Misalin ƙarfe goma na safe na kammala shiryawa, Halimah ma ta shirya dan Yaya Baffa zai kaini Tasha tako ce lallai sai ta bishi an rakani da ita Faisal ya dauki jakata ya kaita napep dake kofar gida, Abban Halimah da mamarsu kuɗi suka ba ni na yi kuɗin mota da inada niyyar ƙin amsa Halimah kuwa ta karɓe ta ce su bata ta bani, tasan halina na musu godiya duka gaisuwa suka ba ni na yiwa su Mamah da ƙannenah, haka muka fito ina sake jin ƙaunar Halimah da ahalinta a raina muna tafe a mota Halimah tana jana da fira har ni kam hankalina baya wajenta tunanikane kala kala a raina ga uwa uba kewar Halima da nake yi ga Batul ma ba mu haɗu ba babu damar hakan hankalina ya yi gida ne, Halimah ta kalle ni
"Haba mana Sumayya sai zance
nake kinmin shiru"
"Yi hakuri Halimah ban jiki
ba”
Yaya Baffa ya ɗan juyo ya kallemu
"Haba keko Halimah tunanin
gida take yi barta ta yi abunta, na san ji take kamar ta yi tsuntsu ta jita
gida, na dauka zakuce ma za ku biya gidansu Batul ai, na ga munzo unguwar"
Kamar jira muke yi ya yi zancen
Batul cikin haɗin baki
muka amsa
"Zamuje mana Yaya Baffa”
Kwanar layin gidansu Batul ya yi ba
wata tafiya mai nisa sai gamu kofar gidan nasu, Dan ƙaramin gida amma jikin
family house dinsu yake Batul ta ce mana duk cikin family house din nasu aka yi
gidan nasu, Kamar jira muke napep din ta tsaya mukayi saurin ficewa a motar, Yaya
Baffa na koramana kashedin kada mu daɗe,
da Batul muka ci Karo zauren gidan nasu muna tura kofar, wani ihun murna ta
saki
"Sumayyah oyoyo ashe kin
dawo ba labari, ƙila ma kina Kano shekaran jiya da mukayi waya, mu shiga ciki”
Halimah ta kalleta
"Ke malamah sauri fa muke da
Yaya Baffa muke, kin san ashe su Sumayya sun koma Gwarzo fa, ni ma sai jiya da
Sumayya ta zo na ji labari, ita ma batada masaniya a gidanmu ta kwana ma, yanzu
Gwarzo za ta wuce muka biyo, muje mu gaishe da Mama dai mu fito"
Batul ta harari Halimah
"To aku mai bakin surutu
aina dauka ma gaishe da Maman ma ba za a shiga yi ba, Abbah ma yana ciki, amma
banji daɗi ba Kamar na
yi kuka”
Da haka muka ƙarasa
ciki Halima na faɗin
"Nima haka na ji Batul ya zamuyi an saba, kamar na yi kuka nake ji”
"Ke dama uwar kuka ba”
Duka dariya mukayi ban da Halimah
da ta haɗa fuska a
tsakar gida brander muka sami iyayen Batul zaune a ƙaton tabarma da ƙannenta
duka ka sancewar Batul ita ce babba ita ma, kamarni, gaisawa mukayi Batul ta
shiga koramusu jawabi cewar mun tashi mun koma garinmu Abban su Batul cikin
rashin jin daɗi ya
kalli Batul
"Amma ba jimawa dai da hakan,
da ai ba za ayi haka ba, indai matsalar haya ne ga gidan Abbahnku sai su zauna
har Allah ya hore musu, aikinma ban da abun Abdullahi ai nema akeyi ba’a zama
haka, amma banji daɗi
ba”
Maman Batul ta girgiza Kai da
damuwa fuskarta
"Nima haka Abban Batul gashi
duk sun saba, za a rabu Kuma, ƙila shi ma yana da buƙatar
komawa, shi ya sa ba labarin kome”
Cikin jin daɗin yadda iyayen Batul suka
nuna jimamin komawar na rashin Jin daɗin
su na yi magana
"Ai mamah mai gidan da muke
hayarne ba zato ya zo ya ba da notice Abbah na san bai samu lokacin tsayawa wani
tunani ba sai haɗa
kaya kawai suka koma gidan duka”
Abban Batul ya dube ni
"Haka ne amma kwanaki baya
mun haɗu ya fara jan
napep ya cemin Alhaji Yassar ya samu daga wajenshi, Ahmad ma ya samu yake ja”
Halima ce tasa baki lokacin
"Ai Abbah napep din Faisal
ya ce ta lalace ba kuɗin
gyara shi ne ya maida musu kayarsu"
"Aini Abdullahi na rasa
irinshi tun da yara sun haɗa
mu ba'abun yana boyemin abubuwa da yashafemu duka ba ne, ko ya zo wajena ko mun
haɗu ba wata magana da
za a taru a jajanta ko abunda ya shafi buƙatar taimako da zai faɗamin na rasa wannan abun
nashi, tafiyar Sumayya ma sai bakin Batul na ji yanzu ai an zama ɗaya, dama ɗaya ne tun da school ɗaya ma mukayi a lokacin da
yake yin masters"Abbah ya ƙarasa zancen da alamun damuwa
Haka duka jikinmu sanyaye muka miƙe
sosai na san halin Abbah shi kullum maganarshi 'yan uwanshi su kasa taimakonshi
inaga wasu abokai kowa yana ta iyalanshi da familynshi, shi kanshi Abban Batul
din ba wata dama gareshi ba sai da muka shiga JS3 muka fahimci akwai sanayya
tsakanin Abbanmu da nasu Batul ɗin
duk da kawai zaman aji ne ba wata gaisawa ake ba ayi lecture ne a fito saiko
assignment ya haɗa ko
presentation ko wani research ɗin
a irin wannan Abbah yasan Abbah Ahmad ɗin
Batul hanyar falonsu ta yi a
maimakon mu ƙarasa
fita waje Halima ta Kira sunanta” mu kam ba falon da za mu shiga”
Batul taja hannuna
"Kin ga Sumayya zo mu shiga
dan Allah, kyale wannan Haliman ta jira mu a wajen, na san saboda Yaya Baffa
kada ya Mata banbami take wannan"
Ummansu Batul ta kalle ni
"Au wai ba ku kaɗai ba ne?, ya kamata ku
kyale Batul ɗinnan, Kuma
zo ku rakata sai ku dawo da Haliman su ajiyeki”
Halimah ta yi saurin amshe zancen
"Eh Ummah mu da Yaya Baffah
ne kuma ya ce sauri yake yi saboda muma ya yi lattin fita”
Ummah da take Shirin sake magana
Batul ta yi saurin marairaice murya
"Ummah dan Allah wata kawai
'yar magana fa zamuyi minti uku ma ya yi yawa”
Ummah ta maka mata harara
"Tatsuniyar gizo dai na san
bata wuce koƙi
zancen dai Yasir ne”
Abbah dariya ya yi wa Ummah
"ai Batul da Yasir ban san
wa ya fi san wani ba, har ni ma na ƙosa na musu auren nan, zance kullum
saboda yana ganin shi ɗin
dan gidane”
Da wannan muka shige falon muna
zama a kujerun Batul dariyar data kunso ta fara yi, Halima ta dube ta
"Kin ga ba musan hauka fa
malama meye wai dama aje mu kikayi ki dinga dariya”
Batul ta haɗa rai kamar ba ita ta ke
dariya ba
"Kin ga Halimah bafa ni
nakai zomon ba, Ni na ce ki ɓata
da naki saurayin mai kan kwakwa”
Halimah da masifa ta dubeta
"Kin ga Batul ki fita idona
da cin mutuncin Aliyu fa, Kuma gwara shi ke naki saurayin kan giginya gareshi”
Ni abun nasu dariya ya ba ni na
kallesu"kunga ya isa haka dan Allah, Halimah barta ta yi maganarta kin san
Yaya Baffa na jiranmu dai ku nake jiyewa karya juyeku a Rijiyar za ki ya kwashi
passenger ko ya dinga yawo da ku da passenger kuma a motar, ko biyu yake samu
ya rage zafin ɓata
masa lokacin da kukayi”
Batul ta makamin harara
"Aniyar ki ta biki mai baƙin fata, insha Allah ke Za ki hau
rigwagwaar mota ban da munafinci ina Kano ina Gwarzo amma tun goma Za ki ce za
ki wuce saboda kin gaji da ganinmu, babu amana, ban san ya za ki koma kikayi
aure ba Hamid ya kwasheki Katsina ya kaiki ya ajiye”
Halimah ta kalle ni kafin ta
kalli Batul
"Kin ga wanne Hamid ai anbar
yayinshi ga Samir nan yayanta kin ga ko banza Abbah Hashim ya mareta ta wata
rana idan bata Kai ga dukan ba”
Batul ta kalle ni” Subhallah meya
faru kumin bayani haba ni dai na san ba lafiya ba, tun da na ga Sumayyah haka
ayam"
"Uhm ina ko lafiya matsiyacin
mutumi nan ya kama Sumayya ya mata shegen duka, yanzu ma saida ta gasa jiki da
ruwan zafi” Halima ta yi zancen ta ƙarasa bawa Batul labarin komai
Batul ta kalle ni cikin tausayawa”,
Kuma yanzu kin amince da Samir din, gaskiya ki yiwa Hamid adalci da babu Hamid
ko dan Abbah Hashim da saiki amince da Yaya Samir ɗin amma kin bawa Hamid dama tun farko"
Na kalli Batul"nifa Batul
wallahi komai ya fita raina fa, na rasa tunanin da ya dace dani Dan Allah ma
kada ku bawa Hamid labari game dani, ni dagashi har Yaya Samir na haƙura da
su, idan na ƙi
karɓar Yaya Samir
saina kega na yi butulci duk da shi ɗan
uwana ne, tun ina yarinya nake jin labarin irin son da Yaya Samir ya nuna min, wajen
Mama kafin su koma Katsina mu dawo Kano da na mantashi da kanshi ya daukeni
kawai dan na tunashi wannan abun da ya faru ƙaddara ce kawai, da na san da cewa Yaya
Samir na Sona ba zan iya amsawa Hamid ba saboda ban san shi ma daga gareshi mai
zan tarar ba”
Batul ta dafani” Dan Allah ki
daina wani tunani ki yi addu'a insha Allah za ki samu mafita, addu'a ita ce
mafita kawai Allah ya zaɓa
mafi alkhairi, kuma ni kaina ban san me zan cewa Hamid ba idan ya tanbayeni
game dake kin riga kin gama masa magana kince ya yi hakuri, tun da Kuma ga ƙudirin
Abbah Hashim a kan hakan kin san halin wasu mazan idan yaga Fatimah ta fiki a
wajenshi zai fi amincewa da ita ƙila a hasashena fa tun da zumun cin naku
ya zama ga irinshi, ni kin ga Yasir babanshi yana da kuɗi sosai amma ba wani wanda yakai korafin
Abbanmu a kan shi talakane kada Yasir ya aureni, kin san ko da muke 'yan uwane
da danginkune sai sun yi, yanzu haka kin ga Yasir har ya kawo kuɗin aurena ma, shi ne zancen
fa da zan muku"
Fatan Alkhairi da addu'a muka
mata, kuma na ji daɗin
kalaman Batul sosai, sai na ji zuciyata ta nutsu
Halima ta kallemu"kunga ku
taso dan Allah kun cikamu da zancen soyayyah ni wayata ma kashe take kada ma ki
yi tunanin Hamid zai kirani blocking nashi ma zan yi dan ban san me zance masa
ba, nifa tun da Aliyu ya ba ni haushi kowanne namiji ciki nake dashi”
Tsaki naja mata” kin ga kin
damemu Aliyu Aliyu dai kawai idan da gaske yake ya turo muyi dai mu gama faɗa kuma ta yiyu ke kika ja tun
da ke ɗin zuma ce sai
da wuta wani lokacin, sanda Kuma za ku shirya ba mu sani ba”
"Allah kina wasa ko Aliyu ya
ba ni haushi ba kaɗan
ba ku tanbayi Faisal ku ji ma shi na ce ya fita ya ce kada Aliyu ya sake zuwa ƙofar
gidanmu"Halimah ta yi maganar tana miƙewa
Batul ta galla mata harara” kin
ga mu fa ba muda lokacin shiriritarnan taku, tun yaushe kike cewa Kun ɓata Kuma a zo a shirya mu
tuno miki zancen ki ce baruwanmu, yanzu na gane ma ciwan so kikayi kwana
biyu"
Halimah ta hararemu duka duk da
ni ɗin bance wani abun
ba” wallahi ku duka ku fita idona, Kuma ni zazzabi na tun kafin muyi faɗa nake yi kada ma ku min
wata fassara”
Da wannan muka fito waje Abbah kuɗin mota shi ma ya bawa
Batul ta ba ni godiya muka musu suna mu gaida su Abbah Abban Batul ya ce zaima
kira Abbahnmu insha Allah, abin da muke gudu muka tarar munsha faɗa wajen Yaya Baffa ya faɗa wa su Halimah saidai ya
ba su kuɗi su hawo
wata napep su juyo gida shi ya makara ma yanzu, Ni dama na san za a rina indai
Yaya Baffa ne, har cikin Tasha muka ƙarasa sai da na shiga mota na zauna Yaya
Baffa ya biya kuɗin
motar kafin suka wuce ba dan naso ba sai dai ya zama dole na rabu da ƙawayena
masu ƙaunata
a dalilinsu na yarda akwai ƙawayen da sun zarce ƙawaye saidai akirasu 'yan uwa sun dauki
matsalata kamar tasu, abin da muka rasa daga 'yan uwan mahaifinmu, da su ya fi cancanta
su kula damu da tarbiyyarmu, a hakan wata 'yar kulawar saboda Abba ce akeyi
mana ita kaina na ƙasa Ina zub da kwalla har motar mu ta ɗaga jin mun Fara tafiya na yi addu'a na ci
gaba da tunanin da nake yi
**** ****
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.