ce wadda muka shaku ba laifi Halima Farouk tun daga
JS 1 muke tare da yanzu muke SS1 Halima ce kawai tun farkon haduwarmu na
fahimci tamkar rayuwarmu za ta zo daya wannan ya sa kawancenmu dorewa, ka sancewar
ita ma Haliman bawai 'yar masu kudi bace, bawai ziyartar Haliman nake ba dan da
tazara tsakaninmu, sai dalilin auren da kanwar Abbanmu Aunty Asma'u ta yi unguwarsu
Halima take ganina shi ma nakan dade banje gidan Aunty Asma'un ba dan mijin da
Aunty Asma'un ta aura mai kudi ne ita ma kuma Aunt Asma'un tana auren ta fara
business har kasar waje take zuwa hakan ya sa naja baya da zuwa gidanta danni
banison shigewa wanda muke da tazara da shi ta arziki dan na girmama tawa
rayuwar, kuma Aunty Asma'un zan iya kirgawa tun aurenta a Kano baifi zuwa biyu
ta yi gidanmu ba shi ya sa ni ma naja baya da zuwa gidanta dan dama ita ma baso
take aje gidantaba hakan ya sa bana sha'awar zuwa, dan tun daga Gwarzo za ta yi
waya a zo a taya ta zama idan mijinta bayanan muda muke a guri guda sam ba za
ka ji ta kirani ba saboda kada na shafawa rayuwarsu talauci nafi yakinin
dalilin da take hakan ke nan
Batun tarbiyyarmu iyayenmu suna
tsaye kanmu ni da kannnena hakan ya sa komai namu yakanzo da sauki dan ko su
Khadija da Rumaisa idan angansu waje saidai makaranta ko aike, basa kulafucin
zuwa makwabta kwadayi, kai ko da an aikesu sunje ruwan gidanma basa sha, idan
ko za mu tafi makaranta tare muke tafiya sai sun fara zuwa tasu nake wucewa
tamu
Yau ma kamar kullum mun fito tare
nida su Khadija da tun fitowarmu take kunkunai na dubeta
"Wai ke mai aka miki ne
Khadija”
Ta ɗan
bata fuska
"Yaya yau ma babu, kudin
tara, ga makarantarmu da nisa kuma ba kudin Napep, gashi mun makara” tayi
maganar tana duba agogon hannnunta
Na sake dubenta
"Haba Khadija cikinmu mu
hudu wa aka bawa kudin taran, kuma ai mun ci abinci ko, kuma da za ki maganar
kudin Napep ko tafiyar kasa da makara baga Sadiƙ ba shi da yake ƙaramin yaro baiyi magana
ba, Dan Allah ki canza”
Baki Khadija ta turo
"To shike nan amma Yaya
ciyayya muke da kawayena kullum suke kawo abin da za mu ci da za mu ci idan
anyi break ni babu abin da nake kawowa, sai suga kamar wayau ne”
Na dubeta sosai
"Khadija ciyayyya fa, ai
kema kin san wayon ne kike, ke da ko kudin tara a sati baifi ki samu sau ɗaya ba za ki yi ciyayya da
mutane, dan Allah ki daina Kin ga koni banayi”
Tace
"Maiyasa Yaya?"
"Kawai bana san gori shi ya
sa, kin san idan kanacin na wani ba acin naka watarana sai anyi ma gori”
Da wannan hirar da muke da
Khadija muka karasa special primary dinsu suka shiga su biyu ita da Sadik sai
ni da Rumaisa muka wuce tamu da Rumaisa take aji ɗaya
a Secondary Rumaisa bata da surutu gata da hakuri halayyarta da Khadija ta
banbanta Khadija yarinyace mai son gayu sosai da son ace ita ajin farko take a
komaima, kyau dai Allah ya bata dan kaf cikinmu ba mai nunawa Khadija kyau, sai
dai duk da hakan Khadija bata jure wulakanci, kuma ita ba mai san gori bace
Har muka karaso makarantarmu da
har an fara taron makara Rumaisa batayi magana ba
"Rumaisa Abdallah"naji
Sajida kawar Rumaisan ta fada da mukaci karo dasu gurin makarar suma an taresu
Rumaisa da bata kula da ita ba sai lokaci gurinta ta karasa, bulalar makarar aka
yi mana, muka wuce ajijuwanmu, sallama na yi na shiga da a bencinmu ni kadaice na
zo, zamana ba wuya Halima ta shigo ita ma tana aikamin sakon hararar harta
zauna
Na fara tambayarta
"Haba Halima mai ya yi zafi
ido zaici wuta mai na yi Miki”
"Ban sani ba 'yar rainin
wayau, tun da na hango ki nake kwala miki kira kikayi banza dani” Haliman ta
karasa fadar hakan tana ajiye jakarta gefen tawa
"Yi hakuri Halima Kena kin
san ban jiki ba ne, amma ya za ayi na yi miki shiru, daga wajen ina kika kirani”
"Kofar makaranta mun sauka a
Napep"
Nace
"Yi hakuri Sady banjiba
hankalinmu ya yi gurin taron makarar da akeyi”
"Kice dai baki jiba dan
Rumaisa ko taji na san ba za ta fadamiki ba, yarinya mai nauyin magana”
Nayi murmushi da dariya ta jin Halima ke korafin nauyin bakin
Rumaisa da ita dinma hakan take
"Ai halinku ɗaya da Rumaisan"
Ta dubi kanta
"Allah ya kyauta, ni ai ba
sunanmu guda ba ke ce kika koya mata
halinki Kika mata wayau"
Sallamar Batul Ahmad da take ita
ma 'yar bencinmu ta katse firarmu data shigo wadda ita kawancenmu baikai
kawancen da nake da Halima ba Batul na zama malaminmu na physics ya shigo
mikewa mukayi muka gaishesa daganan muka fara lesson da ba laifi ana gane
karatun Malam Hamid da yake bautar kasa ta kawo shi makarantarmu, sai dai
bahaushene ɗan aalin
garin Katsina ne
Bayan watanni
Haka rayuwarmu ta ci gaba da ka
sancewar cikin godiyar Allah dan sai na ce yanzu al'amura sun sake rincaɓewa fiye da da, dan yanzu
Abba saiyaje kasuwa ya yini baiyi cinikin dari ba, wannan abun idan na tuno
yakan sani hawaye tare da tuno makomarmu a haka
Sallamar Halima da na ji ya sani
sauke tagumin da na yi da hannu biyu na kirkiri murmushi na dorawa fuskata, ganin
Haliman da na yi da nake zaune tsakar gida ina tsare gida Mama ta fita makwabta
barka, yara suna ɗaki
suna kallo ka sancewar akwai nepa garin, sallamar na amsawa Halima ta zauna
gefena a kan tabarmar da nake kai gefena ta aje kula
"Halima mene ne wannan"
Na nuna kular gefen nawa
Halima ta yi murmushi
"Abin da kike so na kawo miki”
Na dubeta da zaro ido
"Dan Allah fa Alala ko faten
doya?"
Tayi dariya
"Faten doya ne, ina komawa
gida na ga shi muka yi shi ne na ce Mama ta zuba Faisal ya kawo miki, to Mama
ta aikesa kasuwa, kawai shi ne na taho ina fitowa na ci Karo da yaya Baffa ya
dawo cin abinci shi ne ya kawoni”
Ba ƙaramin dadi na ji ba dan yau babu abin da
muka girka tun safe sai ruwa da nakesha da cikina ya fara kullewa da muka dawo
makaranta ma ba mu tarar an girka komai ba, Halima na kalla ina jin a raina
Halima ta kara matsayi a gurina duk da dama tana da shi hawayen da ban san sun
zubo ba sai duminsu na ji na yi saurin gogewa na dubi Halima
"Halima na gode”
Haliman ta girgiza kai
" godiya babu tsakaninmu, kuma
kukan mai kike, na sani, baki taba ƙoƙarin fadamin abin da ya shafi rayuwarki
ba amma ni ina ƙoƙarin fahimta, Sumayyah idan kina farin ciki na sani, haka idan
kina sabanin haka, mene ne na hawayen"
Nayi murmushi
"Babu komai”
"Kya ji da shi dai, ina Mama”
cewar Halima
"Ta shiga makwabta, barka
yanzu za ta shigo"
"Aiko dai sauri nake ki
gaidata, ta yi maganar tana mikewa
Na dubeta "badai tafiya za
ki yi ba, ba za ki jira ta zo ku gaisa ba”
"tare da Yaya Baffa muke
shiya kawoni a adaidaitarsa, kar ya yi ta jira na, ko gida bai shiga ba na ce ya
kawoni ba zama zan yi ba”
Hijabin Rumaisa dake kan igiya
nasa na rakata har gurin adaidaita Yaya Baffa
"Ina yini yaya Baffa”
Ya amsamin da cewa
"Lafiya lau, ya
karatu?"
"Alhamdulillah Yaya”
Daganan Halima ta shiga
adaidaitar ya ja suka tafi bayan mun yi Sallama
Yaya Baffa ba mutum ne mai surutu
ba iyakacin ka da shi gaisuwa ce, ko da gidansu naje
cikin gidan na dawo inda na tashi na koma na zauna ina jiran Mama ta dawo a kasafta faten dan ba iya yunwar kowa ke jinta musamman Mama da take goyon Khalil a lokacin na sani duk ta fimu ji, ban san a wanne mataki zan aje Halima a cikin zuciyata ba tana ba ni kulawa da tausayina fiye da 'yan uwanmu da suke watsar damu saboda mu din ba wasu ba ne idan an zo gurinmu mai za a samu dan ko a yanzu kafin ka ga mai kudi yana mu'amala da talaka za ka shekara da shekaru kana bincike kafin ka samu, amma Halima tana tare dani tun kafin tasan wace ce ni kuma har ta sani hakan bai canza ba, duk da Haliman talakawanne amma a hakan take ƙoƙarin kyautatamin, kafin na fadamata matsalata take fahimta idan tanada maganin hakan tana ƙoƙarin yi min, hawaye na goge tunowa da Aunty Asma'u da kaf layinsu Halima da unguwarsu baki ɗaya ba gida irin nata amma da biyar bata taɓa tunanin kawo mana na nuna kyautatawarta garemu ba, sai Halima da kaf layin gidansu ne na kasa dake zagaye da langa langa, yayyenta maza guda uku ke yin komai na gidan ka sancewar mahaifinsu baida cikakkar lafiya hawan jini da ciwan sugar ke damunshi, amma a haka take ƙoƙari duk ranar da taga wata damuwa fuskata take ƙoƙarin kawomin abinci data koma gida, saboda zuwan da take gidanmu ta fuskanci rayuwartamu.
**** ****
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.