Yau da ta ka sancewa asabar tun da kannena suka tafi tahfiz na yi shirina na zuwa gidansu Halima da ni yau na Sallama tahfiz din ka sancewar shirin da mukayi da Batul za mu gidansu Halima da Batul din nake jira da za mu dubo jikinta da tun laraba rabon Haliman da makaranta da tunaninmu bai ba mu Halimar batada lafiya ba, saida class master namu ya fada a aji a jiya data ka sancewa juma'a da cewa litinin za a dubata gaba ɗaya ajin namu dalilin da ya sa mukayi shirin zuwa yau ke nan
Sallamar Batul da na ji na kuma
ji muryarta tana gaida Mama da take aiki a tsakar gidan ya sa na karasa daura
dankwalin da tun dazu nake fama da shi na kasa daurashi
Ina ji Mama tana cewa Batul
"Sumayyah tana dakinsu"
Dakinmu ta shigo tare da sallama
Na amsa sallamar gami da
harararta
"Sai yanzu kikayi niyyar
zuwa wajen sha biyu saura da na san ba za ki zo da wuri ba da na tafi makaranta
kawai”
Batul da ta zauna kusa dani tace
"Kai Sumayyah kina da
matsala ba gani na zo ba, kin san unguwarmu wuyar adaidata sahu ake”
Na kalleta
"Kai Batul daɗina dake akwai share guri, yanzu
Magashin ce ba’a samun napep kamar kauye”
Tayi dariya
"Ai ta shigo kauyen gandun
Albasa ne basa son yi”
Na mike ina yafa mayafina dan na
daka ta Batul ba za mu tafi yanzu ba
"Kin ga muje da wannan firar
taki mara ƙarewa”
Mama mu Kama sallama ta ba ni kudin
Napep naira dari har za mu fito Mama ta kirani ta fadamin na biya gidan Aunty
Asma'u na gaidata, ba dan na soba na amsa mata da cewa zamu
A dari da hamsin daga gidanmu aka
kaimu zoo road har kofar gidansu Halima
A ɗakinsu
muka tarar da Haliman itada Mamarsu bayan mun gaisa da Mama Haliman da mukewa
sannu ta juyar dakai mamarsu Haliman ta yi dariya ganin taƙi
kulamu Haliman
"Ai dama ta ce ba za ta kula
kuba ko da kunzo, kwana da kwanaki bata da lafiya ba ku zo dubata ba”
Nice na kalli Haliman da duk ta
rame
"Mama ba mu sani ba, sai a
jiya, ki bata baki”
Mama ta miƙe ta ba mu guri tana cewa
"Kunsan dai halin Halima sai
dai ku lallasheta tun da kune kuka mata laifi” da haka ta fita tabar mana dakin
Dakyar muka lallashi Haliman ta
hakura mun dade muna fira da ita har wajen uku saura a lokacin na tuna da zani
gidan Aunty Asma'u, Batul na kalla
"Kin ga sai yanzu na tuna
zani gaida Aunty Asma'u"
"Lah ni ma na manta”
Har na miƙe na kalli Batul data
sake gyara zamanta
"Ba za ki rakani ba ne”
Ta girgiza kai
"Sai kin dawo, dan gaskiya
ko da take kanwar Abbanku ba zani inda za a wulakantani ba, da dai 'yar uwata
ce da sai na ce ta zamarmin dole, watarana ta yiyu na sake zuwa gidanta”
Sosai na ji haushin maganganun
Batul amma na sani ita ba ruwanta abunda ke ranta ko baida daɗi saita faɗama, wannan ɗabi'a ta Batul ya sa ba ma shiri
sosai, Halima ce tawa dako mai abunda za a mata idan mun je dangina bata
nunamin taji haushi, bare harta faɗawa
wani, duk da ita ma Batul ni da ita take faɗamin
ba wani take fadawa ba, amma hakan ba daɗi
Zaman mayafina na sake gyarawa da
banji haushin abin da ta fadamin ba
"Nace karki je, dama Halima
ta fiki mutunci”
Hararata tayi
"Eh na ji”
Halima ta dubi Batul
"Yanzu Batul da gaske kike
ba za ki ba, ni da zan iya tafiya mai nisa da na rakata”
Batul ta harari Halima
"Halima nafa rantse ko
Mamarmu ɗaya da Aunty
Asma'u ba zan sake zuwa gidantaba haba kin manta wulakancin data yi mana, muna
zaune a gidan ko ruwa bata ba mu ba, ƙannen abokan mijinta na zuwa, ta aje musu
soyayyun kaji da ruwa da yoghurt saboda su suna da wadata, haba nifa kin ganni
ko da ubana baida komai ba wadda ta isa ta riƙa wulakantani, da na fahimceki zan ja
miki layi ko ya muke”
Haliman data ja zancen tace
"Ya isa haka Batul mene ne
na tada abunda ya riga ya wuce, tun da kika ce ba za ki ba ai shike nan, ɗan uwa fa ɗan uwa ne”
Murmushi ta yi
"Halima ke nan wani ba”
"Kowanne ma”
Jin zancen ba zai ƙareba na
sani barin ɗakin dan
kaina ma zai iya ciwo ba kasafai nakeson hayaniya ba, kuma ni ma na tuna
wulakancin data mana da sai da waɗacen
baƙin
nata suka tafi taja mana farantin ƙasusuwan naman da suka rage, wai a
matsayina na 'yar wanta uwa ɗaya
uba ɗaya talauci ke
nan 'ya'yanta kuwa babu wanda ta bari ya zo gurinmu suna can saman bene ba ma su
sauko ba dan dama can kayan wasansu yake da komai da tun da nake so ɗaya na taɓa hawa up din
Da wannan tunanin na karasa
fitowa daga cikin gidansu Halima da ina fitowa na ci karo da Yaya Hakeem yayan
Halima yana ƙoƙarin
shiga gidan ni kuma na fito gaisawa mu kayi ya dube ni ka sancewar jinina da
shi ya haɗu fiye da
sauran yayyen Haliman biyu da Yaya Hakeem ɗin
shi ne babban a gidannasu
"Badai sai yau Kika zo duba ƙawar
taki ba”
Na ɗan
rufe fuska alamun kunyar abunda na yi
"Eh Yaya Hakeem ban san da
rashin lafiyar Haliman ba sai jiya”
Yace
"Ban saniba jiya har
unguwarku naje gurin wani abokina, kin ga da na san baki sani ba da na biya na
faɗamiki, ko da ke ma
idan naje bakiso na zo gidanku"
Na ɗago
kai na kallesa
"Eh mana, kwanaki da naje
unguwar na ga Ahmad a waje nasa ya kiraki mu gaisa, ƙin fitowa kikayi” ya ƙarasa
maganar shi ma yana kallona
Nace
"Lokacin aiki nakewa Mama, kuma
bata nan lokacin"
Ya harareni
"Daɗina dake daɗin
baki, har kin fito za ki tafi?"
Na girgiza kai
"A'a zanje gidan Aunty
Asma'u ne, tare da Batul mu kazo"
Yace
"To shike nan saura ku wuce
ba ku min sallama ba”
Murmushi na yi
"A'a za mu yi ma insha
Allah"
Daganan ya shige ciki ni ma na
wuce ina tunanin halayyar su Halima duk gidansu suna da kirki ba su da matsala
takowanne fanni, duk abin da wani daga cikinsu ya nuna yanaso suma suna sonshi,
Yaya Hakeem kuwa kamar Yaya haka yake a gurina, yadda muke shiri da shi ko da Halima
basayi haka, duk abin da ya yi wa Halima to ni ma saiya yi min Batul ma yana yi
mata sai dai ba kamar ni ba ina tafe ina wannan tunanin har na karasa gidan
Aunty Asma'u
Sai da na buga gidan mai gadi ya
leƙo
duk da ba wani sani yayi min sai dai yadda nake zuwa gidan jefi jefi ya sa ya
ganeni da kuma kamar da muke da Aunty Asma'u dani dangin mahaifina na ɗebo sosai ba abunda ya
banbantani da Aunty Asma'u saidai ita hutun data samu yanzu ya sa kyawunta ya
fito sosai, kofar ya buɗemin
da murmushinsa ciki na shiga ina gaida mai gadin
Ya amsamin
"Lafiya lau, 'yar hajiya
ashe kina nan, yaushe rabonki da zuwa”
Nace
"Baba makaranta”
Ya ɗaga
kai
"Haka ne Allah ya taimaka”
Na amsa da Amin na wuce
Saboda kamar da muke da Aunty
Asma'u Baban ya tanbayeni alaƙarmu da Aunty Asma'u ya muke na
shaidamata tun daga ranar yake faɗamin
'yar hajiya, harabar gidan da motoci a kalla uku suke kuma duk masu tsada na
wuce kofar falon na karasa na yi knocking ka sancewar gidan upstairs ne na yi
sa'ar ina knocking na ji kofar buɗe
na tura kaina falon da ƙamshi Mai daɗi
ya bugi hancina Aunty Asma'u tanada tsafta sai dai matsalarta ɗaya rashin san talaka duk abin
da talaka zai yi mata baya burgeta ko da ɗan
uwantane tun ina yarinya idan mun je Gwarzo nake ganin hakan waima ni dalilin
da ya sa bata min wulakanci kamar ƙannena saboda kamar da nake da ita amma
dai duk da hakan bawai tsira na yi ba a gurinta, da 'yar aikinta da bata wuce
tsarata ba na ci karo, tana goge center table da ya ka sance na glass, sallamar
da na yi ta amsa, tana yi min
" sannu da zuwa” muka gaisa
ta shige ciki da towel din goge gogen a hannunta tana cewa bari ta kira Aunty
Asma'un "to" kawai na ce na bita da kallo, ina ayyana wannan Harira
da yake sunan 'yar aikin wanne irin zama take gidan Aunty Asma'u dan Harirar ba
wata wayewa tare da ita gaskiya tana hakuri dai da Aunty Asma'u a raina na
ayyana hakan faɗan
Aunty Asma'u da na jiyo ya katse min tunani
"Sai akace ki ce mata bari
ki kirani, Wai maike damunki Harira”
Naji muryar Harirar
"Ya hakuri Aunty gani na yi
'yar uwarkice”
Cikin faɗa Aunty Asma'u na ji ta ci gaba
"Da take 'yar uwata mai zan
yimata ni ma ba wani abu gareni ba, idan ma wani abu ubanta ya turo ta karɓa masa danni ba ni na ce yaƙi
neman nakansa ba, koya zauna da mace mai ƙashin tsiya, tun da Allah ya rufamin
asiri dangi duk an zuramin ido"
Banga laifin Aunty Asma'u ba
saboda NA CANCANTA ta faɗamin
hakan laifinane a karo na barkatai na sake tun karar rayuwar da gininta bai
dace dani ba, karar takalmanta da na ji ya sa ni maida dubana ga matakalar
benen da Aunty Asma'u take sakkowa da takunta na kasaita daka ganta za ka tabbatar
kuɗi sun zauna mata
duba da kalar kayan jikinta da yanayin jikinta fatarta sai sheki take alamun
hutu ya ratsata da murmushin da nake da tabbacin ƙirƙirarsa ta yi ta karaso cikin falon tana ƙoƙarin
zama kujera tace
"A'a Sumayyah kece a gidan
nawa yau"
Na ɗan
murmusa ni ma
"Eh Aunty ina yini”
"Lafiya kalau, ya mutanan
gidan ya hanya” ta faɗi
haka tana danna remote ɗin
da ta ɗauka a kujerar
da take zaune
Nace” Alhamdulillah, Aunty dama
gidansu Halima na zo bata jindaɗi
shi ne na biyo mu gaisa "
"Allah ya bata lafiya” ta faɗa
Na amsa da
"Amin", daganan na miƙe ina
gyara zaman mayafina tamkar babu komai na ji tace
"A'a ba dai har tafiya za ki
yi ba ko ruwa ba’a kawo miki ba”
Nayi murmushi mai ciwo
"Alhamdulillah, da batul
muke tana jira na ne”
Ta miƙe ita ma
"Eh duk da hakan dan Allah
koma ki zauna na kawo miki kudin ko napep saiki hau da su"
Nace
'A'a Aunty ki barsu da kuɗi a hannunta”
"Eh duk da hakan nawa dabanne”
ba tare da na sake cewa komaiba ta sake hayewa sama ban jira dawowartaba na yi
saurin ficewa daga gidan a raina ina ayyana nida gidan Aunty Asma'u ko ba har
abada ba zan daɗe ban
jeba dan wanna abun da take min tunaninta na ji abin da ta ce ne shi ya sa yau
bata yi min rashin mutuncin data sha yi min ba, a haka na iso bakin gate ɗin ganin banga mai gadinba
ya sa na buɗe kofar na
fice dan raina ɓace
yake ba zan iya jira ya dawo banbarmata gida ba, a haka na fito a raina ina mai
takaicin rayuwa irin wannan saboda damar da Allah ya ba ka hatta danginka saika
zaɓi da waɗanda zaka yi huldar zumun
ci dasu nida kaina na sani muba masu dukiya ba ne da abinci yau da gobe yake
gagararmu bare har a zo inda muke dan kyautar dubu ashirin ba za mu iya
bayarwaba da itako Aunty Asma'u ɗari
ma ta bayar ba abun a tambaya ba ne dalili mai ƙarfi ya sa ta ɗauki duk mai zuwa gurinta kwaɗayayye muddin ba mai kuɗi ba ne, niko a nawa
ra'ayin duk da idan aka ba mu muna buƙata amma ba zanje inda za aci fuskata ko
aƙi
darajani ba duk da NA CANCATA a yi min hakan a tunanin mafi rinjaye a cikin
al'umma amma ni anawa tunanin da yardata Allah ke rabawa ni ma zai iya rabawa
ya bani, duk da ba kudi gareni ba a hannuna amma na gwammace na tafi a kasa
saboda maganganun marasa daɗin
da kunnuwana suka jiyemin, koma ba haka ba nasaba zuwa biyar bata hadani da ita
kawai inaso Aunty Asma'u ta fahimta a cikin talakawanma akwai wanda yasan
darajar kansa, ban san irin yadda zan misalta canjin rayuwarnan ba da ƙarƙarin
ko da kyautar muce ga 'yan uwan Abba dubu biyar shi ma sai Mama ta haihu dan
mai kuɗi inda yake kai
kyautarsa inda yasan za su dawo, bawai gurinmu talakawa ba, amma na sani Allah
yana tare damu hawayen da suka zubomin nagoge ganin na karaso gidansu Halima, ko
minti goma ba mu ƙaraba bayan komawata gidan muka fito a ƙasa muka fara tafiya dan
ba kuɗi hannunmu
ragowar hamsin ta rage mana da sai mun je unguwarmu Batul za ta hau napep ta
karasa gida da sai bayan fara tafiyarmu na tuna da Yaya Hakeem ya ce na masa
magana idan za mu tafi.
**** ****
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.