Mun daɗe muna fira da Halima duk dai zancen na makaranta ne rabi da kwatarshi, Ina ƙoƙarin kashe wayar na tuna banma Halima zancen Aliyu ba danako san zansha mita gurinta Halima ta Aliyu rabin zancenta na shi ne indai kun yi sabo da ita soyayyarsu tana burgeni Halima ɗin ni ma da nake mace tana sona a matsayin da yama wuce ƙawa sai dai 'yar uwa bare Aliyu kuma na katse tunanin tare da yin hanzarin cewa
"Au Halima ya Aliyu?"
Kamar ba za ta amsa ba na ji ta a
hankali tana
"lafiyarshi ƙalau
na ɗauka ba za ki
tanbayeshi ba dan har zai fushi”
Jinjina Kai na yi Kamar tana
ganina "ah ni na isa Halima ai Kira dubu zance Aliyu sai ya yi dubu zan
miki” na ƙarasa
zancen ina dariya ƙasa ƙasa
Haliman ta fara” A'a Musa please
stop sarkin ƙarya,
na samu yanzu da kikayi ɗaya
ma”
Nayi dariya na ce” toh Ina laifi
ai zancenshi yana wajenki mu ji ne namu amma na cika zancenshiai kya tanbayi
ba'asi ya Batul ?bari na katse na kirata”
"Uhmm uhmm fa kina da Hamid ɗinki ga Yaya Samir ai na
saurara miki dan kin yi zancenshi banace komai ba, ok Batul bana faɗa miki wani a family house
nasu za ta aura ba ai ta yi shiru abunta ba yawo yaushe rabanta da gida, uhm
mene ma sunanshi Yasir"
Na yi dariya” Kai Halima na san
kishinki na baki labari na haɗu
da Malam Hamid ɗin ai
ya ce ma zai zo wajena, oh su Batul ashe akwai labari, gaskiya bari na yi
azamar kiranta zan yi ma, Mrs Yasir ma zan kirata da shi”
Halima ta sa dariya” ya dai
kamata ni Mrs Aliyu da baki kirani da hakan ba kema ya kamata ki tsayar da
gwaninki, mu sha bikinki kafin ma namu ni kin san Ina sha'awar zuwa garinku ɗinnan, ko yaushe gwarzo dai
muje mu ga ni dai ya Gwarzon taku take dai”
Nidai dariya na yi
"Kai Halima, ai Yaya Samir
ku kuke shagalinku ba saurayina ba ne, ƙila dai Hamid ne tom shike nan insha
Allah za ku zo Gwarzo kuwa, amma fa ƙauye ne”
Halima ta karɓi zancen
"Kai Sumayyah anya kuwa
akwai fa lauje cikin naɗi
amma gaskiya Hamid ya rigashi, dan ni har na cire Malam a gefe, gashi saurayin ƙawata
danko ko har yanzu yana school namu gaskiya dai ban iyawa Malam din nan, sai
dai karfa ki ƙi shi ki kama yayanku please matsalar ina faɗa maku ke da Batul soyayyah
da saurayi ɗaya tafi
daɗi ku bakwa gane
karatun gashi nan Batul ta sha Yasir ya yi ta maza, tom saura ke, Kai Sumayyah
ban da ƙarya
Gwarzon ku dagajin sunan garin ba ƙauye bace na san tafi dai wannan anguwar
taku a nan cikin garin, Bari ma zan tanbayi Aliyu yana da friends 'yan garinku
may be ma familynku ɗaya
za mu yi maganar dai insha Allah"
Na bita da "tom shike nan
"jin zancen bai ƙarewa zaro abunta take kawai gashi ko Umma ban kira ba bare
Abbah, gani da zumuɗin
jin labari wajen Batul, har wani sauri nake bayan mun yi sallama nasa layin
Batul, dan Mama sai anjima Abbah ya dawo gida toh hirar ma dai kusan gaisuwa ce,
sai Ahmad sarkin zance ya karɓe
wayar ga Rumaisa, ga Khadija kuma
Bugu ɗaya biyu na ma Batul ta ɗaga ba wata tsayawa sallama
na yi saurin Fara magana” Mrs Yasir, Sumayyah Abdallah ce dan ubanki”
Dariya ta kemin daga bangaren ta
"Kai Sumayyah har da zagi kinje katsina fa ko kin kwaro zagi?, ai za mu zo
mu tarkato ki da kayanki mu maidoki, na san Halima ta miki zancen Yasir, a
makaranta ma haka duk an kama Mrs Yasir, ai Halima ba’a sirri da ita, ƙilama
yanzu ku ka gama wayar ko na kirata line busy, ashe ana nan ana zancenmu ni da
bawan Allah, baki ga yadda yake ganin girman Halima ba nan bai san mutuncin ta
ragagge ba ne”
Dariya na yi” na ce kunfi kusa da
Haliman dai, tare ba barku, ba wani zance fa, kawai dai ce min ta yi kinyi, saurayi
a family house ɗinku
yake Yasir, kin san Halima ba ma za ta samu natsuwar min zancen dallah dallah, ba
murna ta isheta na yi waya ne fa, na faɗa
miki iPhone
Ƙara Batul ta samin"Wow Masha Allah, Alhamdulillah
congratulations, na yi murna ki ce za mu sha photunan candy da ita ki ƙoƙarta
yawwa Sumayyah ki dawo gida anata wuce ki fa karatu"
Na ɗan
yi Jim kafin na ce” Ina nan dawowa insha Allah, eh kam za mu sha photo kin san
iPhone akwai camera”
Batul ta ce” yawwa eh haka ne
hala Halima ta cika ki da surutun Aliyu da gulmata nida Yasir bata baki news a
kan school ba?, ai Halima ta ba ni ita dai ke Aliyu ai gwara muyi muyi candy ɗin nan ayi musu auren nan, ni
Allah ya sa ya samu da ita haka ma”
Nayi dariya ka ɗan "ai Halima ranta na
san Aliyu, da gani ɗin
yana santa ɗinne ai ba
banza ba, da kin ji zancen shi, ya Mata laifi ɗin
idan ko da ya na yi ko baya santa Kamar ita din"
Batul ta yi tsaki” wai Halima ɗin kin manta halinta ke nan,
abu na cinta bata faɗa
kai dai ta dameka da san ji ko ta fahimta, da kanta”
Nayi murmushi kawai Kamar gani ga
Batul ni ma tuno halayyar Halima nake yi halinta ni kaina na burgeni ba ruwanta
harkokin ta ta keyi ni ban taɓa
ji ma tamin zancen damuwarta ba ita dai kullum ta saka farin ciki Aliyu kuwa ba
na ce ga irin ƙaunar da take masa ba kai a jiki na sai nake ji dole ne ma
kowa na da nashi damuwar ciki harda Halima kuwa rufewa take yi kawai ko ba ta
yi yawa ba dai akwai ta na sani, maganar Batul ta katseni
"Ya dai Sumayyah kin tuno ko
ai halin Halima sai ita, ita dai ki ga kamar Bata da damuwa haka take
al'amuranta, ni dai muyi candy ɗinnan
ta yi auren dai kawai ta kyalemu da zancen Aliyu Ni yanzuma na rabu da ganinshi,
ko dan bana zuwa unguwarsu yanzu?"
Na ce” Eh haka ne Batul lokacin
da za ki ba lallai ya zo ba, ni ma dai burina dai muyi SSCE ɗinnan mu gama mu sha bikin
mu wuce wajen, har ke ma”
Batul ta sa dariya” au kefa din
kina maganarmu, Dan Allah ki cire wasa Sumayyah ki natsu ki karɓi Hamid ki yi aurenki ba za
muso muyi mu barki ba, duk ko wanne yanayi muke Mai sauƙi ne a kan naku, Dan
Allah karki biyewa wasu mu za ki biyewa ki karɓi
Hamid tun da da gaske yake ki bashi dama kawai”
Batul ke nan ba dai nasiha ba, ita
tasan ba kowa yake kamarta ba, ita Kuma Halima gani take kowa tunaninta gareshi,
duk kowa da yadda sanin ya kamatarshi take ina alfahari da su ni kam sun wuce ƙawaye
na, sai dai su tsaya matsayin Rumaisa da khadijah, harma sun fi haka saboda su
age mate nawa ne na dai ƙoƙarin danne tunanin na ce” Insha Allah Batul ina ta ƙoƙarin
hakan ya ce ma zai zo shi bai dai faɗamin
ranar ba”
Batul ta ce” oh hala baki kirashi
ba ke nan Bari zan turoma ki layinshi Hamid mutumin kirki ne Sumayyah"
Da haka muka yi sallama ba daɗewa na ji karar message lambar nake ta kallo ina jin kamar na kira Kamar kar na Kira shawarar ƙarshe na dauka na dauki lambar na danna Kira. . . .
**** ****
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.