Na Cancanta (Kashi na 13)

    Sallamar Abid ta katse min tunanin da nake yi sai da na amsa masa ya shigo daga cik gefena ya zauna ya miƙomin wayar dake hannunsa

    "Yaya Sumayyah ki amsa waya Yaya ya ba ni Æ™awarki na kiranki”

    Ban tsammanin kiran kowa ba bayan Halima Kuma ita ce dai ƙawar tawa da Yaya Samir ke da number ɗinta haka nan kuma na ji gabana yana faɗuwa haka dai na daure na anshi wayar, wayar Yaya Samir babu password hakan ya sa na karɓa na danno number ɗin Halima na bi kiranta

    Sallama na yi mata bayan ta É—aga jin bata amsamin ba ya sa na cire wayar a kunnena na duba wayar ba wai an katse ba ne haka na yi tunanin ko ba service haka dai na sake maida wayar kunnena na sakeyin wata sallamar kukan Halima na ji da shashshekarta tuni na ruÉ—e gabana ya ci gaba da faÉ—uwa na daure na fara tambayar Haliman

    "Halima lafiya maike damunki, ba za kimin magana ba sai kuka mai yafaru dan Allah ki sanarmin kar ni ma ki sani kuka”

    Da wannan lallashin da nake yiwa Halima ya sa ta yin shiru tana ajiyar zuciya zuwa can ta soma magana

    "Sumayyah Æ™addara ta riga fata duk Æ™oÆ™arinmu ba xamu guje mata ba, kuma kowanne bawa da irin yadda Æ™addararsa ke zuwar masa, haka dole kowa ya yi haÆ™uri da irinta sa, saboda cikar imaninka”

    Shiru na yi Ina sauraren Haliman Kuma bugun zuciyata na tsananta ƙaruwa na dai daure na ce

    "Halima dogon jawabin nan ya isheni duk na san da hakan, ki sanar dani abin da ke faruwa dan Allah, hankalina ya kasa kwanciya”

    Halima ta É—anyi shiru kafin ta ce

    "Exam din mu ta ƙualyfying ta fito sai dai Sumayyah ajinmu mutum goma suka samu ciki. . . "

    Gaba na ya ƙara faɗuwa na dakarta da Halima idona yana zubar da hawaye masu zafi

    "Babu ni a cikin waÉ—anda suka ci ko?"

    Nayi mata tambayar saboda Ina da yaƙinin haka ne jikina kawai ya bani

    Shiru ta yi na sake jefa mata tambaya

    "Ban ci ba ko?"

    Cikin ƙinƙina ta ce

    "Eh. . ey"

    Bata kuma sake cewa komai ba

    Nice ma na sake ƙoƙarin yin magana amma na ji ta yi shiru alamun ta katse wayar hakan ya sa na cire wayar a kunne na na miƙawa Abid da hawaye suka cikamin idanuwa na

    Abid ya soma magana

    "Yaya Sumayyah mai yafaru ne kike kuka”

    Hawaye na na goge na ce

    "Bakomai Abid"

    Kallona ya yi ya ce

    "A'a da komai fa Yaya Sumayyah ki faÉ—amin Dan Allah"

    Na sake ce masa

    "Bakomai Abid, kaje ka kaima Yaya wayarsa”

    Ya ce

    "To shike nan zan kai masa amma dai zan faÉ—amasa kuka kike bayan kin gama wayar"

    Haka Abid ya tashi ina kallansa sau tari idan na gansa muna wata firar Ina tunawa da Ahmad da yake kusan kamarsa, haka a halayyarsa nakan tuna Ahmad saboda yadda shi ma Abid ke da kyawun hali sam ba ruwansa da sabgar 'yan gidansu, shi da Yaya Samir halayyarsu ta banbanta da 'yan uwansu su akwaisu da tausayi da son zumun ci saɓanin sauran kowa halin iyayensa ya biyo, batun ƙualyfying ɗinmu ta faɗomin a raina na rasa mai zan yi kuka zan yi ko me da zan ji sauƙi a zuciyata kaina na kife a ƙasan carpet ɗin da nake kai zaune ina wani irin kuka Mai ciwo shike nan karatun da na saka rai zanƙarasa ba zai samu ba, karo na farko na faɗi jarabawa, shin ta ina iyayena za su nemo kuɗin da za a biyamin na kammala karatuna na sani babu mu ɗin da neman na yau da kullum muke ta yaya za mu nemo kuɗin biyan jarrabawa, duk da Ina da yaƙinin a cikin dangin mahaifina akwai waɗanda mutum dubu za su biyawa jarabawa ba tare da arziƙinsu ya girgiza ba amma inada yaƙinin ban da ni hakan ya sa ma ban saka rai ba, ya sa kuma na shiga damuwa mai tsananin gaske

    Sallamar da Abid ya sakeyi ta dawo dani daga tunanina ta Kuma tsayarmin da kukan da nake amsa masa sallamar na yi ya Kuma shigo ya maida kallensa gare ni

    "Yaya Sumayyah kuka kike ko, ina jiyowa tun daga kofar É—aki ki barwa Allah komai”

    Na _daga masa kai

    Da ga nan ya ce

    ", Yaya yana waje ya ce kije yana compound"daga nan ya fice ni ma ba nida zaɓi illah na saka hijabi na bi bayansa

    A tsaye na hangosa fuskarsa babu wata walwala sallama na masa ya amsamin na gaishesa ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar tawa, wanda ban san dalilin hakan ba yana nuna min kujerun robar da ke kusa dani yana ƙoƙarin jan ɗaya daga ciki ya ce

    "Ki zauna ma na” hakan ya sa na ja ni ma na zauna da Bismillah baki na

    Kallon da Yaya Samir yake min da na kasa jurewa na yi ƙasa da kaina

    Shirun da ya ratsa tsakaninmu can Yaya Samir na ji gyaran muryarsa ya fara magana

    "Sumayyah dan Allah ki yi haÆ™uri da duk yadda rayuwar za ta zo miki na sani hakan babu daÉ—i, na ji kamar ina ma nine ke, rayuwarki tana ba ni tausayi duk da na sani jarabtace daga Allah, na san komai Sumayyah, ni Haliman ta fara yiwa maganar ban san ta Ina zan tunkareki da zancen ba hakan ya sa na ce ta sanarda ke da kanta, ko damuwar za ta zo da sauÆ™i a gareni, Sumayyah ba ni da sauran nutsuwa duk da na san kin cancanta na miki komai sai dai yadda zan riÆ™a kyautata miki ba tare da na É“atawa su Abba rai ba, ban san ta ina zan misalta boÉ—adden halayyar Abba da Ummi ba dan Allah kiya haÆ™uri Sumayyah ki É—auki komai na rayuwarki bisa kaddara kuma komai zai wuce”

    Kai kawai na É—agawa Yaya Samir don ban san irin amsar da zan basa ba don zan iya fashewa da kuka ina fara magana, magana shi ma ya ci gaba dayi

    "Yanzu ki kwantar da hankalinki, zan yi magana da Abba zan biya miki kuÉ—i ki zana a private idan lokaci ya tashi”

    Ban wani gasgata lamarin ba dan na san abin Kamar da Kamar wuya shiga islamiyya ma sun hanani bare Kuma biyan kuÉ—in zana exam, hawaye suka cikamin idanuwa na don ina da tabbacin kawai lallashi ne kawai, na dai daure na ce

    "Yaya Samir ko ban zana na ba na karÉ“i kaddarata, amma Yaya Samir Halima da Batul nake so na ji sun samu, hankalina ya fi tashi idan na tuna su ban san tasu makomarba”

    Yaya Samir ya kalle ni

    "Ki share hawayenki Dan Allah, sai na faÉ—amiki komai”

    Ba nida zabi illah na goge hawayen na fara saurarenshi

    "Batul da Halima duk sun samu, Sumayyah kece kawai Allah ya Æ™addaramiki hakan ba wai dan baki da Æ™oÆ™ari ba illah kawai jarrabata ce daga Allah hakan Allah yaso, idan Allah yaso zai jarrabci bawa saiya jarabceshi da abubuwa kala kala bawai dan bai sanshi ba, sai dan yana nufin mutum da wani alkhairi”

    Bana sauraran zancen Yaya Samir sosai na kife kaina jikin gwiwa ta ina kuka da bana jin akwai mutumin da nake buƙata a yanzu bare jin muryar wani, a kusa da ni, ƙaddara ce na sani amma ban san kalar ta wa ba a lokaci ƙanƙani komai ya sauya min, ni ka ɗai na san ciwan da na ke ji da raɗaɗin da nake ji da babu mai fahimtata.

    Bayan wasu kwanaki da na ɗauki komai a bisa ƙaddarata na Kuma amshi hakan, walwalata ta soma dawowa saboda yadda kullum na yi waya da Umma a wayar Yaya Samir takan kwantarmin da hankalina

    Yau da shirin zuwa aiken Ummi na ta shi, dutsen safe za mu ni da Abid gidan Æ™anwar Ummi Aunty Ramla ka sancewar weekend be Æ™arfe goma muka fito bakin titi ni da Abid da nake sanye da doguwar rigar material sai mayafina kalar brown kwalliyar fulawar jikin material É—in muna tafe muna fira cikin wasa da dariya mun yi matuÆ™ar sabo da Abid matuÆ™a kamar mun shekara da shekaru tare haka muka tsaida napep muka shige muna faÉ—amasa unguwar da zai kaimu dutsen safe low-cost, babu laifi mun yi 'yar tafiya, kafin mu isa unguwar har Æ™ofar gida aka Æ™arasa damu, muka miÆ™amasa kuÉ—i muka fito ni da ma ban taÉ“a zuwa gidan ba Abid ne yake jagorantar tafiyar sai da muka Æ™wanÆ™wasa gate É—in gidan da mintina kafin zuwa can muka ji alamun tafiya, hakan ya sa muka tsaida buga gidan Aunty Ramla din ce ta buÉ—e kofar da fuskarta ba yabo ba fallasa ta yi mana izinin mu shigo ciki bayanta muka bi har zuwa ciki a babban falo muka zauna saman kujera muna gaishe da Aunty Ramla din haka dai ta amsa tana É—an shan Æ™amshi har mamakin hakan na yi ganin da Abid na taho ya kamata a ce ta É—an saki fuska ko danshi duk da ban san halin Aunty Ramla din ba Æ™ila hakan take ba mu jima sosai gidan ba muka fito Dan yaran Aunty Ramla biyu duk basa nan, suna gidan kakanninsu, ba mu samu napep ba a nan Æ™ofar gidan ganin za mu daÉ—e ya sa muka fara tafiya a Æ™asa duk da saÆ™on da muka amso masu nauyi ne amma ba muda zaÉ“i ban da muyi kama kama muka riÆ™e hannun ledar nida Abid muka fara tafiya zuwa bakin titin hankalinmu kwance muna fira da Abid yana ba ni labarin Aunty Ramla Wanda a labarin na fahimci halayyarta ce shariyar data mana, amma duk da hakan har dama wulaÆ™anci na faÉ—a a raina labaran Aunty Ramlan ya dinga ba ni na tun kafin ta yi aure har zuwa yanzu wani abun har dariya take ba ni a raina Kuma "ina lallai su Abid tona asiri ne”

    "Sumayyah!, Sumayyah!!, Sumayyah!!!"

    Kin kiran ba É—aya ba ba biyu ba ya sa ni waigowa tare kuma da san tuno Mai muryar tsammanin da na yi ko hakan ne

    Malam Hamid ne idan ba idona ne suke min gizo ba, domin a sanina lokaci baiyi tsawon da zan manta da shi ba, kallon mamaki nake masa, ni ma shi yake min a hakan har ya ƙaraso inda muka tsaya, gaishesa na yi ya amsa da murmushi fuskarsa haka Abid ma ya gaishesa Malam Hamid ya miƙawa Abid hannu suka gaisa yana tambayarsa sunansa Abid ya yi murmushi ya faɗa masa da alamu Malam Hamid ya birgesa guri na ya juyo ya maida dubensa gareni

    "Wato da ba za ki juyo ba ko?, harna fara tunanin Æ™ila bake bace, dan muryarki kawai na ji harna ci gaba da tafiya na yi tunanin ke ce”

    Nayi murmushi nace

    "Eh ni ce ni ma da farko ban yi tsammanin kai ba ne, saboda ban yi tunanin sake ganin ka ba”

    Murmushi yayi

    "To saboda me, bayan kin san nan garinmu ne”

    Shiru na yi dan ba ni da tacewa danni ganin mai kuÉ—i nakewa Malam Hamid Ina zansa wa raina tunanin ganin sa, karo na biyu

    Maganar Malam Hamid ta katse min tunanina

    "Kinyi shiru kullum na kira Halima saina tambaye ta ya kike takan cemin lafiya lau, Kuma har lambarki na buÆ™ata ta ce baki da waya yanzu haka da ta yayanki na nan kuke gaisawa, ni kuma banwai amsa ba saboda ban san mai zance masa ba idan na kira”

    Na jinjina kai alamun na gamsu da maganarsa

    Ya ci gaba da cewa” na samu labari jarrabawar ku batayi kyau ba Allah ya sa hakan ya yi sanadiyyar samun nasararku a nan gaba, abun sam baimin daÉ—i ba Sumayyah saina ji kamar ni abun ya faru dani”

    Duk da bana son a tuno min abunda ya faru amma haka nan na daure

    "Nace Amin na gode”

    Bai ƙyale maganar haka ba, ya ce

    "Yanzu kin ga rana ta farayi kimin kwatancen gidanku na nan sai na samu lokaci na zo, mu Æ™arasa maganar da ba mu Æ™arasa ba a baya”

    Shiru na yi Ina tunanin maganar da na san ta soyayya ce take nufi ba dan ina da buƙatar sa a rayuwata ba na masa kwatancen gidan tare da jagorancin Abid a kwatancen kawai dai saboda kirkinsa na yi masa kwatancen amma gaba ɗaya a Raina kulllum ba ni yake Malam Hamid ba sa'ana ba ne a soyayya bare kuma aure duk da ban san koshi waye ba

    Haka muka yi sallama yana Mai min alƙawarin zaiso a satinnan insha Allah, daganan muka ci gaba da tafiyarmu Abid yana tambayata waye shi wannan, na masa bayaninsa, a matsayinsa na malaminmu ya dube ni

    "Gaskiya Yaya Sumayyah yana da kirki sosai”

    Nayi dariya na ce

    "Kai Abid daga ganin mutum haka ai ba’a shaidar mutum Karan farko"

    Ya jinjina kai ya ce

    "Haka ne”, daganan muka sauya firar da wata” har muka Æ™araso bakin titi

    Abun abun mamaki nan ɗinma babu motoci ga zafin rana haka na ji Kamar nasa hannu ka na fashe da kuka dan tsabar takaici da bakin ciki ga fangon kaya a hannu tsugunnawa mukayi muna roƙon Allah ya kawo mana mafita, babu jimawa mota mai kyau sosai ta tsaya kusa da mu da ni ba ma'abociyar sanin mota ba bare na san sunanta ko kuɗinta horn aka yi mana ganin ba mu san mai ita ba mukayi shiru jin ƙarar buɗe motar ya sa muka ɗago kanmu, Abid na ga ya ƙarasa gurin mutumin da yafito daga motar da alamu Abid yasan mutumin ni ma kallansu na yi

    "Kawu"naji Abid ya faÉ—a

    Saurayin da Saida ya kirasa kawun na kallesa tabbas yana yanayi da Umminsu Abid

    Tambayar Abid yayi

    "Yana ganku a nan Abid"

    Abid ya sosa kai

    "Mota muka rasa”

    "Ku shigo na kaiku gida yi ma waccen da kuke tare magana” kawun ya faÉ—a da ba musu ya Æ™araso guna Abid É—in niko tun kafin ya Æ™araso na miÆ™e dan gajiye nake dama, kayan muka kinkima mu ka Æ™arasa wajen motar, Abid ya buÉ—e min gidan baya na shiga a lokacin har kawun ya shiga mota abid É—in ya shiga gidan gaba kusa da Kawun nasa sai a lokacin na gaida Kawunsu Abid É—in ya juyo ya amsa kafin ya juya ina jinsa yana cewa

    "Abid wannan wace ban gane ta ba”

    Abid na ji ya ce

    "Yaya Sumayyah ce, 'yar Æ™anin Abbanmu ce Abba Abdullahi”

    Naji yana ce wa

    "Au ita ce rannan naje gidan na ku, Ummin ku ke ba ni labarin zuwan nata”

    Waigowa Kawun ya yi ya sake kallo na na ji ya ce

    "Yasu Asma'u ai sai yanzu na ga Kamar ki da Asma'un"

    Na ce masa

    "Suna gida lafiya lau"

    Da haka ya ja motar cikin mintina ƙalilan muka ƙarasa gida parking ya yi muka fito harda Kawun su Abid ɗin shi ne ya ɗauki ledar saƙon yana janmu da hira har muka ƙarasa cikin falon da ba kowa a falon sai Yaya Samir ɗin, yn danna wayar shi d Tv kunne Amma babu volume, sallamarmu ya amsa yana murmushi fuskarsa kusa da shi kawun ya zauna ya bashi hannu

    "A'a Malam Samir ana gida ke nan"

    Yace

    "Eh wllh Kawu Mahmud, yanzu da na ji shiru ba su dawo ba nake tunanin Kiran lambar Aunty Ramlah"

    "Ayya wllh a hanya na haÉ—u dasu suna jiran abin hawa”

    Ba muƙarasa jin zancen ba muka wuce ciki, kitchen Ni na nufa, na kawo musu lemo zan tashi Yaya Samir ya ce

    "Zauna mana firarki mu keyi da kawu Mahmud, ya ce waya ya kamata na siya maki ya ce kin isa riÆ™ewa”

    Kallona na mayar ga Kawu Mahmud ganin mun haɗa ido ya sa ni cikin jin kunya na maida kaina ƙasa, Muryar Kawu Mahmud na ji ya na cewa

    "Eh mana ki É—ago kanki mana Sumayya aikin isa riÆ™ewa na san Æ™awayenki duk wasu na da ita kuma insha Allah na san ba ba za ki wani abu mara kyau da ita ba” Har ya gama maganar ban É—ago ba sai ma ci gaba da kallon carpet da nake yi

    Kawu Mahmoud na ji ya É—aura da cewa

    "Tun kafin na gane ta na daiga yanayi da Asma'u tunanina ma da ko ƙanwar Asma'u ce saina tuna Asma'u bata da ƙanwa ashe ƴar tace, sosai tana da natsuwa Samir"

    Muryar Yaya Samir na ji ya bashi amsa da cewa

    "Eh na yi tsammani za ka ganeta tana yarinya a Gwarzo tana maƙalewa gurina Ummi tana cewa Sumayyahn Samir"

    Naji kawu cikin ƙosawa ya ce

    "Zaka fara surutun naka da sai anfi awa ba a ƙare ba ke nan ko?dan Allah tashi muje yanzu a siyo mata wayar nan tun ina da kuɗi a jikina idan mun dawo sai ayi firar, in Kuma an kirani wani gurin shike nan"

    Dariya ce take neman zuwarmin jin tattaunawar da suke yi, saika ɗauka abokaine ko na ce ƴan biyu ko cousin brothers sun burgeni sosai duk da inada yaƙini Kawu Mahmud ma ya girmi Yaya Samir tun da har ta yi soyayyah da Aunty Asma'u duk da cewa ban san a yana shekara nawa sukayi soyayyar ba, ƙila soyayyahr ƙuruciya ce kawai, hakan sosai ya ƙara burgeni

    "Taso muje ki zaÉ“a da kanki”

    Maganar Kawu Mahmud ta katse min tunanin da nake yi miƙewa na yi, hanyar komawa ciki na yi na kira Abid mu tafi tare ya tayani zaɓar danni ba wani zaɓen da zan iya ba na sani

    "Ina za ki kuma?"

    Muryar Yaya Samir ta sani juyowar na kuma tsaya da tafiyar da na fara idonsa na tsaye akaina yana kallona daurewa na yi cire idona daga nashi sannan na ce

    "Abid zan kira yaya”

    Yaya Samir ne ya harareni kafin ya ce

    "A'a Malama dawo wuce mu tafi” ya Æ™ara sa maganar yana nuna min hanyar fita falon

    "Toh Yaya” na iya faÉ—a na dawo da baya inda suke da Kawu Mahmud har ya buÉ—e Æ™ofar falon yana Æ™oÆ™arin ficewa ni ma na bi bayansu

    A motar Kawu Mahmud muka fita, Ba muyi tafiya mai nisa ba muka ƙara sa inda za mu siya wayar Green House parking Yaya Samir ya yi muka fito duk a tare muka shiga ciki

    Nida ban san wayoyi ba bare na iya zaɓar waya Yaya Samir ya zaɓarmin Iphone, da ƙarama maxfone da Kawu Mahmud ya ce a ɗaukar min acewarsa saboda iPhone bata riƙe caji sosai shi ne kuma ya biya kuɗin wayoyin, har layuka aka siyamin akamin register Yaya Samir ya yi min register saboda shi ne mai National ID Card sai ko Kawu Mahmud da ya ce ya bar nashi a gida, Murna sosai nake yi da yin wayar tawa dan ban taɓa kawowa raina ba na kuma dinga musu godiya kamar kujerar Makkah suka biyamin, dan kam wayar babbace sosai wanda ya siyama wannan wayar ya samu dama da rabon ka Makkah ɗin ma zai biyama dan ina gani Kawu Mahmud ya ciro Atm ɗin shi aka cire dubunnan kuɗin wayar da sai lokacin na gasgata kuɗin wayar dan dan ko da aka faɗa da farko ban gasgataba

    Naka sa Kuma fahimtar dalilin hidimar Kawu Mahmud mai yawa haka wajena Nidai na san ba mu da wata alaÆ™a ban da ka sancewarsa Æ™anin Ummi Saidai tun da ya ambaci Aunty Asma'u na fara tunanin Æ™ilashima yana cikin samarin Aunty Asma'u tana budurwa ta yi samari babu laifi "Hakanne ma ban da hakan ai ba zai miki hakan ba” zuciyata ce ta faÉ—a min hakan ta gasgastarmin, Duk da a halayyar Aunty Asma'u ban yi tsammanin akwai wanda zai mata matukar so hakan ba saidai ance so gamon jini ne

    ***********************************

    Ban jira na caza ƙaramar ba, Na kira layin, Halima, duk abin da zan yi bana manta Halima ita ce take fara faɗomin a raina, inasan Halima, fiye da tunani, ina jin wayarnan dama tana nan tare za a siyamana, Batul kam ba tada wata matsala, ita dai biye mana take yi, aurenta ma, tana gama makaranta za ayi nafi tunanin kirana duk da ban tabbatar ba

    Har wayar ta gama ringing ta katse Halima bata ɗaga ba hakan ya sani tunanin ko tana wani guri ko takai wayar caji da wannan tunanin na miƙe na maida ba wayar caji, na ci gaba da saƙa da kwancewa wata damuwa ta fara ƙoƙarin ziyartata

    Wayar na maida caji ina ci gaba da tunanin Halimah Allah ya sa dai ba wata damuwa idan kaji shirun mai ƙaunarka ya kamata ka shiga damuwa dan masoyi ɗaya ya fi ma maƙiyinka sau million

    Tunanin nawane ya katse jin ƙarar wayata daga cajin na ciro ta ina duba mai kiran nawa da bana raba ɗaya biyu Halima ce dan ita ce zan iya cewa kaɗai na kira a wannan lokacin

    Da sallama bakina mai haÉ—e da zumuÉ—i na É—aga wayar Halima É—in

    Ba tare da ta amsamin ba sai ƙarar murnar ta da ta cika kunnena ta ɗaura da cewa

    "Sumayyah, ba dai kin yi waya ba, "

    Nayi murmushi mara sauti Halima ke nan na yi maganar a zuciyata daganan na furta

    "Oh Halima haka kike yi kuma yanzu, kin cikamin dodon kunne da Æ™ara”

    Tsaki Halima ta yi min ta ce

    "Kiji 'yar rainin wayau dan ina murna shi ne kike min wulaÆ™anci, bari na kashe wayata dama ba katin gareni ba” 

    **** **** 

    Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
    Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
    Lambar Waya: 08124915604
    Na Cancanta

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.