Na Cancanta (Kashi na 10)

    Kuka ba zai zama maganin komai ba, ina roÆ™onki kar ki yi kuka, hakan idan ki kayi zan ji daÉ—i saÉ“anin hakan kuma zan ji babu daÉ—i saboda Sumayyah tunanina gida za ki je kowa naki ne a gidanmu, idan wani akasi ya faru ba yadda muka so ba kina dani, zan yi miki abunda ko wanne Yaya yake yiwa kanwarsa Sumayyah dan Allah kar ki yi kuka saboda hakan zai É“atamin rai zan ji ya sagarmin da gwiwa” Maganar Yaya Samir ita ta ratsamin zuciya na É—ago na kallesa bayan yakai Æ™arshen maganarsa

    "Yaya Samir ba kuka nake ba” nayi Maganar ina maida kaina Æ™asa

    "Kina jin babu daɗi ko, rabuwa da iyaye Sumayyah saidai bisa dole kema ki ɗauki hakan tamkar dole, kuma ina fatan ki ɗauki nawa iyayen kamar naki, bana so ki yi maraici ta dalili na, ni ma zan yi addu'ar Allah ya sa ba za a samu matsala tare da nawa iyayenba, Sumayyah inasan zumun ci, kuma inason yinshi da ƙarfina da kuɗi na, kimin addu'a Allah ya sa kar nida iyayena muci amanar zumun cinmu"

    Murmushi kawai na yi Jin Maganar da Yaya Samir yake yi, da maganarsa tasa hankalina ya kwanta sosai harna daina jin zullumi sosai haka dai na daure na ce

    "Amma Yaya Samir zan kai yaushe kafin na dawo gida”

    Murmushi ya yi da na gani kan fuskarsa ya ce

    "Sai mun yi aure tukunna za ki zo ki ga gida” ya Æ™arasa zancen yana hararata

    Duk da na san wasa yake yi sai da gabana ya yanke ya faɗi jin batun aure danni a ƙaddarata bana fatan Allah ya ƙaddaramin auren zumun ci musamman yadda zumun cin ya ta ɓarɓare, Maganar Yaya Samir ta katse min tunanina

    "Ya kikayi shiru Ƙanwata wasa nake miki, ba za ki daÉ—e ba za ki dawo, amma saikin saba da mu 'yan uwanki, dan tun farkon zuwana na fahimci kamar tsoronmu kike ji, wanda baikamata É—an uwa ya ji tsoron É—an uwansaba, shi ya sa na yi alÆ™awarin zan É—aukoki ki zauna tare damu, ken samu har sai za ki yi aure ki dawo, idan ma a katsinan ne da nafi kowa jin daÉ—i” nidai shiru na yi dan gaba É—aya bana fahimtar inda zancen Yaya Samir ya dosa barci ma na ji ina ji hakan ya sa na yi shiru na fara gyangyadi, tsayawar motar ya sani buÉ—e idona parking Yaya Samir ya yi gefen titi dai dai Rufaida fura and yoghurt na rijiyar za ki fita ya yi a motar ba tare da ya ce min komai ba, dan nafi tunanin yaji haushina ne, ya yi magana ban basa amsa ba, bai jima da fita ba ya dawo ya miÆ™omin ledar Rufaida yana cewa” ga wannan dan tafiya Katsina ba dai nisa ba na san za kiji yunwa kafin mukai”

    Godiya na yi masa, shi ma na shi da ya siyo ya sa bayan mota muka ci gaba da tafiya da muke tafiyar ina tunanin makomata a nan gaba kaɗan, kaina na mayar ƙasa ina tuno komai na rayuwata yau ni ce wai zanje inda ba muda wata daraja a idanunsu, gidan mutumin da saboda Mamanmu ya hana Abbanmu aiki a haka har zan yi tunanin akwai wata soyayyar da zan tarar a gidan wan mahaifina, zan jure komai na yi alƙawari ba wai dan kowa ba sai dai Yaya Samir da a baya na ɗauka ni ɗin babu wani Wanda zai so rayuwa da mu, a cikin dangin Abba, amma sai ga Yaya Samir yana so na rayu har abada a tare da su, da a ce dangin Abba kamar Yaya Samir suke da na san babu abin da xamu rasa a rayuwarmu, duk da ba wanda yake azurtawa sai Allah amma dai na san da abubuwa da dama sun ragu

    Sai wajen ƙarfe huɗu da mintina muka ƙarasa Katsina dan Yaya Samir ba wai gudu yake a mota ba, kuma gashi Katsinan ma akwai tafiya babu laifi Katsinan ta burgeni sosai duk da ba wai takai inda na baro ba amma dai tana da abun birgewa ita ma

    A Kofar gate É—in wani gida upstairs Yaya Samir ya fara horn É—in motarsa wanda ko ba’a faÉ—amin ba gidan Abban Katsina ne, cikin mintina Æ™alilan aka hangame gate din gidan, ya kunna hancin motarsa cikin gidan mai gadi yana É—aga masa hannu da ce masa "sannu da zuwa” Gurin aje motoci ya Æ™arasa ya parking É—in motar ya fito, ni ma ba nida zaÉ“i da ya wuce na fito gabana yana tsananta faÉ—uwa da addu'ar da na fara ta rage haka har na tsaya na bi gidan da kallo tabbas gidan ya yi kyau sosai, dan za suyi kyau É—aya da gidan Aunty Asma'u daga fara kallonsa da na yi, a raina na ci gaba da ayyana muna da masu kuÉ—i haka duk a 'yan uwan Abbanmu amma rayuwarmu take haka babu Wanda zai kalle ni ya ce akwai dangina masu kuÉ—i musamman idan ka ga gidan da na fito Maganar Yaya Samir ta ktsemin tunanina

    "Kizo mu karasa ciki, Malam Musa zai shigo da kayanki cikin gida” ya Æ™arasa zancen yana fara tafiya ni ma ba nida zaÉ“in da ya wuce bin bayansa da na yi Kofar falon muka Æ™arasa knocking mukayi ta buÉ—e muka shiga da sallama babu kowa a falon sai Æ™arar fanka da Ac kawai a falon tsayawa na yi kawai kaina a Æ™asa dan bana so a lura da Æ™auyancina shi ya sa na maida kaina Æ™asa

    "Ki zauna mana bari na kira Ummi na sani tana ciki” Maganar da Yaya Samir ya yi ya sani É—ago kaina da kafin na zauna Yaya Samir har ya fara tafiya hakan ya sani zama a kujera mai É—aya ina ware idanuna a kan komai dake cikin falon komai ya yi dai dai da tsarin falon komai na falon brown ne harda labulaye, Maganar da na fara ji ya sani maida kallona ga inda nake jin maganar Yaya Samir ne sai Mamarsu da kallo É—aya na yi mata na ganeta inda nake suka Æ™araso

    "Maraba da Kanawa, ansha hanya”

    Naji Maganar mamarsu Yaya Samir kamar daga sama da ban tsammaci hakan daga gare taba, murmushi na yi da a lokacin take ƙoƙarin zama kujerar dake kusa da tawa da shi ma Yaya Samir ya zauna kusa da mamarsu

    "Ummi in yini” nayi maganar da alamun rashin sabo

    "Lafiya ƙalau Sumayyah, ya kuka baro su mamarku"

    Na ce” Alhamdulillah"

    Daganan Ummin ta fara ƙoƙarin kunna Tv tana cewa

    "Bari a kawo miki abinci ko ciki za ki shiga, ki huta, ki yi sallah"

    Kafin na yi magana Yaya Samir ya rigani

    "A'a Ummi gwara ta shiga ciki ta gaji sosai koni buÆ™atar hutun nake”

    Ummin ta ce

    "Shike nan taje É—akin, Fatima ka nuna mata tun da saika wuce bangaranku"ni dai kallon Ummin kawai nake dan har yau na kasa fahimtar farin ciki take da zuwa na ko akasin hakan, Yaya Samir ne ya miÆ™e tare da cewa” taso na raka ki”

    Ban musa ba na miƙe na bi bayansa jikina duk a sanyaye da tunani da yawa a raina kodai za su barwa Yaya Samir da yakawoni gidan ɗawainiyatane, da wannan tunanin nawa muka fara taka step har muka ƙarasa hayewa Yaya Samir kallona ya yi bayan mun gama ƙarasa hawan

    "Sumayyah kiya hakuri da yadda kika ga Ummi ta yi Miki, ita É—in haka take, sam bata fiye son mutane ba komai zance ne”

    Murmushi na yi

    "Yaya Samir to mene na faÉ—amin hakan"

    Murmushin shi ma ya yi ya ce

    "Sumayyah inaso Allah ya kawo sauyawarsu su so duk wanda zai raÉ“emu ko da ba muda alaÆ™ar jini, dan su É—in, bari dai kawai za ki tabbartawa kanki, yanzu ki shiga ki huta ki yi sallah ga É—akin Fatiman nan" ya Æ™arasa zancen yana nuna min dakin da hannu da ganan ya yi gaba ba tare da ya jira mai zance ba ba nida zaÉ“i da wuce shigewa É—akin, komai na gidan masu kuÉ—i ya yi É—akin kansa kamar na tawa amarya yake Kuma É—akin budurwane kamar ni, dakin ya burgeni sosai, komai na dakin ya dace da muhallinsa, sallah na yi kawai ka sancewarta Æ™asaru ma, daganan na kwanta saman carpet ba yunwa nake ji ba, dan nasha yogurt É—in da Yaya Samir ya siyamin a mota, ban jima ba barci ya É—aukeni da tunanin makomata, a irin wannan gidan da Yaya Samir ya fara sanar dani, wanda dama na sani ba su san talakawa, amma har yau naka sa fahimtar dalilin É—aya Æ™waƙƙwara da ya Sanya Yaya Samir kawoni cikin rayuwar da bata dace dani ba” .

     **** **** 

    Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
    Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
    Lambar Waya: 08124915604
    Na Cancanta

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.