Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 19)

Sallamar da Halimah ta yi ya sa ni saurin dawowa daga tunanin da na shiga yi na yi saurin dagowa na kalleta gami da amsa sallamar, Haliman duk ta rame sai na ji tausayinka nake ba wai nawa ba, ɗaurin ƙirji ne jikinta har wani rawar sanyi take yi bata kai ga ƙarasa bushewa ba da ka ga alamunta daga wankan ta fito kuwa

Faɗaɗa fara'arta ta yi tana ƙoƙarin zama gefen gado

"Mutanan Katsina ashe kina Shirin dawowa ko maganar ba mu yi ba jiya”

Na dubeta yadda take maganar da take ƙoƙarin dauko Mai saman drower ɗin da ke gefen gadon

"Halima ba wannan ba, ashe ba kida lafiya haka Sam baki ba ni labari ba, kuma kin san zazzabin naki ki kaje ki tsalo wankanki kina ta rawar jiki”

Murmushi tayi

"Kyale zancen nan dan, Sumayya ina shafa mai na nemi kaya nasa shike nan, Umma tana kada na yi wanka ina zazzabi Ina ganin batanan naje nayo shi saina fara tashi ai Ina tsami, na ji sauƙi kwana 2 ne da fara zazzabin nawa”

Tausayinta na ji ya sake kamani

"Halimah rigima ke nan"

"Ni dai na ji ba ni labari na ga jakarki kuma, baki je gida ba ya aka yi ne?, duk na ji ma jikina ya ƙara sanyi Sumayyah mai ya faru?"

Hawaye na goge kawai, banasan tadawa Halima hankali amma ya zan yi faɗar shi ne zai kwantar mata da hankali, na san ta da abu kaɗan ke sata damuwa

"Halimah, su Mama sun koma Gwarzo, ina dawowa yanzu na samu labari”

Dan Allah Sumayya ba ni labari sosai yadda zan gane na fahimceki sosai, yadda ta buƙata na ci gaba da bata labarin komai da ya faru yadda ta buƙata Halima ba ƙawar da zan ɓoyewa damuwata bace ba na ci gaba da maganar

"Har yanzu Halimah naka sa fahimtar ta ina na cancanta ɗin nan, na yarda da maganar Abbah Hashim ba nida wani cancanta saboda yadda rayuwar take tafiyar mana mu talakawa ne abincin yau da gobe yana gagararmu, Yaya Samir bai dace da ni ba ma, bana tunanin Hamid zai dace dani”

"Sumayyah kin cancanta da komai ke ɗin abar a sadaukar da komai ce a tsira da rayuwa saboda samunki, fatan alkhairi ko wanne second da mintina nake ma ƙawar ƙwarai, ki goge hawayenki Sumayyah, akwai ranar da kowa da kowa zai fahimceku da rayuwarku, ranar waɗanda suka kasa ka sancewa da ku harku ci alfarmusu sune za su zo suna ci ki yarda ubangiji yana juya lamuransa cikin ƙanƙanin lokaci, ki miƙa lamuranki da naku gaba ɗaya bisa ga ubangiji”

Kuka na fashe da shi jin kalmomin da Halimah ke anfani dasu wajen ban haƙuri gareni da lallashina, bisa ga dole na haƙura ganin zan ƙara ɗagawa Halima hankali ganin bata jin daɗin jikinta

Kaya Halima ta nema ta saka doguwar riga ta yadin material mai kauri kyawunta ya ƙara fitowa, Haliman kyakkyawa ce sosai, dan hasashena har nake jin ma ta zartani fara ce, mara girman jiki, rigar ta yi mata kyau duk da ba tsayawa ta yi kwalliya ba

"Bari na zubo miki abinci na san kinsha yunwa, dan Allah ki bar damuwar haka ina jinta ni ma saina ji kamar ni ce” da wannan zancen ta miƙe ni Kuma na bita da kallo ba jimawa ta dawa ɗakin, da plat cike da abinci ta ajiye gabana jallop ɗin shinkaface tana ƙanshin kifi

"Ba zafi dai kin ji yi haƙuri haka, na san za ki iya ci ko, bari na bawa Faisal ya siyo miki ruwa”, Faisal ta ƙwalawa Kira sai gashi ya shigo ɗakin

"Gani Yaya Halimah"

"Yanzu Sumayya ma ta zo mutuniyar taka ko ruwa ba ka siyo mata kai Faisal anya kuwa, ko ba danni ba Ahmad fa abokin kane”

Kai ya sosa "Yaya ai babu kuɗin ne, kin ga ma na manta Haris ya faɗa min su Ahmad sun koma garinsu, da baki da lafiya ba muyi zancen ba”

"Haka nake samu labari, ka ansa wajen Yaya Baffa kace inji ni, za a siyawa Sumayya ruwa, na san su Yaya Hakim sun fita ko?"

Ya ɗaga kai” Eh sun fita sai dai inji ki ɗin kuwa Baffa ba mutunci abin shi bai ciyuwa, kema ban san yaushe kuka jone ba, ko dan kin yi zazzabi ne”

Dariya Haliman tayi” Wato Baffa ai shike nan wuce ni ka siyomin abin da na aikeka”

"Dan fa Yaya Sumayya zani duka 2years Kika ba ni kike wani ba ni command haka”

Sai lokacin Faisal ya wuce, Halima ta juyo

"Kin gani ko Faisal ya rainani wai shekara biyu na bashi, gaba ma zai ce ya girmeni ne yaga ya yi tsawan ƙafa”

Dariya na yi "irinsu ke nan su Ahmad ai yanzu wasu tunaninsu ma shi ne yayana sai an zo anji yana Yaya, ake tantancewa, yana faɗin ma ya kusa daina cemin Yaya mama ta ce shi ma an kusa daina ce masa Yaya”

"Ai kuwa shike nan"

Ina cin abinci muna taɓa firarmu ta school dai dama tafi yawa kafin na tsokanowa Halima zancen Aliyunta

"Yawwa Halimah ya Aliyun naki”

Tsaki ta jamin"kyale wannan a gefe ina da abinyi”

Dariya ta bani” tofa ko dai hyperlove ya kamaki ba ni da labari”

Kai ta girgiza” Ko ɗaya dama dai bana jin daɗi mu kyale batun shi, damuwar ki tafi maganarshi, muhimmanci, yanzu na san rayuwar da za ku fuskanta idan Kuma koma, kina ba ni labarin Hajiya maman Abbah"

Nima ɗin sai lokacin na sake tuno wancen rayuwar tamu ta baya gabana faɗuwa ma yayi

Halimah ta dube ni "kinyi shiru kawai da kuɗin da Yaya Samir ya baki ki bawa Abbah ku kama haya ko da irin kalar wannan gidanne da kuka kama anan, ni wayarma ki sai data indai za ta yi kuɗi to me za ki yi da ita din, da a ce kin dawo da wuri kafin ranar da mai zaisa ku tashi kuma, na san dai a gida za a sha labarin Samir ya baki wasu kuɗaɗe dai, da ku ɓatar a banza gwara ku yi abin da ya dace dasu"

Ni mamakin tunanin Halima na yi, da ni ban yi shi ba

"Haka ne Halima, sai yanzu na yi wannan tunanin, wayar ma saidata za a yi, tun da da kwalinta Abbah ya ja jari da kuɗin su kam dama 'yan uwan Abbah ai sun iya ƙananun maganganu"

"Yawwa Sumayya, ai Aunty Asma'u ma na ji ance taje gwarzo ɗin ai”

Shiru na yi kawai da zancen nata, dan da Aunty Asma'u a cikin 'yan uwan Abbah gwara babu har gwara ma Abbah Hashim ɗin saboda shi namijine, amma ita ɗin mace ce bata fahimci ciwon mu ba, Faisal ya kawomin ruwa harda lemo na Pepsi na yi godiya, Faisal yana jaddada a rage masa Dan saida yasha wahala har bakin titi wajen siyowa, ko da iyayen Halima suka dawo suka sameni ba abunda suka nuna min, da dare Halimah ta tsokano min firar Hamid, sai lokacin nake hango ya zaiji idan ya samu bana nan ɗin ya za su ƙare da shirmen Abbah Hashim, ni sai lokacin na ga alamun hauka a tare da shi ban da haka ina Sumayya ta koma Fatima kuma, hassadar tashi tama koma hauka, saina ke jin tausayin Abbah da alamun ƙiyayyarshi a tun farko da 'yan uwanshi shi ya sa ba su ƙaunar ci gabanshi, amma Abbah na san 'yan uwanshi shi ko, kullum da ko yaushe suna ranshi da tunaninshi, na rasa yadda zan ɓullowa lamarin duba da ni ɗin ba wai babba bace tunanin nawa ya kasa tsawan da Zan gama fahimtar Mai ya dace da rayuwata amma na san addu'a ita ce mafita. . . . . . . . . .

 **** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments