Na Cancanta (Kashi na 22)
A washe garin ranar da na dawo Aunty Asma'u ta dawo daga Katsina da zallar abunda yafaru dani acan ta dawo ƙarya da gaskiya, haka suka tattara maza da mata a gidan suna maida yadda aka yi Abbah ne da yaji Hajiya ta fara zaginshi a kan zancen har tana cewa bai ba mu tarbiyya ba mu tattara mu bar mata gida ba za ta iya ba kar a ɗebo mata abun faɗa a gari ashe shi ne sakamakon komawa kanon da Abbah ya yi saboda mu zamar masa jari yanaso yaji daɗin mu zama 'yan iska har yaran 'ya'yan masu kuɗi suna sona inba da lalata ba dame za su so ni ina 'yar matsiyata tana sake jaddada za su ga ƙaryar Hamid Fatima za su haɗashi da ita suga ko gaskiya yake yi zancen ni dama munsa ba lalata a Kano bincikeshi za suyi inko suka samu bahaka ba ne Kuma yaƙin amincewa da Fatima to ita ma ba da yawunta ba a kan Abbah ya aura ma Hamid ni saboda ban cancanci aure a zuriyya irintasu Hamid ba, su Aunty Asma'u da Abbah Jafar ƙanin Abbah ba ne shi ma sai Abbah Imran suke sake zuga Hajiya suka rufarwa Abbah da cin mutuncin su Aunty Luba kuwa su tunzurawa sukeyi da sake cin mutuncin Mamanmu suna faɗin sun yafeshi ga Hauwa'u, ina tsakar gidan ina share bangaren Hajiya nake jiyo zancen nasu har na gama ba su gama ba, shiko Abbah sun hanashi tasowa dama na yi tunanin haka za ta faru ko fiye da hakan maganar wayar da banji anyi ba tunanina ya ba ni ko ba su san zancen ba inako Shirin barin wajen na ji Aunty Asma'u na cewa” Ai iskancin Sumayya harda tsohon saurayina ƙanin wannan matsiyaciyar matar ta Yaya Hashim, matsiyata ne fa ba suda komai indai ba lalata sukeyi da Sumayya ba, ina xai kwashi maƙuda kuɗi ya siya mata waya iPhone kunsan tulin kuɗin da ake siyan wayar kuwa”
Hajiya na ji tana ƙoƙarin
rushewa da kuka” Abdullahi yanzu mazinaciya kake ƙoƙarin maida 'yar ka ta tabbatar shi ne
dalilin turata Katsinan ke nan, Hashim kuma yayi min waya namanta ma ya ce ko
ku fito masa da ɗansa
ko ya maka ku ƙotu"
Abba murya rau rau na ji yana cewa”
Hajiya Dan Allah ku daina jifan 'yata da kalma Mai muni kalmar zina, duk
talaucinmu da halin da muke ciki da rashin taimakonku insha Allah ba zan haifi
mazinaciya ba, koni nasa ta ta yi zina dakaina ni uba, danasan abin da Hashim
zai sakamin da shi ke nan da ban amince Samir ya daukarmin 'yata ba, sun
tozartata a ƙarshe
ya Mata dukan da koni uba ban taɓa
yimata ba, Kuma yana jifana na boye masa ɗa,
ina kiranshi ya zo ya yi min duk abunda yaga zai iya yi, kuma Ni ban taɓa ma 'yata sha'awar aure
nan kusa ba bare ma mai kuɗi”
Abba Imran na ji muryarshi yana
kuma tafa hannu"dama Abdullahi ina zaka yi sha'awar aurar da Sumayya kana ƙoƙarin
maidata karuwa tana kawoma kuɗi,
wallahi Hajiya fitinar da ke damun al'umma ke nan yara 'yan 17, 18 zuwa sama
sun zama karuwai ƙarfi da yaji saboda sun haɗu
da uba mai matattar zuciya, kuma mata da maza yaran manyan ke wannan shaiɗancin dasu wayasan mai
Mahmud ɗin ya yi da
ita ya bata wannan wayar"
Hajiya tasake rushewa da kuka” Abdullahi
ka cuceni kuwa ashe da mazinaciya nake zaune a cikin gida, shegiya munafukar
yarinya kalar uwarta, tun da na haifeka abun goma ba zan ce wannan ɗana Abdullahi ya ba ni ba, wallahi
ba zan iya zama da ku ba inko na zauna daku tsinke na daina daukewa saidai
mazinaciyar 'yar ka ta yi shi”
Abbah a fusace na ji ya fara
magana” Hajiya ki dakata iya nan da izinin ubangiji ban haifi mazinaciya ba kaf
'ya'yan da na Haifa da zuriyyar su Kuma ba Wanda cikinku nake bi da baƙin
baki, Kuma rashin taimakon da kuka kasa yi min, aiki kuka kasa samarmin bai
hana Ina kyakkyawar rayuwa ba Mai tsafta zama cikin ku Kuma na barshi ke nan, ke
uwata ce amma kan talauci na gaji da munanan kalman da kike jifana da shi da
matata harda 'ya'ya ma yanzu, kuma ni Hauwa'u ko wacce 'ya za ta haifarmin
wallahi ta fiyemin harke a gurina na gaji da cin mutuncin da kukeyi min, ba ni na
halicci kaina ba, kuma 'ya'ya na wallahi sun fiyemin kaf 'ya'yan ku daga yau
Zan iya cewa babuni babu ku gida kuma ku Bari mai gidan ya zo ya koreni da
kanshi ba zan rasa inda zan tsugunna ba da talaucin nawa, za a karɓe ni”
Kofar ɗakin na je na tsaya ina zubar da hawaye ina jin
yadda Abbah ke faɗa a
fusace ban taɓa jin
haka daga Abbah ba yana juriyar abunda ke faruwa kai kace bai San wani abu ba'cin
rai bare yadda akeyi ba
Maganar Abbah Imran a tsawace, tasa
ni ni ma tsorata "Abdullahi kayi haukane Hajiya da ta haifeka kake faɗa wa magana haka saboda ba
kada tarbiyya ba ka san mutuncin iyaye ba ba ka san zafin haihuwar da ta sha ba”
Tsaki Abbah yaja” ita wace ce
Imran ka fita harkata haihuwata ta yi bata halicceni ba, tarbiyyar da ta ba ni nake
gwadawa yau aina yi haƙuri ma kuda kullum kuke cikin gwada musu ita fa amma kune
mutane ni talauci ya maidani bare, yaranku sai su bangajeni ma a haya saboda
ina yawo a tsiyace, abun ya wuce nida matata ina koƙarin bawa 'ya'yan da na haifa
tarbiyya kuna ƙoƙarin iskantamin Sumayya indai ta lalace to duka 'ya'yan da na
haifa haka suke da yardar ubangiji ba za mu ga haka Kuma ga 'ya'yan ku ban muku
fatan suga haka, dan zina babban illah ce ga rayuwar namiji ma bare mace”
Abbah Imran na ga ya dauke Abbah
da mari "mu kake faɗa
wa haka Abdullahi”
Abbah a zafafe ya ɗago ya wanke Abba Imran da
marin shi ma
"Imran na faɗa ma kuma zan ci gaba da faɗama kowannenku muddin cin
zarafin da kuke mana nida matata bai isheku ba Kun daura min da yarana, kunsan
hukuncin zina a addinance, maiyi hukuncinshi ko Sumayya kuka kama tana yi
muraran saiku fallasata ku ƙaramin wani masifar da ya haɗarmin
na samun iyayena da 'yan uwana amatsayin ba ku ƙaunata saboda abunda ban isa na yiwa
kaina ba”
Dakin na faɗa na rungume Abba ina kuka
ina” Abbah ka kyalesu dan Allah mun fisu laifi da muke ƙoƙarin zama dasu da shiga
cikinsu duk da ba mu cancanta da haka ba” rarumar da aka yomin ta baya ya sa ni
sakin Abbah na yi ta baya baya, Aunty Maimuna na gani ta zabgamin mari” Sakeshi
dan uwar uwarki, matsiyaciya munafuka masu laɓe
kun rabamu da ɗan
uwanmu wallahi ko ba Abdullahi kuka nememu a dangin uba sai kun tabbatar da mun
daɗe da yankeku a
cikin jininmu"
Abbah a zuciye shi ma ya wanke
Aunty Maimuna da mari haka Abbah ya ja hannuna jiri na ƙoƙarin ɗibarshi na kakkamashi dan
ko abincin safe a yau dinma bai ci ba har ukun rana tayi, ina riƙe da
shi muka ƙarasa
ciki Mama muka samu tana kuka Kamar ƙaramar yarinya ko ni na yi dauriyar ƙinyi
sai hawaye bare ita danasan daga ɗaki
take jiyo hayaniyar ka sancewar dakunan da muke jikin na Hajiya ne, gurinmu ta
nufo ta kamashi ta shigar da shi falon sai da muka zauna Mama ta dubeshi
"Haba mana Abdallah zakaje
ka sawa kanka wani ciwan a banza ba ka da mai damuwa da hakan, tun da suka fara
ka fito mama amma kamar, an dasaka”
Tari Abbah ya fara, na tashi na
dauko masa ragowar pure water na bashi Mama ta amsa tana cemin"Jeki kawo
masa abincinsa a kitchen, kitchen na nufa na kawo masa haɗe da cokali na saka a ciki”
lokacin da na dawo ya tashi zaune
Mama ya kallah bayan Fara cin
abincin"Hauwa'u na gode miki da halaccin da kike min da kyautatamin na ƙoƙarin
zama dani cikin wannan halin da hantarar 'yan uwana ita ce gaba da komai a
yanzu gareki abun ya wuce wajenki har wajen Sumayya, Hauwa'u familyna basa tare
dani saboda ni ɗin
bawani ba ne, face talaka, abun yana damuna, ban san ya abun zai daura ba idan
bana nan"
Mama hawaye ta share ni ma ta ɓangarena haka ne
"Dan Allah Abban Ahmad ka
daina wannan maganar wallahi ina jima tsoron hawan jini, yanzu ya zama abun da
ya zama abun kasa ba ne, da abunda ke faruwa, kafiso ka ɗaga hankalinka muka ɗaga mana”
"Hauwa'u dole na damu da
yawa wannan fitinar tasu yau taron dangi kina ji sukayi min ya kamata ma, ku
bar musu gidan ki tafi gidan Gwaggo, yanzu ni na riga nawa ne, Zan fiki juriya
kawai na san nuna min kike kina jurewa, "
Mama jin maganar Abbah ta ɗago ta na kallanshi” Amma
Abban. . . . "katseta ya yi da cewa” Dan Allah Hauwa'u karkimin musu ku
tafi ke da Sumayyah tun da yara nacan ma, idan suka gama shuka tsiyartasu zuwa
dare suka tafi sai ku dawo kin san Asma'u sai ta shigo har ciki ta faɗa miki magangana, ga
Mubaraka ma sun haɗu،ni kin san ba bakin komai
nake a wajensu ba ni nasu ma bareke sunajin haushinki”
Ba yadda muka iya Mama tasa
hijabi ni ma na zari mayafina na yafa, ka sancewar mun yi wanka, muna fitowa ɓangarenmu ni da mama muka ƙara
sauri muka buɗe get
gararau muka fice muna jin Aunty Mubaraka na cewa
"Wanne ɗan iskane ya buɗe mana kofa ya fita da
gudu"
Aunty maimuna muka jiyo Muna ƙoƙarin
tura gate ɗin tana
"Futa ki gano mana ko barawo
ne, ko yaron Yaya Abdullahi ne aka fara sace sace ya na bin yaron nan Shu'aibu
na gidan Malam Habu"
Ni abunma dariya ya ba ni su dai
lamuransu sai addu'a mama ta kalle ni” ya da dariya Sumayya” Na ce "mama
bakiji mai Aunty Maimuna ke faɗa
ba” ta ce” naji mana kin san shashasha ce Maimuna, ni dan kar siyo kaina na ƙara
saurin nan gwara su ci kansu indai sune kafin kowacce ta tafi sai kin ji kansu
batse batse kuwa”
Muna tafe muna fira har muka ƙarasa
gidan su Mamah, gidan na ƙasa ne da simintin shi amma da sauri na na riga Umma shigewa
da Omm Habibah ƙanwar mamah da Zainab da ita ce ƙaramar ƙanwarsu Mamah na ci Karo a tsakar gidan
da na kwaɗa sallamata
juyowa sukayi suna kallona da amsawa suka bini da kallo "oh Sumayya anyi
girma” Omm Habibah ta kalli Zainab ta ce” ke kin ga Zainab har ta fiki girma ma”
Zainab takalleta” to dama Sumayya
ai ta girmeni kusan kece tsararta ma ya kike haɗa
ni da ita”
Da wannan Mama ta shigo ita ma
sallamar da ta yi muka amsa Omm Habibah ta kalli Mama "yawwa Yaya Hauwah
Zainab ce sa'ar Sumayya ko ni”
Mama ta yi dariya” ke ce Mana ki
yi zuciya ki yi girma na ga kin maida Zainab ce babba tun da kin maida Sumayya
sa'ar Zainab"
Dariya na yi na ce” wallahi Mama tun
da nashigo Omm da zancen ta tareni ko ni ce sa'ar Zainab"
Mama ta harareni da cewa” Ƙaniyar
ki da Zainab in ba Za ki ce mata Aunty ba ita ma Omm Zainab ce”
Zainab ta ce” barta Yaya ni ma
zan hana Ahmad yana cemata Yaya, ba dai na hannun dama na ba ne”
Dariya mama ta yi ta shige ciki
ta barni da su Omm Habibah, da suke wanke wanke dama kujera na jawo na zauna
kusa dasu hirar littafi suke yi” omm Zainab ta ce "yawwa Ommu an turo
without my dreams ɗinnan
kuwa Dan Allah Kika anso charge ku ba ni na karanta ni ma, na ji labarin Munira
ni kin san ina team din ta”
Dariya na ji omm Habiba tayi” lallai
yarinyar nan, tom ko ki canza sheƙa team din Hidaya yafi, saboda mamarta ta
nada kirki ita ba Kamar kaltume ba”
Ommu Zainab ta kalle ni” kin ji
fa Sumayya ya kamata ki bawa Sumayya ta karanta ita ma, amma Munira ai ta yi ƙoƙari a
dai matsayin roll ɗin
da tafi to, kuma indai kin san Hidaya kin san Sumayya Kamar fa nida Omm Habiba
din ne, kaɗan ya
banbanta, su Kuma sa'anni ne ma Kamar twin suke”
Nace "wai Aunty Zainab ba zan
gane ba gaskiya adai 'yanmin nkaranta, yawwa ni ko ina wannan book din na
Rufaidah da Abdurra'uf akaƙi musu aure sun haɗu
ne a super market ShopRite ne ma, tom ba su sake haɗuwa ba sai bikin wata friend ɗin Rufaida Samiha, namanta
sunan littafin ya min daɗi
Allah ya sa an ƙarasa wancen zuwannamu na tarar ana posting nashi”
Tsaki Aunty Zainab ta yi tace” kin
ji fa Ommu kin san littafin da take nufi JININMU ɗAYA,
na wannan sabuwar marubuciyar da kika cemin Sadiya Khalil ne ko Halimatu Khalil
ne oho ita tasan da wanne take using sai ku masu wayar"
Omm Habiba ta ce” nafa gane shi
na ji ana za ta ƙarasa shi yanzu ma duk anma manta shi ƙila sabon updating za ta ƙarayi
ko ta daura tasa mutane na neman document din na baya, kin san rubutu na da cin
rai inji su dai masu ƙoƙarin yi amma ta iya book wasu ke cewa Kamar irin ta gwanance
tun farko da ta fara, tasan me take kamar dai, amma ni yanzu fav ɗina a rubutu marubuciyar
without my dreams wallahi, Kuma littafinta ɗaya
na karanta wannan da take rubutawa without my dreams"
Ni kam na ce "taɓ ai ni kam ko dan Halima
tom Halimatu Khalil ce fav dita a masu tasowa a rubutu, gashi a littafin maman
Rufaidah sunan Mama gareta gashi akwai Abdul Abdul a littafin Abdulahid, Abdulmalik
waye waye kuma gata sunan Abbanku Abbanta gareshi”
Aunty Zainab ta ce "ke
wannan lissafin naki, munji ni bance ina ƙin book nata ba da Habiba, za ki ma, ko
yanzu ta yi saban book ommu taga ana poster wa zan ansa na karanta shi, ba
laifi ta iya, amma baruwana da lissafin nan ni da ake bawa waya dakyar Ni ba ma
na duba sunan marubuciyar ma, nake karantawa, Ni karatun bai dameni ba littafi
ana farawa ba continuation ko na tura wayar Gwaggo document wasu ma su damu
mutane na kuɗi ne, ni
fa ko za su dinga Allah ya isa an karanta saina karantashi kuwa, abin duniyar
mu talakawa Ina muka ga kuɗin
biya duk ribar da za su ci, Kamar abun samun lada mtsew"
Aunty Zainab uwar jaraba shiru
muka mata har tagama zancen, can za ma wani mukayi tun da Zainab ta ɓata firar share wajen na
taya su kafin muka shiga dakin Gwaggo muka gaisa aka fara fira su Rumaisa an
nausa cikin gari gidan yayar Mamah Aunty Maryam ka sancewar mamah ce ta biyu a
gidan nasu. . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .
Na Cancanta (Kashi na 23)
Humairah da take ta barci a bayan
mama tunma kafin a fara rigimar ta fara kuka mama ta sauketa daga bayanta, daga
ita sai pant jikinta nan mama ta fara bata nono, Gwaggo dasu Aunty Zainab suka
kalleta "lafiya haka Aisha ba kaya jikinta”
Gwaggo ta ɗora” ko Bata da lafiya ko wani abun ya haɗa ki da surikan naki gama
dai ansaba, hala ƙannan nasa suka ci miki mutunci ke sakarai Kika kasa ramawa
Kika taho mana nan ki tayar wa da mutane hankali, shi ya sa sam banji daɗin dawowarku nan ba kinacan
asirinku rufe muma namu haka Atika Kuma na ɗan
taimaka muku, da ko da aka koreku kunje gidanta ai zatasan yadda za ta yi a
samo muku wani gidan ko a unguwar ne, sai abu ya faru a kasa tunanin da ya dace
to kundawo nan din, in dukan kawo wuƙa za su miki nidai da sanina ƙannanki
ba za su je ba, inma rigimarce dasun kada Miki da 'yar taji ciwo da paracetamol
ba za su taimaka muku ba, wannan jarabbabbun mutane hukuma ma sunfi ƙarfinta,
haka suke rigimar su dukansu da surikansu da ƙannan miji da yayye su Mubaraka da
Maimuna haka sukeyi danma sun haɗu
da daidai su ne abun ke zuwa da sauƙin wulaƙancin su Kuma duk laifin surikan naku ne
da basasan laifin 'ya'yansu"haka Gwaggo ta ci gaba da sababi,
Ita dai Mama haƙuri ta
bata da cewa” Mama ni ba ma dani suke ba da ɗan
uwansu sukeyi shi ne ganin ko kar haushin ya ƙarasa ƙarewa kaina ya ce na taho nan tun da yara
suna nan", mama da jajayen ido take ci gaba da maganar, "Gwaggo
wallahi na gaji da zama da mutanan nan ko a can ban tsira ba su bar mu ma da
talaucin dake damunmu da ubangiji ya sa ka sancewar mu haka maimakon su
tausayama na, shi ne dalilin da Allah ya Samar da Mai kuɗi da talaka saboda mai shi ya taimaki mara shi
ko da da shawara da kwantar da hankali ne, amma babu dukkansu ba mai taimakon
mu sai jifanmu da mugun alkaba'i ba su ba 'yan uwanshi hatta da iyayenshi, wallahi
saina ji kamar na zube musu 'ya'yan ko kotu naje a raba auren nan, indai ni ce matsalarsu"
ta ƙarasa
maganar tana rushewa da kuka mai ban tausayi dan Mama abar a tausaya mata ce, cikin
yana yin tausayi su Gwaggo suke bata haƙuri harda Aunty Zainab Gwaggo ta ce” inkin
kashe aurenki Hauwa'u kikazo nan wa Kika bawa ajiyar dauke miki duk
dawainiyarki su Sha'aban suma buga bugace kina gani ba wanda ko maganar aure ya
Fara ma da ya dace a ce sun fara shekaru tafiya suke tayi, kuma kinada tabbacin
za su kula 'ya'yan naki sun riga basa ƙaunartaki kuma ba ma kece basa ƙauna
ba Abdullahi ɗinne
basa so har su iyayen nashi, dan da suna sanshi murna za su yi dake da Allah ya
sa ya samu ya yi auren, ya auri matar rufin asiri ai ita mace a wajen miji
kamar katanga ce, kuma daraja da haiba take ƙarawa namiji kamar yadda ita ma yake
zamar mata, in ba kaso matar ɗanka
ba ba ka sanshi ke nan matar rufin asiri, in kin ga ana ƙin surika anawa ganin sai
baƙin
halin nata yakai iyaka, shi ma a ce tana munanawa ɗan naka shi ne kake ƙinta, amma dan surika ta
ta mai sauki ce sai taje inda suke ko ta sauraresu za ayimata, saidai ko
fitsararta ta takai ƙarshe, ni yanzu su Jabir nawa suke amma ji nake kamar ko da
kaina na samu kuɗin da
Zan aurar dasu na huta na ji da su ommu da Zainab, amma su sunfisan ɗaga ma ɗansu hankali bare ke kisa
ran naki zai kwanta shi ne basa so ba ke ba”
Jin maganar Gwaggo ya sa ni fara
magana” wallahi Gwaggo haka ne basa ƙaunar Abbah ne kawai” labarin komai da ya
faru ni da aka yi komai zai iya cewa a gabana na shiga basu, ransu in ya yi dubu
ya ɓaci haka suka ci
gaba da mamakin su Abbah Imran ɗin
amma Gwaggo faɗi take
Abbah duk da haka bai kyauta ba da ya farfaɗawa
Hajiya maganganu su Aunty maimuna da Aunty Asma'u ya kamata a ce ya zanesu duk
abunda zai faru ya faru za ta fi jin ciwan hakanma, Ni dai shiru na yi Mai
faruwa ta riga ta faru, haka muka ci gaba da labaran duk na gidanmu ne, ba mu
muka bar gidansu Mama ba sai dare har Abbahsu Mama Saida yadawo Gwaggo ta shiga
bashi labarin abin da ya faru shi ma duk labarin gidansu Abbahn yana da shi ko
tantama baiyi ba yasan fiye da hakan za su iya ma dan Abbansu shi cewarshi
harshi Abban namu sai ya samu warwara za a tantance shi nashi halin dan zumun
ci yanzu yana samu za su shirya shi ma ya manta aibunsu tun da 'yan uwanshi ne,
itadai Gwaggo ta ce wa Malam anya kuwa haka za ta faru kuwa, haka muka tattaro
da su Rumaisa muka taho gida, da sallama bakinmu muka tura kofar gidan muka
shiga a tsaye kofar dakin Hajiya muka samu Abbansu Abbah yana kallon kofar
gidan da alama shigowarmu yake jira tsaiwar da tsumayenmu ta yi kama hasken
wutar nefa ya haska mana fuskarta shi da take cunkushe ba alamun fara'a
Mamarmu da muke koƙarin
shigewa ciki saboda ganin hakan mama bata masa magana ba dan tasan ba abu mai
daɗi zai biyo baya ba
tsawar da Abbah ya dakawa mama mukanmu saida muka tsorata
"Ke Hauwa'u "ya ambata
cikin daga murya da karaji, Mama a firgice ta tsaya muma muka ja muka tsaya ta ɗago ta kalleshi jikinta na ɓari ta kasa cewa komai ya ci
gaba da magana cikin zafin zuciya
"Na sallamawa Abdullahi ke
kin zama uwarshi to inaso ki zama ubanshi, babu ni babu shi, ba zan ce ya rabu
dake ba saboda girman kuskuren da ya yi mana da butulcin haihuwarsa da mukayi
da ya yi saidai mu barshi da ke, alfarmar kwana ɗaya
a gidannan na yi muku in ba haka ba, zan muku abin da acan gidan hayar ba’a yi
muku ba sainasa an muku taron dangi an fasa muku jiki an wurgar muku da kayanku
waje, duk da hakan banji na wuce abin da Abdullahi yayi min bare Kuma na ce uwarshi
ta wuce ni kika sa ya wulaƙantani da tarbiyyar da na masa, kika mayar masa da 'ya karuwa
saboda kema halinki ke nan"
Cin zarafin na ji ya yi yawa ciki
ƙeƙashewar
zuciya na kalli Abbahn su Abbah din babu alamun tsoron mai bakin yake faɗa da abin da za a mayar
masa ko kuma abunda furucinsa zai ja masa ko da a gaba ne take maganar da
kaurarata ya tsaidamin uwa yana maganar san ranshi, Mama na kalla tare da cewa
"mama ki taho mu shige ciki idan yana da magana da mu ya biyo mu ciki, in
bahaka ba zan masa rashin kunyar karuwai, saboda na lura babu imani bare tsoron
Allah a furucin mutanan nan, baki zama Abbah ba kuma ba suda alaƙa dake
saboda ba su mayar da ɗansu
ɗa bare ke ki sa ka
rai za a maida ke ɗan
wani abu a ransu"
Banma jira sake jin muryarsa ba
da nake jinta tafi komai munin ji a wajena ba dan komai ba sai jifan da akemin
da kalma mafi muni banji ba bangani ba
"Ku taho mu shige in kun ga
za ku ci gaba da sauraran shashancinsa ku ci gaba” suku ku suka bi bayana har
Mama da na san ban da ranta ya ɓaci
sai ta mareni kalmar da nake faɗawa
Baban musamman ta ƙarshe har muka shige ciki ban ko sake jin tarin shi ba alaƙa damu
dama ya yanke ni kaina kan ƙaya zan kwanta gidan na kwana ɗaya
sallama mukayi da Ahmad ya yi ƙoƙarin yi mah shirun da muka ji muka ƙarasa
shiga muka fara leƙa falo a nan muka samu Abbah da alama gyangyaɗi yake dukanmu da tausayawa
muka shiga ciki muka sameshi muka fara "Abbah mun dawo"firgigit ya
tashi a rikirkice ya kallemu"Kun daɗe
sai kace ba za ku dawo ba, ku nake ta tsumaye, Hauwa'u na yi zaton ko Gwaggo ta
hanaki dawowa ta inda yaran za su ɓullo
nafi zaman jira da fargabar abunda zan ci karo da shi na Fara gyangyaɗi danni da nake cikin
jarrabawar da jiran hukunci da ƙudirar ubangiji a kainah zan ka sance shi
ne na yi imani da shika shikan imani yadda da ƙaddarar jarabawa mai kyau ko akasinta ina
jin a raina ubangiji yana kusantani da alkhairi ko da bayan raina ga iyalaina, dan
kune komai na, duk labaran da nake ji bantaɓa
jin kalar nawa ba, a ce abun ya tsaurara haka ban ci musu ba sha musu ba, na
rasa ina ma zan saka kaina ne, Musa ya zo bayan tafiyar ku ya maidomin ma wayar
nan ya ce ta yi tsadar da za ta zama zargi a kan yadda aka yi aka same ta wani
ma zai iya sharrin tashi ce aka sata mutane ba tsoron Allah, ko Kuma a taya ta
kuɗi banza saboda za
suga ko an matsu da sai dawa, ya ce Sumayyah ta ci gaba da anfani da ita a
gabanshi Baba ya cimin mutunci ya ce gobe gobe mu bar gidannan, shi ne bayan
tafiyarshi Musan ya ce akwai wani gida inda ya yi haya kafin ya ƙarasa
gininshi to bakowa ciki ya ce zaizo da mota a kawoshi kayanmu ko da asuba
mukeso mu koma za mu iya saboda gidan a hannunshi yake shi ma rigingimu da ƙannanshi
da matarshi ya sa ya bar gidansu ya Kama hayar wannan gidan amma shi abun nashi
baikai kwatar wannan ba”
Tun da Abbah ya fara magana har
ya kammala hawaye nake yi zuciyata a cunkushe take, a cikinmu ina jin Khalil ne
kawai ba zai iya fahimtar abin da ke faruwa ba, nama kasa yarda a kan talauci
ake ƙiyayya
damu saina kalli abun muddin haka ne a matsayin jahilci babba, saboda suma da
suke da shi specific abunda za su kalla suce ya samar mu su da shi ƙarya
sukeyi, Abbahnmu ya yi karatu tuƙuru yana da ilimin da ya wuce na
kwalayenshi hakan ya sa banjin ko kaɗan
karatu ne arziƙi, arziƙin ka da shi ka samu kyakkyawar rayuwa da yawa daga manyan
shaharrun masu kuɗinmu
na jiya da yau ba suyi ilimi ana wasu da ga cikin na yau ƙwalin
SSCE ba su haɗa har
zuwa yau ɗin banaji ko
familynsu Abbah sun san haka ko fahimtar gaskiya ta rufe musu ido, kalaman Mama
ya katseni
"Muma yanzu Baban ya taremu
kasa cewa komai na yi sai Sumayyah ta masa magana ita ma ɗin ban yi zaton za ta iya ba”
Abbah ya yi murmushi "Ai ko
zaginsu ta yi ba zan musa ba saboda kalamun su musamman akanta yanzu sun yi
tsauri fiye da nacan baya, Hauwa'u dan kana babba ba ka da izinin tauye ƙarami,
ba za ka ce zakaita shimfida isarka ga ƙarami kuma na zalunci kace ba zai yi
magana, ko da ɗanka ne
ka ɗabi'ance shi da
kyakkyawar daɓia hakki
ne akanka ga dukkan mutane duk yadda kake kallonsu a ƙasƙanci ba ka san alaƙar
bawa da ubangiji ba wani ba zai ɗaga
hannu yana roƙon Allah ayi ruwa ba face bai sauke hannu ba Allah ya ƙaddari
hadarin ya haɗu anyi
ruwan akwai abubuwa da yawa da za su sa mu hankalta amma bamayi, Allah ya kawo
mana mafita kawai”
Mu ka amsa da "Amin"
Shi dai Ahmad tun da aka fara
zancen bai sanya baki ba ban sani ba ko ys rasa mai zaice ne ma, da haka mukayi
shirin kwanciya barcin sam ni kasa samuwa ya yi a tare dani na ma rasa maike
min daɗi ma abubuwan
kamar a almarane zance rushewar takai ƙarshe duk dai kan Mama ne zan iya cewa ni
kam tausayinsu nake musamman ma Maman da ko rabuwa ta yi da Abbah ba za su iya
amsarmu ba saidai su dauki nasu kawai tun da abun nasu haka ya nuna, ji nake
zuciyata ta ƙeƙashe ina
jin zan zama ne mace kamar namijin da zan kawar da mikin dake tare dasu, kuka nake
mara ƙarfi
duk dalilina abun ya taso haka kuma dalilin zuwana Katsina ne, sai yau na
tabbatar da illar zuwa hurumin da bai dace da Kai ba ko da janka aka yi aka
kaika kai ya kamata ka gudo ne da ƙafafunka kabar rayuwa da San birge wanda
yake gani ya fika ba za ka taɓa
burgeshi ba ina jin ko a 'yan uba aka samu irin wannan matsalar za a jinjina
amma uwa kuma uba ɗaya
hawaye suke bin saman fuskata ina jin sharewar ba shida anfani saboda wani ne
zai sake biyowa, ban san iya lokacin da na dauka ba a haka har barci ɓarawo ya yi awan gaba dani,
tashin da Mama tayi min ya sa ni fahimtar asuba ko safiya ta yi idona na buɗe na kalli waje haske har
ya fara fitowa mama ta kalle ni
"Lafiya Sumayyah haka kikayi
nauyin barci haka, sai Ahmad ya tashi su Rumaisa ke ko yama tasheki baki tashi
ba”
Muryata a shaƙe ta
alamun wadda tasha kuka "wallahi Mama barcin ne ya kasa daukata saikace
mai dannau"
Maman ta ce” Dannau din kuka ba, wallahi
Sumayyah ki kyale mutane ubangiji ma baya iyama yawancinmu ki bar kowa da
fahimtarshi ko da bahagon tunanin ƙiyayyarsa akanmu a kan abin duniya da ba
mu dashi, Allahn da ya raba yaba kowa zai raba ya ba mu idan yaso idan be so ba
haka za mu faru mu tafi ba tare da hakan ba Kuma insha Allah dukkan jinkiri
alkhairi ne”
Na jinjina maganar Mama dan
kaifin basirar ta ka sance mace mai shi kalamanta ga masoyi abun yadda ne da
san jin ta yi su, nidai na san bata taɓa
nuna mana aikata mummunan aiki ba muna fama da yau da gobenmu ne muna barci da
zullumin ya gobenmu za ta Kaya za mu samu abin da za mu ci ko a'a ko sau daya
za mu samu kawai shi ya sa ba ma muda lokacin ƙulla wa wani wani abun bare musa ran dan
aiken ya dawo kanmu kana girbar abin da ka shuka ne nake kallon abunda duk za
ka shuka ne ɗin, na
ajiye tunani na ce” Mama kukan ai yana zama sauƙi a kowacce zuciya ne a kan ƙuncin
da ta riski kanta a ciki kuma da kuna yi za ku samu sauƙi a zuciyarku na san kuna
cikin shi duk da miƙa lamura ga Allah ko ya ya za a samu wani miki a zuciya ne na
tunani”
Mama dai ta ce” ci gaba da kukan
ki idan hawayenki ya ƙare za ki bari, kuka ma aikine babu wanda yasan kina yi kuma
ga mutanan da ƙiyayya ta shafe komai akanmu ba za ki samu sassauci ba”
Na ce ina miƙewa” Mama
Kuma ranar da kuka fara naku ba zan hanaku ba abunda kukeson yi tsawan shekaru
kuka kasa sai a lokacin na san za ku rage raɗaɗin da zuciyarku take yi” daga
nan na fice yin alwala dan Kam gari ya waye ne danma bisa barci na yi rashin
sallar lokacin duhun asuba, a dakin na dawo na same ta a falon da muke kwanciya
ta zuba tagumi da hannu biyu ne har na dawo na yi sallar na idar bata ji ba sai
da muka fara jiyo sallama na ganta firgigit ta miƙe tana dube dube tsayawa na yima kallonta
ganin duk ta kiɗime na
ce” Mama lafiya kuma?"sai sannan ta daidaita kanta ta ce” yawwa tashi su Rumaisa
su fara fitar da kayan na ji sallamar kamar ta Abbah Musa” Ni dai kallan ta na
yi tana ficewa na girgiza Kai kawai wannan fitinar kam dole ta gigita mama din
tashinsu na yi kawai na fara tashinsu.
Na Cancanta (Kashi na 24)
Haka muka gama kwashe kayanmu da
ba yawa garesu b dama muka ƙarasa lodasu a akori kura dukkanmu ba wanda yana yinsa yake
cikin daɗi muka bar
gidan kafin su fito ma su sake ɓata
mana rai a ƙasa
muka tafi haɗe da
Abbah Musa da shi ne yasan gidan, ba laifi tafiya ce mai ɗan nisa ba ma ɗa ba mai nisa ce ma ba
sababbin unguwanni ba ne ba, gidane ginin ƙasa Abbah Musa ya nuna mana shi da muke ƙoƙarin ƙarasowa,
ba shida ko filasta ma amma Alhamdulillah ya fi mana gidansu Abbah da suka cire
soyayyar iyaye da ɗansu
suka wulaƙanta
shi kanshi Abbah ma bare mu da mama a ƙofar gidan muka toge muka jira Abbah Musa
ya bude kofar da a zauren muka isar da kayanmu harma an kawo su gidan sun juye
da Abbah Musa ya ba su ɗaya
daga cikin key din gidan gaba ɗaya
muka shiga cikin gidan da cikin azama muka fara kinkimar kayan zuwa cikin gidan
mai daƙuna
uku da banɗaki sai
kitchen na langa langa da alama muguwar zuba yake yi kitchen ɗin amma gaba ɗaya muna farin ciki da
samun canjin da Abbah ya kasa ɓoyewa
ya dubi Abbah Musa” Musa ban san da wanne ido ko kalmomin da zan dubeka ko na
furta ma ba na gode sosai ka taimakeni lokacin da nake jin a yadda matsalar ta
tasomin nafi kowa buƙatar taimakon"
Abbah Musa ya girgiza kai” Haba
Abdullahi ai yiwa kaine duk wanda zai taimaki wani to ya sa a ranshi kanshi ya
yiwa ba wani ba, kamar wanda yaƙi taimakon kanshi ya yiwa, ladan bai ishe
ni ba ai da zan gaza yi ma taimako dan ko da ƙarfin jikina zan yi ma, muma a harkar
karatu ka taimakemu ai kayi karatu amma ka bari muyi exam tare da saboda mu
karatun baima dame mu ba, sai gashi mun rigaka cin moriyarshi, Abbah Musa ya faɗa murya raunane da alamun
rayuwar tamu ta dameshi da muke ciki” ni da na yi tsaye kusa da su hawaye na ji
suna zubomin cikin rashin shiri
Abbah ya dafa shi” Haba Musa
karka damu dan Allah samunku ai nawane ba gashi ba ka fahimceni ka dubemu abin
da a cikin gidan mu hatta da iyayena sun kasa wannan fahimtar, ni haka rayuwar
ta namun daɗi ina
fahimtar abubuwan da a cikin yalwar arziƙi ne ya yi kaɗan na fahimta”
"Allah ya mana suttura
Abdullahi wucewa zan yi akwai rijiya a makwabta nan gida jikin nan ɗin kusa su samo muku ba
matsala batun ruwa sai dai ko su yaran suƙi zuwa danni sai na siya sanda muka zauna
yarane masu ƙyuya
Allah ya bani” cewar Abbah Musa yana koƙarin ficewa
Abbah ya ce” sunga kana samunka
ne niko karsu ɗebo ma
su ga ni”
Abbah Musa ya tsaya da fara
tafiya "na shafa'a ba muyi sallama da Hauwa'u ba, na san sai tama ciwan
baki ka san mata”
Abbah ya yi dariya kawai ya kira
Mama ta fito t sake ma Abbah Musa godiya sukayi sallama ya ƙarasa
fita Abbah n biye da shi zuwa rakiya waje
Sai sannan na shiga ɗakunan ina leƙawa da
babu isassun siminti a ƙasa duk ya cire tabarmi muka shishshifiɗa da ba manya ba ne dandanan muka shiga
ayyukan gidan da share share muka yi muka gama su Rumaisa suka shiga ɗebo ruwa ni ma har dani ba
laifi daga shigarmu gidan matan gidan suna da kirki gidan kuma mai kyau ne babu
laifi ba kamar wanda muke ciki ba akwai yarinya kusan sa'ata a gidan Malika da
shiga ta muka fara fira ta nada kirki kamar iyayenta da na ga alamar hakan haka
muka dinga kinkimo ruwan saina zauna ma ni ce nake jawowa suna kaiwa gidan
Malika dake wanke wanke a gefen rijiyar tana ɗan
san muyi fira na dai ɗan
sake da ita muna firar makarantah, ita ma mate ɗaya
muke bata samun ƙualyfying ba amma shirin biya mata akeyi ma kuma tana tunanin ɗora karatu ma, na ji ina ma
ni ce ita haka na taya ta murna tana tambayata wanne course ya kamata idan ta
zo jamb tasa ka na yi dariya na aje gugar da na gama jan ruwan
"Wallahi ban sani ba duka fa
tare za muyi candy ai sai dai ki tanbayi yayunki da suka taɓa jamb ɗin, suka samu wucewa
University ai”
Tayi dariya” ok na tuna fa haka
ne, zan tambaya zumuɗi
ne fa kawai kin san ba’a tashi farawar ba ma”
Na jinjina kai "Nace haka ne
kuma, Allah ya taimakemu, bari na tafi, mungode”
Malika ta ce” Amin tom sai na
shigo ko anjima ne, na ƙarasa aiki, kina kitso ne?"
Na yi murmushi” A'a bana yi
Mamarmu dai tana yi, inkinaso zan mata magana saikizo ta miki” na lura dai
Malika surutu gareta har ya wuce nawa da da ma banwai cika surutu ba
"Kai da kin kyauta min ya fi
sati a tsefe na baki labari inata kame kamen mai kitso inda nake zuwa ya yi nisa
yanzu na rage san yawan kuma” cewar Malika na bita da "uhmm haka ne sai
anjiman to da haka na fice ina mamakin surutun ta haka daga haɗuwa abun har mamaki ya ba
ni ma
Ina shiga gida sallama Mama ta
amsa min da ta yi shinfiɗa
a waje, tana murmushi "Ai su Khadijah sunce min kin yi sabuwar ƙawa a
gidan ɗebo ruwan"
na zauna gefen Mama ina ce wa” Mama ke dai bari kawai kamata ta ke tare zamuyi
candy amma surutu tsiya gareta daga haɗu
wata da ita har naso na gaji”
Mama ta harareni” ke kin manta
naki surutun cakwaikwaiwa ke nan, kin sake haɗuwa
da kalar ƙawayen
naki ke nan ai”, jin Mama ta ƙi yarda da zancen surutun Malika na ƙyaleta
ai za ta zo gidan za ta tabbatar nata surutun ba irin namu ba ne ba, na canza
zancen da "Mama Abbah har yanzu bai dawo ba wallahi na fara jin yunwa”
"Eh na san dai yana hanya
insha Allah"Mama bata gama rufe bakin taba mu kaji sallamarshi ya shigo
hannunshi ɗauke da
icce da na san ba zai wuce na ɗari
biyu ba sai leda kuma ita ma a hannun, miƙewa na yi na ansa iccen na yi hanyar
kitchen Rumaisa ta ƙaraso ansar leda ita kuma na ji Abbah yana "ƙyaleta
Rumaisa fulawa ce a ƙasa saman wayar Sumayyah ce, samo roba a zuba fulawar a ciki
ayi ko ɗan wake ne”
Inda muke zaune na dawo na zauna
Rumaisa ta wuce samo roba na ɗan
ɓata fuska Abbah dake
gefen mu ya kalle ni ya kalli Mama” Hauwa'u mai kika ma Sumayyahn taki ne”
Dariya Mama tayi” me zan mata
kuwa ka san ba tasan ɗan
wake shi ne taji za a yi take ɓata
rai”
Abbah ya kalle ni” Au wai shi ne
abin ɓata rai bari toh
ayi wainar fulawa amma in ba ku ƙoshi ba ruwana” na amsa da toh, Mama ta
taɓe baki” ka dinga
biyowa yaran nan musamman Sumayyah ma”
Dariya Abbah yayi” toh naƙi biye
ma ta, ita da ba yayye gareta da za su biye mata ba, indai inada hali kam
hukuncin Sumayyah da ta yanke shi za a riƙa zartarwa a gidannan ba ma na iya abinci
ba, kema kika yi wasa saita ƙarasa har kwashe fadar yarda da
shawararki a wajena, nifa kin san ba ruwana babba mace ne ko namiji yana nan
dai matsayin shi”
Mama ta yi dariya "naji dai
ai ni na haifi a bata ba zan ji haushi ba, amma kar a waremin Ahmadi na, duk
hankalin Sumayyah shi namiji ne ya fita tunani”
Abbah ya ce” oh my God, ai ni ma
namiji ne nafi Ahmad tunani in na tanbayi shawara na ji baiyi ba wadda Sumayyah
ta bayar to zan shawarina da kaina, ya bari ta ci fadarta shi ko yaushe muna
tare”
Ahmad dai bai san wainar da ake
toyawa ba yana ɗaki
ana sana'ar barci kamar kasa haka yake na san da tuni mun kacame da gaddama, Rumaisa
ta dawo da roba da saida ta nemo ta ajewa ta yi aka fara ciromin wayata a
kwalinta yadda aka ba da ta Abbah ya miƙamin a bata yana "Ai Abbah Musa na
faɗamin kyan wayar nan,
da inada kuɗi ai na
siya miki n siyawa mamanku da ni kaina kuma” na yi dariya daga cikin kwalin ya
cirota ya miƙamin
yana” kona kunnata a ba ni aro ma” nidai dariya nake yi muna ƙoƙarin
haɗa ƙullun
waina ɗin hankalin mu kwance
ba muda zullumin komai sai yau da kullum amma ba bu tunanin cin mutumcin kowa
duk da dai ba kayan wani muke ci bashi ba amma a wannan rayuwar na dauki cin
mutunci basai haka ta faru ba, kawai a kan abin da babu mai yiwa kansa ma sai a
ci maka mutunci duk dan ko bahagon tunanin gazawarka ce, haka muka fara soya
wainarmu Ni Kam a na cireta daga kasko nake cinta danma fulawar da yawa a ƙalla
kofi biyu da na tabbatar ni zan kusa cinyeta ma, da yamma yaran sun fice da
Abbah ya samu islamiyya zai kai su ni kam na ce ba yau ba sai an huta gaskiya
zan fara zuwa haka dai Abbah da bai cika San takuramin ba ya amince Mama ko sai
faɗa take tana aiko ta
yarda na yau amma bata yarda gobe ba kuma ni zan wanke wanken gidan rashin dai
zuwan baisa na huta ba shi ko Abbah makaranta ya samu iya kuɗin Laraba ake kaiwa kuma
yaji ana da karatu yaga gwara ya yi ta maza dan zaman gidan ma bari ta ishesu
ma, yaga kuma ga sauƙi ya zo
Sallamar da na ji na yi saurin leƙowa
daga ɗaki da nake
kwance sallamar Malika na ji amsa mata sallamar na yi ta ƙarasa
shigowa ta dube ni
"Yayi Sumayyah barci ma kike
yi ko, kitso na zo fah"
Na ce "ya fara ɗauka ta dai, shi go na ma
mamarmu magana”, Cikin ɗakin
ta shigo ta zauna ni kuma na fito na je na faɗa
wa Mama Malika ta zo kitso, a waje mamarmu tasa na yi shinfiɗa na dawo ɗakin ina faɗa mata ta fito
"Ban ga ƙannan
ki ba, suna ina” cewar Malika
Na ɗan
yi murmushi na ce” Sunje Islamiyya Abbah ya kai su ance bayan gidan nan ce, ba
kuɗin term ake biya ba
ban san sunan makarantar ba”
Malika ta kalle ni” lah ni ma
makarantar nake yi ai, kwarai ta kyauta ce sisi ba’a bayarwa sai goma ashirin
kuɗin Laraba, to mu
makarantu a nan kusan duk na kyauta ne ma, to kuɗin
babu yawa”
Na ce” Allah sarki mu a unguwar
da muka zauna a cikin Kano ba laifi da tsada gaskiya”
Malika ta ce” Haka ne ni ma dan
da karatu ya sa ba’a canzamin makaranta ba yaka mata kema ki shigo gaskiya”
Nan nake shaida mata ni ma gobe
zanje da haka muka fito, Mama da tuni ta fito haka Malika suka gaisa da Mama ta
zauna ta miƙa
ma kibiya aka fara kitso Malika nada gashi sosai har mamakinshi na yi na
kalleta "Dole kiƙi yin kitso da wuri gaskiya”
Tayi dariya kawai na ɗaura da Allah "Masha
Allah kina da gashi "
Mama ta ce” oh Sumayyah anga
gashi an ruɗe”
Malika ta ce” wallahi kuwa Mama
kamar ita ɗin bata da
shi”
Kukan A'isha ya sa ni miƙewa
naje na ɗaukota Mama
ta ce” haɗo da zani ki
goyata, yanzu ta yi barcin goyata na yi ina jijjigata, har ta koma barcin, labarin
Islamiyyar da Abbah yakai su Rumaisa na ke bawa Mama da cewa nan Malika ma take
yi, Mama da farin ciki take cewa "shike nan kin huta kin samu ƙawa ƙila ma
a barki a jinsu"
Nace” Wallahi Mama ni ma na ji daɗi sosai da na ji haka”
Sallamar da muke ji kamar daga
sama ya sa jiki na daukar rawa kamar mazari Muryarsu Aunty Asma'u nake ji, da
ko jiran amsa wa ba su yi ba suka faɗo
cikin gidan mama suka shiga nunawa su uku ne Aunty Asma'u, Aunty Mubaraka, Aunty
Maimuna, Mama da take kitso kanta na ƙasa dan bata ɗago ba ko da taji sallama nan suka shiga
nunata suna cewa” Hajiya ce ta turo mu ta jaddada miki ta yafe miki ɗanta da haka kike so kika
kuma shirya, shegiya 'yar gidan talakawa da duk wanda ya auri irinku cikin
tsiya yake ƙarewa,
kuma ku raba shi da 'yan uwanshi da iyayenshi kuma Yaya Hashim ya ce na shaida
muku yana nan gobe zuwa garin, zai shigar da ƙarar tuhumar mijin naki hukuma ya fito
masa da ɗansa kuma
wani abu ya sa mi Samir sai Sunje ko kotun ƙoli ce a kan hakan, dan mun riga yanzu
mun yafewa Abdullahi ke bare kuma yaranki suyi tunanin raɓarmu anyi gadon makirci da
mugun abu masu ƙashin tsiya” Haka suka ci gaba da ciwa Mama mutunci kamar su
rufeta da duka kai jin shirun nata ma ya yi yawa sai su kayo kanta Aunty Asma'u
ta yi kukan kura sai Mama taji saukar duka nan Mama ta zuciya ita ma suka fara
faɗa ko kawa ganin
haka suka rufarwa Mama mu kam baya mukayi ina kuka sai Malika ce ta fice waje
ta kira maza aka fitar dasu daga gidan da kyar ranar kam na ga bala'i na rasa
mai muka tsarewa mutanan nan haka muna takanmu da abin da za mu ci sunce abar
musu gida an bari amma har nan ma saida sukayi bincike aka musu kwatance, ba
wadda nafi mamaki sai Aunty Asma'u kinada yadda za ki yi kina rigima da waɗanda kin fisu da ƙulla
musu sharri ba su ji ba ba su gani ba, ba mu tsare musu komai ba Malika mamaki
ta shiga yi sosai na abunda ya faru da jin alaƙar mu da su, nan aka cewa Mama za a kaisu
wajen hukuma ta ce "a ƙyale su kawai” dan mu kam ta mu ta ishe mu banji ban da wainar
fulawar nan za mu sake samun wani abu mu ci ina muka ga ƙarfi ko bakin rigima harda
dambe ni saboda baƙin ciki ban ko tanka ba, dan banida bakin magana ga goyon
A'isha bayana kawai na barsu da ubangiji ya gaggauta saka mana banida bakin
tsiya dan rigimar tasu duk sanka da faɗa
to abun nasu yasha kan kowa, Malika harta tafi da mamaki da al'ajabi take
kallan abun, duk da ba wai tasan wani labarin akanmu ba, iya abin da ta gani na
yau kawai ta sani, ko da Abbah ya dawo haƙuri ya shiga bawa Mama dan shi ma ya rasa
yadda zai yi da abubuwan, yadda na hasaso ɗin
ba abinci yau ma kwaki gari, muka samu mukaci shi ma ba dan ƙoshi
ba ba wai rigimar ce ba za mu iya ba dasu ƙarfin tane ba mu da shi mu ba wani abu
garemu ba bare muce muna ci rigima kuwa ai sai ana da yadda za ayi shi ya sa
ganin haka ma suke takamu abin da Abbah ya guje mana ya sa ta kwashe mu kusa da
shi to ga yadda Ubangiji ya tsara komai nan da tsammanin zuwan dame gobe za ta zo
garemu shin Abbah Hashim zaizo da gaske tuhumar Abbah ɗin ko a'a naka sa wani tunani ma bare ko na
tuna wata mafita da zan samar mana na har zuwa wayewar gari.
Na Cancanta (Kashi na 25)
3:00pm da misalin ƙarfe
uku na rana sallamar da na ji kofar gidanmu da nake tsugunne gefe daya ina
wanke hannu na da bakina ka sancewar tuwon dawa miyar kukar da na gama ci ke
nan lokacin, da yau ma da safe ba mu samu karyawa ba sai ruwa da muka dinga sha
Khadijah da Khalil ko kwanciya sukayi shame shame dan ga yunwar daren jiya ga
shi da safen ma ba’a samu anci wani abu ba, sai da Abbah ya lallaɓa ya fita sai gashi da
dawarshi kwano uku da kayan miya harda kuka da Maggi duk Abbah Musa ya bashi, ya
ce masa kafin ya ɗan
bashi jari ya fara juyawa yana ƴar wata sana'a kafin daminar ta zo a fara
noman dan noman ma sai da kuɗin
tun da ba taɓa yi ya
yi ba yanzu zai fara, Abbah Musa ma ya na da kirki sosai a cikin abokan Abbah
na nan ya fi sauran taimaka mana, ko da muna ƙanana muna zaune a Gwarzo haka Mama take
ba mu labarin Abbah Musa, kuma yanzu dawowarmu bai gaza ba duk da shi ma famar
yake amma akanmu kam Alhamdulillah zai ce tun da har yana da ƙarfin
halin taimaka mana, ka sancewar shi akwai zumun ci ko Abbah bai zo ba wajenshi
shi zaizo dalilin hakan ma tasa ya fi sauran abokansu Abbah fahimtar halin da
muke ciki, Abbah Musa mutum ne gaskiya yana aikin gwamnati da noma duk da
koyarwa yake albashin ba mai yawa ba ne amma Alhamdulillah
Sake jin kwaɗa wata sallamar ya sa ni
dawowa tunanin da na faɗa
gaba na na ji yana tsananta faɗuwa
nan na fara addu'a, la'ilah ha'illa anta inni kuntu minaz zalimin, haka na ci
gaba da ambata a cikin zuciyata ina addu'ar Allah ya sa kada maganar Aunty
Asma'u ta tabbata kada Abbah Hashim ya zo tuhumar Abbah ɗan shi, a tafi hukumar da Aunty Asma'u ta
anbata daga nina ƙaramar matsala ce amma saina ɗauka
tun da ana san wulaƙantamu kotu ma sai a tafi hawaye na ji masu ɗumi na sauka a kan fuskata
na rasa gane laifinmu kawai dan muna talakawa sai a dinga wulaƙantamu
abin har hukuma mah, a ce tana ƙoƙarin shiga ma wannan rayuwa wacce iri ce
mukeyi a cikin ƴan uwan mu, abin ya wuce muke ganin ana ƙin mu
a'a abu ne da duk mai hankali zai yi wannan shaidar ko da yana zullumin faɗa to a ranshi tabbas zai yi
wannan tunanin, na rasa gane ta ina Maman take da laifi, kasa matsawa na yi
daga inda nake a tsugunne na yi dan yadda gaba na ya ci gaba da dukan uku uku, ga
wata sallamar an sake dokawa jin sallamar har karo na uku na jiyo Abbah da ga
inda nake yana magana
"Ah'a wannan sallamar fa na
san dai ba Musa ba ne, Ahmad taso kaje ka gani waye, danni kam yanzu ina tashi
daga abincin nan na ƙoshi kuma”
Ahmad da shi yama rigani kammala
ci shirin tafiya islamiyya ma ya fara dan uku ta yi harma suna neman makara ni
ma Malika nake jira ta kuma cemin sai uku da rabi za mu tafi dan da muka shiga ɗebo ruwa ko wanka bata da
niyyar yi makararrace dai danma farkon zuwa ne na biyewa shiriritar Malika ɗin, duk da dai yau rashin
samun abinci ya sa dole za mu makaran ma, Ahmad da banji fitarshi ba sai
sallamar dawowar shi da ya yi ya sa na sake jin bugun zuciya ta ya ƙaru
kasa amsa masa sallamar na yi haka ma su Mama na ji Abbah yana ce masa
"Lafiya wanene Ahmad"
Amsar Ahmad ya sa na ji dum a
zuciya ta na dafe kirji nah cikin inda inda na ji Ahmad ya ce wa Abbah
"Eh. . . uhmm. . Abbah. . . Ɗan
sanda ne Abbah da kaki na ganshi ya ce na faɗama
kazo police station yanzu kai da Yaya Sumayyah, ana san ganin ku"
A zabure na miƙe daga
gurin da ni ke na nufosu
"Abbah ɗan sanda ni me na yi kuma” na
yi maganar idona ya yi rau rau
Mama ta ce” Mai kukayi dai za ki
ce Sumayyah, shi ma Abbahnku ba abin da ya yi musu kawai don a tozarta shi ne, amma
ina zai kai Samir inda bai kaiku ba, talauci ai ba rasa imani ba ne”
Abbah ya cire hannu daga cin
abincin ya dubi Ahmad ya ce "jeka kace masa muna zuwa yanzu"
Ahmad sai da ya fice ya dawo da
dubenshi ga Mama ya ce” Hauwa'u ai a ganina ni ya dace su tuhuma ba Sumayyah ba,
tozarcin ya fi dacewa ya tsaya iya kaina yanzu da me garinnan za su riƙa
kallon Sumayyah"
Mamah ta goge hawayenta
"Bakomai Allah na tare daku kuma ya isar muku ku nemi agajinsa baya
zalinci kuma ya haramta zalunci a cikinmu bayinsa ke nan shi mai ji ne mai
ganin zahiri da baɗini,
na san mun yi kuskuren tura ƴar mu inda kai uban ta ba’a sanka a wajen
bare saka ran za aso jininka, Allah dai ya dubemu da niyyarmu" Abbah ya
amsa da "Amin" niko ka sancewata a ruɗe
ko hijabi kasa shiga na ɗauko
na yi sai Rumaisa ce ta ɗaukomin,
haka na bi bayan Baba zugui zugui gaisuwar kirki ɗan
sandan bai tsaya ya yi da Abba ya ja machine ɗin
shi ya yi gaba ganin fitowarmu, da na fi tunanin ko tunani yake Abbah zai nemi
wani taimako daga gare shi bayan ga ubangiji da taimakon shi duk muke nema na
san a irin yana yin da ya gan mu ba sile ba sisi banjin zai iya taimaka mana ko
da yana da hanyar haka a dai yana yin da na ganshi da alama yana cikin waɗanda suka yiwa talakawa kuɗin goro na hassada da ƙyashi
da kwaɗayi da maulah
da shishshigi da ya yi wa wasu tsiraru cikinmu wannan halin yawa a cikinmu, amma
a zahiri na gaskiya matsaloli sunsha mana kai da ba mu da mataimaka a cikin ƴan
uwanmu sai dai muna samun taimako daga wajen ubangiji sai ya ka sance ya sadar
damu da mutanan kirki masu ƙaunarmu a yadda muke basa tunanin gazawarmu ce ko kasawarmu, basa
kallan talaka a matsayin wanda za ka masa rana ya yi ma dare, basa kallan mu a
matsayin waɗanda ko
nan gaba za a haɗa
baki da mu a aika ta musu wani abun basaji ransu za mu ci amanar su sun amince
mana ɗari bisa ɗari, tabbas na sani akwai
talakawa da ba wai talaucinsu ya damesu ba, amma babu mu a cikinsu kukan
rayuwarmu kawai mukeyi ba muda ƙarfin aikata aiki makamancin wannan fatan
ubangiji ya ƙara
tsarkake zuciyoyinmu kaɗai
a ko da wanne lokacin mukeyi, da wannan tunanin kan muka ƙarasa
station ɗin da bata
cika nisa sosai bah muna shiga muka ci karo da Abbah Hashim sai su Aunty Asma'u,
da tun a harabar station ɗin
muka ci karo da tsadaddiyar motar Abbah Hashim ɗin
da nake tunani cikin tashi motar suka shigo dukansu dan banga motar Aunty
Asma'u ba a wajen, cikin kayansu na alfarma suke zazzaune dan Abbah Hashim ma
waya yake amsa wa kallansu nake yi sama da ƙasa kafin na maida kaina kanmu dan ko su
Aunty Maimuna da suke aure Gwarzo masu rufin asiri sosai suke aure, amma a
hakan wai ake tuhumar mu da ɓatan
ƙaton
saurayi da ya isa ya tara iyali ma kawai dai tozarcin da suke mana a gidan ne
bai ishesu ba harda hukuma, saida ya gama wayarsa ya kallemu a wulaƙance duk
da gefensu muke tsaye muna kallonsu gefensu saida ya kallemu tas da Abbah wani
koɗaɗɗan yadi ne jikinsa ni ce
ma kayan nawa masu ɗan
kyau cikin kayan su Aunty Abida, da Aunty Malika da suke bani, Abbah Hashim ya
fara ma wani ɗan sanda
magana ba wanda ya sa a kiramu ba ne wani daban da gani shi ma ba kirkin zai yi
ba
"Yallaɓai ga sunan tuhumar su nake
shi da ƴar
sa kamar yadda na faɗa
muku a kan ɓatan ɗana Samir nake tuhumarsu, dan
tun da ƴarsa
ta fito da halinta a gidana da tajemin hutun jarabawa, ranar da na ce tabar
gidana shi ma ranar ya bar gidan wayoyinsa a kashe na kira su ya fi a ƙirga ita
ma mahaifiyarshi ta shaidamin ba tasan ina ya tafi ba, na san talakawa da
muguwar sakayya shi ne nakeso a bincike min su har sai sun fito min da ɗana ko da gawarsa ce sun
tsafeminshi saboda suna so suyi kuɗi,
ban sani ba, dan su ba talaucin da suke ciki ba ne ya dame su sun riga da sun
nuna hakan tuntuni dan da shi ya damesu ba za su aje mugunta haka bah a
ransu"
Yadda ya tsara kalamansa da yadda
suka ganshi alamun kuɗi
sun bayyana a garesa ya sa ba tare da jin ta bakinmu ba kawai suka kwashe mu
zuwa cell suka rufe mu da cewa har sai an samu number nashi kuka na ji ya kwace
min a cikin cell ɗin
har sai yaushe za mu samu a fitar damu addu'a kawai nake yi da tunanin su Mama
a raina ya za suji idan suka ji haka haka su Abbah Hashim suka gama cike cike
su kabsr station ɗin
da na san yau zuciyoyinsu sun yi wasai dasu.
Na Cancanta (Kashi na 26)
Har yamma gaf da magriba muna
cikin cell ɗin, ba
wanda ya waiwayemu, banjin Mama tasan tsaremu aka yi ba, ina cikin cell din na
ga shigowarta ita da Abbah Musa da kana ganin ta za ka san bawai a hayyacin ta
ta shigo ba tambayarsu aka shiga yi "lafiya”, nan na ji Abbah Musa na
labarta musu wajenmu suka zo wani cikin police ɗin
da a lokacin da muka iso ban ganshi ba ya ɗauki
file da case namu yake ciki ya karanta ya kalli su Mama” kunga ku zauna ai case
ɗin ba wai babba ba ne
sai na ga duk rashin fahimta ne ma, yanzu in kuna da number ɗin yaron ku kirashi” yana
yin yadda ya yi maganar na fahimci wannan police ɗin
ba shida damuwa
Mama ta share hawayenta ta fiddo
wayoyi biyu hannunta tawa da ta Abbah da na san kayana ta bincika ta nemo ƙaramar
wayar tawa da ban fara amfani da ita ba, ta nunawa police ɗin"ka ga wayar nan ta
Sumayyah da Abbahnsu ɗin
ce tun da suka taho nan nake kiran Samir ɗin
bana samu"
Ya girgiza kai ya sake duban Mama”
ki sake trying Aunty ko za a samu ta shiga jin lafiyar yaron ce za ta fiddasu
banji za su yarda a ba da belinsu", jin haka Mama ta sake ɗaukar wayar ta kirasa ta wa
ta raruma ta danna tasa a kunne a loudspeaker ta sakata cikin rashin zato ta
shiga number ɗin sai
aka katse, Mama ta ɗago
tace” Ta shiga amma an ka. . . "bata ƙarasa maganar ba kiransa ya shigo, Mama
da hanzari ta ɗauka ko
sallama bata yi ba ta fara” Samir kana ina ne muna ta kiranka ba ma samunka dan
ka kira Abbanku ka sanar masa inda kake hankalin kowa ya kwanta” ka sancewar
loudspeaker ta sake danna wa na ji Muryarsa yana cewa” Ummi Hauwa'u ki faɗa min maike faruwa dan
Allah, ina ita Sumayyah ɗin"Mama
ta ce” Dan Allah Samir ka fara kiran Abbahnku ka shaidamasa kana lafiya” yana ƙoƙarin
sake cewa” Toh amma Ummi. . . ", Maman ta katse shi "dan Allah Samir
kayi abin da na ce maka hankalin kowa ya dawo jikinsa” daganan ta katse
wayar"Mama da sakin murmushi ta furta” Alhamdulillah"Abbah Musa ya
kalleta ya ce” Hauwa'u kin ji wani abin mamaki ga yaro ya amsa waya hankali
kwance shi bai san da faruwar komai bama, amma ana neman wulaƙanta
Abdullahi har abun ya yi tsamari haka”, ɗan
sandan da bai gama fahimtar komai ba ya ce "To yanzu dai Alhamdulillah tun
da an sameshi a waya Allah ya tsare gaba bari na shiga ciki na sanarwa da dpo ɗin a kira su suzo da wuri
dan kwana cikin gurin nan sai dolen dole dan yanzu ma na san zai sa a fiddo
su" su Mama suka ɗaga
kai” Mungode Allah ya saka da alkairi” da haka yabar wajen Mama da Abbah Musa
suka ci gaba da tattaunawa can sai gashi ya dawo yake sanar da su Mama DPO zai
kira su Abbah Hashim yanzu a waya a zo a ƙarasa maganar case ɗin ya wuce, sai da Abbah
Hashim ya dawo, danshi kaɗai
ya dawo sauran nafi tunani daya kwasosu sun tafi gidanjensu, dama Aunty Luba
ita ban da ita duk da bata da mutuncin ita ma amma mijinta bai cika barinta
unguwa ba, sai sannan aka fiddomu cikin cell ɗin,
da sai gaf da Isha ya zo nan ya fara cewa musu yaronsa ya kirashi ɗin, a nan aka kashe maganar
sai kuma iyakar da Abbah ya nema da Abbah Hashim ɗin
haka sukayi baran baran kamar ba su fito ciki ɗaya
ba Abbah ma ya yi haƙuri da shi a dai yadda ya daɗe
yana nunawa
Abbah Hashim ya kalli Abbah da
sauran mutanan wajen kafin ya ci gaba da magana” iyakata ta ƙarshe
da kai Abdullahi ka raba ɗiyarka
da ɗana dan ko zai
mutu ba aure ba zai auri wannan ƴar iskar ƴar taka ba, yaron da suke sheƙe
ayarsu da ita tun da na masa zancen Fatimah bai sake neman mu ba”
Abbah da kallo yabi Abbah
Hashim"Ai tun da ka nuna ga abin da kake so ni kuma ba zan yi ba, kaje ka
cusawa ɗan ka halinka
firstly ka nuna isarka akanshi, amma ni ba za ka nuna min isa a kan hakan ba zumun
ci shi in yaga zai yi damu ba zan Koresa kona ci mutuncin sa ba yadda ni kama
tawa, lalacewa kuma da kake kallan ƴata lalace take da ɗan ka suke lalacewa amma
kuma har yanzu ba su taka ƙafarka ba ɗaga
ƙafarka
ma basuyi ba, kuma maganar yaro da kake yi yaga iskancin da ɗan ka ya koya mata kazo da
wanda ya fi nasu, dan na yi imani a yadda tunaninka yake akwai matsalar hankali
tare dakai ko akwai cutar raina abin da ubangiji yabaka ga cutar hassada da ba
ka ganin samunka saboda rashin godiyar Allah sai talakan talau shi ne kake
ganin yana da samun da za ka tsaya jayayya da shi”
Jin maganganun da Abbah ke
mayarwa da Abbah Hashim ya sa ya fara muzurai” kungani dai irin cin mutumci da
yake min a ƙarasa
yi mana iyaka ni dashi”
DPO ɗin ya kalli Abbah Hashim ya na cewa” Alhaji ai
an gama muku iyaka, ko da ba'ayi ba inshi yana da hankali ba zai sake shiga
rayuwarka ba ko da ya rasa dangin da zai yi hulɗa
dasu, saboda ƙaramin case haka ka kawoshi nan an sashi bayan kanta da ƴar shi
da na ga fiye da wannan ma za a iya yi a gida a sasanta, mu bi yadda kake so ne
saboda bamasan maganar ta yi tsawo tun da ga yarda ƙarin naka ya ce a kan maganar
yara ka jawa naka kunne ka faɗa
masa abin da bakinka yaso akansu shike nan, dan Allah ku tafi haka bamasan wata
hayaniya kuje gida ku ƙarasa maganganunku, ko ku tafi ofishin sasanci mu dai ga iya
sasanci da za mu iya yi muku an bi ma haƙƙinka da kake nema shike nan, duk mai
gaskiya tsakanin ku watarana za ta bayyana, in kuma rayuwar talauci ce tun da
shi ya ɗanɗana ba kaji komai ba, da ya
dace ka tausaya musu komai za suma saboda rayuwarku ta banbanta ka kuma taimaka
musu taimako na zumun ci da Allah da Manzonsa su sukace ayi shi a sadar dashi, to
in ba kayi wasa ba kaima za ka ɗanɗana ko ga kuɗin sukasa amfani a gareka
komai mai sauƙin ne a gurin mahaliccinmu"
Da haka dai muka fito ko takan
Abbah Hashim ba wanda yabi yanata faɗansa
muka wuce ya zo ya wuce mu a mota ya baɗemu
da ƙura
ya fi motar da ƙarfi ta gabanmu, nidai su Mama ke tattaunawa ni ko har muka zo
gida ban iya cewa komai ba da kallo nake bin kowa na gidanmu haka na shige ɗaki A'isha da Mama ta bari
gida ta sha kuka har Rumaisa ta goyata abinci Rumaisa ta kawomin ɗaki na ce mata na ƙoshi shi
ne maganar da zance na yi tun shigowar mu a zahirin gaskiya ba yunwar ce banaji
ba cinne ba zan iya ba ƙwaƙwalwa ta ta kasa aiki yadda ya dace tunanin na kasa yi kukan
ma na kasa yadda nake jin labarin depression, a makaranta sai nake ji kamar ina gaf
da shiga cikinsa, to gani ke nan inaga Mama da Abbah amma ina jin tausayin
kaina a ƙananan
shekaruna ina fuskantar hakan kaina da da cikina suka ɗauki ciwo a tare lokaci ɗaya haka nake zub da hawaye
kamar ruwa na tsiyaya wata irin azaba nake ji kaina kamar ana dokamin guduma na
rasa gane maine ke shirin faruwa dani ina jin labarin mu ko a littafi da film
ba’a kwatanta kamarsa ba, saida kan ya lafa na miƙe na yi alwala na dawo na tada sallolin
da ake bina suma a zaune ina idarwa ko azkar ban yi ba na kwanta ina jin ko a
kwance zan yi addu'ar idan tunanin matsalar dake faruwa ta barni da hakan nake
jin Allah ya dubi zuciyata ya kawo mana canji ba wai ni kaɗai ba dukkanmu Allah ya
gani an mana zalinci an kasa fahimtar mu saboda talauciy, na fashe da kuka mai
cin rai ina ambatar Allah"ya Allah ka dube ni da dukkan Musulmi da Allah
ya jarabcesu ta koma wacce fuska ce ka kawo mana canji, Allah ya ba ni ikon
ambatonka a zaune a kwance a tafiya a lokacin samu a lokacin rashi, Allah kada
ka ba ni ikon kokawa ƙaddarar jarabawoyinmu ko dan kada ka bar mu dasu"nama
rasa me zan ci gaba da yi wayata da Mama ta ba ni a hanya silent na dannata ma.
"Yaya Sumayyah ana kiran
wayarki tana haske” maganar Rumaisa da na ji cikin barci da dakyar ya daukeni
ya sa ni buɗe idona da
kyar saboda kaina dake saramin na kuma kasa magana a samo min magani, da na san
Mama taji hakan saita min faɗan
saka damuwar nan acewarta danaji ta dasu Abbah a hanyarmu ta dawo wa, fiye da
hakan ko bai faru ba zai iya faruwa kada wannan ya sa Abbahn damuwa, wayar
nakai hannu na ɗauka
na duba na ga Yaya Samir ne haka dai na ɗauka
jiki a sanyaye na kasa cewa komai na yi shiru, sai shi ne na ji yana cewa
"Sumayyah kina jina
ko?", dakyar na amsa da "Eh Yaya” Sumayyah dan Allah kiya haƙuri da
abin da Abbah ya sake yi, wallahi ban sani ba amma muna waya da Ummi ai shi ne
dai ya ɗauki fushi
dani inji Ummi ta ce na bari sai ya wuce na kirashi, ban san abin da zai yi ba ke
nan kuma ban san yana kirana ba, wallahi Sumayyah na rasa mai ke damun Abbah, halinsa
ya ƙara
sauyawa sai kace bashida imani, haba samu ai da rashi na ubangiji ne abarku
mana haka” tun da ya fara maganar nake zubar da wasu hawaye masu zafin gaske
har ya ƙarasa
banajin zan iya magana mai yawa ma ko da a zahiri bare a waya na ce” Yaya Samir
sai da safe za mu yi magana”, na ji yo sa yana cewa” Sumayyah kina jin haushina
ko babu laifi kiji haushina ai na cancanci hakan, amma ki duba ba laifina ba ne
ban san zai yi ba Ummi batasan ya zo ba dan Allah kada ku kamamu a kan laifin
Abbah ba muda masaniya ni ɗan
uwanki ne, ina ƙaunar farin cikinki da naku duka ni ɗin kamar uwa ubane nake wajenki Sumayyah, tun
ranar da na barki hankalina ya kasa kwanciya nata kiranki shiru wayarki, ashe ɗin bakwa yana yi mai daɗi na ji duk abin da su
Abbah Imran sukayi da barinku gida ina nan amma banajin daɗin komai dake faruwa na ma
rasa wanne mataki zan dauƙa Saddiƙ na Abbah Imran ne y ba ni labarin komai abun babu daɗi Allah ya ganardasu ya
muku sakayyah"haka Yaya Samir ya ci gaba da yi min kalaman kwantar da
hankali har na ji zuciya ta ta rage zafin da take yi daganan mukayi sallama na
kwanta barci mai cike da mafarkai iri iri da na san yana yin da nake yabawa
shaiɗan galaba akaina
ya sa nake mafarkan kala da kala duk marasa daɗi,
irin yadda yana yina yake, Har hakan ya sa na farka a barcin saboda mai ɗumbin mafarkan tsoron da nake
yi, addu'a na yi kawai na runtse idanuna hawaye na sake bin kuncina, na rasa
ina zan dafa ina zan saka raina mah zafin ƙiyayyar ya yi yawa ban yarda duk a
dalilin Mama ba ne, ko wani waje kalar abin da zai yi garemu ke nan, yaushe kukan
zai ƙare
namu zamuyi farin ciki ya mantar damu ƙuncinmu yaushe waɗanda suka ƙi mu za su ci tamu alfarmar yadda Halimah
ta faɗamin Halimah ɗin nakan tunota a duk
lokacin da na shiga damuwa musamman irin ta yau da Halimah ya dace ta sani sai
kuma Baatul yana yinmu tare da farin ciki nake tunowa muna yin abu irin matured
ɗin nan, hawayen dai
kam yau da za su ƙare da sun ƙaremin na rasa juriyar da na saba arewa a
yau ɗin, tunani nake
tabbas akwai masu matsalolin da sunfi nawa tare dasu suma a wannan daren sun
kasa runtsawa ɗin, kuma
babu damar su samu ƙarfin yin nafilfilu yadda ni ma banida zuciya ta babu ƙarfi
irin na sauran lokuta da a wannan yana yin nakesamun damar nafilfilu da kaiwa
Allah kuka na, Allah madogara ne na san kuma baya zalinci ya haramta sa a
tsakanin mu Allah zai dubi zalintar mu da aka yi Allah yana saurin amsa addu'a
na wanda aka zalunta ko dama bai kai ƙarar mutumin da ya yi zalincin gabansa, saboda
ya zama abin haramci garemu, ba kuma Sudan tabbacin ta ina sakayya za ta zo taka
sance. . .
Na Cancanta (Kashi na 27)
Suku ku na tashi gaba ɗaya kuma har lokacin kaina
bai bar ciwon ba sai dai ya yi sauƙi mun samu ragowar tuwon jiya mun ɗunɗunma mun ci, ƙanne na da aka samu hutun term yau da ta
kama monday duk muna gida, tunanin kuɗin
da na ba Abbah da yaya Samir ya ba ni na shiga yi dan indai kam ya taɓa su za mu ga sauyi sai dai
banji ya taɓa ta yiyu
wani abun yake nufin ya yi dasu dan indai ba’a juya ba to ƙarewa
za suyi bare ma ba yawa ba ne dasu sosai ba su wuce dubu Ashirin ba a yadda na ƙiyasta
nake jin kuma dasu za a samar masa gonar da zai yi noman dan na san ita ma sai
anbada wani abun, kowa a wannan lokacin yana fama da abin da ya dameshi, ina ma
laifi in mun samu duk da za mu ba da wani abu wani ko nawa za ka bashi bai
yarda aci arziƙinsa ba ya gwammace ya aje gonar bai noma ba har damina ta
wuce mutane iri iri gasu nan muna rayuwa a tare da su, Allah dai ya azurtamu da
manufar alkhairi a zama mutanan kirki, saƙon da Mama ta aiko Rumaisa da shi wajena
ya katse tunani na, cewa naje mu tafi ɗebo
ruwa gidansu Malika haka na zari hijabi muka fice ba dan wai ina jin ƙwarin
jikina ba, dan dai ina cewa ga wata damuwata zan ja Mama ta tsareni a kan damuwa
na cireta Ita kuwa na ɗauke
ta dole ce ko ba ka so sai ta ziyarceka, haka muka tattara kayan ɗebo ruwan muka fice, gidansu
Malika muka shiga muka gaisa da iyayenta muka fara ɗibar ruwa banga Malika ba ban kuma tambaya ba,
"can muka ji ƙarar buɗe
kofar da nake tunanin nan ne bayin gidan da bucket ta fito jikinta ɗaurin ƙirji
ne da alamun ruwa a jikinta da yake shaida wanka ta fito ta kalle ni da nasa
Rumaisa da ja ruwan na tsugunna a gefe
"Sumayya ashe za ki shigo
yanzu nake niyyar na shirya kafin na wuce inda zani na leƙo
gidanku", na yi murmushi na ce” Eh kin ganni dai kaɗan ma za mu ja ruwan za ki iya shigowa ai” Malika
ta dawo inda nake ta zauna saman bokkitin ƙarfen ta ci gaba da cewa” kin ga ba fa
lallai zuwan na ji labarin mai ya faru, zullumina kar a ce gulma ta kawo ni, yara
suka shigo suke faɗa” Ni
dai kallan Malika nake kawai banjin ta cancanta na zauna bata labari haka duk
da yadda na ga alama daga ita har iyayen ta suna da kirki, amma sai na ga kamar
akwaita da sanjin zance ko dake da abu na faruwa ba ka san dalili ba gwara kaji
ba'asinsa yadda yake ko ka samu natsuwa kuma abune da za a kallemu bahagon
kallo dashi, amma saina ga lokacin ta sani baiyi ba na dubeta da canza zancen
"zafa ki bushe fa kinzo kin
zauna haka” Malika ta miƙe "Au namanta saboda zafi mah shi ya sa”
Rumaisah bayan wucewarta ta ce” Yaya
Sumayyah wannan Malika ɗin
kamar munafuka wallahi” Nasa dariya jin abin da Rumaisah ta faɗa na ce "Ba wani
munafunci son jin zance gareta kawai”
Rumaisa ta ce” uhmm aji daɗin ba da labari ba ansan
daga A har Z"na girgiza kai na ce” oh Rumaisah ai ba mu tabbatar ba ai, kawai
nafi tunanin tana cikin mutane ne da sunfi san suji labari daga farko har ƙarshe don hankalinsu ya ƙarasa
kwanciya hakan ma kulawa ce nake gani” Rumaisah ta ajiya gugar gefe” gaskiya
dai banga ma yarda da itaba kina gani saboda gulma bucket ta kafa ta zauna”, Ni
dai naka sa sanin a inda zan aje Malika ɗin,
da haka muka ɗauki
sauran ruwan bayan mun musu godiya muka fita, takalma da na gani ƙofar ɗakin Mama ya sa ina aje
Bucket ɗin na shige
dan na san baƙin namu ne na arziƙi ne waɗannan
dasu Aunty Zainab ƙannansu Mama na ci karo a ɗakin
Zainab ta kalle ni kafin na ƙarasa zama "To zauna mutanan cell
kai Sumayyah ƴan uwansu Abbahnku ba su da kirki, ai yanzu muke tambayar Yaya
Hauwa'u ta ce kuna ɗibar
ruwa makwabta, gidan ma da ta mana kwatance gidansu Malika Tukur Bello ne ƙawa ta
ce ma, a boko, "
Ni dai na zauna gefensu iyayen
labari sunzo kuwa kafin na fara bawa su Aunty Zainab labari” Kai kadai bari
Aunty Zainab mun sha cell jiya ashe labari har ya kai muku"
Omm Habiba ta kalle ni” lallai
Sumayyah ai yanzu mutum ake kiwo duk wani mutsinka a idan mutane yake kuma kaɗan suke jira, Yaya Jabir ya
zo da labarin nan, ni nama rasa mai kuka musu ma, wulaƙanci ne kawai, kudai
Allah ya kare ku sharrinsu" na ce” Amin", Aunty Zainab ta ɗaura "Allah ya kawo
muku canji na alkhairi duk dan ba ku da shi ne, Allah shi ya sa kuma ko a
littafi ban ci karo da yana yin wannan zumun ci naku ba uwa ɗaya uba ɗaya hakan ke faruwa, ko
littafin Zumun cin Zamani banajin yakai naku labarin ƙunci duk da dai a kan Zumun
cin yake magana ai a wannan yana yin fa in fa ba kada shi ba'ayi dakai karka ɗaura ko nauyi ne” Nanfa
labarin littafin aka buɗe
shafinshi su ne dai masu karantawar ni saidai na ji labari, yadda muke firar ka
shigo gidan za ka ɗauka
su Aunty Jamila ne suka zo saboda yadda muke firar tare, yini sukayi a gidanmu ka
sancewar sunsan yana yin da muke ciki ko ƙorafi ba su yi ba, har Abbah ya dawo da ɗan wani abun dafawar dai, sai
da yamma sai ga Malikah ta shigo gidan nan ta shiga mamakin ganin su Zainab
gidan bayani suka yi mata, nan fa fira ta ɓalle,
Mama ta koramu ɗakinmu,
nan muka ci gaba da fira sai lokacin n ski jiki fiye da da Malika ɗin, sai dare suka tafi gida.
Abubuwan yanzu sai na ce sun yi
sauƙi
ba kamar da ba Abbah ya fara sana'a saida kayan miya duk da ba wata riba
musamman ko dan ƙaramin jari garesa ga gasu kayan gwari wasu duk ruɓewa sukeyi da cinikin ba
duka kowa yasan yana saidawa ba a kofar gida yake zama, wani lokacin Ahmad a
lokacin Mamah ta fara dafamin awara ina soyawa a kofar gida ka sancewar layin
mu babban layi ne muna dawowa islamiyya nake fara soyawa Malika kullum tana
wajen ita da take 'yar fira hakan ya sa ita ma mamarta ta ce ta dinga mata
dankali da zaman da take yi haka muke sana'ar mu asirinmu rufe, muna samu, batun
Yaya Samir ba ma wani waya da shi ko yana kirana ban sani ba dan wani lokacin
kashe wayar nake yi, ta yi kwana biyu ma kashe babbar ce dai Ahmad ya fi anfani
da ita dan shi dama mayen waya ne, niko saidai na yi kallo ko karanta Novels da
ita hakan ya sa na maida Sim din da yke ciki a wayar, ganin ban fiya anfani da
itaba tafi zama flightmode, Yaya Samir inashan faɗa
wajenshi wai in dinga kashe wayata na ce masa matsalar caji ne wai su Halima na
ga ya dace na kira tun dawowa ta ba muyi waya ba
Duk muna tare ɗakin Mama ni da ƙannena
da ita yau gidan Aunty Maryam yayarsu ta tafi dubo jikinta bata jin daɗi ka sancewar juma'ah ma ya
sa jin rashin lafiyar ta ta lokacin za a jiƙa wake Mama ta ce abari ayi gobe insha
Allah tun da yau juma'a ma, Ahmad dake game shida Sadiƙ d Khalil a wayata su na
kallah na ce” Ahmad ba ni wayar nan na kira su Halimah, tun da na dawo ba mu taɓa gaisawa ba” Ahmad ya sa game
pause ya tsaidata ya miƙomin wayar yana cewa” Gaskiya Yaya Sumayyah baki kyauta ba” na
amsa ina” toh yaxa'ayi Ahmad hankali ba kwance ba bari na kira dai” duka na yi
rashin sa'a wayoyinsu a kashe,
Na miƙa masa wayar "ci
gaba da game ɗin ka ba
sa'a duka wayoyinsu a kashe suke” amsa ya yi yana cewa” yawwa niko Yaya ana
yawan kiranki da wata number idan wayar na wajena ganin baƙon
number ya sa bana faɗa miki sai jiya ne ma na ɗaga akace ke ake nema na ce
bakya kusa da wayar shi ne ya ce mai kiran in kindawo na ce Hamid ya kira”
Tunma kafin yakai ƙarshen
zancen na san Hamid zai faɗa
dan Yaya Samir munfi gaisawa a ƙaramar waya tun da na ce masa Ahmad ya fi
anfani da babbar da ɗaya
sim ɗin shi ko Hamid
number na ɗaya gareshi,
na dai kawar da tunanin na ce ma Ahmad "Malam Hamid ne fa, da ya mana
service a makarantar mu", Ahmad ya ce "Ok na gane shi wanda kuka haɗu a Katsina kwanaki har
Abbah Hashim ya dokeki akansa” na ce "Eh shi ne fah"Ahmad ya ce” lallai
ai Yaya kwarya bin kwarya take tun da kikaga haka dagaske masu kuɗi ne, gwara ma karki
saurareshi, dan kayan saiti ma complete Abbah bashida shi saidai a dangin Mama
ayi karo karo" na ce "Haka ne kam, kawai inya ƙara kira kace masa wrong
number ne ko kaƙi ɗagawa,
kawai a rabu lafiya, Allah ya ba ni daidai dani”
"Haba Yaya Sumayyah yana
sanki Allah uncle Hamid Kuma yana da kirki, ba lallai suyi mana yadda su Abbah
Hashim sukayi ba, tun da wasu keyi masu kuɗin
ba duka suka taru suka zama ɗaya
ba” Rumaisah ke wannan zancen
Harara na galla mata rai ɓace na ce” Banza sakarai
dake nake magana, in Kuma kin ga ban kyauta ba ki je ki auresa tun da kinfini
sanin waye Hamid ɗin"Tsaki
na mata nama tashi daga wajen Rumaisah ta na cewa” Allah ya baki hakuri” ko
takanta banbi ba na ma shiga ɗakinmu
na ɗauki hijabi na
shige gidansu Malika da mukai matuƙar sabo yanzu, tana yanka dankali da za ta fitar na same ta.
**** ****
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.