Ticker

Na Cancanta (Kashi na 28 - 36)

Na Cancanta (Kashi na 28)

Sai da nafara shiga ciki na gaishe da su mamansu sannan na dawo wajen Malikan na jawo kujera na zauna kallona tayi

"Ya na ga kin samu kujera kin zauna ba awarar za ki fitar ba?"

Hararar Malikan na yi kafin na ce” kin ga ƙari wuƙa na tayaki yankawar kina abu salo saloh kamar mara lakka a jiki”

Ita ma hararar ta wurgo min"ina tambayar ki kina wani zancen daban saboda kin raina ƙoƙari na yankan dankali ba kamar yankan awara bace Malama”

Tsaki na yi na ce” kin ga ba wani nan ke dai ɗin ce ba kida saurin aiki, kawo na ƙara sa kigani” wuƙar ta muƙamin tana ce wa” na sakar miki gwada mu gani, ina dariya na anshe na ci gaba da yankan

"Yawwa kawo kiga yadda ake saurin aiki dama Rumaisa ta ɓatomin rai na zo nan na ga kina neman sake ɓata min, Allah so na yi na kwaɗama yarinyar nan mari ma ta cika yi min shishshigi saikace wata ni sa'arta ce amma dan taga Mama ba tanan ne”

Dariya Malika ta yi jin kawo ƙarshen zance na” Allah sarki Rumaisa kace ta kusa shan mari Kamar za ki iya ba sai Rumaisah ta tumurmusa ki ba, ƙila ma gaskiya ta faɗamiki da baki santa, ina mamar ta tafi ne?"

Wata harara na gallawa Malika” Allah Malika za ki sa na yi zagi fa Rumaisah za ta dakeni aiko za ta iya tasan halin Abbah, ke ɗin gaskiyar kike so?, Mama taje gaisheda Aunty Maryam ne, tun ɗazu ma yanzu na san tana gab dawowa”

"Toh ni dai yi haƙuri kar idan ya faɗi ƙasa kan harara ko ki jema ki yanke, Allah ya huci zuciyar Sumy baby, Allah ya bata lafiya in za ki dubiya zamuje tare”

"Amin" na furta na yi ƙwafa na ƙara maida hankali kan yankan dankalin Malika ta miƙe "yawwah bari na haɗo kayan ana gama yankan sai dai mu wuce, na ji ana yi min kwafa” da "toh"na amsa mata ba tare da na bata amsar ƙarshen zancenta ba, ta ƙara sa barin wajen Mamansu Malika na ji muryarta

"Har kin gama firar ke nan Sarkin ƴan shiririta, anya sana'ar nan za ta ɗaure kuwa idan kin gaji ki faɗa min ko Na'im sai nasa ya riƙa yi” cikin hassala take yin maganar

Ƙasa ƙasa na ji Malikan na magana” Haba Ummah karfa wasu suji suyi dariya ina ƙoƙari daidai fa nawa” Tsaki ta yi ma Malikan ta na cewa” naga alama ai wa kika barwa yankan?"

"Sumayyah ce Ummah yau basa awarar ne Mamansu bata nan"Umma ta furta "Naji wuce ni ki kwaso kayan na haɗa su"

Dariya na yi kaɗan jin diramar Malika da mamarsu haka ta kwaso kayan ta ajesu gefe zuwa lokacin saura uku na gama yankawar na dubeta da ɗago kai ina dariya ƙasa ƙasa cikin ƙufula ta dube ni "yi dariyarki san ran ki akwai ranar ramawa ai” tsaki na yi na ce "sai me Hajiya Malika ai dama kin saba” na ƙara sa maganar na aje yankan na miƙe "ga kayankinan ki ƙara sa abinki mashiririciya” wajen kayan na nufa Na'im da ya ke ƙoƙarin shigewa ciki da shigowarshi ke nan na kallah "Yawwah Na'im fitar da waɗannan ka tayani, aka biye wannan sai akai isha ba’a fita ba” kayan na tsinta marasa nauyi na miƙa masa ni ma na kwashi wasu na ji Malika na cewa” ki ta yi dai zan rama amma ba ni saƙo wajenki bari na fito" ban bi takanta ba muka fice

Haɗa wutar na yi da Na'im ya samo rushi dandanan ta kama na ɗauka kasko na zuba mai da sai lokacin Malika ta fito da robar dankalin tana ajewa na fara zubawa har man ya ɗauki zafi tashi na yi na bata guri ina cewa” Yawwa zauna wajenki Ni wucewa zan yi gida kar Mama ta dawo"kallona Malika tayi” nafa ce za muyi magana amma kike ƙoƙarin guduwa na gode” ta ƙara sa maganar ta na zama kujerar da na tashin, "kai Malika na manta ne fa, ina sauraronki” na ƙara sa maganar ba dan naso ayi zancen ba duk da ban san kallar sa ba

Malika ta maida dubenta gareni kafin ta fara magana” Yawwah Sumayyah Jurayd yayan Alhassan ya ba ni saƙo wajenki”

Tsaki na yi na kalleta” kin ga Malama ki yi maganarki direct ba tsaitsayawa kin san sauri nake yi”

Dankalin ta ɗauki matsami ta fara juyawa kafin ta ce” shi ne hardamin tsaki na gode nuna anshi saƙon ai ta yi kai kuma, dama cewa ya yi yana sonki kuma da gaske yake da niyyar aure ya zo"

Gabana na ji ya yanke ya faɗi inada tabbacin jin batun aure ya sa ni jin hakan me su Abbah garesu a yanzu da za su aurar dani abubuwan da banasan tunowa bayan komai ya lafa nake ƙoƙarin tunowa dafanin da na ji anyi ya sani dawowa tunanin da nake yi Malika ce, kallona ta yi da cewa "yana ji kin yi ɗif ko bakisan Jurayd ɗinne, ya kamata ki yi tunani mai kyau kafin ki ba ni amsar da zan faɗa ma sa Juraid bashi da matsala dai kin san da hakan"murmushi na yi na ce” To ki barni na yi tunani zan faɗamiki abin da na yanke ɗin"daganan na miƙe na bar wajen ba tare da na sake furtawa Malika komai ba gida na ƙara sa shigewa da sallama bakina ban tsaya sauraran amsa min ba na faɗa ɗakinmu na kwanta rigingine saman tabarmah idan na cire Halimah da Batul rayuwa ta sai Malika tana ƙaunata kuma tana sake ƙaunata ko yaushe haka ma iyayenta duk da rana tsaka ƙaddara ta haɗamu amma a zaman da bai wuce na wata biyu ba zaka yi tunanin mun shekara tare na san ba za ta haɗa ni da abunda zai cutar dani ba ko da ni ban san Juraid ba iya ita ta sanshi bare na san Juraid ba iya shi ba har gidansu na sani suna yin markaɗe a gidan jefi jefi muna kai markaɗan awara gidan zuwa siyen awarar tasu kuwa kullum ne shida ƙaninshi sun yi karatu kuma suna aiki da sana'a sun kammala gininsu gidansu tuni ma suna da kyakkyawar rayuwa da san junansu shi da ɗan uwanshi basa rabuwa nan da cen komai tare sukeyi harta da wajen aiki guri ɗaya suke zuwa amma matsala ɗaya ce Abbah ba shida kuɗin aurar dani ni ma a wannan gaɓar da karatunma ya tsaya nafi buƙatar auren amma babu halin hakan, hawaye na ji wasu na korar wasu a kuncina na rasa gane ta ina zan kalli kalar rayuwar mu da ƴan uwan mu komai ya tsaya bisa rashin adalci da halarci a tamu rayuwar tabbas matsaloli na faruwa makamancin namu amma namu uwa ɗaya uba ɗaya ne har zumun cin ya lalace har haka saboda talauci abun ya wuce harda sharruka wayata na lalubo ƙasan filo jin tunanin ba mai ƙare wa ba ne kar na ɗaurar da ciwon da bashida mataimakin magani, lambar Halima na nemo na danna kamar ɗazun yanzu ma kashen take hakan ya sa na kira Batul bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga da sallamarta bata jira amsawa ta ba ta ci gaba da magana

"Mutanan Gwarzo ba’a ko nemanmu an haɗu da family an manta mu"

Wani abu da na ji ya tasomin na danne saina ji kamar tasan komai amma sanin bata sani ba ya sa na kauda tunanin da nake na ce” Ba haka ba ne Batul kwana biyun ne bana samun caji ba ma kuma kuɗin sakawa”

"Kawai ki yarda kinmantamu dai Amma flashing fa, kin Kira Halima ne?"maganar dake raina Batul ta rigani furtawa na tambayar Halima hakan ya sa na yi saurin cewa” Tom tuba nake, maganar dake cin raina ke nan na kirata amma kashe yanzu ma na gama kiran sannan nakiraki ɗazu ma na kirata haka a lokacin kema bansameki ba”

"Na kai wayar caji ne wallahi, kwana biyu ba mu samun nefa, ita kam Halima ta canza Sim card tun kwanaki na ji ta ce ta rufe wancen ne tsohon"cewar Batul ke nan

"Allah ya kiyaye gaba garin shige shigen Halima ta kulle na san"Batul ta furta” ke dai bari Halima ce fa keni kuma kulle layin yama yi mata anfani ma, ina baki labarin mutuminka Hamid, yana ta kirana wai ko maiyafaru dake yake kira baki ɗauka yanzuma ya gaji da kiran nawa”

Gabana ya yanke ya faɗi jin maganar Hamid ɗin na ce” ke kyaleshi Batul wallahi na rasa ta kamaimai Inna ɗaya wayarsa me zance ɗazu muka gama hayaniya da Rumaisa fa a kan yana kira bana ɗagawa”

"Gaskiya dai bai kamata ba saiki ɗaga ki bashi haƙuri ai, na tabbatar da Samir ne za ki ɗauka shi dama abun yafaru dansu, na tabbatar abun bai tsaya iya nan ba nifa har mamaki nake wai ciki ɗaya ake wannan abubuwan"

Murmushi na yi mai ciwo "hmm abun ya fi wanda kika sani ma Batul sai dai addu'a Allah ya ƙara karemu da kariyarsa”

"To Amin Sumayyah, ya makaranta wallahi ki ake batun biyan Neco ɗin nan ki sa Abbah ya kaiki makaranta a saki SS2 saiki ga ko da rabo kin samu kinci ƙualyfying ɗin muma a class ɗinmu su Marakisiyya su Khaulat duk sun koma SS2 to babu kuɗin biyan gwara ki yi maza ki koma dan suma shirin zama ƙualyfying sukeyi”

Cikin farin ciki na furta” kai amma na ji daɗin wayar nan tamu. . . "maganar da nake ƙoƙarin ƙara sawa ta maƙalemin jin sun fara sanar dani kuɗin har ma sun ƙare ko 1minute remaining banji sun faɗa ba waya ta ɗauki daɗi haka na cire wayar kunnena ina doka tsaki, katin ɗari biyu na samu na saka na ke ta alkintashi gashi ya ƙare na san zan jima ban saka ba sai ko Yaya Samir da jerin jefi yana sakamin duk da bawai san hakan nake ba dan nafi burin ya barmin rayuwata ko dan samun zaman lafiyarmu, ganin Batul bata biyo kiran ba ya sa na fahimci ba tada kati ita ma wayar na mayar inda take na ajiye daidai lokacin na ji sallamar Mama da sauri na fito daga ɗakin da ɗokina dan labarin dake cin zuciyata ba zan jira Abbah ya dawo ba Mama tafi dacewa da fara ji sallamar na amsa mata ina washe baki Mama ta dube ni” ke da wa haka Sumayyah ko Makkah Allah ya kiraki zuwa?"

Dariya na yi na nuna kaina "Mama Makkah fa dan dai kin kira Allah ne da sai na ce a mafarki ki ke maganar kuma gashi muna ido biyu"

Mama murmushi tayi” yawwa tun da na kira ubangiji aina gama magana kuma sai kiga ya tabbata hajjin bana a tafi dake, maiya faru kin ga Malika ta ba ni dankali a baiwa A'isha ma” ta ƙara sa maganar tana nuna min dankalin hannunta cike da farar leda babba "ƙanwa ta yi ma yayarta kyauta ni ko da na ta yata ko ta turo Na'im ya kawo min, dama Mama da Batul mukayi waya ne take faɗa min zan iya komawa SS2"naƙarasa maganar ina ƙara murmushi Mama ta furta "kunfi kusa da Malikan ai, Alhamdulillah ni ma na yi tunanin hakan fa, da zaman haka gwara ki je ki ƙara sa karatun Allah ya kawo warwarewar komai, bari Abbanku ya shigo sai muyi maganar" na furta "Amin" a hankali da haka Mama ta shige ciki ni ma ɗakin na koma da murna fal raina ina wani tsallen murna tuni namanta da batun Jurayd dan ina matuƙar san karatu shi ma yana sona saidai ubangiji baya taɓa haɗa ma biyu na san da a ce muna da hali zai wuya naso yin karatun haka hasko kaina nake na koma makaranta kuma gashi na ci ƙualyfying ina hasko kaina a wata duniyar haka na kwanta ina wannan hasashen, sam zancen Jurayd ya ɓacewa tunanina a wannan lokacin

Na Cancanta (Kashi na 29)

Mama na kallah da nake gefen ta zaune” Wallahi Mama yunwa nake ji kin ji cikina kuwa kamar banci komai ba nake ji gashi Abbah har yau shiru"

Ahmad da yake gefena ya fara magana” ai dole muji yunwa tun safe fa rabanmu da abinci, ni dai Mama ko awara da safe ki riƙayi koni zan ɗauka wallahi”

"To Ahmad ai matsalar babu jarin ne da ina zama ya kamani kullum kuna kukan yunwa idan sanadinta rayuwarku ta shiga haɗari fa, ƴan uwan mahaifinku dariya za su yi suna murna” cewar Mama da a raunane take maganar

Ni ce na yi hanzarin cewa” Mama ki anso rance wajen Gwaggo ko Aunty Maryam duk fa za su baki, kina gani Abbah tun safe ya fita ko ɗuriyarshi babu ta yiyu babu ciniki ne a kasuwar"

Ahmad ya furta "yawwa Mama wallahi Yaya Sumayyah ta faɗi gaskiya”

Jim mama ta yi kafin zuwa wani lokaci

"Banasan karatunku ya samu hanyar lalacewa Ahmad amma in hakan zai zamo mafita sai mu riƙa yi bari Abbanku ya dawo muji ta bakinshi”

Tabbas maganar Mama tana kan hanya amma da gurɓatar gobenmu gwara rasa wani ɓangare na karatun namu dan yanzu ma da wannan yunwar dake fafakar mu su Rumaisa sukayi barci in mu muna jurewa to waɗanda suka fi ƙanƙantar jikinmu duba da yadda rayuwar ta sauya, taimako ko sai waɗanda suke mana sun samu abunda za su taimaki wani, rashin dawowar Abbah ita tafi tsayamin rai na a yanzu

"Assalamu alaikum" inda nake jiyo sallamar na waiga ina kallo Abbah ne mai sallamar hannunshi riƙe da Kwando aje sa ya yi gefe ya ƙaraso ciki ganinshi ya sanyaya zuciyata da bugun da take yi tun da munsamu dawowarshi lafiya Mama ce ta yi hanzarin amsa sallamar gami da miƙewa

"Wa'alaikumussalam, Abban Ahmad yanzu muke zancen daɗewarka da yara, Sannu da zuwa”

Fuskarsa ɗauke da farfaɗan murmushi ya ƙara so inda muke zaune ya zauna kusa da Mama

"Sannu da zuwa Abbah"muka haɗa baki gurin yi masa

Kallonmu yake yi da fitilar wayar da take gefenmu jingina a kunne "wai duk damuwar rashin dawowa ta ya sa ku ƙinyin barci tara fa na san ta wuce, ko dai yunwa ce?"

Kai muka girgiza dan kwantarwa Abbah hankalinsa kan shi ma ya girgiza ya juya ya dubi Mama yana faɗin"An samu dafa wani abun kuwa?"

"To Abbahn Ahmad ba ka dawo ba tun safe, nan kuma bakomai sai jarin awarar nan da har zan taɓa na yi tunanin ko shirunka ba asamu ciniki ba ne kar na taɓa a zo kuma a rasa jarin"Mama ta yi maganar cikin raunin murya

"Kinyi dabara kuwa Hauwa'u ai tun safe da na fita har daren nan ɗari biyu na yi ke kin ga kasuwa yadda ta cika da attaruhu, da nake bawa Musa labari ya ce yana da alaƙa da wannan ne zuwana na farko kasuwar, kin ga yalo ma na siyo mana da kuɗin, Ahmad duba cikin kayan miyan can ka ɗauko ka wankoshi sai asamu aci kar ku kwanta da yunwa” Abbah na ƙara sa maganar Ahmad ya miƙe kamar ya faɗi ina kula da yana yinshi ba jimawa ya dawo

Abbah ne ya miƙe, Mama ta dubeshi "ya ka tashi Abbah Ahmad kaima Ya kamata kaci fa”

"Kuci kawai ni na biya ta gidan Musa ai na samu na tarar yana cin abinci mun ci tare”

Nidai kallon yana yin Abbah nake yi wanda ba lallai ɗin gaskiya yacin ba ne ba kawai ya faɗa ne dan ya kwantar mana da hankali sai da ya shige ɗaki kamar mai tangaɗi da na sake tabbatar da zargina yunwa ce ke cinsa kalaman ya faɗa mana dan muji sauƙi kan yalon na dawo na fara ci firar ma kasa ta mukayi ni ce na riga tashi dan yalon ma baya yi min daɗi sai da safe na musu na bar gurin

Tunani ma banbanta nake yi ga wani ciwo mai tsanani da kaina keyi har zuwa yau naka sa sabo da yunwar da mukan kwana mu tashi da Iran mu yini da ita, ɗumamun hawaye ke zubomin har zuwa yanzu tunanin dangin mahaifina yaka sa barina suna da komai amma sun wofantar damu ba dan da kwakkwarar laifi ɗaya kwakkwara da muka aiwatar musu amma suka aiwatar mana haka naka sa fahimtar meye ne laifin Abbah maiyayi musu ba za su dubeshi jarabawar da take tare da shi ba wayata na ji tana ƙara na yi hanzarin lalubarta na duba mai kiran, Yaya Samir ne kamar ba zan ɗauka ba sai kuma na ɗauka ina faɗin

"Assalamu alaikum Yaya Samir ina yini”

Ajiyar zuciya na jiyo ya sauke ya ce” Wa'alaikumussalam Alhamdulillah Sumynah ya mutanan gida na ɗauka ba za ki ɗaga wayata ba ko kin yi barci?"

Murmushi na yi wanda ba wai dan yinsa mai daɗi bne da cewa "uhm uhm Yaya ban kwanta ba lafiya ƙalau"

"Sumayyah ku ƙara haƙuri inanan dawowa insha Allah daga lokacin komai zai wuce zan zo kuma muyi aurenmu insha Allah"dariya ce da kuka lokaci ɗaya ke ƙoƙarin kwacemin duba da san kai na yaya Samir haka duk da ba san kai ba ne burinshi ke nan akaina amma banajin hakan zai ka sance nakan tuno komai kamar yanzu ne sai dai tada zancen ɓacin rai wani ƙarin ɓacin ran ne da tattarar da damuwa a ruhi

"Kinyi shiru baki ce komai ba Sumayyah?"maganar shi fargar dani daga tunanin da na faɗa

Cikin rashin kuzari na sauya zancen da batun karatuna da shi ya fi damuna” Yawwah Yaya Samir zan koma SS2 yanzu zan koma makaranta har yanzu babu kuɗin biyan necon har an gama registration"

"Duk laifina ne na sani Sumayyah da ban ɗauke ki ba na fahimci taimakon a tare da iyayenki kikafi buƙata da wani abun na yau da suke faruwa ba su faru ba, ni kaina da san zuciyar Abbah ba zan iya rayuwa tare da shi ina ji inagani na assasa gurin yanke zumun ci ba dan wani girman laifi ba, na rasa yaushe za su fahimci abunda nina fahimta girma da muhimmancin zumun ci” kawai jinsa nake ba tare da zancen nasa na shiga ta ba Yaya Samir illah iyaka na san mutumin kirki ne amma mahaifin sa ya ansasa wani irin zafin zuciya tsakanina da shi, ina jin inama ban taɓa gani ko jin labarin ƴan uwa na jinin Abbahn ba

"Sumayyah ba kyasan waya dani ko?, shike nan zan baki lokaci ki fahimci muhimmancina a wajenki” jina yi kamar na bigesa da gabana yake tsabar irin zafinsa da nake ji sam bana buƙatar ko jin muryarsa inaso ya kyaleni na huta gaba ɗaya ko ƙarajin zancen sa ban yi ba na katse wayata da ko sallama ban yi masa ba yana zancen muhimmanci sa a tare dani wanda ta yiyu nama fisa sani danni mahaifina ba kalar nashi uban ba ne, ya zamarmin dole ma na yarda da Jurayd na yi auren ko zan samu wani raguwar wasu lamuran kirana ya sake yi saida ta katse dan kanta na juya kai na kwanta ƙarar message na ji ban duba ba na gogeshi na kashe wayar ma gaba ɗaya da wannan hanyar nake tunanin zan rabu da Yaya Samir kar na janyowa mahaifina ƙarin wani tozarcin in na janyo masa wazai fiddasa sai dai ubangiji amma ya ce tashi na taimake ka na sani inasan Yaya Samir tun kafin na san kaina har zuwa yanzu yana da muhimmanci a zuciya ta da sauran ƴan uwana ba suda shi yana da niyyar taimako gareni sai dai matsalar tana wajen mahaifinsa baya san Abbah ni ma ya zamarmin dole na san muhimmancin Abbah har wajen shi kanshi Samir ɗin saboda mahaifinsa ciwan kan da yazamar min jiki da shi na kwana a yau ma

"Ba dai fita zaka yi ba Abbahn Ahmad ka manta da wahalar da kasha jiya ne?"

Mama na jiyo tana faɗin haka da nake cikin kitchen ina ɗunɗuma tuwon da Na'im ƙanin Malika ya kawo mana yanzu ba daɗewa da har goman safe ta wuce mun yanke tsammanin za mu samu abincin yau ma

"To ya za ayi Hauwa'u haka yau ɗin ma zan fita ɗin amma keken Musa zan ara ina yawo da attaruhun unguwanni ko zan samu a siya na ji musan na cewa ana ciki, ya za a yi da ƙaddarar ubangiji zaman hakan ba zai yiyu ba ina tsoron ranar da haƙurinki zai ƙare ki tafi ki barni da yara nan suma sukasa haƙuri su faɗa harkar da bata da ce ba” tausayin Abbah ya kamani jiyo kalaman sa sai abu ɗaya da nake jinsa raina wai Abbah zai riƙa yawo da kayan miya unguwanni matsayinsa na ɗan boko mai ilimi Addini da na zamani na rasa wacce irin al'umma muke ciki da har taɓarɓarewar zumun cin ya kai haka ɗan uwa yana cikin wannan halin ba ka sani ba ko ka sani ka kasa taimakonsa saboda san zuciya da san kai dake da mun mutane masu ɗumbin yawa

Mama na sake jiyo tana cewa” Dan Allah ka daina faɗar haka Abbahn Ahmad, kana karyarmin da zuciya, ka bari kuma kaci abinci mana, Sumayyah xoki kawo masa tuwo in ya yi zafi”

Jin kiran da mama tayi min da abin da ta faɗa ya sani saurin cewa da ƙarfi yadda za ta jiyo duk da ba nisa tsakanin inda suke da kitchen ɗin"To Mama ganinan zuwa”

Kwano na ɗauka na ɗan ballomasa dan tuwon bana a zo a gani ba ne na zuba miya na na rufe na fito a ɗaki na same su shida mama suna fira na aje ma Abbah tuwon na fito

Abincin ba inda ya je mana da muka zuba muka ci gaba ɗaya tare saboda rashin yawanshi, Ahmad yana siɗar hannu ya kalle ni” wallahi Yaya Sumayya ba inda tuwon nan ya je min kamar na ci babu nake sake ji, keni tasomin da wata azabar yunwar yayi”

Rumaisa ma ta ce” wallahi ni ma Yaya haka yunwar nan ta daren da na kwana da ita ban yi maganin ta ba bare ta yanzu" Ahmad ya kalleta "Aini gaskiya bara zan tafi na lodo abincina wallahi tun da ba masu ba mu masu ba mun da suka yarda ba su da shi” murmushi mai ciwo na yi na dubi Ahmad ba ni da hurumin hanashi dan ni ma son a samo a banin nake yi dan zuwa yanzu ban da taimakon Ubangiji abin da ya fi ulcer za a samemu da shi sai dai Ubangiji baya haɗa ma biyu na ce "to ku tafi da Sadiƙ da Khadijah mu dai muyi aikin gida idan ansamu shike nan"Ahmad ya miƙe yana faɗin "wallahi Yaya ana samu ma su fa mukhtar shi suke yi mamarsu ke cewa suje suyo su samo musu, bari na faɗa wa Mama Abbah ma na san bai kai ga fita” kai na iya ɗaga masa kawai yarda cikina ya wani murɗa wannan abincin ai yunwa ya ƙaramin ma bakomai ba na ayyana hakan a raina dakyar na lallaɓa na koma ɗaki na kwanta ina kukan zuci da na san ubangiji bai manta mu ba, zai kawo mana ɗauki da izinin ubangiji banji tafiyar su Ahmad ba saboda barcin wahalar da na yi hayaniyar su da na ji ya sa na buɗe idanu na kallesu abincin da suka samo Rumaisa take kasaftawa a nan na tabbatar harsun dawo kuma sun yi sa'ar samowa amma banasan mu dauwama a bara sana'ar dai ta awarar da safe da Ahmad ya faɗa za mu fara ga jarin ta yamma da mukeyi ai ba batun neman wani jari mu jima da yawan da kayan miyar da Abbah zai fara yi a keke da na san ƴan uwan Abbah lokacin za su zuba ruwa a ƙasa su sha amma Alhamdulillah halak ɗinsa yake nema abincin da aka kasa na samu na sake ci kuma da yawa na samu Mama ma saida aka zuba mata muna ci Ahmad na ba mu labari yadda fitarsu ta ka sance

"Ai wato na ba ku labari nafi su Sadiƙ samu wani gida na samu na shiga ina barar aka kirani matar gidan da ta ba ni ta ce na riƙa zuwa ina mata aike aike da wanke wanke mai mutumci ai kin ga yawon abincin da na zo da shi Rumaisah" faɗin Ahmad, Rumaisah kai ta ɗaga tare da cewa” Eh Yaya Ahmad harma mamaki na yi, na ga kafi su Khadijah samu" Ahmad ya ce” ai matar tana da kirki ne sosai har tambayoyi ta fara min ni dai ban sake mata na bata amsa ba”, ni dai nake zuba lomar tuwo mai daɗi na shinkafa miyar ganye murmushin farin ciki na shiga yi jin aikin da Ahmad ya samu a gidan na san abinci mai daɗi daidai gwargwado za mu samu ko ba yawa da mu ɗin a samu asa farin maggi da gishiri ma, Mama da ta tarar da zancen ita ma ta goyi bayan hakan.

Na Cancanta (Kashi na 30)

Bayan wasu kwanaki a yanzu al'amuran sun soma sauƙi zan iya cewa dan mun fara sana'ar awara da safe da har gida ake zuwa siya ana gama soyawa a siyo wake a jiƙa na yin yamma ke nan, bawai dan riba mukeyi ba dan muke cinye ribar dan cinikin Abbah na attaruhun ba wani a zo a gani ba ne ba bare ayi maganar riba a tsakanin Abbah da Mama ban san waye ya fi rama ba ga Mama na shayarwa al'amuran dai suna tafiya da godiyar Allah kawai, Yaya Samir a yanzu ko wayarshi bana ɗagawa kwana biyu dan wayarma bana wani yawan kunnata saboda caji, babu yadda na iya da takurar Malika takemin na amince da soyayyar Juraid tun a washe garin ranar ba laifi yana zuwa wajena kuma duk ya zo zai ba ni ɗan wani abu wannan ya ƙara sa Jurayd matsayi a zuciya ta saboda inada buƙatar tallafin ko da da Naira Ashirin ce duba da ni a matsayina na budurwa, sai dai wasu sunfi ganin rashin cancanta ta da hakan, baya ga wannan Juraid mutumin kirki ne matuƙa fiye da yadda na yi tsammani, bara kuwa duk ranar da babu ita ƙannena ke zuwa ni ce dai ban taɓa zuwa ba, aikin da Ahmad ke yi wa Hajiyar da yasamu yana samo abinci har ya rage mana, wanke wanke da shara da ƴan aikace aikace yake mata shi ma sai da yamma saboda makaranta sai weekend yana zuwa da safe ba kuma a wata tana ɗan bashi wani abu ina yabawa halayyar matar dan jinake ina ma ni ce nake aikinnan ganinake zanfi Ahmad samu

A tsaye nake ƙofar gidanmu da yammaci nida Juraid dawowarmu islamiyya ke nan ya tsaida ni kallona yake yi kamar ba zai bari ba hakan ya sa na yi ƙasa da kaina dariya kaɗan ya yi kafin ya ce” Sumy ƴammatana kin yi kyau"murmushi na yi masa na ce” kyau kuma fa Jurayd daga fa islamiyya na dawo fa ba komai fuskata, bari dai na shiga ma kar Mama ta yi min faɗa” kallona ya sake yi” ok namanta za ki fito da awara ko, zan jira ki ni yau zan tayaki suyar awarar ma” murmushi kawai na yi masa na ce” toh Allah ya kaimu lfy" daganan na shige gida da sallama Mama dake zaune saman tabarmah a tsakar gidan tana yanka awara ta amsa sallamar tawa ta ɗaura da cewa” ai na yi tunanin ba zai kyaleki haka kiƙarasa kawo lada gida ba” murmushi na saki dan batun Jurayd takemin da nake jin daɗin ayi min zancensa yadda ya kamata ɗakinmu nake ƙoƙarin wucewa ina tafiya ina cewa "Haba Mama bahaka ba ne, yanzu dai bari na ajiye jakata na sauya hijabi na zo na fita suyar awarar kar Malika ta rigani tayi min gori” mama ta ce” badai kin tsaya soyayya ba ke” murmushi na yi kawai na ƙara sa shiga ɗakinmu abin da na yi niyyar yi na aiwatar na fito da na tarar ƙannena sun fidda komai sai ni ya rage na fita awarar ma Rumaisa na ji Mama ta kira ta zo ta ɗauka yadda mu kayi da Jurayd ina fita na sameshi a kan Lifan ɗinsa yana zaune, kusa da inda nake zama, murmushi na saki ganinshi dan ko inasan Jurayd abin ba acewa komai yana da abin da za asoshi danshi ɗin kirki ga natsuwa da wayewar rayuwa ina zama Malika ita ma ta ƙara so da ita ma yau anyi sa'ar ta, ta fito da wuri dan ko fitowata har na tarar an haɗa wuta, kallonta na yi nace” yau basa ban ba” hararata tayi” zan dungureki Allah saboda munfi to tare kike maganar ke ban da ma taimakon ƙannan naki basai kinkai magrib ba ki fito ba, kin yi saurayi mai na ci ai Abbah ina jin saiya fara rakashi da bulala” sai da ta kai ayarta Jurayd ya yi gyaran murya daganan ya ce "bama za a kai ga haka ba ai aurenmu zamuyi” Malika kai ta ɗago "Au wai dama kana nan dama gaba ɗaya hankalina baikai gare ka ba” murmushi ya yi ya ce” ai dama na ga alamar hakan"Ni ko dariya na yi ma Malika hararata ta yi tace” Malama ni kikewa dariya ko?"na murmusa na ce” yi hakuri ƙawata” dukkanmu kasko muka ɗaura a tare dan ni ma wutar da Rumaisa ta haɗo na fifita ta kama sosai muna ci gaba da firarmu da yau harda Juraid dan ya ce sai fa mungama zai tafi kiran sallahr magriba ya tayar da shi ya ce mana bari ya je ya dawo sannan muma ƴan siyan awara da dankali sun fara zuwa an aje firar

Sallamar Jurayd tasa na ɗago kaina na dubeshi muka amsa masa, saman machine ɗinsa ya sake hayewa da har lokacin idona na kansa na ce” ai ban yi tunanin za ka dawo yanzu ba?, ɗauka ta za ka koma ta gida ku dawo da Alhassan?"ya ce "A'a zai nemeni ma bare ma yasan inanan ɗin, yawwa ina hanya na tuno da maganar makarantar da kika cemin za ki koma na ji shiru?"shiru na ɗan yi kafin cikin raunin murya na ce” ai ba muyi maganar da Abbah ba sai gaba kaɗan"Malika ta kalle ni ta ce” gaba kuma wacce gaban kuma gashinan mu muna shirin fara Wa'ec ma kina maganar gaba Allah ya taimaki mashiririciya” harararta na yi nace” to dake ake magana ne wai?"ta ce” Allah ya baki haƙuri” maganar da na yi niyyar sake faɗa mata Jurayd ya riga ni yin magana” Please ki daure ki masa maganar ni in abun zai zama shiririta zan kaiki da kaina bakisan yadda na ƙosa ki koma ba, ina son ba da jimawa ba na turo iyayena gidanku na san za ki ce kuma saikin gama karatu za ki yi aure?"tun da ya fara maganar gaba na yake faɗuwa har ya gama tunani na shiga yi ta ina abun zai fara ne, me zai faru a Mu'amalarmu da Jurayd nan gaba, girgiza min kafaɗa da na ji anyi ya sani firgigit na dawo hayyacina a firgice nakai kallona ga Malika da itan ta girgiza ni a hankali na ji ta furtamin"lafiyarki kuwa Sumayyah?, tunanin me haka kike ƙoƙarin shiga?, Jurayd yana ta magana” a hankali na ɗago na kalleshi ni ma ya kalle ni ban yi tunanin har ya sake wata maganar ba bayan wadda ya yi na tsinci kaina a tunanin"kodai auren ne bakyaso?, ko nine bakya so ne Sumayyah?, ko kinada wani muradin ne daban daban sanshi ba?"Jurayd da yana yin damuwa yake jeromin wannan tanbayoyin, ƙasa na sake yi da kaina ina juya awara da na yi sa'ar bata soye ba” tambayar ki fa nake yi?"na sake jiyo amon muryarshi har kaina na ji maganar saboda yadda yana yin nawa ya juye a wannan lokacin saboda gudun kar ya fahimta wani abun bayan wanda yake ƙoƙarin fahimta na furta” babu komai karatuna nake tunowa gashi ƙawayena har za su yi graduation"ina yanka zancen da dagaji ba alamun gaskiya ni dai a zuciya ta banji maganar ta yi daidai ba, kallonsa na ɗago na yi har da murmushinsa na alamun ya yarda na ji sa yana cewa” Ai babu komai Sumayya haka ubangiji ya tsara, zan baki kuɗi ki yanko uniform ma, idan kun yi maganar da Abbah saboda na san ba shida kuɗi a wannan yana yin dai, na san ƙila abun ya sake shiriricewa ma idan ban shiga maganar ba” ɗaya daga cikin abunda ke ƙaramin son Jurayd ke nan mutum ne mai fahimta yasan halin da muke ciki a gidanmu duk da ba zancen na taɓa masa ba, mu'amalarmu da ƴan uwan Abbah bana ji ya sani ko ya fahimci wani abun yana ƙoƙarin yi min abunda baifi ƙarfinsa ba a duka abunda bai yi wata ɗaya da fara soyayyarmu ba idan na ce ba zan amsa ba sai ya ce ai a matsayin ƙanwarshi ya ɗaukeni shi ya sa ya ba ni ɗin, Abbah ba dan ranshi naso yake yarda da kyautar ba sai dan bashi da shi ne yana yawan faɗa mana ni da Mama shi tsoron kyautar namiji wajen ɗiya mace yake yi wasu ba dan Allah sukeyi ba duba da yadda zamani ya canza haka firarmu ta ka sance da Jurayd da jefe jefi Malika kan saka baki ko Jurayd ya ambaceta a firar tamu, har lokacin sallar isha'i ta yi ya miƙe ya je ya dawo ya na dawowa bai jima da zama ba Alhassan da Yaya Nasir yayan Malika suka zo wajen da muma lokacin gaf muke da ƙara sa suyar dan ana yin isha'i muke tashi dan ko muna samun ciniki sosai muka ɗai ne a layinmu muke awarar saɓanin wasu unguwannin ko wasu layukan Yaya Nasir ne ya siya musu sauran awarar da dankalin Jurayd da ya kasa tafiya ah lallai sai na haɗa kaya na tafi gida ina miƙawa yaya Nasir awarar Jurayd ya ce "Malam Nasir kufa ragemin tawa” tsaki yaya Nasir yaja” toh yayanmu ko ɓalli bata raguwa soyayyah ta ƙosar da kai” Alhassan ya ce” dan Allah Nasir kyaleshi kai ka kula ɗan rainin wayau shi lallai Romeo ai, ba ka ga neman da na masa ba a yau ɗin nan ashe yananan lafe” ganin za su tafi su cinye awararsu ya sa Juraid miƙewa da ga kan machine ɗin sa ya buga shi ya tayar yana furta "zakuga iskanci ni a machine ma zan buga na tafi inda za ku je cin awarar"tsaki Alhassan ya yi ya na cewa” saifa mun yi niyya zamuje inda kake tunanin, da dai ka zauna kasha soyayyahr kasha ruwa ka tashi kwanciya dan yau tuwo akeyi a gidan"da haka suka tutse su uku a lifan ɗin suka bar wajen Malika ta waigo ta kalle ni tana dariya tace” saurayin wata yarone sai gaɓunta ya iya” harararta na yi nace” naji ai nafi mai ƙarar samarin da tsoho za ta aura ma ƙila a ƙarshe” ina dariya na tashi na fara haɗa kayana dan ko na san na ƙular da Malika aiko nan ta fara masifa ni Ko dariya nake ƙunshewa har na gama haɗa kayan na ɗiba wasu na kai gida ban da Ahmad na sake fitowa ya ƙara sa kwashemin ina dariya na kalli Malika da har yanzu bata ƙara sa kwashe kayan ba” sai da safe Madam Malika, Ahmad ka taya ta kwashe kayan"na yi maganar ina jin wata dariyar ta zo min, "za ki san dani kikeyi zan zo har gida na bawa Mama labari kina neman gogemin harda” cewar Malika da ta kwashi kaya fuu tana gama maganarta Ahmad ya ce” tofa Yaya mai kika ma sahibar taki” tsaki na yi nace” bari kawai Ahmad Juraid ta cewa yaro shi ne daga namata batun tsoho ƙila za ta aura shi ne fa taji haushi na take ta masifa ka san dai Malika” dariya Ahmad ya yi ya ce” kunfi kusa bari naje nakai mata kayan kar tayi min masifar ni ma” banjira dawowar Ahmad daga kai kayan ba na shige gida.

Shigowar Abbah da na ji sallamarsa ya sani miƙewa na bi bayanshi dan kar na sake mantawa da maganar makarantar da muka gama da Jurayd dan na san Mama tausayin Abbah zataji shi ya sa ta kasa maganar ƙofar ɗakin Mama da na hango hasken fitila da na san Abbah na ciki a nan na tsaya na gabatar da Sallamata Abbahne na ji ya amsa min hakan ya sa na shiga sannu da zuwa na yi masa ya amsa min shiru na yi ba tare da na furta komai ba

"Kin shigo kin yi shiru ?ko Mamanku kike nema?, ai tana kitchen"Abbah ya yi maganar yana sake kallona kai na girgiza na ce” A'a Abbah dama maganar makarantar zan yima na ji ance ana komawa SS2"na yi maganar da ina ƙasa da kaina saboda kunyar da na ji ta zomin dan ganin kamar ina ƙoƙarin matsanta masa duba da yana yin da muke ciki ban san da ya zai ƙarɓi zancen ba, muryar Abba na ji yana cewa” kiramin mamarku"miƙewa na yi daga tsugunnen danake kusa da Abbahn na fito daga ɗakin na shige kitchen Mama na kira har zan fito ta kalle ni "kiran me kikaji Abbahn naku na yi min" na furta "wallahi ban sani ba, nadai yimasa maganar makaranta ɗazu Jurayd ya sakemin maganar ya ce ma zai yi min uniform ɗin ma” kallon tuhuma Mama ta yi min kafin ta ce” roƙonsa kikayi ke nan?, kin san Abbanku bayasan wannan ɗawainiyar da yaronnan ya fara yimiki, so kike ya riƙa ganin laifina ko Sumayya?"kai na girgiza na ce wallahi Mama ba haka ba ne ba ban taɓa roƙon Jurayd ba ya ce gani ya yi lokaci naja” miƙewa mama ta yi ba tare da ta kulani ba saida za ta fice na ji tana cewa” ki zauna ki ƙara sa girkin inma tambayar kikayi dai keta shafa nidai baruwana” bata jira cewa ta ba ta fice abin da ake dafawar na buɗe taliya na gani da ba za ta wuce guda ɗaya ba a tukunya, hawaye na goge dan ita ce za mu ci a daren mu tarfata a hannu a hannu saima an gama za a tashi sauran ƙannena da har sungaji da jiran abinci sun haƙura sun yi barci. NA CANCANTA!

Na Cancanta (Kashi na 31)

Ban san yarda Mama sukayi da Abbah ba sai washe garin ranar da safe na kammala wanke wanke gidan ya rage dagani sai Mama inda Mama take kwance a tsakar gidan na nufa ina riƙe cikina na zauna mama ta dube ni

"Lafiya kuwa Sumayyah?"

Hawaye na ji suna ƙoƙarin zubo min da in ban manta ba tun abincin jiya da daddare ban ƙara sa komai cikina ba sai awara guda uku da ba inda tajemin yau kuɗin siyo kokonma sun gagara hawayen na ji sun zobomin, mama tsawa ta dokamin

"Wai ke lafiya?, ina tambayarki ko baki da baki ne?"hawaye na share na dubi Mama na ce” Mama yunwa nake ji kamar zanci babu"tsaki Maman ta yi "to kici babun mana, tun da kinfini jin yunwar ai, kuma ba kinci awara ba ɗazu?"

Kai na girgiza” Wallahi Mama banci ba sai wadda aka ba mu uku ukun nan"

Tsaki Mama tayi” To ina laifi Sumayyah iya abin da ya samu ke nan, ki daina ƙoƙarin tayarmin da hankali, ƙirjina ciwo yake yi”

Bani da yadda na iya na tashi kamar na faɗi saboda yunwa Abbah na gani ƙofar ɗaki tsaye kamar an kafasa kallonsa na yi da alamun tausayawa ya rame ya rame sai idanu da hanci kawai har zan wuce na ji muryarshi a cikin kunnena

"Ki shirya ranar Monday zan kaiki makaranta”, duk da na san ba iya wannan maganar bace bakin Abbah dan inada tabbacin sai Mama ta bashi labarin Jurayd ya ce zai yi min uniform da Abbah na san sai ya nuna ɓacin rai akaina yadda nake bari Jurayd na yi min hidima, da dan ya kwantar min da hankali yaƙi yin zancen dan na san yaji duk firarmu da Mama "toh Abbah" na bisa da shi na ja ƙafafuna da kyar zuwa ɗakinmu kwanciya na yi a saman yaloluwar katifarmu kwanciyar kasa yi min daɗi ta yi sai juye juye cikina kuka yake hannuna rawa yake yi kamar zanci babu in samu kwarin da zan iya fita ko barar na yi makwafta na samu ta gagara ban san tsawan lokacin da na ɗauka a haka ba har barci ya kwashe ni yunwa ce da ta taso min fiye da ko yaushe, cikin barci na ji ana kiran sunana a hankali na shiga buɗe idanuna na saukesu tas a kan Ahmad da yake gefena a tsaye murmushi yayi min yunƙurawa na yi dakyar na tashi na jingina da bango ina sake kallon Ahmad

"Ahmad lafiya kuwa ba dai an taso makarantar ba?"na ƙarasa maganar ina kallonshi

Kai ya girgiza min"A'a break aka yi mana saina biya gidan Aunty dama ta ce naje kin gani abinci ta ba ni ma, ina zuwa Mama ta ce kina kururuwar yunwa ɗazu na zo na kawo miki "

Sai lokacin da ya yi maganar na ga kular dake riƙe hannunshi gidan da Ahmad ke aiki matar na sanshi sosai kamar ɗan ta yadda yaran ta ke kiranta haka Ahmad yake kiranta shi ma dan kam yana ba mu labari, murmushi na yi

"Amma kaifa Ahmad?, Mama ma yunwa takeji na san ga Abbah da zai fita”

Kai Ahmad ya girgiza” Kin ga ki aje lissafinnan ni da Abbah mazane Mama kuma ta fiki juriya, inkin ƙoshi ki rage mata a yanzu munfi buƙatar ingantar rayuwarki a kan tamu ai Yaya, in kin gama ci dama saiki kai mata kular kin ga zan makara idan zan koma kai mata ai za ki gane kwatancen gidan Please”

Kai na ɗaga ba tare da na sake cewa komai ba har Ahmad ya ajiye kular ya fita na san gaskiya Ahmad ya faɗa dan kam batun hankali gurin Ahmad har ya fini Ka sancewarsa namiji kuma Allah ya sa dai mai hankali ɗin ne buɗe kular da ya aje gabana na yi ƙamshin abincin yafara shiga hancina shinkafa da miya ce tasha kifi tun kafin na fara ci nake haɗiyar yawu dan yaushe rabona daganin irinta ai ko a makwafta ma namanta rabon in ganta duk da ɗin ba makwabtan nake shiga ba sai da na ci na ƙoshi na fito na miƙewa mama sauran da inda take na same ta tana jijjiga A'isha da ita ma ba wani girman da ta yi dan ko ta kusa wata biyu a yanzu ma, inda na hango buta na nufa na jiyo Mama na cewa

"Ba dai harkin ƙoshi ba?"

Ba tare da na furta komai ba na ƙarasa wajen butar na yi sa'a da ruwa na wanke baki da hannuna na sha ruwa na dawo kusa da Mama na zauna ganin ta aje abincin na dubeta

"Mama kin ƙoshi ne?, Ahmad ya ce fa nakaima Auntyn kular in na gama”

"Ba yanzu ai zanci ba ɗauko guri ki juye ai da ragowar omo ko?"cewar Mama

Na bata amsa da "Eh mama akwai” daganan na miƙe kwano na ɗauko na juye na ɗauki kular na wanke sosai, ɗaki na shiga na lalubo hijabi cikin kayan wanki da baicika dauɗa ba nasa na fito tsakar gidan da har lokacin Mama tana nan na ɗauki kular

"Yawwa Mama bari naje gidan Auntyn Ahmad dai yau dama ina tasan zuwa ne”

Mama tabini” toh dashike nan ki gaisheta, a dawo lafiya” na bita da "Amin"

Daganan na fice da tuno kwatance da Ahmad ya yi mana na gidan tuntuni na isa gidan da baida wani nisa da namu, gidane mai kyau tun daga ƙofar gidan tura ƙofar dake jikin gate ɗin na yi na yi sa'a buɗe take na shiga tun a farfajiyar gidan na fara sallama har da ba lallai ajini ba ƙaton gidane upstairs dan a tsarin gidan da kyansa tun daga wajen yaso ya fi na Aunty Asmau ni dai mamaki nake dama irin wannan gidan Ahmad yake aiki nidai bai taɓa ba ni labari ba ka sancewar zuwa na ne na farko gidan na rasa inda zan lalubo kofar shiga cikin gidan haka na shiga dube dube sai daga baya na samu ƙofar, duk da Ahmad yake ba mu labarin kirkinta saida na ji zuciyata ta tsinke da na tura ƙofar shiga cikin gidan sallama na gabatar a ƙaton falon da yake ɗauke da manyan kujeru sai ƙamshi da ke tashi ga karatun Alƙur'an a Tv ɗin bango da yake tashi a hankali shiru na ji kamar babu kowa wata sallamar na ƙara yi jin na yi uku shiru ya sani ƙoƙarin buɗe ƙofar falon na fifa ganin ko ni ce ban gane kwatancen ba tun da ya daɗe da yi mana yauko yana sauri ya so makara komawa break baiyi min wani ba

"Wa'alaikumussalam warahmatullah wa barakatouhou, ya za ki koma kuma?"

Sakin handling na ƙofar da na kama na yi na juyo fuskata murmushi matar ta yi min kyakkyawace Masha Allah na faɗa haka a raina, da doguwar rigar atamfa a jikinta sai ɗan kwalin da ta rufawa kanta ba tare da ta ɗaura ba da gashinta ya zubo har kafaɗa, a ƙiyasina Auntyn za ta yi kamar Mama saidai ita hutu ya zauna mata ba za ka fahimta hakan ba sai dan ƙibar da take da duk da ba ta a zo a gani bace

"Shigo mana ciki, ina kitchen ne ban jiyo sallamar da wuri ba”

Firgigit na yi na saita kaina jin maganarta a cikin kunnena yarda ta faɗa na yi na ƙarasa shiga ciki gaisheta na fara yi kafin na zauna kujerar

"A'a ki zauna mana saimu gaisa, ga kujera nan"tayi maganar da murmushi fuskarta tana nuna min kujera

Zama na yi ita ma ta zauna kujerar da ke kallon wadda na zauna remote ta ɗauka ta kashe volume

"Saboda magana gwara a ƙarasa cire volume”

Murmushi na yi jin maganarta ta daga nan na furta” Ina kwana Aunty"

Da fara'a fuskarta ta amsa min "lafiya Alhamdulillah ƴammata”

kular na fiddo daga cikin hijabi na ajiye a ƙasan carfet

"Aunty ga kular nan Ahmad ya ce lokacin break ya wuce kada ya makara shi ne ya sa na kawo miki”

Murmushi ta yi da na san sai yanzu ta ganeni ma dan ba wata kama na cikayi da Ahmad ba, Maganar ta ta katse tunanin da nake shirin faɗawa

"Allah sarki Ahmad da ya bari saida ya taso ma ya kawo koma yaushe ai, ke yayarsa ce ko ƙanwarsa”

Kaina a ƙasa na ce” Eh ni yayarsa ce”

"Oh Sumayyah ko? ina jinsa da shi da Jabir da Muhammad in yana ba su labarin ku"

Murmushi na yi na ce” Eh nice” Daga faɗin hakan na miƙe

Kallona ta yi "Ba dai tafiya ba, ki zauna mana na sauya miki tasha ki yi kallo"

Na yi saurin girgiza kai” ai ban faɗa wa Mamarmu zan daɗe ba”

"Duk da hakan ai tasan inda kika taho, kin yi candy ne?"

Na girgiza kai” Abbah zai yi faɗa, a'a ina SS2"

"Insha Allahu ba zai yi ba, amma ya akai baki je ki school ɗin yau ba”

Shiru na yi na rasa mai zance mata

Murmushi ta yi ta tsaida idonta akaina” Wato babu amsa ke nan ko kawai fashi kike ba dalili, yanzu karatu ya lalace shi ne kike tunanin Abbahnku zai yi faɗa idan ma zai yi saidai ko na fashin makaranta ita ma kuma mamarku zan zuge ta ta yi miki”

Murmushi na yi ni ma ɗin ba tare da na faɗa mata gaskiya ba ita ma bata damu da jin hakan ba ta ɗaura da wani maganar

"Allah ya taimaka a dage da karatu fashi ba shida anfani kin ji ko Sumayyah ana wuce mutum abin da ya fi da cewa ya sani”

Na amsa mata da "Amin insha Allahu zan daina Aunty"

Lallaɓa ni Auntyn ta ciga dayi dole saina zauna zuwa wani lokacin tun da banje makaranta ba yau ba yarda na iya haka na zauna, ganin har roƙo na take yi babba kamar Mamata na roƙona ya sa ni haƙuri da tafiyar na san Mama da Abba in suka ji ba za suce komai ba, fira muka ci gaba dayi ta sauya min tasha zuwa Bollywood, da ta yi saurin shiga raina Auntyn tamkar na saba da ita gata da san fira ko ba ka amsa mata indai za ka jita za ta yi maganarta

"Subhanallah girki fa nake yi, za a kaima Muhammad ɗan rikici ina zuwa” ta miƙe da hanzarin ta wata hanya na ga ta nufa na bita da murmushi kallon da nake na ci gaba dayi tana da kirki a zuwana na farko gidan na tabbatar da zancen Ahmad ban yi tsammanin akwai masu kirki guri kusa ba acikin masu arziƙi ba na ƙara cirewa kaina wannan tunanin tun da gashi na haɗu dasu, na yarda mutanan kirki sune 90%da suka daidaitar da rayuwartamu ko a haka ɗin sai dai ta yiyu munada tazara dasu a yayinda mafi kusancin a tare damu suka ka sance a cikin 10%na mara sa kirki da suka fitinar da tamu zuciyar da dukkan burikanmu da yaƙininmu

"Sumayyah!, Sumayyah!!" Na jiyo sama sama kamar Aunty na Kiran sunana hakan ya sa na dawo daga tunani na jin alamar kamar kiran na naje ne na yi saurin miƙewa na bi hanyar da na ga tabi hangota na yi ta ƙofar kitchen ɗin tana ƙoƙarin sauke tukunyar dake saman gass ɗin sallama na yi ba tare da ta amsa min ba

"Yawwa ɗaukomin kular da kika dawo da ita, ki yi sauri Please”

"Toh"nace cikin hanzari na koma falon na ɗauko na miƙa mata

Murmushi ta yi "Yawwa thank you kular Muhammad ce shi ya sa na ce Ahmad ya dawo da ita sai bayan ya tafi na tuna ta Jabir tana nan ma, dan da bata ɗin haka zai dawo da abincin indai ba anashi flask ɗin aka zuba masa ba Muhammad akwai tsari”

Murmushi na yi kawai ba tare da na furta komai ba jallop ɗin taliya da take ƙamshi da ganin ta taji kifi na gani da ta buɗe tukunyar falon na koma na ci gaba da kallon Bollywood ɗin da na keyi

"Yawwa na gama da wannan ɗan rikicin Alhamdulillah"jin maganar Auntyn na ɗago daga kallon ina kallonta riƙe take da ƙaton basket an zuge zib ɗinsa ta ƙara so ta zauna inda ta tashi

Ta ci gaba da cewa” shi ne Autana Muhammad ɗin ne kin ga hotonmu nan"

Inda ta nuna na tsaida idona kai ƙaton frame ne da hankali baiyi wajen ba sun yi kyau a hoton su huɗu ne a jiki ita da mijinta sai yaranta biyu dagani babu tambaya kamar da na gani a hoton yaran duk da iyayensu suke kama duk sun ɗauko iyayen nasu muryarta ta ka tsaneni

"Ni da Abbahnsu ne sai gefe Jabir ɗaya gefen Muhammad da gashi ban sake haihuwa ba amma inasan yara musamman mata ma, su zama kamar ƙawayena, suko suna wajen babansu, Jabir na JS 3 sai Muhammad primary 5"

Ba tare da na san me zan ce na yi ƙoƙarin furta” Allah ya yi musu albarka, kun yi kama dasu "

Ta furta "Amin Abbahnsu na cewa muna kama na ce masa wayyo kawai yake min amma ya ce Muhammad munfi kama ma”

Kallon frame ɗin na ƙarayi suna kama amma dai sun biyo Aunty ɗin da Abbahnsu ba wanda ya biyo ɓangare ɗaya kaɗai hakan ya sa suka ƙara yin kyau Masha Allah muryarta ta katseni

"Haka ne muna kama ko?"

Na ɗaga kai murmushi ta yi "yawwa thank you, yawwa Sumayya na tambaye ki mana?"

Na ce "ina jinki Aunty"

Ƙarar wayarta ya sa ta sakin zancen ta ɗauki wayar dake saman hannun kujerar da take zaune, wayar ta ɗauka banji me akace ba na ji dai ta furta "toh" ta aje wayar tata

"Sorry ɗan rigimar ne za azo amsar abincinsa, mu ci gaba da magana dama muryar ki ce na ji tana kama da ta wata friend nawa a secondary school, sai kamar da kuke a fisge ban sani ba ko kuna da alaƙa ne”

Mamaki ya cikani ganin ban taɓa ji wani ya ce muryata nakama da ta kowa ba saidai a fuska ana cewa ina kama da Aunty Asmau

Maganarta ta katse min tunanina "Kinyi shiru sosai yana yinki da kamanni da murya komaima zance copy ɗin Hauwa'u Ibrahim Alhassan tare muka fara tun da makaranta primary zuwa secondary saida aka kaini Federal College Bakori SS1 muka rabu bayan na kammala na koma Kaduna na yi karatu gidan Aunty na sai aure da ya dawo dani gida ko labarinta ma banaji sai kwanaki da na tuno na tanbayi wata class mate ɗin mu ta ce min tana nan tana cikin garin Kano da zama da mijinta "

Ba wani kokonto Mama take nufi na yi murmushi

"Na cika surutu ko?, shi ya sa kin yi shiru"

Na girgiza kai

"To maiyasa kikayi shiru ko don baki saba dani ba ne”

Na sake girgiza kai na yi ƙoƙarin yin magana

"A'a Aunty kawai dama mamarmu ita ma haka ne sunanta, to ina tunanin ko Mama ɗin ce”

Da mamaki take kallona ta nuna ni” ba ma ƙoƙonto Sumayyah tun farkon shigowarki kamar zan kiraki da Hauwa'u sai na kalli yana yin ƙuruciyarki abin ya ba ni ko ke ƴar uwar tace, saboda kallon shekarun nake kamar yau ne ban yi tsammanin Hauwa'u za ta haifi kamarki ba shi ya sa tunanin bai kaini can ba, duk da cewar tun zuwan Ahmad na farko nake kallon kamarshi da ita amma saina shiga mamaki maiya haɗa yaran Hauwa'u da bara duk da na san canjin rayuwa amma an faɗa min a gidan da take aure” da raunin murya na mai shirin kuka ta ƙara sa zancen nata

Murmushi na yi nace” Aunty mamarmu ce . . . . "

Inda nake ta yi saurin tasowa ta dawo kafin na ƙara sa maganar rungumeni ta yi tare da fashewa da kuka cikin kukan take magana” yanzu ni Rumaisa ina raye na watsar da zumun cina tsakanina da Hauwa'u har yakai ga kuna bara, ina ganin Ahmad na ji tausayinshi ya ratsar min raina na ji sa tamkar Jabir ban kyauta ba sam Sumayyah"kuka ta fashe da shi ni ɗin ma da nake jinsa tuni a raina na rasa waye zai zama abokin kukan nawa jin tana wannan surutan ya sa ni fashewa da kuka a zahiri na san ba muda alaƙa ta kusa ko ta nesa da Aunty haɗuwar makaranta ce harta zamo tafi wanda muke kusa a dangin mahaifinmu tausayinmu da tausayin Mama kafin akawo ga Abbah ni ce na taƙaita da kukan na fara ƙoƙarin zame jikina daga na Auntyn na yi dauriyar cewa

"Aunty muna lafiya fa dan Allah ki bar kukan"

Girgiza kai ta yi cikin kukan"A'a Sumayyah bakwa lafiya bara fa Ahmad ya zo yi gidannan a nan na haɗu dashi, na jima ina mafarkin Hauwa'u ashe ba haɗuwa ta samu rayuwa kalar tawa ko fiye da tawa ba. . . . . "bata ƙara sa maganar ba ta sake fashewa da kuka

"Dan Allah Aunty ki daina kuka Mama tana lafiya” na yi maganar ina ƙasa dakaina jin kwallar da take shirin zubomin ina tunanin wasu abubuwan. . [7/19, 7:18 AM] Halimatu Ibrahim Khalil: NA CANCANTA!

Na

Halimatu Khalil

Ayi afuwa in a kwana biyu anjini shiru abin ƴar koyo ne

Na Cancanta (Kashi na 32)

Aunty kiran mijinta ta shiga yi a waya lallai ya taimaka ya barta taje taga Mama bai hanata ba hakan ya sa harta abincin Muhammad ta ajiye sa muka fito ta rufo gidan

 Sallama ɗauke da bakinmu tun daga zauren gidan namu har zuwa ciki daga cikin ɗaki nake jiyo Muryar Mama tana amsa sallamar tamu tana mai leƙowa kofar ɗaki, Aunty ce ta yi wajenta da saurinta ta ƙara sa wajen Mama rungume Maman ta yi da nake shaidar Maman har zuwa lokacin ba ta gama ganeta ba Aunty cikin kuka ta ɗago ta kalli Mama

"Hauwah kece haka kodai mai kama da ke ce, na kasa fahimtar komai, sauyawarki ta yi yawa”

Cikin karayar zuciya Mama na ji tana magana” Rumaisah dama zan sake ganin ki tsawan yawan shekarun da ba ma tare”

Auntyn ce ta saki Mama tana goge hawayenta cikin alamun wacce ta yi kuka muryarta da ta nuna

"Ba kya nemana ne Hauwah kina cikin wannan halin har bara Ahmad yake yi baki nemeni ba, ni ce kullum na haɗu da ƙawaye nake tambayarki ban san kun dawo gida ba ban san rayuwar ta tuƙe muku har haka ba ban yi tsammani ko a mafarki za ki yi wannan rayuwar ba” tana maganar tana ci gaba da goge hawayenta ni ma da nake tsaye kamar an da sani a gefensu hawayen nake ji da karayar zuciya

"Kin tsaya kallonmu ki mana shimfiɗa mana” Mama ce tayi min maganar cikin sauri na wuce ta gefen Mama nashiga ɗakin maman na ɗauko tabarma na yi shimfiɗa

"Aunty ga shimfiɗa na yi ki zauna” na yi maganar cikin ladabi ina ƙasa da kaina zaman ta yi Mama ma ta zauna kusa da ita ni ɗin ma zama na yi gefensu daga ƙasa don banajin zan iya barin wajen ji nake kamar Aunty za ta zamar mana sanadiyyar samun sauƙin sauƙaƙar lamuran da sukayi tsamari garemu ji nake kamar za ta fitar damu daga wannan yana yin ji nake kamar Mama ta samu inda za ta yi kukanta a samar mata mafita ba kamar inta faɗa a gida ba iya haƙuri ne kawai za su bata suma ta kansu da rayuwarsu sukeyi tamkar matsi ne idan muka takura musu da faɗar halin yau da kullum da muke ciki, ban taɓa jin Mama ta ba mu labarin wata ƙawarta Rumaisa ba da har ƙawancensu yakai Mama ta sawa Rumaisa sunanta duk da banida tabbacin hakanne amma yanda zumun cin su yake nunawa hakan ne ya faru bana tantamar cewa Mama ganin bata da shi ya sa duk wasu ƙawayenta ma bata nuna mana su ba bata bibiyarsu suma kuma hakan saboda yanda yau da kullum mai wahala maganar Aunty ta katse min tunanina

"Sam baki kyauta ba na jima ina mafarkin ki na yima su Maryam Hashim maganar ki sosai duk inmun haɗu ko naje gidansu ko sunzo nawa sai suce min bakya yin zumun ci ko kinzo gari saidai suji labari na nemi lambarki suka cemin ba su da shi wallahi Hauwa na damu da jinki shiru ɗin nan ban sani ba ko dan haka nake mafarkinki”

Mama murmushi ta yi "nima na damu da rashinki tun da muka dawo nake san nemanki abubuwa suka zo suka cakuɗe shi ne dalilin da ya sa har nakai wannan lokacin ban nemeki ba”

"Amma ai a cakuɗewar abubuwan ya kamata ki nemeni ko zan rage miki wani abun amma ba a ce a sanadin barar ɗanki ba, da na hanashi kona koreshi ba, da har zuwa tuƙewar lamuran sufi nada ba za ki nemeni ba, mamakin da na sakeyi ma ancemin gidan surikanki kike kuma na ganki anan"Aunty ta yi maganar tana tsaida idan ta kan Mama

Mama ta yi ƙoƙarin maida kwallarta da take ƙoƙarin zubowa” sun koremu a gidan an kusa wata ɗaya ke nan"

"To me kuka yi musu mijin naki ba ɗan gidan ba ne”

Mama ta girgiza kai "Ko ɗaya amma korar ce mafi alkhairi ma a wajenmu. . . . . "

Nan Mama ta shiga bata labari a takaice na yi mamakin yarda Mama ta iya zaman ba da labarin rayuwar da muke ciki har haka sai dai ganin yadda taransu ya ka sance a baya da na fahimci ya fi nawa da na Halima ya sa na cirewa kaina mamaki domin kuwa abokin kuka ake faɗa wa mutuwa

Aunty ta jinjina kai "Waɗannan ko ba su san gamawa da duniya lafiya wanda zai wulaƙanta zumun ci har haka ai tikitin watsewar rayuwa ya ɗaukarma kansa amma Hauwa ki haƙura da auren ɗan uwan nasu mana kin ga yadda kika dawo kuwa, ki barsu da shi indai zai samu sauƙin wani abun daga garesu Allah ya san alkhairin da yin hakan zai haifar na miki alkawarin zan riƙeki da ke da yaranki ko da sunfi hakan nema, inasan yara musamman mata sai Allah ya ba ni maza kuma guda biyu duk da ban fidda rai ga samun wasun ba amma a yanzu biyunne”

Mama ta goge hawayenta da suke ci gaba da zubowa” Ban yi tsammanin za ki faɗi hakan ba Rumaisah, karki ƙoƙarin zama kamar su mana, kina ƙoƙarin canza hanyar da na san kina binta a baya shi ne dalilin da ya sa na kasa neman ɗaya daga cikinku saboda gudun abin da zai je ya dawo, bana so ku zama sanadin maishe dani da yarana marayu ƙarfi da yaji a kan ƙaddararmu"

Dafata Aunty ta yi "ki nutsu Hauwah, wannan shi ne maslaha a zaman ku ki dubeki a da ki dubeki a yanzu har gwara san da na sanki a da ɗin kin canza kin lalace haihuwa kikayi da bana tantamar cewa baki wanka na kwana 20 ba cikakke ba sun tsangameki sun tsaneki ki yi nazari ko iyayen mijin naki da sukayi hakan saboda ke sukayi ba wanda bayasan nashi shi namijine ke mace karki kashe kanki a sanadin kinasan ki yi masa halacci, halaccin shekara 18 ya isa haka ai”

Mama rai ɓace ta miƙe tana haɗe hannunta biyu"Rumaisah ya isa haka ki tashi ki barmin gida dan Allah indai maganar da za ta kawoki gidannan ke nan, ban yi tsammanin tsawan shekarun da ba ma tare za ki zo da makamancin wannan maganar ki kalli kanki idan kece a irin halin da nake ciki ke da kike da yara biyu ma na zo miki da kalar wannan maganar na san ba za ki yarda bare ni yara ɗaiɗai har shidda dangin mahaifinsu sun gaza tallafarsu bare kuma na yarda ke ɗin da kika fara kawo wannan maganar da babu alaƙa tsakaninmu yarda ƴan uwa suke kasa hakan ba yarda zan yi na yarda zumun cin ƙawance zai yi hakan, kinaso rayuwar yarana ta lalace matuƙa a dukkan lokacin da na zaɓi saki daga hannun mijina kawai ba tare da ƙwakƙwaran dalili ba saina talauci shi ɗin da ya haƙura da hatta iyayenshi saboda ya zauna tare damu"

Aunty ce ta miƙe ta dafa Mama” karki ce haka Hauwah iya gaskiyata na faɗa miki ƙuncin da kike ciki ya isa hakan karki cirewa kanki yardar dan ke ƴan uwan mijinki suke hakan, ki kuma sawa ranki wani ƙawance yana da tasirin abin da ɗan uwan jini ba zai tasirantar ma ba, amma zamanki a wannan halin bashi da anfani ko kaɗan ke a wahale mijinki a wahale yaranku a wahale, ki kashe aurenki nafi jin daɗin taimakonki amma ba zan taimakeki kina tare da ƙaddarar zaman dake kika ɗaurawa kanki kin zama mujiya a cikin dangin miji, sun jahilci rayuwarki, da jahilin tunani mafi muni da ban taɓa yarda cewa akwai mai ƙashin tsiya ba sai akansu"

Hawaye wani na bin wani suke ci gaba da zubarmin banso sa'insa kalar wannan ta zama abin farko na haɗuwar ƙawayen da suka ɗauki tsawan shekaru ba su tare ba na yarda Aunty tafi Mama gaskiya duba da yadda Mama ta koma da na san cewa ko ba daɗe ko ba jima Mama za ta gano gaskiyar Aunty muddin rayuwar tamu ta tuƙe da wanzuwa a haka

"Addu'a ya dace ki yi min Rumaisa dan Allah ki tafi ki ba ni guri ki barni haka na ci gaba da zaman jiran ƙarshen abun da zai faru a zanen ƙaddarata, bana farin ciki da haɗuwar mu na gwammaci na ci gaba da kallon Rumaisa a madadinki ba wai ko a mafarki na hango ki ba saboda yarda munin mafarkin zai zamo gareni sai gashi a zahirance kike furta hakan gareni saboda ra'ayin son zuciyarki”

Tsaki Aunty ta yi jin furucin Mama "zanen ƙaddarar da kika ɗaurawa kanki ba tun da kin kasa fahimtar abin da nake ƙoƙarin fahimtar dake” Batare da Aunty ta sake jiran cewar Mama ba ta fara ƙoƙarin saka takalmin ta riƙo hannunta na yi da sauri ina kuka

"Aunty dan Allah karki tafi ki bar mu a wannan halin mun yi haƙuri har ba musan iyakar shi ba”

Aunty ta ɗago fuskata tana gogemin hawaye na da nata yake zuba” ki ya haƙuri Sumayyah mamarku ta kasa fahimtar abin da nake ƙoƙarin fahimtar da ita, tana mummunan kallo a gareni na nufin cutar da ita a matsayina na masoyiyarta mai ƙaunarta da na san shaidar hakan ya sa ta sawa ƴarta sunana amma soyayyar miji ta wahalarwa ya sa batasan ka sancewata a tare da ita” Tana kaiwa nan ta saki hannunta daga cikin nawa ta fice ba tare da ta waiwayo wajen Mama ba ni ɗin ma ɗakinmu na shige dan wani haushin abin da Mama ta yi nake yi kaina haɗa da gwiwa ina shiga ɗakin hawaye suna zubowa masu zafi a idona na yarda da zancen Aunty na san ba za ta faɗi san ranta ga abin da ya shafi Mama ba damu kanmu indai na hango ƙawancena da Halima saina hango girman na Aunty da Mama ya zarce namu na yarda kirkin Aunty ba za ta yi abin san kanta garemu ba saidai ta taimakemu tabbas lamuran dangin Abbah sun isa ga duk masoyin Mama har ta Abbahn yaji haushinsa duk da shi babu ruwansa na daɗe zaune wajen sai da na fara jin muryar ƴan makaranta ƙannena na miƙe ina goge fuskata don karsu fahimci damuwata

Ahmad ne ya shigo ɗakin da nake yana kallona” Yaya maiya faru Mama ta ce na daina zuwa gidan Aunty, ko wani abu ta yi miki da kika je?"

Shiru na yi ba tare da na san amsar da zan bashi ba tambayar tawa ya sakeyi” ki ba ni amsa dan Allah meya faru?"

Canza zancen na yi da kallon shi” Amma dai ba a tashi makaranta ba ka dawo gida ko?"

"Dan Allah ki ba ni amsa zazzaɓi nake ji shi ne da suka ba ni magani suka ce na taho gida”

Hawaye na goge tuno yarda ubangiji ya kawo mana canji har gida Mama ta nuna bata so"Ahmad Aunty fa ƙawar Mamarmuce ta faɗawa Mama gaskiya shi ne ya sa ta ce ka daina zuwa, rayuwarmu tafi ta baya lalacewa. . . . . "labari na shiga bashi

Ahmad bai iya furta komai ba ya fice daga ɗakin namu

Sai La'asar yau Abbah ya waiwayo gida ba dan ansamu abin da akeso ba sai dan ya gaji da yawon nashi kuɗin taliya ɗaya da muke samu yau ɗin babu su ba alamarsu, saima zazzaɓi Abbahn ya dawo da shi gida hakan ya ƙara karyar min da zuciyata

"Abbah ya jiki” na furta kaina a ƙasa

"Alhamdulillah Sumayyah kunci abinci kuwa?"

Kai na girgiza” A'a Abbah bari na siyo maka maganin zazzaɓi”

Abbah ya girgiza kai "A'a dawo ki zauna ai na ji sauƙi, ina Ahmad ɗin yau Alhamis ai baije gidan aikin ba?'

Shiru na yi ganin yadda idan Mama yake akaina hakan ya sa na miƙe na fice ba tare da na iya bawa Abbah amsa ba

Haka yinin ranar muka ka sance da yunwar da dama kullum cikinta muke har zuwa dare da na fita da awara Juraid ya ba ni kuɗin yadin da yayi min alƙawari ina shigowa na nunawa Mama kuɗin sannan Abbah bai dawo ba

Rumaisa ce ta shigo ɗakin da nake da sallamarta cire hannuna na yi daga tagumin da na zuba da duka hannayen nawa tunanin abin da ya faru ɗazu nake kamar yanzu yake faruwa na janye tunanin nawa ina amsa mata sallamar

"Yaya Sumayyah Abbah na kiranki” jin abin da ta faɗa ya sani miƙewa

"Toh gani nan zuwa”

Ƙasan filo na ɗaga na ciro kuɗin da Jurayd ya ba ni a ɗazu dubu uku da har na taɓa wasu, ganin Rumaisa tsaye har lokacin

"Ba zuwa za ki yi ki ce masa na ce ina zuwa ba?"

Rumaisa ta girgiza kai” Barci na ji ina ji shi ne zan shigo ɗaki ya ce na kiraki, suna tsakar gida shi da su Mama” Harararta na yi uwar ƴan tsara zance ke nan

 "Naji toh haba, barcin ne kikayi min tsaye”

Ina gama faɗar haka na fito daga ɗakin hasken da ya mamaye tsakar gidan na wayata da ta zama fitilarmu ya ba ni damar hango su da shi da Mama da Ahmad sai su Sadiƙ da suke kwarkwance a tabarmar da take babba hakan ya sa ta ishesu inda suke na ƙarasa

"Assalamu alaikum Abbah ya jikinka? dama Rumaisah ta ce min kana kirana?na yi maganar ina kai ƙafafuna ƙasa saman tabarmar da sunkuyar da kaina

"Wa'alaikumussalam, Sumayyah jiki Alhamdulillah aina warware na ci abinci dama nafi tsammanin yunwa, a kan maganar Juraid ne da yake zuwa wajenki na ce ta kiraki, na ji ɗazu Mamarku ta ce ya ce zai miki uniform yanzu Mamarku take faɗa min kince ya baki kuɗin siyo uniform ɗin"jin shirun Abbah ya sani ɗago kaina na maida su kallan ƙasan

"Eh Abbah ya ba ni amma wallahi Abba ba roƙarsa na yi ba ra'ayi yayi, ya ce idan zan koma makaranta zai yi min uniform dan da namayi shiru da maganar komawar da na ga ba ka da kuɗi shi ne ya tunamin"

"Eh na ji ba roƙarsa kikayi ba amma ki daina amsar komai nasa daga yau babu hujjar da zan zuba ido ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba yaron nan na kawo miki abubuwa kina amshewa shi ba wata kwakkwarar maganar da ya zo da ita samarin da da na yanzu sun bambanta a da ma ana samun ɓata garin bare zamani” jin Abbah ya gama faɗan na ɗago da jajayen idona dan kam Jurayd haɗuwar mu da shi yadda yake kashemin kuɗi ya taimakeni ta fuskokin da dama duk da kashe kuɗin ba nufina dubunnai ba dan da babushi yau sai dai dukkanmu mu kwana da yunwa a cikin kuɗin yadin na ba da wasu kuɗin muka siyo fulawar ɗan wake duk da ba isarmu ta yi ba amma mun yi maganin wata ƙofar yunwar na san yana yin da Abba yake tunani ga Juraid amma shi sam ba hakan yake ba

"Kaganta ta yi shiru ko?, na faɗa ma harda laifinta ma da take amshewar, ga kayan Ummu Habibah da Zainab lallai sai anyi sabon tana cewa tanaso za su bata "maganar Mama ta katse min tunanina

"Ni dai na yi iya faɗana na fita ya rage miki Sumayyah, samarin yanzu ba su da amana ba a gane manufarsu ga mace har sai anga sun aureta shi ma auren ba ana yi ake ganowa ba, kuma duk amsar kayansu ke janyo hakan ki kula da kyau Sumayyah"

Kai na ɗaga jin ƙarshen kalaman Abbah tare da furta” insha Allahu Abbah"

"Ahmad yau ko kaje gidan. . . . "Ƙarar da wayar Abban ta yi ya sa shi maida sauran maganar ta shi da na san ta gidan Aunty zai yi da ɗazu ma sai da ya yi da yake kwance, daga aljihun rigarshi ya zaro wayar murmushi ya bayyana fuskarshi yana mai kallon screen ɗin wayar

"Ahmad Muazu ne mai kiran fa Hauwah" ya yi maganar yana kara wayar kunne Maman ma murmushi ta yi ni ɗin ma haka dan nage waye mai kiran mahaifin Batul yake nufi

"Wa'alaikumussalam Malam Ahmad ya gida?, ya yaran ya harkoki” cewar Abbah da iya maganarshi muke iya ji da yake kusa damu kuma wayar ba a handsfree take ba

"Alhamdulillah, a'ah babu komai, ni ma naso na kiraka tun dawowar Sumayyah na yi ma godiyar abin arziƙi da aka haɗota dashi, mun gode Allah ya ƙara arziƙi ya bar tare, wato wulaƙanci yaso yi mana kuma na wulaƙanci shi ya sa babu wanda na sanarwa ma tun da ya zo babu shiri” Abbah ya sake faɗar hakan ya ci gaba da sauraron Abbah Ahmad ɗin tsawan mintina ya sake ɗaurawa da cewa

"Toh bakomai ai inda rabo gaba za mu dawo, Na gode madallah a gaida yaran sosai da mai ɗakin Allah ya ba mu alkhairi” Da haka Abbah ya cire wayar daga kunnensa yana ƙara farfaɗa fara'arshi

"Allah sarki Ahmad na Allah baya ƙarewa a duniya, gidan ɗan uwansa yaso nemar mana mu dawo mu zauna baiji daɗin yanda muka dawo ba sanarwa ba yanata faɗa, ya ce cewa lokacin ba'akai ga samun wanda zai zauna ba, yaso taɓani a waya tuntuni Allah bai nufa ba, shi ne nake masa bayani abin da ya faru"

Mama murmushi tayi” Ai hakan ma mungode da kulawarsa garemu, yana da kirki Ahmad sosai”

Abbah ya ɗaga kai "Sosaima Hauwah yana daga cikin abokaina na makaranta da nake ganin mutuncinsa fiye da yarda bakya zato saboda tarin alkhairin sa gare mu indai wani harkar kuɗi ya haɗa ku musamman kamar su assignment a lokacin yana harkokin samu ba yanzu ba da komai ya tsaya masa saidai godiyar Ubangiji”

"Bakomai komai ya yi farko zai yi ƙarshe a hankali a hankali insha Allahu"cewar Mama da ita kullum a ƙarfafar Abbah take yi

"Alhamdulillah Hauwah dole dai na ci gaba da godiya irin halaccin da kikemin ba duka mace ba ake samu sai ɗaiɗaiku, kullum ƙarfafa ni kikeyi bakya taɓa jin ki ƙosa baki taɓa nuna min a fili ba da na yi imanin har azuciyarki haka ne abin da ƴan uwana suka kasa aiwatarwa sun gujeni da ni da ƴaƴana harke ɗin ma hakan baimusu sharri suke ɗauramin kala kala ban san da bakin da zan gode miki ya isa ba, Allah ya yi miki albarka Hauwah "

Mu duka har Mama muka amsa da "Amin"

Mama da taka sa bashi amsar kalamansa ta canza maganar da cewa

"Ai namanta ma Sumayya ta ce ma ankawo kuɗin auren yarinyar shi Batul ka kira kamasa Allah ya sanya alkhairi na shafa'a da faɗa maka sai yanxu na tuna da kuka gama wayar"

"Bakomai na kira sa ko zuwa da safene Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokacin lafiya” Cewar Abbah da muku ma muka amsa da "Amin ya rabb". . . .

Na Cancanta (Kashi na 33)

Misalin ƙarfe goma na safe da duba agogon wayata ke nan na fito yin wanke wanke, na kwanukan suyar awarar safiya da mukeyi

"Assalamu alaikum kamar daga sama nake jiyo murya mai kama data Aunty da ban tsammanin sake zuwanta ba guri kusa sai dai abun mamaki jiya aka yi abun yau ma gata ta dawo jinjina soyayyar da Aunty ke yiwa Mama nake yi da na kasa ganin wadda Mama ke yiwa Aunty a yanzu harta a kwayar idanunta ta rikiɗar dasu

"Wa'alaikumussalam, mene ya kawoki gidana? karo na biyu na yi zaton mun kammala maganar da zamuyi ko?"Muryar Mama na jiyo na ɗago da kaina na dubeta tsaye kofar ɗaki da tabbacin sallamar Aunty ya fiddo ta daga ɗakin inda Aunty take ta nufo

Aunty na maida idona kallo da take ƙoƙarin ƙara sowa ciki ita ma sai kuma taja ta tsaya ganin ƙarasowar Mama inda take

"Na zo na ji dalilinki da ya sa kika hana Ahmad zuwa gidana bayan iya haihuwarshi kikayi amma Ahmad ɗana ne halak malak, inke ƙinƙi tayina bai dace ki hana ni na rayu da yarana ba” da raunin murya Aunty ta yi maganar

Mama murmushi ta yi da na tabbatar na takaicine "indai kin yarda ɗanki ne da sauran yarana bai kamata ki zowa da mahaifiyarsu magana a kan mahaifinsu ba inba mai daɗi ba ya dace ne ki taimaketa ta kowacce fuska na san za ki iya Rumaisah, ki bawa uban ƴaƴana aikinyi ko taimakonsa da jarin da zai riƙemu"

"Kwarai kuwa Rumaisah AlMustafa Matazu za ta iya komai ga Hauwa Ibrahim Alhassan sai dai ban da samarwa mijinta wani abu a rayuwa duba da yadda kika ba ni labarin ƴan uwan mijinki, taya zan samar masa bayan ga jahilcin tunaninsu akanki ki yi nazarin me zaije ya dawo za su hanashi yi miki komai idan suka janye nasu bakisan alaƙar jini ba ne Hauwah, Rumaisah ba za ta iya ba”

"Dan Allah Rumaisah karki rinjayar dani da bahagon lissafinki mara anfani ki canzamin tunanina ki yaudareni”

"Idan kowa zai yaudareki ki cire ni a ciki ki tuno wace ce ni mana, ba wai wannan maganar takawoni ba ki bar Ahmad ya ci gaba da zuwa gidana dan Allah, na kwana da jin babu daɗi a raina a game da abin da kikayi” Aunty ta ƙara sa maganar tana haɗe hannunta duka biyu alamun roƙon Mama

"Dan Allah Rumaisah ki tafi ki barmin gidana banasan kowanne taimako dama ƴan uwana na jini ba su da abin taimakamin da shi da yau na tabbatar da girman alaƙar jini dabance, kawai ina zaune lafiya da mijina da yarana kinzo min da wasu lissafin da zuciyata ta gaza a ɗaukar su"Mama ta ƙara sa maganar da take ƙoƙarin barin wajen

"Ehem"gyaran muryar Abbah na ji da hakan ke tabbatarmin ya daɗe tsaye wajen hawayen dake kwararrarmi suka ci-gaba da zubomin abin da nake gudu saida ya faru Abbah yaji halin da ake ciki da na san hankalinsa zai ƙara tashi

"Hauwa'u tun ba yanzu ba na fahimci cewa ƴan uwana sun daɗe da ɓata zama a tsakaninmu, na san da ƴan uwanki nada wani ƙarfi da iko da tuni sun tilastamin na rabu da ke wahalar ta yi yawa, karki kasa amincewa da ƙudirin ƴar uwarki akaina ba tare da kin san gobena ba banasan rayuwarki ta faro ta ƙare a rashin jin daɗi ki yi tunani”

Mama dake ƙoƙarin buɗe baki ta yi magana Abbah ya ɗaga mata hannu

"Karki ce komai na ji komai harda na jiya ma, ba ni da yarda zan yi da ƙaddarata Hauwa'u iyayena sun kasa tallafata fa taya ƴan uwanki da masoyanki za su jure ganinki a hakan ?, kibi shawararsu na san ba za su cutar dake ba, Rumaisah jinin jikinkice kullum ambatarta kikeyi a yanzu data nemeki da kanta ya dace ki sake tabbarwa da gaskiya take tare dake iya gaskiyarta ta faɗa miki kowama hakan zai yi indai yasan wasu lamuran dake faruwa tsakaninmu"

Aunty da nake kallon yarda jikinta ya yi sanyi lokacin da Abbah ya ƙara sa maganar da yake yi

"Abdullahi ka gafarceni ba nufina na rabaka da matarka ko haifar da wata husuma tsakaninku ba, tunanina rabuwar za ta fi muku zama alkhairi, saidai yanzu tunanina ya ba ni ni ce ya dace na haƙura da Hauwa'u da abin da ya shafe ta domin ta samu ta zama cikakkiyar uwa ta haƙura da mijinta ba dan komai ba sai dan goben yaranta, karki damu Hauwa'u zan tayaki aikata hakan zan bar miki rayuwarki har sai lokacin da kikaji ya dace ki nemeni ba zan sake gaggawar nemanki ba bayan na san kinada yaƙinin inda za ki sameni” takai ƙarshen maganar tana dafa Mama da hannu ɗaya ɗaya hannun kwallar idanta take gogewa

"Kiya haƙuri Rumaisah ba na ƙi bin shawararki ba amma ki dinga kallan kanki idan kece a halin da nike ciki naje miki da zancen kibar mijinki da yaranki idan kin bi zancena kina tsammanin kin yi halacci ke nan gwara ka bar mutum a lokaci samu ba a lokacin rashi ba ya kamata ayi gwagwarmayar rayuwar da kai daga baya kasamarwa kanka mafita. . . "

"Ya isa haka Hauwa'u"Aunty ta katse Mama da rufe mata baki daga nan tasa kai ta fice, ba tare da ta waiwayo ba

_Nima wanke wanke na aje na tashi na koma ɗaki kuka nake mai tsumar da zuciya da ba nida mai lallashina, ƙaddarori sun samu muhallin zama a rayuwarmu, a kullum cikin jiran sabbin matsaloli mukeyi, da gaske yanzu Aunty ta bar mu ba za ta sake waiwayarmu ba ya za ka ji idan mutumin da ya amsheka a yanda kake tun kafin yasan komai akanka ya tafi ya barka saboda yadda muradanku suka bambanta sai zancen da na ji a bakin Abbah yaji maganar su Mama jiya ke nan a jiyan ma ya zagayo gida yarda yake yi a wasu lokutan kamar yadda ya yi yau kodai zancen da yaji ya sa shi jin zazzaɓi da ya ce a jiyan yanaji bana tantamar hakan ce ta faru domin Abbah akwai juriyar yunwa har yaji ta ƙare masa ba za ka fahimta ba saidai yanda jikinsa yake komawa ya nuna hakan_

_Ringingtone ɗin wayata ya katse min tunanina da tsaidar da kukan da babu mai lallashina akansa, Number ɗin Halima na gani a kan screen ɗin wayata, da tun kwanakin baya Batul ta turomin ita bansamu damar kiranta ba ajiyar zuciya na sauke na danna wayar na saka a kunne da saisaita muryata dan yanzu na san Halima za ta iya ruɗewa idan har za ta fahimci damuwa game dani jin shirunta ya sa na fahimci fushi take yi dani_

_"Assalamu Alaikum kaina bisa wuyana Limah baby" na furta da murmushin da na ƙaƙalosa a fuskata_

Tsaki Halima ta janyomin

"Wa'alaikumussalam, a'ah Limo ba Limah mara mutumci ai wallahi na yi fushi matuƙa dake da sam ba zan kiraki bama”

Murmushi na yi jin zancen da Halima ke faɗa

"Kiyi haƙuri Aminiyata naso kiranki babu kuɗi ne”

"Eh fa a babu kuɗin kika samu kiran Batul kika shareni mai zan ce miki ban da na gode”

Dafa kai na yi tamkar Halima na wajena” oh Allah Halima a lokacin ba nida sabuwar number naki ne sai bayan wayarmu da Batul ta turomin ita”

"Toh shike nan na ji dai yanzu yasu Mama da Abbah, da su A'isha?"

"Duk suna lafiya ya Aliyun naki?" na yi zancen ina dariya

Tsaki na ji Halima tayi” Wato Aliyu ne uwata da ubana da ƴan uwana ya yi miki kyau"

Dariya na sakeyi” Au to meye a ciki matsalata dake ke nan ƙorafi kafin a kira kowa kinfisan fa akirashi har bala'i kikeyi aka ƙi kiranshi”

"Naji ke yawwa ina Hamid yake ne, fatan kun shirya yanzu?"

Ɓacin rai na ji yana ƙoƙarin zuwarmin jin zancen Hamid a ganina alaƙarmu ni da shi babu sauranta duk da ƙasan zuciyata ina jinsa wani lokacin saidai ban ɗauki hakan da muhimmanci ba” Kina min maganar Hamid kamar kin manta abin da ya faru, tun ina ganin kiranshi da message nashi yanzu ya haƙura ya bari dan bana ma karanta message ɗin nake gogesa, bana san janyowa kaina wasu fitinun ne”

"Haka ne Sumayyah Allah ya baki wanda ya fi alkhairi”

Kamar na yi mata zancen na samu Jawad sai kawai na yi shiru sai abun ya kankama tukunnah na bita da "Amin"

"Na baki labari Tahfiz ɗinku taro za su shirya na gangami har da wanda ya gina makarantar zaizo ma” Har jira nake takai ƙarshen zancen da wani murna na karɓe zancen

"Dan Allah fa Halima dagaske kike?waye ya baki wannan kyakkyawan labarin inama inama”

"Wallahi da gaske nake Haris ke ba mu labarin jiya ranar Lahadi za a yi kin ga ke nan gobe ne, saidai ban sani ba ko lahadin wani satin, Muhadara za a shirya gagaruma har kyautuka za a rabar ga ɗaliban da suka fi hazaƙa a makarantar"

Da farin ciki na furta "Alhamdulillah, ni abin da ya fi min daɗi ma Alhaji AbdulYassar mai makarantarmu zaizo shi ma, inasan mutumin nan Halimah yana da alkhairi ina ma ace. . . "

Halima tasa dariya da katseni” ina ma da kuɗin mota ai ni kaina inasan zuwa Sumayyah ka ganewa idonka abinci, zan kira Batul na ji ko zataje da dake zuwan zaifi mana daɗi amma fa yanzu ko ka shawo gajiya ba inda za ka huta”

"Ke dai bari Halimah Allah inasan dawowa nan cikin garin amma yana iya babu damar hakan nifa saboda kuma nafisan dawowa”

Da haka muka ci gaba da fira da Halimah kamar ba za mu daina ba saidai ban yi ƙoƙarin bata labarin komai da yafaru a tsakaninmu da ƴan uwan mahaifinmu ba saida Halimah ta gaji dan kanta ta katse wayar daidai lokacin Mama ta shigo ɗakin kallona tayi

"Wancen wanke wanke wazai ƙara sa miki?, aiya kamata ki taso ki ƙara sa ko?"kallon Mama nake tun da ta fara zancen har zuwa ƙarshe ramewarta kullum ƙaruwa take yi da da kuɗi ya kamata a ce ta nufi asibiti saidai na san da da kuɗin ma ba za ta yi wannan ramar ba, abunda ya fi damuna yadda yanzu babu mai zuwa gidanmu a ƴan uwan Mama kosu Aunty Zainab da suke ƙananu gashi babu hayaniyar data gifta a tsakaninmu dasu anya suma ba ido suka zuba mana ba, anya ba maganar data shiga tsakaninta da su makamanciyar ta Aunty

Zancenta ya katse min tunanina” Tv kika maidani ke nan ina magana kin tsareni da ido ko toh ba za ki iya faɗa min ba”

Ƙasa na yi da kaina ina jin ɗumin hawaye "Mama dan Allah ki yarda da zancen Aunty mana babu cutarwa a maganganunta sainake ganin"na ƙara sa zancen ina jin faɗuwar gaba dan na san halin Mama a kan shiga harkar da babu ruwanka gashi kuma yau ba shiga

"Sannu Gwaggo nace, da kan wani kika faɗi wannan maganar sai na ce bakisan ciwansa ba amma a kan mahaifinki san zuciyarki kike gwadawa dai Sumayyah to ni ba dani za ki yi wannan shiriritar ba” tayi zancen da ƙoƙarin ficewa daga ɗakin da saurina na tashi na riƙi hannun Mama

"Dan Allah Mama ki fahimceni wallahi kin rame kin canza mune ya dace mu zama dole mu karɓi kaddararmu bake ba, ko su Gwaggo yanzu basa taimakon mu da komai bana tantamar sun faɗamiki gaskiyar da Aunty ta faɗamiki banasan a kan Abbah ki zaɓi rabuwa irin wannan da ƴan uwanki da masoyanki”

Shiru Mama ta yi ba tare data iya furta komai ba har nakai ƙarshen maganata sai hawayen da ke zubowa daga idanunta hannuna ta cire daga nata ta riƙo fuskata ta juyo da ita kallonta ta fuskar

"Ki kalle ni sosai Sumayyah ni ɗin ma ba hakan naso ba komai ya ka sance sau tari da na sani ya fi gurbin zama a zuciyata ina jin inama bawa na hango ƙaddararsa tun farko da ban zaɓi wannan ba, su Gwaggo sun gaza fahimtata Rumaisa da kullum mafarkin sake ka sancewarmu tare nake ita ma ta zo da wannan kalaman, ba dan kowa na kasa hakan ba sai danku gobenku nake kallowa ƴan uwan mahaifinku idan nabarku saidai su wofantar daku su maisheku bayinsu Rumaisah ba za ta iya ɗaukar ɗawainiyata gaba ɗaya da ƴaƴana ba, sai sauran tausayin mahaifinku dan Allah karki ƙara min wannan maganar"ta ƙara sa maganar tana haɗe hannunta biyu da nufin roƙona daga bisani ta fice batare da na iya sake furta komai ba

Zubewa na yi da zafin zuciyar da nake ji ga tsananin ciwan kai ganin tunanin bashi da alfanu na miƙe na fito ƙarasa wanke wanken da nake yi ina yi ina share hawayen idanuna da sun kasa tsayawa na rasa ya zan kallon rayuwarmu na sani maganganun Mama suna kan mizanin gaskiya amma jin daɗin da nake buƙata ga rayuwar Mama ta samu yafimin tarin gwada mizanin mune ya dace muyi linƙaya a kowace duniya da Abbah ba wai Mama ba mu kanmu ba dan komai ba sai dan alaƙar jini amma ya zan yi Mama sam ta gaza fahimta. . . . .

Na Cancanta (Kashi na 34)

Ina kammala wanke wanken na koma ɗaki wani barci mai nauyi ya ɗaukeni

"Ke dalla can ki tashi” dukan da na ji an makamin a baya tare da jin muryar Malika cikin barcin na yi hanzarin miƙewa ina sosa bayana saboda yadda dukan ya shigeni

Kallona Malikan ta sakeyi da faɗin "Gaskiyane ke barci ma kikeyi?"

Tsaki naja da gama wartsake idanuna cikin yana yin ɓacin rai” Wallahi bakida mutunci Malika ina barcina kika san da yadda na yi kin maka min duka haka, Allah ya isa wallahi kuma in ban yi barci ba mai kike so na yi?"

"Masifa ni za ki yiwa Allah ya isa daga taimakonki, na ga mai rakaki siyo yadin makarantar danni yanzuma ba zani ba rana ta yi ba zan je na kwaso uwar ranar nan ba” sai da yanzu na tuna da abunda yake gabana

Murya na marairaice na ce” Haba Malika daga faɗin hakan wallahi namanta ne, kuma barcin ya ɗaukar min daɗi”

Tsaki Malika ta yi tana ƙoƙarin tashi na yi saurin riƙe hannunta” Dan Allah ki zauna mana, kefa matsala ta dake ke nan, nifa ba sanin garin nan na yi ba”

Hararata ta yi ta ce” za ki sani ai ƴar rainin hankali ni dai koma zani ba zani cikin tsawon ranar nan ba wallahi”

Kai na dafe Malika matsala ke nan haka duk Malika take ko ita kaɗaice hakan ban sani ba dan Aunty Malika ba sabo tsakaninmu da zan fahimci hakan daga gareta na cire tunanin kar na sake ɓata mata rai

"To da yamma fa?"

Sororo ta tsaya kallona” Wacce yammar islamiyya?, zan fasa zuwa ko kuwa dai nufinki na fasa sana'ar da nake yi na raka ki?"

Murya na sassauta” Amma Malika ni ma fa ina islamiyya ɗin nan ina kuma sana'ar tun da ba za ki ba amma shike nan"na ƙara sa maganar ina komawa kwanciyata

Kallona na ga Malika ta yi "Malama haka zamuyi dake ke nan wato barci ma za ki koma wato matsalata ce bataki ba”

Cikin ɓacin rai ni ma na tsaida idona kanta” To ya zanmiki tun da kinkawo uzurinki bakomai zan biya gidan Gwaggo naja Rumaisa ta rakani yanzu ma tun da na san sai yamma za su dawo"

"Wai cewa na yi miki ba zan rakani ba ne, ki ce za ku sha yawo kafin ku gano inda za ku samu yadin a ca muku kuɗi kuma ku bayar a ɗinka muku ba mai kyau, saidai idan kinaso kija Zainab da kuma na san ba za ta rakaki ba ba shiga ba fita na san halinta”

Jin ƙarshen zancen Malika na kalleta na ce "Toh ya zan yi miki ne Malika koma mara kyau zan samu ai yfimin jiranki ɗin tun da ba za ki ba”

"Allah zan fasa rakakin da na yi niyyaryi yanzu wallahi” rigima Malika ke nan ko ina ta ce yanzu za ta rakani, naja numfashi na ce

"To yanzu yaushe za ki rakani ɗin"na ƙara sa maganar da murmushi

Baki ta taɓe” ya zan yi kinyi min asarar islamiyya wajen 3 na yamma saiki shirya da wuri kar ki sake rainamin hankali”

"Toh shike nan na ji Na gode” na yi maganar ina juya kaina dan kar a sake cewa anfasa rakon

"Kin ga ni ma tafiya zan yi gida ba sai kin juya kaiba, idan kin yi niyya ki gama shiriritarki wajen 3 na rana za ki iya zuwa mu ta fi”

Ko amsa ban bata ba dan na ƙagu ta tafi rikicin Malika sai ita sam bata fahimtar situation ɗin da mutum yake ciki ma wani lokacin

Uku saura na samu na shirya dan zullumin kar Malika tacemin ta fasa Mama na leƙa ɗakinta na faɗa wa mun tafi addu'a ta yi mana daga bisani na fito gidansu Malika na shiga,

Ummansu Malikan na samu a tsakar gida tana tankaɗen gari gefenta Na'im ke wasa da motar yara gaisheta na yi cikin sakin fuska ta amsa min ta ɗaura da cewa

"Malikan na ciki har ta fara mitar ta za ta ma fasa rakakin"

Na yi murmushi na ce” Kai Malika Umma uku fa mukayi za mu tafi kuma har yanzu bata ƙara sa ba”

Ummata ce” Ai kin san halin Malikar taki”

"Haka ne Umma da ya yana ta yarda za ta rakani ɗin"ina faɗar hakan na ƙara sa shigewa ciki dan Malika kamar ƴar kwaya take karma ta ce na tsaya gulmarta ta ce fasa rakanin ɗakin su Malikan na ƙara sa shiga gefen gado na same ta zaune an gama caɓa ado ana feshe jiki da turarenta bodyspray saurin maida turaren ta yi jikin murfinsa ta sa cikin kwandon kayan kwalliyarta ta miƙe da cewa

"Karma kisa ran za ki fesa wannan turaren da kuɗina na siya kinacan kin ɓoye wannan turaren mai shegen ƙamshi da Juraid ya siyo miki ko dangwale baki taɓa ba ni ba”

Tsaki naja ni sam bata san ba damuwar turare ta dameni yunwar dake fafukata tafi isata na dai daure na ce” oh ni Sumayyah wallahi Malika kinada muguwar matsala ni bakiga na ɗauka ba, kuma turaren da kike magana na Juraid kiji tsoron Allah duk idan kika biyomin Islamiyya saikin feshesa, kawai neman magana ya miki yawa dan Allah yi sauri kisa hijabi mu tafi”

Tsayawa Malika ta yi kallona sororo"Yayi kyau kinamin tsaki nifa gaskiya kin fara isata wallahi a yaushe ma nake fesa turaren?"

Na gama fahimtar abin da Malika takeso muyi rigima ta ce ta fasa rakani hakan ya sa na miƙe da ƙoƙarin sauya wani zancen

"Yanzu dai saka mayafin ko hijabi dan Allah mu tafi kin ga lokaci na ja fa”

"Ke na ji” cewar Malika tana ƙoƙarin buɗe Sib ta samo hijabi, shiru na yi mata har ta saka muka fito

"Yaya Malika zan biku dan Allah"cewar Na'im yana ƙoƙarin ƙara sowa wajenmu

Tsawa Malika ta daka masa” Islamiyyar fa wazai je maka su Khalid tuni sun tsufa makaranta tun da kaji na ce zani unguwa shi ne ka zauna kai a yawo, sa takalminka mu fita tare ka yi hanyar makaranta”

"Bi min ɗa a hankali ba zai bi su Khalid ba su mammakeshi ɗin da kike so"cewar Ummansu Malika

"Yaronne ai ba shida kunya Umma, mudai mun tafi sai mun dawo"tana maganar tana dungurar Na'im "Ni saka takalminka muje

"Kardai ki jiwa ɗan Autana ciwo a dawo lafiya karki manta saƙon nan dai” faɗin Ummah

Malikan ta sake dungureshi da cewa” Wannan ne Autan Allah ya kyauta wallahi sai kin yi biyar bayanshi” ta ƙara sa maganar tana jan hannunsa

"Sumayyah ki kularmin da yaronnan kar Malika ta ji masa ciwo ba imani ta cika ba” Umma ta yi maganar muna ƙoƙarin ficewa daga gidan nidai dariya na yi muka fice

**"Wallahi Malika ji nake kamar in faɗi tun a wajen ɗinkin can dan Allah mu biya gidan Aunty Maryam, na huta”

Kallona Malika tayi” faɗuwa fa kika ce sai kace mai jin yunwa?"

Da kyar na iya furta "Yunwar ce mana kin san rabona da abinci tun awarar safe da ɗan kokon da na haɗa da ita”

"Taɓ kuma kikayi wannan tafiyar sannunki wallahi aini nan da can ina jin yunwa bana iya zuwa ko dake kin saba”

Na yi murmushi” wanne sabo da yunwa ke dai ayi sha'ani”

"Allah ya kawo mafita dai muma fa kwana biyu sai addu'a shi ya sa ko tuwo yanzu fa baya raguwa wallahi abin sai addu'a”

Murmushi na yi dan kam ni ma na fahimci su Malikan kwana biyun sai addu'a tuwon da suke kawo mana lokaci lokaci yanzu babu na dakyar na iya lallaɓawa muka isa gidan Aunty Maryam da har bakina ya mutu har muka shiga gidan da Malika ta iya sallama muna shiga na riga Malika faɗa wa ɗakin Aunty Maryam na kwanta a doguwar kujera ina nishi Aunty Maryam da tana ɗakin gado muka shigo ta shigo falon

"Aunty Maryam ina yini” ko gaisuwar Malika Aunty Maryam bata saurara ba ta maida dubenta gareni tare nuna ni da cewa

"Ita wannan meke damunta ta zo ta kwanta haka?"

Malika da yana yi tausayi ta kalle ni tare da kallon Aunty Maryam

"Wallahi Aunty Maryam yunwace yanzu take faɗa min tun ƴar awara d kokon safe rabonta da abinci kuma gashi tafiya mai nisa mukayi”

"Ahaf aini na san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoki, sannu Sumayyah bari na kawo miki abinci ni ma dai saurane yara sun cinye, ina tausayin halin da kuke ciki amma uwarku bata tausayin kanta bare ku ita lallai tanasan mijinta ba za ta iya rabuwa da shi ba kuna cikin wannan ƙangin wahalar ƴan uwan mahaifinku sun watsar daku sun watsar da ubanku duk saboda ita amma ta kasa ganewa ta zauna wahalar da kanta tanaso ta kashe kanta a banza”

Maganar Aunty Maryam ke fisgata saidai bayarda na iya tun da ta ce za ta ba ni abinci dole na zauna amma idonta ya rufe nake tunanin batasan gaban Malika take maganar ba ne saida ta gama takai aya ta tashi tana tashi Malika ta kalle ni tare da cewa

"sannu Sumayyah"

Na ɗaga kai ina jin hawaye na zubomin

"Dan Allah. . . . "sai kuma ta yi shiru jin sallamar Aunty Maryam ta ƙara sa shigowa ɗakin da flat ɗauke da abinci a hannunta ajiyemin ta yi a ƙasa

"Ki tashi kici kin zauna kuka mara anfani da banga dalilinshi ba idan ma maganata ta ɓata miki rai dole na yi saboda uwarku ce ta janyo muku wannan gallafirin rayuwar tun asali mu ba gashi ba muna zaune cikin rufin asiri ba ranar dabama ɗaura abinci uku a gidajenmu, duk laifinta ne ai data kafe sai mai degree za ta aura ga degree da masters nan sun mata rana ai, kullum baƙin cikin yau daban na gobe daban baƙin cikin yunwa me ya kaishi bala'i, nan Rumaisah taje gidan Gwaggo tana kukan tasa baki a fiddo Hauwa'u da wannan ƙangin talaucin, amma Hauwa'u ba za ta yarda ba”

Ni dai ban iya cewa komai ba wannan irin lissafi na Aunty Maryam nidai na san komai inka ɗauke maganar Aunty da tayi, kawai Malika take zayyanawa dan ita ce bare da na yi sa'ar ma Malikan tasan wasu lamuran namu dalilin da ya sa banji ɓacin rai sosai ba ko da Aunty Maryam ta yi maganganun a gaban nata, Da wannan ɓacin ran nake tuttura abincin da ba ƙoshi na yi ba nadai toshe wata kafar muka tashi wanda har na gama Aunty Maryam na surutanta a kan halin da take ganin Mama da kanta ta sanya kanta raina babu daɗi ba damar na furta komai Aunty Maryam ta ce na mata rashin kunya da iya kyautatawa da soyayya suna yiwa Mama gajiya sukayi dai saboda irin yadda gidansu Abbah suke nunawa Mama shi ya sa har Maman ta ba su haushi ga kuma abin da ya faru tsakaninta da Aunty amma Aunty Maryam ba tada matsala abunne dai na tabbata ya isheta hakan ya ƙara sawa na yi mata uziri haka na lallaɓa muka isa gida dakyar na iya ƙara sawa saboda jirin da nake ji ga amai dake tasomin da gudu na shige cikin gidan yadda aman yake ƙara tasomin ban iya cire ko hijabi ba na fara kelaya amai kamar zan amaye hanjina

 Mama da take kwashe awara ta dubi Malika cikin ruɗewa ba abin ta aje kwasar awarar ba

"Malika meya sa meta?, daga shigowa sai amai”

Malika da muryar tausayi na ji tana cewa Mama” wallahi Mama yunwa ta ce tanaji shi ne muka biya gidan Aunty Maryam ta ci abinci to ina jin daɗewar da ta yi bata ci abincin ba shi ne tanaci ta yi aman shi”

Sannu Mama ta yi min Malika ma ta shiga jeromin sannu ta miƙomin buta na gama na wanke baki ban iya tashi ba saida Malika ta kamani ta kaini ɗaki nan na fara rawar sanyi

Hijabi Malika ta ƙara samowa ta rufeni ta ajiye ledar kayan da muka ɗinko a kusa dani tare da hijabin jikinta

"Bari na gyaro inda kikayi aman na dawo, sannu"Malika ta yi maganar tana ficewa bata jima ba ta dawo ta zauna kusa dani ta kalle ni

"Sannu Sumayyah yunwa ce wallahi dan Allah ki daina zama da yunwar nan haka ko gidanmu in kikaji dugu dugu ki riƙa shigowa mana muna ci tare ko ɗan ya ya ne ya fi a zauna bakomai, na tabbatar yanzu ma ba abin da kuka ɗaura, ni wallahi da unguwar nan gani nake ba wanda ya kaimu talauci sai da kukazo na sake godewa Allah kuma ku ci gaba da kallon na ƙasa daku insha Allahu komai zai daidaita nan ba da jimawa ba babu abin da ke dauwama ai a wannan rayuwar insha Allahu ƴan uwan Abbah saisun zub da kukan nadama da da na sani a kan abin da suka yi muku"

Murmushi na yi na jin daɗin kalaman Malika lallai ne ubangiji shi ne mai yin yarda yaso lokacin da yaso na cika da kewar Halima da Batul sai ga wasu ƙaddarorin sun sake haɗa ni da wata ƙawar mai alkhairi

"Insha Allahu Malika, amma ƴan uwan Abbah ba za su taɓa ganewa ba Halima tana faɗa min komai zai wuce, amma na san ba za su karɓemu a yarda muke yanzu ba”

Dafani Malika ta yi "Kiya haƙuri dan Allah Sumayyah da wannan maganganun kin ga bakijin daɗi, bari naje gida na samo miki magani ko dake ma sai kinci abinci magani zai samu shiga” nidai shiru na yi dan zazzaɓi ya yi nasarar rufeni a yau dai wayata ta yi ƙara na yi hanzarin nunawa Malika inda take ta ɗaukomin miƙomin ta yi da cewa

"Juraid ne ungo"

 Ka girgiza kai na ce

"Ki ɗaga mana ki ce masa ba ni da lafiya ina jin zuwa yayi” yarda na ce ta yi ta ɗaga wayar da sallamarta

"Assalamu alaikum mai wayar batajin daɗi”

Ban san amsar da ya bata ba na daiga ta aje wayar ta juyo ta kalle ni

"Yace agaisheki zaizo dubaki anjima”

Na ɗaga kai alamar toh, daganan shiru ya ratsa tsakaninmu Malika na ɗan danna wayata da da lafiyata ƙalau ban barinta ta shanye cajin wayar Malika ta aje tana mai kallona

"Sannu Sumayyah, ko naje gida na duba miki magani na ga ko Umma ta gama girki ma, gama saƙonta bari naje” ta yi maganar tana miƙewa ledar da muka shigo da ita ta duba ta ciro aiken Umma na barkono tana ƙoƙarin fita ta ce

"Allah ya ƙara sauƙi sai anjima” dakyar na iya furta Amin a saman maƙoshina tana fita hawaye suka fara kwaranyowa idona ba iya zuciyata ba gangar jikina ma ta fara gazawa da halin rayuwar tamu ina tsoron yarda halin zuciya ke sauya tunanin bawa rana tsaka shin ya gobena za ta ka sance da sauran ƴan uwana harta da ibadar ma bata iya yiyuwa yarda ya kamata idan har jiki bai samun sinadaran da yake buƙata ba. . . . . .

 

 

Na Cancanta (Kashi na 35)

Har bayan magriba babu abinci bare magani, bare zuwan Juraid da na san ko zaizo sai bayan isha'i Malika kuma ta aikomin Na'im cewa ba a gama tuwon ba mu kuwa dama ba mu samu yin abincin ba, Tunanin nawa ya yi saurin tsayawa cik jin ƙarar wayata ban yi tsammanin Juraid ba ne mai kiran ba zan kuma iya ɗaga wayar ba sai sa'ar Khadijah dake gefena ita ce ta ɗaga wayar

"Assalamu alaikum bata da lafiya” Banji mai akace ba a ɗaya ɓangaren ka sancewar ba a speaker aka danna wayar ba saida ta aje wayar ta faɗa min

"Yaya, saurayinki ne ya zo dubaki zai shigo"

Tana faɗin hakan na gane Juraid take nufi duk da ban tsammaci zuwanshi ba amma na san zaizo dakyar na iya ɗaga kai na kalleta da muryar rashin lafiya na iya haɗa kalmomi

"Ki. . faɗa wa. . Mama. . shi kuma ki fita ki ce masa ya shigo"da "Toh"ta amsa min ta miƙe ta fice ni

Sake jan hijabin da Malika ta rufamin na yi sosai na ci gaba da rawar sanyi, mintina kaɗan na fara jiyo sallamar Juraid sama sama da ina jin sallamar na san bashi kaɗai ba ne ba, ba su shigo ɗakin da nake kwance ba hakan ya ƙara ba ni tabbacin sun fara shiga ɗakin Mama gaisheta, Banji fitowar su ɗakin Mama ba sai sallamarsu da na ji a ɗakinmu ban iya amsawa ba na dai ɗago kaina na gansu Khadijah ita ce ƴar jagorar shigowar tasu ita ce a gaba sai shi Juraid da Alhassan da Yaya Nasir

"Sannu da jiki Sumayyah"Dukansu suka furta hakan suna ƙoƙarin zama can gefen da nake kwancen

Kaina na sake ɗagowa na kallesu a hankali na iya furta "Yawwa” wadda ba nida yaƙinin sun jita

"Sannu amma ya kamata kisha magani ko ayimiki allura ma” cewar Alhassan da shi ne ya riga su zama

Ban iya ba shi amsar komai ba saboda azabar da nake sake ji

Muryar Juraid na ji yana cewa da Alhassan"Ai na zoma ta da magunguna ɗazu na zo wajen Malika na tambaye ta yana yin jikinta shi ne na biya wajen Idris na siyo magunguna” ya ƙara sa maganar da sanyin muryarshi da yanzu ta sake yin sanyi

"To masha Allah Allah ya ƙara lafiya Sumayyah"faɗin Alhassan ɗin

Sun ɗan jima a ɗakin kafin su fita da kallo na bisu ina sake kallon yana yin Juraid da duk ya canza tashi ɗaya duk kuma na san ciwona ya sanyashi komawa hakan babu ƙoƙonto a kan soyayyar da Juraid yake gwadamin ita, gefen da suka tashi na kalla ƙatuwar leda viva ce cike da ban san mene ciki ba, Khadijah dake zaune na kallah a hankali na furta

"Khadijah ki kiramin Mama”

Da saurinta ta miƙe tana furta min "Toh Yaya”

Bata jima da fita ba sai gata sun dawo da Mama ɗin Mama ce ta kalle ni” Sannu Sumayyah ya jikin?, jiran Abbanku nake yi a sama miki magani”

Kai na ɗaga na daure na furta” Yawwah Mama amma magani ma Juraid ya kawomin suna cikin kayan nan"na ƙara sa maganar ina nuna mata ledar da suka ajiye

Mama wajen ledar ta nufa tana cicciro kayan ciki Yoghurt freshyo da lemuka peach a ciki sai Maltina da madara, leda guda magunguna Mama ta ɗago ta kalle ni tana riƙe baki

"Sumayyah hidimar nan ta Juraid tana yawa fa, ki duba fa ki gani?"s

Na ɗan yi murmushi a hankali na iya furta” Ai na gani Mama”

Mama ta jinjina kai” Allah ya tabbatar da alkhairi”

Daganan Mama ta zauna ta buɗe Yoghurt ɗin"Tashi ki karɓa kisha kafin na ɓallo maganin"

Daƙyar na iya tashi na zauna ina miƙawa Mama hannu ta ba ni magani miƙomin ta yi na fara sha a hankali

Mama da ta fara duba maganin na ga ta dubi Khadijah tana cewa” Ke! Khadijah tashi ki ɗaukomin yarinyata na barta ita kaɗai a ɗaki” Mama bata gama rufe baki ba Khadijah ta fice yau ance ta ɗauko A'isha shi ne ganɗokin nata da Mama bata bari su ɗauketa

Mama ta ɗaura da cewa” Yaran nan daga cewa Rumaisah ta fidda awarar nan duk suka ɓuya suka bita” Nidai shiru na yi Maman ta ɓalle maganin ta ba ni sannan ta fice

**"

"Ya jikin naki Sumayyah?"

Abbah ya yi maganar da yake tsaye ƙofar ɗakinmu ya leƙo da kansa

Na yi ƙoƙarin tashi zaune ina furta” Alhamdulillah Abbah ina kwana?"

"Lafiya ƙalau, za ki iya zuwa makarantar kuwa? kin san yau litinin"

Da sauri na ɗagawa Abbah kai jin zancensa na makaranta "Eh Abbah zan iya zuwa”

"Toh ki yi sauri ki shirya kin san zan dawo na wuce tallar kayan miyan nan"Abbah ya yi maganar yana ƙoƙarin barin wajen

Shaf na shafa'a da maganar makarantar tawa da su Ahmad sun jima da tafiya wayata na lalubo na duba agogo har tara da rabi lokacin da yau ma na ga Abbah bai fita da wuri ba, Batun saukin jiki na samu sosai tun a washe garin ranar lahadin dama yunwa ce musababbin komai, Da tun da Juraid yayomin wannan siyayyar da magunguna na fara sha na ji na warke sai dai rashin ƙarfin jikin nawa, Juraid kullum yana kirana waya a ƙalla sau uku a rana ko sau huɗu da tambayar yana yin jikina

Miƙewa na yi na lalubo uniform ɗin nawa da Malika jiya ta aiko ta amsa ta gogemin ta haɗa da nata, kayan na saka na shirya kafin Abbah ya leƙo har na shirya tsohuwar jakar makarantata na ɗauko na fito a tsakar gidan na sameshi tsaye da Mama da alamun shi har ya fito

Abbah ya kalle ni tare da cewa

"Yawwah ashe kin shirya da har ina cewa mamarki ko kin ji ba za ki iya ba”

Na girgiza kai” A'ah Abbah ai na ji sauƙi”

Mama ta kalle ni gami da hararata” Aifah ko bakiji sauƙin ba za ki ce kin ji saboda kin ji maganar makaranta, duk sona da makaranta ni dai ban kai ki ba ƙila Abbanku kika biyo dai”

Abbah ya yi murmushi ya furta” Ba dai ni ba mu da muke guduwa in anyi break sai dai ke”

Mama ta gyaɗa kai” Kwarai kuwa na yarda a hakan harka tara ɗumbin karatu lokaci ƙanƙani ka fito da first class kuma”

Murmushi Abbah ya yi "Ke dai Hauwa'u ban maganar bautawa bokon nan tawa da na yi a hana ido barci, gashinan babu aikinyi daidai da na sharar Office, Makaranta, Asibiti, babu ita ba alamarta da karatun addini na bautawa haka da na san tuni na ci riba biyu ga sanin ilimin yadda zan bautawa ubangijina yadda ya dace harma takai na sanarwa wasu na ruɓanyar da ladana ga. . . ga babu adadi dai”

Mama da yana yin damuwa ta ce” Wannan ɗin ma insha Allah ko ba daɗe ko ba jima za ka samu abin da kake buƙata koma fiye da hakan ubangiji shike da ikon komai sai lokacin da yaso ya nufa zai faru, kuma insha Allah shi ma za ka samu hanyar ruɓanyar da ladanka ta hanyarshi ilimin bokon indai zaka yi kyakkyawan aiki da duk ni'imar da ubangiji ya ba ka ai shike nan sai ka zama kafi malamin da bai anfani da iliminshi da saninsa ta hanyar da ya dace ba”

Abbah ya yi ƴar dariya "Toh Malama Hauwa'u bari nakai ɗiyar taki makaranta saina dawo da wuri gida dan yau na fahimci matar tawa wa'azi da nasihohi takeji”

Mama dariya ta yi "A'a fah kar muyi haka dakai, koma ka dawo sakata zan sawa gidan ina bawan Allah marashi yaga ta zama a wannan yana yin"

Ni dai da na fara gajiya da tsaiwar dan indai su Abbah da Mama suka buɗe shafin fira sai ka gaji ka ba su guri duk son jin labarinka bare kuma yau ɗauken zuwa makaranta nake yi muryar Abba ta katseni

"Mu dai mun wuce, na daka ta taki sai a taso ma makarantar ban kai ta ba”

Addu'a ta yi mana muka fito, makarantar bata cika nisa sosai ba Abbah ya kaini ya yi min cike cike da aka yi sa'ar makarantar gwamnati ba’a cika amsar wasu kuɗaɗe da ƙarin babbar sa'ar ma Vice principal ɗin sun yi class ɗaya da Abbah shi ne dalilin samun komai cikin sauƙi da na san ban da hakan sai dai Abbah ya ce a bishi bashi bashin da babu ranar biyanshi, sai da aka gama komai Abbah na tafi yabarni da Vice principal ɗin zai kaini ajin da za a sakani, Batun ko godiya Vice ɗin ya shata har babu adadi har haushin godiyar da Abbahn yake yi na yi ganin inda da mutunci ai komai ma za suyi min ba ma yafe ƴan ƙalilan ɗin kuɗin registration ba saidai tuno waɗanda suke sunfi kusa da Abbah ba suyi ba waye kuma zai yi

SS2A aka kaini Science class da tun shigata ajin na fahimci ƴar rainin hankali ne aka tara a ajin inda aka nuna min wajen zamana na nufa na zauna su biyu ne bencin na samu hakan ya sa na musu sallama da ban jira amsawarsu ba na zauna space ɗin da na gani ɗan kaɗan ka sancewar na gansu duk ɗin su biyun ƙanana ne ba su da girma kamar yadda nake, Su kam sunacan hankalinsu na kan firar da suke da ajin babu malami a gaɓar da aka kaini ajin, ta gefena na ga ta taɓo ɗayar ta ƙarshe tana cewa

"Ke! ana sallama muna can fira”

Tsaki na ji ta gefen ta yi ta na cewa "shi ne sai kin taɓoni za ki amsa sallamar ko sai duka mun amsa ne, Wa'alaikumussalam, na amsa na fiki lada”

"Inji wanne malamin kuma ai ladanmu ɗaya, tun da ɗaya ya amsa ai wakiltar da sauran ko sun yi dubu kuwa” ta gefen nawa ce mai faɗin hakan

"Injini nan Malama Maimunatu Hussain Kamal, tun da ta gefen ita shi sensory nerve ya fara kai mata saƙon jin"dariya amsar da wadda ta kira kanta Maimuna ta ba ni hakan ya sa na fara dariya ƙasa ƙasa

Ta gefena ta kalle ni” Kin gaji da gani da dariyar lamuran Maimunatu, yawwah sake shigowa ciki muyi gabatar da juna” ta ƙara sa maganar tana ƙara matsamin shigar na sake yi ciki da jin daɗin yadda na samu sit mate ɗin nawa may be duk ajin haka suke na yi judging ɗin su ne kafin na yi mu'amala dasu wanda hakan sam baidace ba a matsayinka na ɗan adam mai tunani

Ta gefen nawa da har lokacin banji sunanta ba ta yi magana” Yawwa ni sunana Hafsah Abdulmumin Nasir kefa?"

Na yi murmushi na furta” Ni kuma Sumayyah Abdullahi Khalil"

Maimuna ce ta sa baki yanzu a maganar tamu"Masha Allah sunan ya yi min daɗi Sumy nidai kin ji nawa sunan Maimunatu Hussain Kamal"

Na gyaɗa kai ina murmushi haka muka ci gaba da firarmu da na fahimci su Hafsah harkokinsu suke a ajin su kaɗai abunsu dan har muka gama firar malami ya shigo ba waɗanɗa suka waigo suka kallemu ko saka mana baki, iya ko ƙoƙari a wannan lokacin ƙanƙani na fahimci su Maimunatu na da shi tun a cikin yana yin firarmu da sukeyin ta cikin ilimi da fahimtar rayuwa daidai da shekarunsu harma sun shiga tunanin mai shekaru sittin ɗin da ya yi ta ba ilimi da fahimtar rayuwa da sanin ya kamata dan kam ba iya ilmin ba ne kaɗai abun lura ba mutum tun fil azal da hankali aka sanshi a saɓanin hakan kuwa dabba ne a siffar mutum ɗan adam, da farin ciki mai wanzar da zuci har ya sauka a fuska na ka sance har aka tashi makarantar litattafai na suka amsa za su ragemin note na Third term SS2ɗin. . . .

Na Cancanta (Kashi na 36)

Haka na ci gaba da zuwa makaranta tare da ƙarin mutunci dasu Maimunatu da sauran ƴan class ɗin mu wani lokacin da Malika muke tafiya duk da ba wani zuwaa suke ba yarda masu Wa'ec suka fara ragamar SS3 ta dawo hannunmu da tun da naje na samu har an raba temporary prefect kafin su fita a ƙara wasu ko a cire wasu ya danganta da yarda suka tsara, su Rumaisa ma da Khadijah makarantar ɗaya mukeyi sai dai tafiyar tamu wani lokacin tana banbanta, Soyayyata da Juraid kullum ƙaruwa take yi a zuciyoyinmu jiran na shiga SS3 yake yi ya turo gidanmu idan na tuna wannan ina sake jin daɗi Maimuna da Hafsah sai na ce sun mayemin gurbin Batul da Halima ga kuma Malika da take da babban matsayi duk da batakai Halimah ba saboda ita ɗin na fara san.

******

Yoghurt ɗin da ya rage guda ɗaya da Juraid ya kawomin na rarumo da yake gefena na ɓalle murfin jikina na kyarma a baki na kafa gorar ban cire bakina ba sai da na shanye tas na mayar da gorar hannuna ina bubbugawa wanda ya yi saura kamar tsohuwar mayya, ko dake ɗin indai yunwa ta yi yunwa inka samu abinci ka kanyi kamar mayyen sai da na gama aikin da nake yi tas da roba na yi Hamdala ina sake neman tsari daga yunwa dan ko ba abin da bata sanyawa duk juriyarka da ita saika gaji da zama cikinta ka nemi abinci ta kowacce hanya dan saita zamarma musababbin wahalar da ba ka iya tunani hausawa suke mata kirari da yunwa ba ƙanwar uwa bace dan ko da ƙanwar uwace da ta yi maka rangwame gami da alfarma dan ta zama wakiliyar uwa mahaifiyarka, ƙoƙarin Mama nake gani yadda take juriya da takura cikinta ta ba mu muci ta haƙuraa mafi yawancin lokaci duk da ta fimu buƙata sai dan ƙarin rufin asirin A'isha ƙarama ce da ko ta kai wata ko huɗu ne sam wannan jinƙan uwa ga ƴaƴanta Mama ba za ta iya aiwatar mana ba ban san iya lokacin da na ɗauka ɗauke da tuƙewar wannan tunanin nawa ba, Har sai da ƙarar ringing na wayata ya fargar dani na yi saurin dawowa hayyacina sa'ata guda ma yau ɗin Lahadi ce, sunan nata da na gani ya sa ni yin murmushi ƴar halak ɗince Halima duk da ban ambaceta ba amma tana da halaccin da za a kirata da kai tsaye ƴar halak ban ɓata lokaci ba na ɗauki wayar

"Assalamu alaikum"shi ne na ambata

"Wa'alaikumussalam, ina kika shige ne kwana biyu?"cewar Halima

Murmushi na yi Tamkar tana ganina daga nan na furta” Bakisan na yi zazzaɓi ba ne ba ma wai?"

"Ke kiji ƴar rainin hankali wazai faɗamin kuma, nakiraki washe garin ranar da ake taron nan wayarki a kashe na san, yanzu ya jikin naki?"

Na yi murmushi na ce” Na samu sauƙi, a ranar da mukayi wannan wayar na fara zazzaɓi”

Halima da muryar tausayi ta ce” Allah ya sa kaffarane, Allah ya sa ba jiya a yau kuke ba har yanzu hankalina ya kasa kwanciya sosai duk da bakimin bayanin komai ba”

 "A'a babu komai fa ai yanzu Alhamdulillah, ki ba ni labarin ya taron ya gudana mana”

"Uhmm kin faɗa na sani domin ki kwantar min shike nan dai ai na baki labari dai zaƙwaƙuran ɗaliban makarantar baki ga manyan kyautukan da aka. . . "

Banjira takai ƙarshen zancen nata na katse ta da cewa” Dan Allah fa waye ya raba musu kyautukan?"

Tsaki Halima ta yi tare da cewa” Matsalata dake fa baki cin ribar zance wallahi, waye zai raba kyautar inba mai makarantarba tun da shi ne ya zo taron, ke harda kema a bawa kyautukan shi ne fa muka riƙa kiranki a ranar bata zuwa, ana gama faɗar ki sai Ahmad da Rumaisa”

"Kin ga Halima kin san banasan kinamin ƙarya gaskiya” na yi maganar ina jiran amsarta dan ni kam ba wai yarda na yi ba duk da na san bana cikin sahun daƙiƙai amma a tunanina ban cancanci har a kira sunana a babban taro ba duba da akwai mutane da yawa da ko ba ajinmu ba suke gabana, maganar ta maidoni tunanin da nake yi

"Wato na saba ƙarya sababbiya ko?, shike nan ki samu wani ya baki labari”

Cikin muryar lallashi na ce

"Dan Allah kiya haƙuri haba Halimatussa'adiyya”

Tsaki ta yi min "Ai na gama magana kuma dama baki nemana ai, ki samu Batul ta ƙara sa miki labarin, ita da kike ɗaukar har shawararta”

Tana gama faɗar hakan ƙit ta kashe wayar, cire wayar na yi a kunnena na riƙe ta a hannun ina tunanin rigimar Halima wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa ina zan lalubo kuɗin da zansa a wayar bare na kira Batul yaushe raban ma na gaisa da Batul bare har na nemi shawararta sanin halin Halima ya sa ban aje zancen raina ba hanyar da zan kira Batul na ci gaba da nema dan Halima ta sakamin ɗokin jin labarin duk da inada yaƙin litattafai za mu samu kyaututtuka tunowa na yi da flashing na Beep call da akeyi a MTN duk da ba ko yaushe yake zuwa ba, hakan dai na yi cikin sa'a suka turomin message ya shiga hakan ya sa na ƙara yi baifi minti goma da yina ba ina ƙoƙarin tashi gurin na ji ƙarar wayata da saurina na ɗauka da tsammanin Batul ce ina ko kallon screen na samu shaidar ita ce ganin sunan da na yi mata saving raɗau a kan wayata hakan ya sa na yi saurin ɗagawa ban jira sallamarta ba na yi saurin rigata gabatarwa

 

"Assalamu alaikum Batul ya kike?ya su Umma?"

A ɓangaren nata ta ba ni amsa da cewa” Wa'alaikumussalam Alhamdulillah, ranar taron Tahfiz ɗinku mun kiraki ya yi sau ashirin amma bata zuwa”

Maganar da nakesan yi mata ta rigani farawa hakan ya sa na bata amsa da cewa” wallahi sai dai matsalar network ranar ma banida lafiya kuma, yanzu ba jimawa muka gama maganar da Halima har taji haushi da za ta ba ni labarin taron ta fasa”

Batul ta ce” Allah ya ƙara lafiya ai ba mu sani ba, meya haɗaku ke da Halima ɗin"

Abin da ya faru tsakanina da Halimah kaf na kwashe na bawa Batul, Ina gama baiwa Batul labarin ta yi ƴar dariya ta furta

"Kin ga kyale wata Halima nan, kyautuka aka rarrabawa zaƙwaƙuran ɗaliban dan mai ginin makarantar ya raba da kansa ku dai da aka kiraku ba kunan ba mu ga kyautukan da aka ba ku ba, ke har marasa fashi sai da aka bawa kyautukan nan kuma kuna ciki Allah kaɗai yasan meye a cikin jakunkunan nan"

"Wayyo Batul inama naje ni namaga mutumin nan nakeda burin yi ma”

Batul ta ce” Ke dai bari Sumayyah, ai mutumin nan ya yi da duk masu kuɗi haka suke da anji daɗi matuƙa da babu sauran mai kukan babu a duniya, kin ga a wajennan yarda ake yabanshi ance kyautar trillion ma indai yana dasu zai iya yi, ai ji na yi ina ma makarantarku nake yi, duk da cewar na ba za ta aka yi, amma na san tun da aka fara za a ci gaba dayi yanzu zakaga kowa ya ƙarawa dagewa” Da haka muka ci gaba da taɓa fira da Batul mai cike da faarin ciki

To be continued insha Allah

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments