A zaune na sameshi kan ɗaya daga cikin kujerun robar dake farfajiyar gidan gabana ya yanke ya faɗi idanshi na kaina har na ƙaraso inda yake da rawar jiki na ja kujerar na zauna ina
"Yaya Samir gani”
Shiru ya yi kamar ba zai amsamin
ba kafin ya ja dogon numfashi” Sumayyah kin kyautamin ke nan ko na ce kin
kyautawa kanki, na daukoki dan kisamu kyakkyawar rayuwa ki zama Kamar Fatima, a
raina na baki matsayin da yama zarce na fatimah, ni na san ciwan ki, nafi
dacewa ki tunkara da kowacce damuwa ko matsalar ki amma malaminku da Kika
tsinta rana tsaka shi ne zaizo har inda kike, a cikin rayuwar da nine nafi
dacewa da ke, Sumayyah, ko da aurenki na ce zan yi ban yi laifi ba, duk
tattalin da nake inaso na samu kusanci da ke ne”
Hawayen na ji suna zubarmin masu ɗumi na ɗago na kalleshi ba Zan jure
kallan yaya Samir ba idanunshi sun Fara rinewa na yi saurin cewa” Yaya Samir
Kaya haƙuri,
baxan sake ba insha Allah"
"Dago ki kalle ni Sumayyah
ki amsamin tambayata”
Dagowa na yi ba dan ina so ba na
kalleshi da hawayen da ke ci gaba da fitowa daga idanuna
"Sumayyah ina San aurenki be,
kece macen da na fara so da ƙauna tun ban san meye soyayya na, Sumayya
ta Samir ce, na jawoki rayuwata ki saba dani da sauran Familynmu, duk da ni
dake abu ɗaya ne amma
babu sabo tsakaninmu, dan Allah karki kalli Abbah ni da shi ba ɗaya ba ne ki amince min, Dan
Allah ki bawa wancen haƙuri idan soyayya ce tsakaninku ba dan Allah Sumayyah, idan ba
kisan aurena ba zan miki dole ba”
Shiru na yi kawai tun da ya fara
maganar Yaya Samir dai ba shida wani makusa a ina sanina shi duk wani shashanci
ba shi cikinsa Yaya AbdulMalik ne dai komai da ruwansa, na san ba wai da Abbah
ko Ummi zan zauna ba hayaniya kuma tunma daga kan AbdulHamid Abbah Hashim ya
fara ta, bare Yaya Samir inasan Yaya Samir saboda halayyar shi, Amma ya zan yi
da AbdulHamid ya ba ni dukkan yaƙini akaina, ya zai ji idan na kawo masa
wani zance daban, gaba ɗaya
lissafina ya dagule so nake na bar musu rayuwarsu gaba ɗaya hankalina ya koma gida idan na koma gaba ɗaya wayarma Banga anfaninta
ba, ba nida wata mafita anan, maganarshi ta katse ni
"Ba ki cemin komai ba
Sumayyah, baki Sona ko?, ban da ce a soni ba ko?, kifadamin?, Dan Allah
Sumayyah wancen ya fini matsayi da cancanta ko?, ki faɗamin mana”
Kuka na fashe da shi amma ba mai
sautin sosai ba, waini Yaya Samir yakema wannan magiya abin kunya ne a wajena
Yaya Samir ya zo neman alfarma na kasa yi masa, ni Sumayyah cikin kukan na Fara
"Yaya Samir dan Allah ka
maidani gidanmu gobe, dan Allah"
"Daina kukan Sumayyah ko yau
kike so zan maidake kin gaji da zama Dani ko bakison ganina yanzu, wani ya
rigani ko Sumayyah, shike nan, zan maidake gida, Ina jiranki amma dama ko da
yaushe na rayu cikin jiranki saboda Jininmu ɗaya,
kuma na dace dake Sumayyah a nawa tunanin nfi kowa sanin ciwanki, fatana ki
samu rayuwa me kyau sumynsamir, dan Allah ki yarda dani Sumayyah"
Maganar nama gaji da jinta wani ɓacin rai yake tasomin, ciki
na miƙe
zan shiga, Yaya Samir ya biyo bayana
"Sumayyah ki tsaya ki share
hawayen ki dan Allah, Kuma yanzu gaban Abbah din Zan nunaki matsayin matar da
nakeson aure, ke ce na tsaya jira a duk shekaruna, ke ce matata insha Allah tun
kafin a haifeki din zuwa yanzu"
Ko kallonshi din ban tsaya yi ba
bare ci gaba da saurararshi saboda komai ya kwancema lissafina da tunanina, kayana
nakeson haɗawa kawai
katsina tamin zafi a yau da ya fi na sauran kwanakin da na yi cikinta kofar
falon na buɗe na shiga
a zaune na samesu Kamar dama jira na suke yi Abbah Hashim da nake koƙarin
shigewa ciki ya dakamin tsawa
"Ke Sumayyah zo nan"
Hawayen da suke fitomin suka ci
gaba da zubowa na dawo jikina na kyarma na dawo na tsugunna ƙasan
carpet kaina na ƙasa Ina jiran tanadin Abbah Hashim akaina
Cikin alamun faɗa ya fara” karki ƙara
kiramin kowanne namiji kofar gidanƙ bare cikin gidana, ki kumayi gaggawar
bararmin gidana idan ba da ubanki na siyeshi matalautan banza Kun kasa zuciyar
tsayawa ku ne ma ku samu, ubanki na tare da uwarku dangin tsiya kaf dangin
Hauwa'u matalautane, gadon ta kukayi ƙashin tsiya garesu, na yi Kuma rantsuwa
Abdullahi da sisina ban taimakonshi sai ya rabu da uwarku ya auro wata ko ya
zauna babu matar, kuma Fatimah ta dace da auran wancen yaron bake ba, yadda
ubanku yake sai dai ku samu irinshi ku aura bana muku fatan ci gaba, idan har
ubanku bai haƙura da wannan matar ba uwarku"
Ummi ta miƙe tsaye Kamar Mai Shirin
faɗa ta ɗaga murya
"Haba Hashim me ita wannan
abar ta sani ita ce Abdullahi ko ita ce Hauwa'u, Abdullahi shugaban ƙasa ya
zama na yi imani ba zai wa ɗiyarka
Fatima haka ba, Kuma 'yata ba da yawuna ba wallahi Fatima tafi ƙarfin
a cusata Dan ba koma baya bace, addu'a nake mata Allah ya sa ta gane waye ke
Kai ta daina biyema, ni ma da naso biye ma wacce riba naci, 'yan uwana da suke
rufamin asiri so kayi ni ma na zama kamarka mu ɓata,
arziƙinka
naka na yaushe ne da ba ka da shi har ubanta ya taimakeka, bare 'yan uwana amma
sune abokan adawarka ba ka san na zauna dasu, ai sun rufamana asiri yanzu
budinka, ya zo"
"Khadijah ki dakatamin kan
wannan yarinyar ni Kika miƙe kina faɗawa
magana san ranki” Abbah Hashim ya yi maganar yana ƙarasowa gaf dani dukan da
yafaramin ba abun wasa ba ne ball yake dani yana "yau ko, Abdullahi ne gidannan
sai ya barmasa gida, bare 'yarshi”
Maganar Yaya Samir na jiyo duk da
dukan da akemin yana
"Abbah ka kyaleta haka za ta
koma gidansu yau din nan ni na kawota Kuma zan maidata, tabarwa Fatima wanda
kake magana kanshi, ni zan aureta, Abbah zan kawo maslaha dan Allah ka barta
haka na ji duk maganar da kakeyi ka yafe mata ta yi kuskure kar ka illatata
Ummi ta yi magana ba ita ba, Abbah ka saketa ni zn aureta”
Abbah ne ya sakeni Ina kuka yayo
kan Yaya Samir a zabure
"Samir me kake cewa za ka aureta
ita Sumayyah za ka aura masu ƙashin tsiyar Abdullahi kakeson zama ke
nan, wannan yarinyar har tana da abin da za ka so wajenta har kayi girman
tunkarata da maganar kanasan auren ɗiyar
Abdullahi, ni Samir, wallahi muddin ka kafe kan maganar ka na zare komai da
nake ma, Zan barka kaje gaka gatanan Abdullahi ya zama ubanka ba dai ni ba, karka
sake ka nemi taimakon sisi na”
Ummi ta ja tsaki
"Wai Hashim yaushe akai dare
garin ya waye, Ni Zan wuce masa gaba, indai tana sanshi ko za ka la'anceshi
wallahi sai ya yi niyyar alkhairi gareshi Bata sharri ba Kuma na fika kusanci
dashi, Ni ce na haifeshi nina raini cikinshi na haifeshi na yi duk dawainiya
dashi, ƙaryar
arziƙi
kakeyi ɗan baƙin
ciki da hassada 'yan uwanka ga sunan ba daɗinka
suke ji ba bare Abdullahi ya sa rai da yake nesa da zama daku"
Abbah Hashim ya nuna Ummin yana” Khadijah
ya ishe ni haka tun da ba ku ganin girmana kuje ku yi abunda za ku yi ku gani, Abdullahi
ba zai ba ku 'yar shi ba tun yanzu na ga alamun jari yakeson maidata, tafi
karuwa iya karuwanci”
Ummi dariya ma dagaji maganar ta
bata” Hashim kanada lafiya kuwa ko dai hassadar takai haka ne, fatanka iya kan
kanka zai ƙare,
'ya'yana ba zai jefesu ba tun da ba ka da tunani har kake ma ɗiyar ƙaninka
fatan karuwanci da 'yarka mace budurwa gabanka, tuni nadawo rakiyarka, iyayenka
ma ba zan shaidar daɗin
ka suke ji ba
Abbah Hashim yana huci Kamar za
ki ya fara koƙarin barin falon
"Na faɗa muku karna dawo na tadda
wannan matsiyaciyar yarinya gidana, karkiga kina magana San ranki wallahi na
dawo na tarar daku ranku zai mummunan ɓaci”,
daganan ya sakai ya fice
Ummi ta bishi da kallo wajena
sukayo ita da Yaya Samir suna lallashi na da ba ni baki a haka na shiga ɗaki na haɗa kayana Yaya Samir yana
jaddamin na yi sauri na fito, wayata da take yashe gado na kalla, Hamid ya faɗomin raina ya zaiji idan ya
samu labarin bana Katsina din da labarin kudirin Abba akanmu zai amince da
Fatiman a madadina ko kuma zai haƙura ne gaba ɗaya wayata na ɗauka
hannuna na rawa na danna lambarshi wajen message rasa ma me Zan tsaya rubutawa
na yi na daure nasa
"Kaya haƙuri” ita
ce kawai kalma Mai saukin da ko tunanina ba zan wahalar ba, wayar na kashe na
yi ƙoƙarin
turata ƙasan
jakar karamar ma da ba Wanda yasanni da layin haka namata raina ina iPhone ɗin banza ma bata da sauran
anfani a duniyata.
Ina kuka Abid mutumina yana yi, Ummi
na bawa Abid baki tana za ta kawoshi da kanta wajena ana hutu, Yaya AbdulMalik
da Fatima ko leƙowa basuyi ba Yaya Samir ya ja motar muka bar gidan a lokacin
12:30pm.
Rayuwar nake tunani yadda komai yake tafiya yake ci gaba da tafiya ba nida tabbacin zan riski farin ciki a rayuwata haka kawai nake ji duk da ina tuna ubangiji shi ne majiɓancin lamuran ko wanne bawa, amma na rasa dalilin da ya sa rayuwar batamin daɗi wajen wasu wannan ƙaramin matsala ne, Ni Kuma da take damu babbar matsala ne a nawa bangaren, na san idan na yi linƙaya duniyar wasu din suna da labarai mabanbanta da zanma ubangiji godiya duk da ko yaushe cikinta din.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.