Na Cancanta (Kashi na 11)

    "Zaman har na nawa ne da zaka yi maganar Islamiyya ko kuma zaman ta ke nan, nufinka ba za ta koma garinsu ba, Samir kana sane dai da cewa Abbanku ba san zaman yarinyar nan yake a gidan nan ba, karka ɗorawa kanka nauyi tun kafin ka aje iyalanka, kamin magana tun kwanaki kan Islamiyya kuma ban goyi baya kasata ba shi ne kawai magana”

    Muryar Ummi nake jiyo wa daga falo har zuwa ɗakina da alamun faɗa da nafi tsammanin saboda ɗaga muryar da ta yi nake jiyowa amma ba na jiyo zancensu, ban san mai Yaya Samir ya faɗa mata ba na ji ta ɗora da cewa

    "To taji mana, ai ba zaginta na yi ba, kawai gaskiya na faɗama shi Abban naku ba ka fishi kusanci da ita ba amma ya yi biris da lamuranta ko kulata ba ya yi a kan wanne dalili kai kuma za ka shiga so kake ka ƙarawa kanka laifi a gurin sa kana gani turka turkar da aka yi kafin ya yarda yarinyar nan ta zo haba Samir ka riƙa tunani mai kyau"

    Kaina ne na ji ya saramin jin maganganun Ummi da ma Abba baiso zuwana cikin ahalinsa ba ko da yake ba wai abin musu ba ne dan yanayin da nake gani a gurinsa ya daɗe da fahimtar dani gaskiyar lamari, tunani nake mai nene makomata a nan gaba a gidannan, zaman nawa kansa mene anfaninsa, tabbas na fahimci akwai wata ƙaddarar da take sargafe dani da zamana a cikin wannan ahalin, ban sake jin hayaniyar Ummi ba hakan ya sa ni jin daɗi ya kuma ba ni da mar ci gaba da tunanina

    Da yammacin ranar na fito a kasalance nake tafiya harabar gidan na nufa dan yau bana sha'awar zaman ko da falon a tsaye na hangosa ya jingina da bishiyar dake harabar gidan da gani tunani yake dan shi bai hango ni ba hakan ya ba ni damar kallonsa sosai Yaya Samir yanayinsa yana burgeni sam bai da kwaranniya daka gansa za ka fahimta mutumin kirki ne sosai, gurin da yake na ƙaraso ina murmushi tare da sallama sallamartawa nafi yaƙinin ta maidosa tunaninsa ya yi firgigit ya dawo daga tunaninsa amsamin sallamar ya yi hakan ya sa ni gaishesa ya amsamin da murmushi fuskarsa ya kuma yi gyaran murya ya fara magana

    "Sumayya ban san ta ina zan fara baki hakuri ba saboda na san zaman haƙuri kikeyi gidan nan daga zuwanki tabbas inaso ki koma garinku a yanzu, sai dai kuma duka zaman da ba'afi sati biyu da kwanaki ba na ce za ki tafi inaga bai kamata ba, dan Allah ki ƙara haƙuri”

    Shiru na yi na mintina da sai da kyar na iya lalubo amsar da zan basa dan gaskiya nafi buƙatar komawa gida da irin wannan zaman da baida wani anfani sam, zama cikin mutanan da ba su san zumun ci ba

    "Bakomai Yaya Samir ni ma ban gaji da zama ba”

    Ya ce” Sumayyah ke nan na sani ba wanda zaizo gidannan ya ce bai gaji da zama ba, muddin ba yana da abin hannunsa ba, gashi batun islamiyyarki ya rushe, dan Allah kimin afuwa ba laifina ba ne”

    Shiru na yi na maida kaina ƙasa ina tuno maganganun ɗazu da kunnuwana su ka ji na dai daure na ce” Bakomai Yaya Samir tun da ba wai zama na ke nan ba idan na koma gida zan ci gaba da zuwa”

    Ya ce” Haka ne Allah ya kaimu lafiya, ya ƙara miki hakuri da juriya”

    Na amsa da

    "Amin"

    Na ci gaba da cewa ina mai duƙar da kai

    "Yaya Samir dan Allah ka kiramin Halima mu gaisa”

    Ya ce

    "Halima wace ce haka Kuma” ?

    Na ɗago na kallesa na ce

    "Ka manta Halima da Batul ƙawayena daka tarar dasu gidanmu ranar da za mu taho nan"

    Ya ce

    "Oh sorry na tuna kina da number ɗinsu ne ni ba nida ita”

    Nayi saurin ce wa” Eh Yaya Samir akwai na haddaceta”

    Ya ce” ok to"

    Da ganan ya miƙomin wayar yana mai ɗorawa da ce wa

    "Saka number ɗin ki kira”

    Wayar na amsa na kira da bugun farko Halima ta ɗaga sallamata da taji ya sa na ji 'yar ƙarar da ta saki tare da ta na ce wa

    "Nayi tsammanin kece, dama shi ya sa na ɗaga ba wani ɓata lokaci”

    Na yi murmushi na ce

    "Shi ne ko amsa sallama babu"

    Naji muryar Haliman tana” ke rabu dani wanni sallama zan amsa, kullum cikin tsammanin kiranki nake yi baki Kira ni ba tunanina ko kin manta da ni”

    Na girgiza kai kamar tana ganina

    "Ya zan yi na manta dake Halima idan na manta dake ban cancanta da zama ƙawar ƙwarai ba kamarke, Yanzu dai ya kike ya Batul da Mama”

    Haliman ta ce

    " ƙawar kwarai ai ke ce Sumayyah na yi rashinki daga ni har Batul, ni ma ina lafiya haka ma Batul da Mama dan jiya i yanzu muna tare da Batul, gidanmu ta yini dan har gidanku na barta za ta biya ta gaida Mama sannan ta wuce gida”

    Naji daɗin jin yadda ƙawayen nawa ba su manta dani ba duk da bana nan sun tuna da mahaifiyata na ce

    "Naji daɗi sosai Halima Allah ya bar zumun ci”

    Ta ce "Amin yawwa baki tanbayeni su Yaya Baffa da Yaya Hakeem ba, da Yaya Yazid kullum suna tambayarki ke har Faisal ma”

    Na ce” yi haƙuri Halimatu, suna raina fa”

    Haliman ta ce

    "Ba wani nan, yanzu yaushe Za ki dawo?"

    Na ce” sai sanda Yaya Samir ya sa rana”

    Halima ta ce” Dan Allah karki daɗe, mun yi rashinki sosai Sumayyah,, kuma ga karatu ma, kin san mun kusa komawa hutu"

    Na ce "Haka ne Halima, ai ba zan daɗe sosai ba duka ma yau kwana na nawa a nan ɗin"

    Haka dai muka ci gaba da fira da Halima Yaya Samir kuma bai ce na basa wayar ba sai da muka gaji mukayi sallama na basa wayar sai da ya amshi wayar ya kalle ni

    "Da gaske kike Haliman ƙawarki ce?"

    Na ɗaga kai na kallesa na Kuma maida kaina ƙasa dan bana jurar haɗa ido da mutane sosai ba ma Yaya Samir kaɗai ba na ce

    "Eh ƙawata ce”

    Ya ce” Kai amma abin ya birgeni kuna ta hira kamar yayarki ko ƙanwarki, ban yi tsammanin akwai ƙawa kamar wannan ba a yanzu"

    Nayi murmushi na ce” Yaya Samir Halima tana da alkhairi sosai kullum fata na na kwatanta abin da ta yi min saboda na san ba zan iya biyanta ba”

    Ya ce "haka ne insha Allah ni ma zan taya ki kwatanta hakan indai za ki tayani” haka muka ci gaba da fira da hirar duk ta Halima ce sai ko Batul da Yaya Samir ya buƙaci na sanar da shi alkhairin Haliman da Batul a gare ni.

     **** **** 

    Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
    Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
    Lambar Waya: 08124915604
    Na Cancanta

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.