Na Cancanta (Kashi na 37)
Gefen Mama nake zaune ina matsar ƙwalla gami da tunani mabanbanta da na ɗade da nasabarwa kaina dasu tun lokacin da Mama ta fara rashin lafiya mai zafin gaske kuma yau sati guda ke nan dole na sallamar da zuwa islamiyya bokon ma karatun bana ganewa tunanina na wajen Mama dafa awarar da komai ninake yi, A baya muna ganin farkon zazzaɓin nata da tasha paracetamol ya wadatar hakan ya sa ko su Gwaggo ba mu faɗa wa ba har saida mukaga paracetamol ɗin ya ƙare babu sauƙi Ahmad ya je ya sanar mata, maganar Gwaggo ta katse min tunanin nawa
"Yanzu haka za ki zauna, ciwo
fiye da sati ba a asibiti ba wani magani babu abinci ta kamaimai da za ki ci
haba Hauwa'u, shi ne dalilin ƙin faɗa
min ɗin ke nan?"
Cikin muryar ciwo na ji Mama na
cewa "A'a Gwaggo ba Sumayyah ta baki labari nasha magani ba sauƙin ne
dai ya kasa samuwa” Mama ta ƙara sa maganar tanajan nishi
Gwaggo da yana yin damuwa tare da
fusata ta ce” Dama ina za ki ji sauƙin da wani paracetamol tuni ciwo a
jikinki yaci ya cinyeki daga ke har yarannaki gakunan a fukace a wahale, aini
yanzu duk na gano gaskiya mijinnaki ne baya ƙaunarki shi ya akai bai koma haka ba
iye?"
Hawaye nake jin na zubomin daga
soma jin kalmomin Gwaggo, lallai ita ma ta kai ƙarshe wajen zafafa
"Gwaggo wallahi yanasona shi
ma baki ga yadda ya koma ma ba laifin na wajen ƴan uwansa” Mama ce mai faɗin hakan cikin wahala
hawaye nabin fuskarta
"Rufemin baki wallahi kona
taso na make bakin naki, da bakisan ciwan kanki ba ki kwana da yunwa ki tashi
da ita wanne ciwone ba zai yi nasarar kamaki ba da na yi zaton abun na
mutuncine, yanzu ina muke da arziƙin kaiki asibiti a wannan yana yin
dubunnai nawa za a cajemu shi garemu ko wani muka bawa ajiya”
Sai yanzu na sa baki tare da cewa”
Gwaggo Abbah ya tafi samo kuɗin
ai”
Gwaggo cikin tsawa ta kalle ni
tare da wurgamin harara
"Ubanki zai basa kuɗinko, ya gama yawan ciranin
nashi bai samo komai ba iyayensa ƴan uwansa sun koresa wa kike tunanin zai
basa, Ni dai ta kama naje mu sami rance a zo akaita asibitin, taji sauƙi kuma
a rabata da ubannaku mara zuciyar neman na kanshi na gaji daganin ɗiyata cikin wannan tashin
hankalin na yau daban na gobe da ban"Gwaggo na gama faɗar haka ta miƙe ta
fice fuu kamar iska ko waigomu bata yi ba
Kuka na kife kaina a jinyoyina ina
yi muryar Mama ta dakatar da shi tana cewa” Kin gani ko faɗan Gwaggo na yi gudu ya sa
na ce karku faɗa mata
gashinan kun faɗa ai
kunji daɗi”
Hawaye na goge na kalli Mama” To
Mama ya zamuyi ai gwara su sani ɗin
duk abin da zai faru ya fi zuwa da sauƙi” bata ba ni amsa ba hakan ya sa na ɗauki mafici na ci gaba da
yi mata fifitar da ita nake yi Gwaggo ta ce na bari ta isa
Sallamar Rumaisah na ji tare da
kukan A'isha da ta ɗauke
ta ta fita da ita tun ɗazu
dama da kukan aka fita da ita gashinan an dawo dashi, kuma Mama ko Nono bata
iya bata kwana biyu sai dai mu dinga ɗinkiramata
ruwa gashi bata isa a fara bata ko koko ba ita ma duk ta rame dama ba wani ƙoshi a
tare da ita, katse tunanin na yi jin Muryar Rumaisah
"Yaya wallahi taƙiyin
shiru na rasa ya zan mata tana barcin fa ta farka ta ci-gaba da kukan, Gwaggon ta
zo kuwa?"
Cikin yana yin fuskar damuwa na ce”
Eh ta zo, ƙara
ɗebo ruwa mu bata ɗin ko za ta yi shiru"
Miƙomin ita ta yi ta fita, na soma jijjigata
ko za ta yi shiru amma kukan take tsandarawa, Rumaisa cikin saurinta ta dawo da
ruwa a hannunta a ƙaramin kofi ta miƙomin tana cewa
"Kin gani ko ba za ta yi
shiru ba yarinyar nan"
Bance komai ba na amshi ruwan na
soma bata tana sha sau ɗaya
sau biyu ta zubo da shi ta ci gaba da tsanyara kuka da nake jinsa har raina na
rasa dame zan ji
"Kawo ta na fita da ita
tsakar gida na lallasheta karta damu Mama, amma wallahi yunwa take ji” Rumaisa
ta yi maganar da miƙo hannu ta amsheta ta fice
Mama na kalla idanta biyu amma ba
damar magana ita tasan irin ciwon da ke damunta
Muryar Rumaisah na jiyo daga
wajen, a lokacin A'isha ta rage kukan da take yi "Wai har yanzu Abbah bai
dawo ba ma ashe”
Na ce mata” Eh"yarda za ta iya
juyowa, dan ko Abbah ya jima da fita, tun kafin a tafi kiran Gwaggo, ya ce zai
je ya samo rancen kuɗi
akaita asibiti amma shiru ba mu jima da maganarsa ba muka jiyo sallamar Abbah ɗakin ya shigo ya zauna kusa
da Mama ya sai kuma na hango hawaye nabin fuskarsa
"Hauwa'u kiya haƙuri
idan ciwo ya samu marashi sai haƙuri, da anyi shawara dani kan ciwan gwara
ni ya kamani, bakiga yawon da na yi ba bansamu bashin ba shi kansa Musa da na
yi tsammani sai ba ni bashi da shi na san wasu ɗin
da na tambaya akwai amma duba da ba ni da abin biyan na san babu mai bani” sai
kuma ya sake rushewa da kuka kamar ƙaramin yaro, ni ma kukan ne na ji ya zomin
haka na fara yi tsakanin Abbah babu mai iya rarrashin wani cikinmu
****************
"Ya jikin Mama ɗin?"
Juraid ya tambayeni da yake tsaye
jikin ƙofar
gidanmu da ba dan naso ba na iya tsayawar a wannan yana yin da nake ciki, sai
dai banasan ya ga kamar na masa wulaƙanci dan tun da Mama ta fara ciwo bana
fitowa wajensa sai ko mun haɗu
wajen awarata, Yanzuma na kammala soyar ne ta dole ya tsayar dani ba dan naso
ba dan hankalina yana gida na duba halin da Mama ke ciki
Murmushin ƙarfin hali na yi na ce” Jiki
Alhamdulillah"
"Amma ya kamata akaita
asibiti fa tun da ga yana yinki ya nuna babu wani sauƙi, Ni zan kaita asibiti ɗin"
Saurin girgizamasa kai na yi jin ƙarshen
zancensa "A'a gobe ma insha Allah za a kaita asibiti Gwaggo ta ce ɗazu zataje ta dawo a kaita
amma na san yanzu ta bari sai safenne”
Kallona Juraid yake yi har na
gama maganar ya cire idonsa akaina” Kawai ki bari na kaita ta yiyu ba su samu
kuɗin da za su kaita
ba, Abbah kuma na san bashida halin hakan da tuni yayi”
Girgiza kai na yi na ce” A'a
mungode, zuwa da safen za a kaita, bari na shiga ciki”
Sallama muka yi na shigo ciki ina
saƙe
saƙe
a raina bana so Juraid yasan komai game da rayuwarmu sai dai kuma abun ya kasa
yiyuwa da hakan gaba ɗaya
baya min daɗi wani
lokacin saidai na sani Juraid mai tsananin sona ne da san abunda nakeso da muradin
shi ma ya ka sance da shi a tun kafin soyayyah ta shiga tsakaninmu yake ƙoƙarin
hakan bare kuma yanzu dan ajiyan ma da a ranar Malika ta bashi labari leda ya
ciko ya kawo na dubiyar Mama Abbah ya gaji da faɗan
hidimar sa gareni harya haƙura dan Juraid baya cikin marasa kirkin samari duk da ba ni ke
da zuciyarsa ba amma ina kyautata masa zato, Ina shiga kukan A'isha ya fara yi
min sallama sai kuma hayaniyar su Aunty Jamila ƙannen Mama da Aunty Maryam yayarta da tun
magriba suka zo shiga na yi ɗakin
Mama na fara yi na yi sallama na sake gaishesu, Ina ƙoƙarin zama kusa da Mama da
ko ido bata buɗewa
Aunty Maryam ta miƙomin A'isha da take kukan har zuwa yanzu
"Amsarta dan Allah ki yi
waje da ita ta zo ta isa mutane da kuka haba muji da abin da ya damemu na ciwan
ƴar
uwarmu, haka nan kawai ta saki jiki sai haihuwa take kamar akuya ai gashinan ni
baƙin
cikin kalar rayuwar da Hauwa'u take ciki nake kwana na tashi da shi baƙin
cikin auren Hauwa'u ban da da zuriyya saina ce ina ma ba'ayi ba”
Amsarta na yi na fara ƙoƙarin
barin ɗakin dan tun da
Aunty Maryam ta fara maganar na san sauran ma ƙannen Mama sun samu hanya, wanda maganar
ba ita bace mafita ba, amma a yaƙininsu ita ɗin
ce mafitar da ina tofa wani abu za su ce rashin kunya zan yi musu kuma ina kallon
kaina idan Rumaisa ko Khadijah ce a wannan halin ta yiyu na yi abin da ya fi nasu,
Har nafara taka ƙafafa da zummar barin ɗakin
na ji muryar Aunty Jamila
"Mu wallahi idan Gwaggo bata
dawo ba tafiya zamuyi tasa ta ɗin
da zamuyi ma mu ba halin kaita asibiti ba, gashi mijinnata ma waye yaga ɗuriyarshi, shi da zaman ya
kama tun da a gidansa ciwan ya kamata ai”
Aunty Asiya ta yi hanzarin ƙarfe
zancen da cewa” Ciwon yunwa da na baƙin ciki ba, aini wallahi yanzu mutumin
nan ya ficemin a raina dubi fa wulaƙancin da iyayenshi da ƴan
uwansa ke shukawa ai dole shi ma mu ga laifinsa mu kuma ji haushinsa”
Da wannan firar tasu na fice a ɗaƙin raina na suya yarda
yanzu dukkan laifin Abbah ake ɗaurawa,
dame zaiji na kasa ganewa, ina ji inama ba mu dawo gidaba, yarda kowa ya juya
mana baya wanda duk laifin da ya faro na ɓangarensu
Abbah, ɗakinmu na
shiga da A'isha da na samesu sunata kuka gaba ɗayansu
kasa zama na yi na nufo waje dan ni ma kukan nake ji na ƙoƙarin zuwarmin kuka dole
ne muyi shi duba da yarda lamuran kullum ke cakuɗe
mana, da yunwar cikin kama ta isheka ko babu ciwan Mama da na san yunwar ma ta
isa mutum kukan danma muna da juriyarta wanda hakan ya jawo mana samun sauƙi dan
da ba mu juriya nata tuni zancen sauran kyakkyawar rayuwa garemu ya sha banban,
Ƙofar
ɗaki na zauna na durƙushe
tsawan lokaci kukan A'isha na sake ta damin da nawa hankalin na rasa ina zan
dosa wazai ji kukana ya sharemin da gaggawa sai na tuna da ubangiji waman
yatawakkal Alal lah fa huwa hasbuh hakan ya sani jin sauƙin wani damuwar dake bijirowa
gareni matsananciya, sai dai kuma kukan nawa ya kasa tsagaita wa ina hango
rayuwarmu idan babu Mama ya za ta fara hango waɗanda
ke kukan maraici nake yi a yanzu da rayuwar ta iyayen ga yadda zumun ci ya yi tsallen
baɗaken aiwatarwa
inaga zumuntar da za a kirata a bayan rai ta ganin idon ta tuƙe sai
mai ƙarfin
imani da sanin meye zumun cin a musulunce mai kuma ƙoƙarin bin kuma abin da ya
sani ɗin. . . . . . .
. . . .
Na Cancanta (Kashi na 38)
Dafanin da na ji anyi ya sani ƙara riƙe
A'isha na miƙe
tsaye da rawar jiki
"Sumayyaah!"Jin Muryar
Aunty na yi kamar daga sama hakan ya sa na rungumeta da A'isha na fashe da kuka
ina cewa
"Aunty ki taimaka mana akai
Mama asibiti kar ta mutu cikin wannan mawuyacin halin"
Bayana ta shiga bubbugawa
"Ya isa haka kukan Sumayyah
share hawayenki insha Allah zan yi iya ƙoƙarin ganin Hauwa'u ta samu lafiya, zan
taimaka muku"
Jin hakan ya sani sakin Aunty, A'isha
dake kwanyara kuka ta amsa daga hannuna ta shiga jijjigata kafin ta ce
"Kaini ɗakin Mamartaku"
****
Aunty tana ganin Mama kwance ta ƙara sa
wajenta ta rushe da kuka
"Hauwa'u sannu Allah ya baki
lafiya na san na yi laifi a karo na biyu na kasa ci gaba da nemanki sai da ɗanki ya zo da kukansa yake
sanarmin"
Da na fahimci Ahmad ne ya faɗa mata fitar da ya yi ɗazu ashe gidan Aunty ya je
Aunty Maryam cikin kukan da Aunty
na farawa ta fara ita ma, ta ce
"Kin ga dai yadda jikin
Hauwa'u tashi guda ya canza Rumaisah, Gwaggo ta fita nemo kuɗi har yanzu bata ɓullo ba shi ma mijinnata
babu shi babu labarinsa”
Aunty ta girgiza tare da
tsagaitawa da kukan da take yi "ku fiddota asata a mota mu tafi asibiti, ai
zama bai kamamu ba, da kun sanarmin ba wanda zaije yasha wahalar nemo wasu kuɗi ai”
Aunty Asiya ta fara miƙewa da
ƙoƙarin ƙomawa
wajen Mama domin tayarda ita Aunty Jamila ma matsawar ta yi sukayi kama kama
suka fidda ta daga ɗakin
dan ko ciwon sati gudan yaƙara sabgar da ita
Aunty ta dube ni
"Yawwa haɗo mata kayanta ki kawomin
mota dan wannan jikin nata ba sallamar da za mu samu washe gari”
Kai na mayar ƙasa na
fara sosa ƙyeya,
dankuwa dai rabanmu da wanki saina ce ban san ranar ba babu sabulu ba omo sai
zamusa muke jiƙawa a ruwa mu barbada omo mu wanke
"Kina ji ana magana kin yi tsaye
kina sosa ƙeya
uwar taki kikewa hakan ke nan?"Muryar Aunty Maryam na ji ta katse tunanina
Kaina na ɗago na kalli Aunty da A'isha ke kafaɗarta tana jijjiga ta ta yi shiru
abunta kamar ba ita ce ke kukan da ta ɗagawa
kowa hankali ba
"Wallahi Aunty babu wankakku
ko ɗaya”
Aunty Maryam ta kalle ni taja
tsaki” Dama na san za a rina, kowacce taɓarɓarewa da lalacewa sun
tattara a kan Hauwa'u, ba'asamu abinci bama, inaga wanki”
Aunty ta katse Aunty Maryam da
cewa” mu je kawai Yaya Maryam na samo mata cikin nawa idan zan taho asibitin
Abban Jabir na san mu yake jira, ga A'isha karta ci gaba da kukan"ta ƙara sa
maganar tana ci gaba da jijjiga A'isha ɗin
Aunty Maryam bata sake cewa komai
ba suka fito ni ma na biyo bayansu, ban yi gigin binsu inda motar take ba dan
na san Aunty Maryam na ganin na bi bayansu faɗa
zansha wajenta ƙila ma ya fi na farko dan gaba ɗaya
laifin Abbah yana ƙoƙarin komawa kanmu, ina tsaye ƙofar gida har motar ta tashi ina share
hawaye da yiwa Mama addu'ar samun sauƙi, rufo ƙofar gidan na yi da tsoro ya fara
ziyartarmin lokacin domin mu kaɗaine
Abbah da Ahmad har lokacin babu wanda ya waiwayo gidan ɗakinmu na shiga na zauna na zuba tagumi da
hannu biyu ƙannena
nake kallo ɗaya bayan ɗaya yarda suke kwance a
cure sun takura kansu da alama ba barcin daɗi
suke ba ba ma da alama ba azahirin gaskiya ma hakan ne ka kwana da yunwa ka
tashi da ita, ga yarda zumun cin yanzu yake tafiya musamman kalar namu da shi
ne musababbin ƙara lalacewar rayuwar tamu izuwa wannan halin, tausayinsu nake
ji fiye da tausayin kaina, Bugun ƙofar da na ji ana yi ya sani miƙewa na
fito da tsammanin kodai Ahmad ko Abbah cikin biyu akwai ɗaya dayake kwankwasowa ko kuma dukkansu ne a
tare
"Wanene?" na yi maganar
ina ƙara
sawa kusa da ƙofar
"Nine” jin Muryar Ahmad ya
sani buɗe wa na matsa
gefe ya shigo kallonsa na yi shi ma ni yake kallo
"Ya jikin Mama?, ko ankaita
asibiti?"
Kai na gyaɗa na ce” Eh mana Aunty ta zo ta kaita yanzu ba
su daɗe da tafiya ba, ashe
kaine kaje ka faɗa wa
Aunty ɗin ma?
Ya ɗaga
kai ba tare da ya ce komai ba ya wuce ni ma ƙofar na rufe na biyo bayanshi na ci gaba
da magana
"Wallahi Ahmad Aunty na da
kirki tama tafi da A'isha”
Ahmad ya ce” Sosaimah Yaya, ganin
da na yi Gwaggo bata da alamun dawowa, Abbah ma shiru shi ya sa naje na faɗa wa Aunty na san za ta taimaka
mana”
Na ce” Sosaimah har suka tafi ba
wanda ya dawo daga Abbah har ita Gwaggon da take ta ke fuffuka”
Ahmad ya ce "kin san halin
dai Gwaggo gaba ɗaya
ta canza, inasu Rumaisah ba dai sun yi barci ba su ci abinci ba?"
Murmushi na yi na ce” kaima dai
Ahmad da wani zance abin da ya zamar mana jiki kwana da yunwar"
Haka muka ci gaba da firarmu a
tsakar gida har Abbah ya dawo muka ɗan
yi ƴar
fira duk dai a kan rashin lafiyar Mama da taimakon da Aunty ta yi mana da saida
Abbah ya dawo gida ya san da ankai Mama asibiti shi dama bai samo komai ba, mun
jima a zaune kafin muka tashi muka nufi makwancinmu
Ƙasa barci na yi na dai kwanta amma ji
nake daren yana yi min tsayi, tunanika ya dabaibaye ni da tsoro musamman na
rashin sanin halin da Mama take ciki ga rashin lambar Aunty bare na kirata na
ji halin da Mama ke ciki zan iya cewa barci ɓarawo
ne ya ɗaukeni amma ba
dan na yi shirin barcin ba
Kukan Khalil da asubar fari ya
tashemu daga barcin da muke yi lallashinsa muke yi dukkanmu amma ina shi gurin
Mama zaije, Abbah ne ya shigo ɗakinmu
ya zazzarewa Khalil ɗin
ido sannan ya yi shiru ya ce mu tashi muyi sallah ya kaimu gurin Mama ɗin, gari na wayewa Abbah ya
bawa Ahmad ya siyo mana koko mu kasha sannan muka sake wanke ƙafafu
kowacce ta daka gawayi ta wanke baki sannan muka fito gidan Aunty muka nufa
danshi Abbah bai je asibitinba ajiyan tun da dare ya dawo yaga ya yi babu kuma
mai rakashi, da wannan dukukun muka fito gida dan kuwa bakwai saura bata ma ƙara sa
ba
A rufe muka tarar da ƙofar
gate ɗin Ahmad
dukkanmu muka kalla
"Ahmad ya gidan a
rufe?" Abbah ne ya yi tambayar
Ahmad ya ce” Ai Abbah saimun ƙwanƙwasa tun
da safiya ce”
Rumaisa ce ta fara ƙwanƙwasa ƙofar
ni ma na taya ta, mun jima a tsayen kamar wasu korarru su Khalil zaune sukayi ƙofar
gidan ni kaina na gaji dan barcin bawai ya ishe ni ba ne, Sautin tafiyar da
mukaji ya sa mu dakatawa da buga gidan saida akazo gaf da ƙofar
gate ɗin mukaji
tsayawar tafiyar muka jiyo ana cewa wanene daga bakin gate ɗin
"Wanene?"Da muryar
namiji kuma ba muryar babban mutum bace da alamu cikin ƴaƴan Aunty ne ko Jabir ko
Muhammad da na sansu a hoto
Abba ya sassauta murya
"Nine Abdulllahi mijin Hauwa'u"
Buɗe
mana gate ɗin aka yi
muka shiga sai bayan mun shiga gidan na ga wanda ya buɗe mana gate ɗin
Jabir ne da na sanshi a hoto kuma bai wuce kamar Ahmad ba a tsaye saidai Ahmad
zai iya ɗan girmarsa
ko babu yawa
Ahmad ya kalla Jabir ɗin da murmushinsa” Allah ban
yi tsammanin ku ba ne ba, ku shigo ciki”
Bayansa muka bi zuwa hanyar falon
muna ƙoƙarin
shiga Abbah ya ce
"Bama sai kun shiga duka ba,
iya kwatancen asibitin ai za ta yi mana”
Jabir dake ƙoƙarin
saka ƙafarshi
cikin falon na ga ya dawo da baya da murmushi fuskarsa” Abbah ka shigo mana
Daddy ma yana falon ai, kuma Aunty ma bata shirya tafiya asibitin ba, na san
kuma ba za ta bari ku tafi ku kaɗai
kuma Ummi Hauwa'un taji sauƙi”
Haka Jabir ya lallaɓa Abbah ya yarda ya shiga
cikin falon shiru muka samu falon, babu kowa
Jabir ya kallemu"ku zazzauna
mana na kira Aunty ko Daddy, Daddy ma yanzu ya koma ciki”
Saida Jabir ya tabbatar mun zauna
ya gaishe da Abbah sannan ni sai su Rumaisa da suka gaidashi, sannan ya miƙe ya
bar wajen da ido na bi Jabir sosai ya kwantamin raina nake jinsa kamar jinin
jikina kamar Ahmad, yana yin tarbiyyarshi ta ƙara burgeni da shi da ko mu ɗin ba za mu nuna masa ba
jinjina wa iyayensa su Aunty nake da suka bashi tarbiyya duk da kuɗin da suke da shi haka kuma
sukayi ƙoƙarin
aiwatar kuma da abubuwa masu kyau idan suna tare da su duk da banga Muhammad ba
amma ina kyautata masa zato murmushi nake yi har ya ɓace a falon
Ahmad dake kusa dani ya taɓoni hakan ya sani dawowa
dai dai na aje tunanina” Yaya Sumayyah Jabir ne fa akwai hankali kin ganshi nan
kuma Aunty ta ce nama girme masa da shekara ɗaya
amma kin gani dai, kuɗi
shi baisa ya sangarce ba”
Murmushi na yi kawai” Sosaima na
gani Ahmad banga Muhammad ba?"
Tsaki Ahmad yayi” shagwaɓaɓɓe ke nan ai ita Aunty lallai shi ne auta shi
ya sa yake yin shagwaɓarshi
san ranshi a gidannan danma Daddy na masa tsawa” Ahmad da yake ɗan gida haka ya ci gaba da
ba mu labari jin sallama falon ya samu tsayawa da firarmu gaba ɗaya kallonmu ya koma falon
Abbahnsu Jabir ne ya ƙara so fuskarsa da murmushi amsa masa sallamar mukayi inda
Abbah yake ya nufa ya bashi hannu suka gaisa, sannan ya nemi waje kusa da Abbah
ya zauna gaishesa mukayi cikin sakin fuska ya amsa mana, sannan suka gaisa da
Abbah
"Wato kai jiya ba ka biyomu
asibiti ba sai yau ka bugo sammako kaji labarin matarka ta fara samuwa ko?, za
ka nuna mana matarka ce?"Daddynsu Jabir ya yi maganar da murmushinsa
"Ko ɗaya ba haka ba ne na fita tun yamma ajiyan na
samu na samu rance ko taimako na kaita asibiti amma haka aka dinga wulli dani
kamar inji ban samo komai ba, sanda na dawo kun tafi ga dare ya yi ga yara su ɗaya a gida shi ya sa na
zauna tare dasu"cewar Abbah
Daddynsu Jabir ya yi murmushi
"To Allah dai ya yassare wannan matsalar rayuwar babu mai kuɗi babu talaka yau ta isa
kowa”
"Toh Amin dai amma ganina
matsalar yau da gobe sai talaka” Abbah ya yi maganar na bisa da kallo yadda ya
saki jiki da Daddynsu Jabir ɗin
kamar dama cen akwai sanayya a tsakaninsu duk da alamu sun nuna hirace kawai
data kama suyi maganar Daddynsu Jabir ta katse min tunani
"Uhmmmm Allah dai ya ƙara
rufa mana asiri, aida Jabir ya faɗa
min ka toge ƙofar
falo"
Abbah ya ce” Eh mana kwatancen
asibitin ai za ku yi mana ba ma son ƙara muku wata wahalar tamu"
Daddy ya yi murmushi” Bar maganar
nan haka kada Rumaisah ta jika dan kuwa saiku ɓata
indai taji kace mata wahalar Hauwa'u, wahalar data damu iya Hauwa'u ce, domin
dai ban taɓa jin ko a
labarai aminta irin tasu ba sai dai makamanciyarta kullum dai zancenta Hauwa'u
dai sai dai haɗuwa ta
yi wuya tsakaninsu, sanda kuke ɗan
zuwa gida kafin ku dawo, mu kuma yawancin lokutan muna Abuja ka sancewar munfi
zama acan sai karatun yara yanzu daya riƙemu, tun jiya Rumaisah ta siyowa A'isha
madarar yara wai a haukanta ma ita A'isha ta zo ke nan bata komawa wajen
Hauwa'u"
Murmushi Abbah ya ɗan yi kaɗan ya ce” Ita ma Hauwa'u
gareta haka ne har sunan Rumaisah aka sanyawa ƴarta ta uku ka ganta nan Rumaisah"ya
ƙara
sa maganar yana nuna masa Rumaisah
Daddy ya ce” Masha Allah, Allah
ya ƙara
aminta tsakaninsu"
Duka muka amsa da” Amin"Daddynsu
Jabir ya miƙe
yana cewa” Bari na kira Rumaisah ɗin
na baro tana bawa A'isha madara
10:00am
Aunty ta riƙemu
saida muka karya muka yi wanka sannan muka fara shirin tafiya asibitin dan
Aunty ta ce tun da dasu Aunty Maryam ba sai mun je da sassafe ba, kuma cewa
take Mama taji sauƙi sai dai hankalina gaba ɗaya
yana wajen Mama ɗin
magana kawai nake yi amma ba dan hankalina yana kwance ba, A ɓangaren Abbah ma hakanne da
Daddynsu Jabir suketa fira duk da na san hankalin Abbah shi ma baya jikinsa ko
abincin kaɗan ya ci, Su
Khalil kuwa suna ganin A'isha hankalinsu ya kwanta ko damuwa ba su yi ba, Daddynsu
Jabir ne ya kaimu asibitin harda Aunty da su Jabir ka sancewar weekend ne babu
makaranta. . . . . . .
Na Cancanta (Kashi na 39)
Asibiti mai kyau aka kai Mama da
alamun ma na kuɗine, haka
Daddynsu Jabir ya yi parking muka fito kai tsaye ɗakin
da aka kwantar da Mama muka nufa tun a bakin ƙofar muke jiyo tashin maganganun su
Gwaggo da Aunty Maryam handling ɗin
ƙofar
Jabir ya murɗa, Gaba ɗaya muka tura kanmu cikin ɗakin da sallama bakinmu
Mama idona ya fara tozali da ita,
kwance take a gadon da robar jini a hannunta yana tafiya idanunta rufe yake da
hakan ya sake tabbatarmin jikin Mama babu zancen sauƙi sai dai na wajen
ubangiji
Ƙarasa shiga cikin ɗakin mukayi da su Gwaggo muka tarar dasu kan
kujerun Roba guda biyu kusa da gadon da ɗaya
Gwaggo ce ke kai ɗayar
kuma Aunty Maryam, tsugunne mukayi gaba ɗayanmu
muna gaishe su da tambayar ya mai jiki
Su Abbah ma haka suka yi, Miƙewa
mukayi muka ƙara
sa gefen gadon da Mama ke kai muna mata sannu duk da ba amsawa za ta iya yi ba
ba, Abbah dake tsaye bayanmu muka dawo ƙasa kan tabarma muka zauna shi kuma ya ƙara sa
gefen gadon yana jerawa Mama Sannu
Gwaggo da tun shigowarmu na ga
yadda ranta yake a haɗe
na ji cikin ɗaga murya
tana cewa
"Hauwa'u bata buƙatar
sannunka Abdulllahi ganinka ma bata buƙatar yi saboda bata farko ta ganka ba, ka
tafi yawon da ba zai amfaneka ba saboda ba kaine ka haifarmin ita ba idan ta
mutu wata matar za ka canza, shi ya sa ka rainawa mutane hankali gaka gaka za
ka je ka dawo ka samo kuɗi
babu kai babu alamunka”
Daddynsu Jabir ya juya inda
Gwaggo take da har da yakai bakin ƙofa yana shirin fita
"Haba Gwaggo baikamata ki faɗi hakan ba gashi gaban yara,
kuma asibiti koma mene ya kamata ayi haƙuri ayi masa uziri, tun da gashi ya zo
yanzu"
Gwaggo cikin yana yin ɓacin rai ta sassauta murya
ta ce” A'a Zaidu ai banso ayi masa wannan uzirin ba, ta kwana matarshi ta fara
tarar da hantsi bai zo dubata ba dama na san ko ba daɗe ko ba jima ungulu gidan ta take komawa ya bi
zugar da ƴan
uwanshi a kullum sukeyi masa akanta saboda ta fara tara ƴaƴa, shi ya sa bai damu da
ciwonta ba”
Daddynsu Jabir da na tabbatar shi
ne Zaidu ɗin goshi ya
dafe” Kash Gwaggo ya kamata ki yi shiru ko ba dan yara ba dan ita Hauwa'u ɗin ki duba fa a yana yin da
take ciki mana Gwaggo, yanzu ma wajen likitan zan koma, kuma Abbahn Ahmad
bakwai ba ta yi ba ya zo gidana yamin bayani kuɗi
yake nema bai samu ba tun da ya fita da yadawo dare ya yi ga yara babu damar
yabarsu ya taho neman asibitin da aka kai matarshi ko ya fara tafiya neman
gidana dan na san bai sani ba, ki masa uziri, ya kamata ki tausaya masa
magidanci kamarsa yana fama da abincin da za suci, ba shida wani mataimaki sai
Allah sai wanda yaga Allah ya yi koyi da annabin tsira(SAW)"
Jin kalaman Abbah Zaid ya sa Gwaggo
kuma fashewa da kuka” Na gode Zaidu duk da ban haifi matarka ba bare kuma kai
da haƙuranka
talatin na ganka da yaranka sai na ce a jiya ma na sanka, amma ka tunasar dani abin
da namanta, inaso na ƙara wa zuciyar surikina wani mikin da yake cin ransa”
Sai kuma ta juyo ga Abbah ɗin tana cewa” Abdullahi ka
yafemin dan Allah gaba ɗaya
damuwar Hauwa'u mantar dani komai take yi tana cikin jarrabawa Hauwa'u ina
tausayinta da yaranta, da babu Rumaisah tayiyu wani labarin ake bana Hauwa'u ba
yau na yarda komai daga Allah ne amma akwai sababi, Allah ya kawo muku canji na
alkhairi waɗanda suka
zalinceku Allah ya yi gaggawar saka muku waɗanda
suka muku alkhairi Allah ya yi gaggawar biyansu da alkhairi linkin waɗanda suka yi muku"
Gaba ɗaya jikinmu sanyi ya yi Abbah ya goge hawayen
dake bin fuskarsa duk juriyar Abbah yau gaza ta yadai daure ya ce” Amin
Gwaggo"
Abbah Zaid ne ya fasa murza
handling na ƙofar
ya dawo cikin ɗakin
"Abdullahi taho muje wajen
Doctor ɗin, ka ga da
ba'ayi maganar nan ba na manta ban ce ka taho ba” Daganan suka fice tare da
Abbah
Aunty da take tsaye tana goge
hawayenta, Aunty Maryam ta miƙe gami da kallonta cikin sanyin murya
tace
"Ga kujera Rumaisah kizo ki
zauna mana”
Aunty ta girgiza kai "A'a
Yaya Maryam nan ma ya yi ina zama A'isha farkawa za ta yi”
Aunty Maryam ta ce” ƙyaleta
inta farka sai ki bawa Sumayyah ko takwararki su lallasheta, Ni gida nakeson
zuwa tun da kunzo dama jiranku ya tsaidani”
Aunty ta ce” Eh haka ne ya kamata
ki je gidan aga halin da ya ke ciki” ta ƙara sa maganar tana dawowa inda Aunty
Maryam ta tashi ɗin
*********
Aunty Maryam na fita a ɗakin su Abbah su ka shigo
tare da likita ledar jinin da ya sanya mata ya kalla da take daidai rabi
"Allah ya bata lafiya, matsalar
da na faɗa muku ita ce
dai ba wani damuwa bayan ita” Likitan da suka shigo taran na ji yana ambatar
hakan yana danna inda jinin ke ƙara gudu
Su Abbah suka haɗa baki gurin cewa
"Amin"
"Yara gaba ɗaya sun ruɗe sunga Mamarsu haka kwance”
Abbah Zaid ya ɗaura da
faɗar hakan
Likitan ya yi murmushi yana
kallanmu "Karku damu insha Allah mamarku za ta samu lafiya da wuri”
Muka ɗaga kai alamun gamsuwa duk da ni nawa ƙasan
zuciyar yana tantama dan na ɗauki
babban ciwo ne kaɗai
kesa ayima mutum ƙarin jini kuma mutum yakai tsawan lokaci yana sharar barci, na
dai fi tsammanin yunwa ta yiwa Mama kamun kazar kuku, Saidai yadda likitan ya
ce Insha Allah hakan ya sa na ajje wancen tunanin na sallama komai ga ubangiji
Mai kunfayakun yana cewa ka sance sai ya ka sance komai da ikonsa yake samun
gurɓin ka santuwa, Ah
saboda shi ne gaba ɗaya
wasu tunaninka ba su samun gurbin zama a zuciyata bare su gurɓatar da tunanina na yarda
komai ya yi farko zai yi ƙarshe kuma duk abunda ya yi tsanani ya yi tsanani ƙarshe
sauƙi
zai haifar na har abada amma saida izinin ubangiji ɗin in yaso sai rayuwar ta ƙare a
haka amma akwai gidan madauwami da idan ka yarda da ƙaddarar Allah gareka sai
yama musanye koba gidan duniya ba toh a gidan Aljannah
Muryar Abbah Zaid ta katse min
tunanin da nake Aunty ya kallah
"Ba yanzu za ki je gida ba
ne zan wuce ne tun da an gama komai”
Aunty da take bawa A'isha madara
tace” A'a zani mana ka jiramu madarar A'isha ma ai ya ƙare saina haɗo wata”
Abbah Zaid ya riƙe baki
da ya dubi Abbah"Abdullahi kaji dai Rumaisah kukayi wasa za ta muku magaji
da ɗiyarku fah"
Abba Zaid Aunty ta hararesa ta
wasa tare da cewa” Nidai banasan irin wannan abun fa haɗa rigima yayima yawa”
Abba Zaid ya hararareta shi ma” Faɗar gaskiyar ce haɗa rigima, shike nan na yi
shiru gaki ga masu ƴar nan"
"Ai ɗiyartace tun da yarinyar Hauwa'u ce saisu ma
fini iko da ita tun da ɗiya
macece” Abbah ne maiyin maganar da sai yanzu ya saka baki a zancen
Gwaggo kuwa ci gaba ta yi da fifita
Mama ko uhmm bata ce ba dan da alama ta barwah yara firarsu ne sai dai murmushi
da yake ɗauke da
fuskarta da ya yi nasarar ɓoye
tsintsar damuwar da lamarin ciwan dake damun Mama
Abbah Zaid inda muke zaune dasu
Jabir ya kallo tare da cewa” Kunga Jabir ku taso mu fara fita tafiyin hanzari
kuma kunsan za ki yi girki ?"
Aunty ita ma miƙewar
ta yi "A'a nifa na shirya, da Sumayyah zan tafi ta tayani aikin girkin ma”
Gwaggo maida dubanta ta yi ga
Rumaisah"Anya kuwa hidimar nan bata yawa Rumaisah kin ga fa su Asiya duk
anjima kaɗan za su zo
kuma kowacce za ta zo da abincinta ga Sha'aban na san zai baiwa ƙannensa
su ƙara
wani a kan na gida ai. . . . "
Da sauri Abbah Zaid ya tsaida
Gwaggo maganar da take ƙoƙarin ci gaba dayi” A'a Gwaggo babu wata hidima ai Rumaisah
komai ta yiwa Hauwa'u ina jin bata faɗi
ba ai abotar makaranta wani lokacin sai ta ma ɗara
wani zumun cin na jini musamman yadda abun ke taɓarɓarewa ki mana fatan Allah
ya karɓi
ayyukanmu"
Aunty ta yi murmushi ita ma ta
cewa Gwaggo"Toh Gwaggo idan banma Hauwa'u ba ma waye zai mata bata da shi mijinta
babu kuma babu sai rufin asiri da za a ce kawai, tare muke komai daga Primary
har junior, muna ma waɗanda
alaƙarmu
bata kai haka bama, shi arziƙi kyawunka da shi ka morawa wasu ai, shi
ne zai sake yalwata”
Itadai Gwaggo rasa bakin magana
ta yi sai zuba sanya albarka take wa su Aunty Ni kaina Aunty da rayuwarta ta
gama burgeni hakan ya ƙara min san Aunty yadda ya kamata a raina Aunty na ansarwa
Aisha na rungumeta muka fito muna gaba nida su Jabir muna fira su Aunty na
bayanmu dan mun rigasu fitowa da Jabir rabin firar tawa nake yi dan shikam
Muhammad saboda Abbah Zaid ya jera damu a yanda na fahimta ke nan dan muna
tafiya yana hangen Aunty a haka muka ƙara sa parking space na asibitin inda
Abbah Zaid ya yi parking motarshi muka ƙara sa muka tsaya jikin motar, kafin su
Auntyn suka ƙara
so suka buɗe motar
muka shiga gidan baya a motarm firar muka ɗaura
da Jabir ɗin duk da ni
a ɓangarena firar
batamin wani daɗi
yarda tunanin ciwon Mama ya addabi zuciyata. . . . . . . . . . .
Na Cancanta (Kashi na 40)
"Sumayyah har yanzu baki ƙarasa
blending ɗin ba”
Muryar Aunty da na jiyo ta
dakatar dani daga blending kayan miyan da nake yi a electric blander da duk
lokacin ta nuna min yadda zan yi aiki da ita juyawa na yi na kalleta mai take
soyawa lokacin tana gaban Cooker Gas Mai zaune jikin lokar kitchen ban iya gane
mai nawa ba ne saboda ba ma anfani da shi kuma ba kalar na gidan Abbah Hashim
ba ne ba ajiye tunanin na yi na ce
"Eh Aunty amma nakusa gamawa”
"Ok ki yi a hankali fa idan
ya soyo man sai a fara saka wanda kikayi blending ɗin, shi ya sa nafisan akaimin markaɗe ya fi saurin aiki toh
kina jina dƙ
mutumin naki Jabir kansa ke ciwo"
Murmushi na yi na ce "Eh
Aunty tun a mota ya faɗamin
da gaske yake”
"Hmmm baki san Jabir da ƙin
aike ba Sumayyah, danshi harma yafisan na barmasa ya yi girki, shi kuma
Muhammad shiririta garesa ne” Cewar Aunty ta ƙarasa maganar tana ɗaukar robar kayan miyan da
na zuba wanda na gama markaɗawar
masu yawa, Kayan miyan suna da yawa ba laifi duk tsadar da sukeyi ita Aunty
bata gani ba acewarta ai Mama inta farko irin wannan abincin take son ci mai
miya mita, shi ya sa har kifi mai yawa Aunty tasa Abbah Zaid ya siyo dan kafin
mu gama aikinsa Aunty ta nuna min yadda zan yi blending ɗin na fara
"Kamar kukan A'isha na ji” tayi
zancen tana ci gaba da juya kayan miyan da tagama zubawa
Kunne na kasa cikin falon da ni
ma kamar kukan na ji kallonta ta dawo gareni ta ce
"Kin ji ko kema?"
Na daga kai "Eh Aunty
wallahi kamar kukanta”
Aunty ta dube ni” Kin ga cire
mana kokwanton jeki dubota, ƙila Muhammad ya bar falon ma a jiye
blending ɗin maza ki
wanke hannu"
Umarnin Aunty na bi na Tara
hannuna cikin fanfon wanke wanken kitchen na sa omo na wanke cikin sauri na bar
kitchen ɗin
Ban same ta tana wani kukan a zo a
gani ba dan idanta rufe take kukan alamun tashi take yi, hakan ya sa na ɗauke ta na fara jijjigata
dandanan ta koma barci ganin Muhammad baya falon ya sa ɗauki towel ɗin
ta na rufe ta da shi na koma kitchen ɗin
Sallama na yi Aunty ta amsamin ta
dubemu nida Aisha ɗin
"Kukan take ko?"
Kaina ɗagama Aunty daganan na ce” Eh Aunty za dai ta
fara tana ƙoƙarin
tashi barci ne, kin gama ta koma”
Aunty ta gyaɗa kai” Wato shi Muhammad ya
fice ya barmin yarinya a haka yakeson ƙanwar zai dawo ya sameni ne”
Dariya na yi kaɗan jin zancen Aunty dan
yadda na san Aunty da Muhammad bata bugunsa ko faɗa
Jabir ya ce batasan a yima Muhammad ta ce mai babban suna ba’a masa faɗa bare zagi, duk da dama
ban da ƙin
jin kaɗan na yarinta
baya komai saidai da ɗan
gatane
"Kina dariya ke nan Allah
kuwa, dan Abbansa na hana ni make yaron nan wani lokaci, juyo na sa miki ita
baya, kema na lura wahala kike so ki baiwa baiwar Allah"
Ni dai shiru na yiwa Aunty jin
zancenta dan Jabir yana faɗa
min za mu fito asibiti cewa Muhammad na kuskurewa sai Aunty ta ce Abbah Zaid ne
kaza kaza alhalin ita ce, Miiƙa mata A'isha na juya baya ta sakamin ita
na ɗaure zanin
Cabbage da Gurji da Karas da
sauransu Aunty ta ba ni yankansu na zauna brander a kan kujera a ƙofar
baya ta kitchen na fara yankawa ganin banajin daɗin
aikin saboda goyo saidai ina miƙewa na sauke A'isha Aunty za ta ce a'a ba
za a kwantar da ita a barta ita ɗaya
ba wani gata nake gani Aunty na nunawa A'isha dan ko Mama albarkarshi, Wani
girma na uwa na baiwa Aunty a zuciya irin yadda take kulawa da lafiyar Mama a
yanzu ita da mijinta danko Aunty batayi hakaba ko waccen maganar ni banga aibun
Aunty ba duk da a kan mahaifinane dan a tunanina a zuciya da ɗan uwan nasu aganii za su
iya ɗawainiyarsa su
masa abin da suke yaudararsa ya rabu da Mama za suyi masa ɗin, sai nake ji ta cire min
wani daga cikin ciwan na idanuna duk da ban shekaru ban taso da saninta ba amma
ta fiye min Aunty Mubaraka, Aunty Maimuna da sauran su musamman Aunty Asma'u ma
da har zuwa yanzu abunda tayi min ya kasa barin tunanina nakan ji ciwo mai
tsanani a raina na tarin girman laifinta da zuciyata take gani
"Ɗauko carpet ki zauna ƙasa
mana Sumayyah za ki fi jin daɗi
ga lokaci yana tafiya ma” Maganar Aunty ya katse min tunanina
Juyawa na yi na kalli daga inda
maganarta hangota na yi ta leƙo da kanta inda nake ɗin, cire hannuna na yi a
cabbage tare da wuƙar ina ƙoƙarin miƙewa na ce "Toh Aunty"
Cikin kitchen ɗin na dawo ina ƙoƙarin
wuceta ta ce
"Yawwa Sumayyah idab baki ga
ko ɗaya a falo ba, ki
duba ɗakin Jabir ko na
Muhammad koma nawa”
"Toh Aunty" Ina zuwa
falon na tarar carpet sallaya ɗin
na ɗauko na dawo na
zauna na zauna na ci gaba da aikin wajen 1:30pm na rana muka gama komai dan
aikin Gas ba dai sauƙi ba, Muna kammalawa Aunty ta dube ni
"Yawwa ki je ki watsa ruwa
sai ki yi alwala akwai zafi ki kwantar da Aishar a gado ki mata addu'a kafin ki
shiga wankan"
Nace "Toh Aunty"
Badan na so ba dan mun yi wanka
da safe gidan Aunty ɗin
kuma yanzu ba a cikin rana mukayi aikin ba haka na fito na shiga bed room ɗin Aunty dake ƙasa da
a nan da safen ma mu kayi komai A'isha na kwantar na mata addu'a da Aunty ta ce
na yi Sannan na tura banɗakin
na shiga Aunty tana da tsafta sosai a ɗari
ɗari na yi wankan da
alwala ma kuma sake wanke bayin yadda na samesa na fito ina jin wani daɗi jikina ga ƙamshin
sabulu mai tsada da nake yi dan Aunty sabon soso da sabulu kalar wanda take
wanka da shi da na ganshi a bayin da safe shi ta aje mana da yanzu ma inda muka
barshi a bayin na tarar da shi
"Alhamdulillah"na furta
a hankali dan kuwa mai wanka da omo ko sabulun wanki ya yi da ƙaton
sabulu haka mai ƙamshi da ban san sunanshi ba Aunty ta cire kwalin ta kawo mana
Mai vaselline dake saman madubi
na ɗauka na fara
shafawa kaɗan ƙaɗan saboda zafi ina cikin
shafawar na ji ƙwanƙwasa ƙofar Handling ɗin
ƙofar
naje na murɗa na buɗe yadda na yi tsammani
Aunty na gani matsa mata na yi ta shigo ciki kallona Auntyn tayi
"Ba dai kayan jikinki za ki
mayar ba?"Kayana dake saman drower ta jikin gado riga da ɗankwali da zanin ke ɗaure jikina nakai dubana
kai, Sannan na kalli Aunty na ce
"Eh Aunty ai banzo da wasu ba”
Auntyn ta girgiza kai” Oh
Sumayyah to ba ga nawa ba sai kisa, tun da ai sun ɓaci wannan ɗin
kin yi wanka da zanin ya yi laima bare ma akwai na Intisar sabo da na yi mata ta
zo hutu ban sani ba ta gudu gidansu ni kuma na ce nafasa bata kayan bari na ɗauko miki kisa ɗaya daga ciki” ta ƙarasa
zancen tana ƙoƙarin
buɗe Sib ɗin ta
Material mai kyau Aunty ta
fiddomin a Sib ɗin ta
ajemin gefen gado
"Yawwah gashinan ki saka ita
Intisar kin ga tama kanta ai”
Murmushi na yi sannan na ce” Na
gode Aunty"
"Yawwah ba ki yi sallah ba
ko?"
Kai na ɗagawa Aunty na ce” Eh na yi alwala
Daddynsu Jabir yana jira zamuyi Jam'i sun sha
barci sun makara zuwa masallaci yi maza ki saka kayan"
Tayi maganar ta na maida kanta
cikin Sib ɗin kaya ta
fiddo ta yi hanyar fita
"Yawwah ki fa zura kayan
kawai in za ki saka powder ki bari ayi sallar"
"Toh Aunty"
Tura ƙofar ta yi ta fita ni
kuma na ɗauki kayan
rigar na ware ina warewa na ga pant a jiki jin daɗi
na yi sosai dan dama ya yi laima na jikin nawa brezia na saka na zura material ɗin da ya yi min cif kamar
an gwada danni aka yi shi gashi mai kauri ne sosai ko ba underskirt za ka sakashi,
nawa under skirt ɗin
da yasha jiki ya koɗe
Black color ne da aka ce kalar dauɗa
sai dai a zahirin gaskiya baƙar kala tafi kowacce kala saurin yin
datti da bayyana shi ina sawa na ɗaura
ɗankwali na sa hijabi
na fito a falo na samesu har sun tada sallah na koma baya naja sahu sai ga
Aunty ta zo ta jera dani mun yi
Da muka iddar Addu'a mabanbanta
Abbah Zaid yake kwararowa kamar ba sallar farilla mukayi ba aka ma Mama addu'a
mukayi Azkar muka shafa addu'a
"Daddy Ina yini?, Aunty Ina
yini?"Jabir da Muhammad na jiyo sun faɗa
cikin haɗa baki
"Lafiya ƙalau"naji
Muryar Abbah Zaid ya faɗa
ita ma Aunty da murmushi ta amsa da "Lafiya ƙalau"
Yadda su Jabir sukayi ni ma na yi
na gaida Aunty da Abbah Zaid cikin kulawa suka amsamin
Su Jabir dake ƙoƙarin
tashi Abbah Zaid ya daka musu tsawa "Ina zakuje?, wuce ku zauna ita
yayartaku ba ku gaidata ke nan?"
Kai suka girgiza sannan suka gaishe
ni suka miƙe
Abbah Zaid inda muke da Aunty ya
juyo ya kalli Aunty
"Kin bawa Sumayyah wasu
kayan tasa ko?"
Ta ɗaga
kai” Eh Daddyn Jabir na bata na Inteesar"
"Ok ya yi ki zubo abinci
muci sai ku tafi asibitin su Muhammad su wuce islamiyya”
Aunty ta ɗan ɓata
fuska” Mu tafi dai zakace ka san banasan driving wallahi”
Miƙewa Abbah Zaid ya yi ya ce” Toh ki zauna
sai dare ni dai zan koma tun da ba za ki yi tuƙin ba, kuma zan kaiwa Maman Inteesar motar"
Miƙewa ita ma Aunty ta yi ta ce” Ina ba zai
yiyu ba zan iya ma”
Abbah Zaid dariya ya ɗan yi ya koma kujera ya
zauna ya ce
"Toh na ji karkimin bori
zubo mana abincin muci”
Hararar wasa Aunty ta ma Abbah
Zaid ta ce” Ni ce ma zan yi borin ko?"
"Bafa borin komai nake nufi
ba Malama”
Kwafa Mama ta yi ta wuce tana
kirana na zo na taya ta fiddo abincin a dining Area muka shirya su Jabir suka fito
muka ci gaba ɗayanmu, muka
ƙara
sa shiryawa zuwa asibiti a babbar kula ba laifi Aunty ta zuba abincin asibiti
ta zuba miya a ƙarama food flask cabbage da sauran a wata ƙatuwar
roba sai farantai da ruwa na manyan ledoji masu sanyi, Jabir ya tatayani
fitarwa muna sawa a boot ɗin
motar Aunty mai kyau sosai, Aunty ta tsaya Kitchen lokacin haɗawa A'isha madara
Abbah Zaid ya buɗe mana gate muka fito tare
da su Jabir za ta ajesu a makarantar Islamiyya
Sosai rayuwar gidan Aunty take ƙara
burgeni musamman yanzu a ɗan
yinin da na yi ina sake fahimtar kyawun rayuwar gidan komai cikin sanin rayuwa
sukeyi da ƙoƙarin
shimfiɗa tarbiyyar
gidan a tafarkin tsira, ba suda wulaƙanta kowanne ɗan adam dan da suna yi duk yadda suke da Mama
ba za ta so ƙara
zama da ita a yadda rayuwarmu take a yanzu ba da sai ta mana wulaƙanci
fiye da na Aunty Asma'u a matsayinta na karatu kaɗai
ya haɗata da Mamarmu
bayan wannan ba zance ga wani abu ba mijin Aunty bai san Abbah ba dan a yadda
Jabir yake ba ni labari Abbah iyayensa a porthacourt suke zaune shi ma
kasuwancin iyayensa da yake yi a gida ya maidoshi Gwarzo, Amma suka karramamu
da mutuntamu karamci da Abbah Imran ba zai iya ba bare kuma Abbah Hashim kuma
zumun cinmu ya gama lalacewa tsakaninmu dasu ban kuma san yaushe ne zai dawo
yarda yake ba, sai dai roƙona Allah ya ganar dasu kawai da mu kanmu ɗin. . . . . . .
Na Cancanta (Kashi na 41)
3:02pm shi ne ya yi daidai da ƙara sa
parking ɗin mu a
parking space na asibitin cire kaina na yi daga kallon agogon cikin motar na miƙa
hannuna na taɓa
handling ɗin motar na
buɗe zancen Aunty ya
katseni tana miƙo hannu
"Kawo Aishar ki sauka saina
miƙo
miki ita” ba tare da na yi musu ba na miƙa wa Aunty, Aisha, Ni Kuma na fito daga
wajen ina fitowa Aunty ta fito da A'isha a kafaɗarta
rufe murfin ƙofar
ɓangaren da na fito na
yi Aunty ma na ɓangaren
da ta fito ta yi ta sawa motar key
"Yawwa Sumayyah dawo tanan
na goya miki ita mu ƙara sa Boot mu ɗauki
abincin"Abin da ta faɗa
ɗin na aiwatar ba tare
da na yi musu ba, kuma ba tare da na ji komai ba bare yazamarma zuciyata ƙorafi
dan ko Mama ɗin haka
take mana ɗin ma indai
munanan mune masu goya A'isha da ɗaukar
ta ni ma raino yabi jinin jikina zan iya cewa
Ƙofar boot ɗin
Aunty ta buɗe muka
ciro kayan sannan ta rufe Boot ɗin
muka ɗauka muka ƙara sa
zuwa ɗakin da Mama
take kwance
A brander ta kusa da ɗakin muka tarar da su
Gwaggo su Rumaisa sai su Aunty Jamila sun shimfiɗa
tabarma sun yi zazzaune ga kulolin abinci gefen su gaisawa mukayi dasu
Gwaggo ta dubemu ni da Aunty da
muke ƙoƙarin
aje kulolin namu abincin gefen Gwaggo
"Har da wata hidimar haka
Rumaisah?, Ai da kin bari ma su Jamila duk sunzo mana da shi yanzu muka gama ci”
Cewar Gwaggo
Aunty ta ɗago fuskarta ta ce” A'a Gwaggo ai ba wata
hidima abincine kuma ba yawa ma sosai, na su Jamila ai dabanne nawa ma dabanne,
zuwa anjima sai aci wannan"
Gwaggo ta riƙe baki”
A'a Rumaisah akwai fa hidima tun jiya da aka kawo Hauwa'u kuke ta faman yi, yanzu
kuma ga ɗawainiyar
abinci kuma haka mai yawa”
Aunty ta girgiza kai ta ce
"Allah Gwaggo ba wata hidima
a nan ban ganta ba, duk abin da zan yiwa Hauwa'u ai ban faɗi ba, Domin na san da
Hauwa'u ce mai ƙarfin fiye da wannan za ta yi min kuma ba tare data gaji ba, kin
tuna dai yadda muke tare dai Gwaggo in ban yi mata ba gani nake wazai mata kuma
ina jinma kamar ubangiji ba zai yafe min ba indai ina da shi ban yiwa Hauwa'u ba”
Gwaggo ta girgiza kai” A'a
Rumaisah kidaina faɗar
hakan ai mune dolen Hauwa'u mu ya dace muyi mata idan ba muyi ba Allah ya iya
kamamu da laifi ma”
Aunty ta yi murmushi ai ni ma
dolenta ce Gwaggo"
Gwaggo ta jinjina kai ta ce” Allah
ya barku tare ya ƙara danƙon zumun ci, Allah ya biya ki abin da kikayi”
Aunty ta yi murmushi ta ce” Amin
Yawwa Gwaggo haka ya kamata ki ce kawai, yanzu dai ya jikin nata ta farka
ko?"
Gwaggo ta ɗaga kai” Eh ta farko ba daɗewa an kirama likita mijinta
yana ciki Likitan ma yanata faɗa
da ya zo ya samemu a ciki gaba ɗayanmu
shi ne kika gan mu wajennan yanzu ma ya ce ko sun fito bame sake shiga sai can
anjima”
Aunty da take ƙoƙarin
zama kusa da Gwaggo ta ce” Alhamdulillah, Allah ya ƙara mata lafiya dama
ba'asan ana damun mara lafiya da hayaniya ai Gwaggo ɗazun ma ina jin abin da ya sa basuyi magana ba
saboda anyimata alluran barci, barcinnata ya yi nauyi amma yanzu zaryar ma sai
an rage ta ai tun da private asibiti ne "
Gwaggo ta jinjina kai gami da
kallon Aunty ta ce "Eh haka shi ma duk ya yi bayani likitan, amma ya za ki
zauna kuma?ai ya kamata ki shiga kema dake fa aka yi komai jiyan "
Aunty cikin ladabi ta ce” A'a
Gwaggo tun da Abdulllahi na ciki kuma shi ne mijinta ba sai naje ba da dai
Daddynsu Jabir ya zo ne sai ya shiga jiyan ma duk shi ne ya yi abubuwan da ya
kamata a ce anyi ɗin
ba ni ba”
Gwaggo ta ce "Haka ne amma
da kin shiga ɗin kiga
yana yin jikin nata kun yi ɗawainiya
da ita da ƙarfinku
da kuɗin ku daga jiya
zuwa yau ɗin nan kuma
abunda kuke buƙata yasamu, Allah dai ya saka muku da alkhairi ya ƙara
zaman lafiya ke da mijinnaki, dan a tunanina a baya gatansu ya ƙare
daga abin da ya faru tsakaninsu da waɗancen
mutanan yanzu saina ƙara miƙa wa Ubangiji lamuranmu na sake yaƙinin gatan kowa Allah ne”
Ina jin Gwaggo na maganar waɗancen mutane na fahimci ƴan
uwan mahaifinmu take nufi da a zahirin gaskiya ma zancensu ma banasan ji wata
tsana mai girman gaske nake ji tana tasomin da zarar na tuna su da me laifin da
marasa laifin duk na musu kuɗin
goro, maganar Aunty ta maidoni cikin tunanin da na faɗa
"A'a Gwaggo ai wannan dan
Allah kawai mukayi waɗanda
ma ba ka sani ba kana yi musu idan ta kama ba tare da ka tsaya jiran komai ba
daga garesu ko da godiyar su ma bare wannan kuma, su kuma Allah ya ganar dasu
in za su gane”
Ni da nake tsaye ƙiƙam ban
iya cewa Amin ba da sauran na ji suna ambata dan na san da wuya dai wanda ya yi
nisa ya gane gaskiya dan wasu ko mutuwa bata zamar musu wa'azi bare halin
rayuwar da wani ya tsinci kansa a dalilin abunda ya yi ya damesu
"Oh Soja za ki ta fi ke nan?
Hajiya Sumayyah"Muryar Aunty Asiya da na ji ta fidda ni tunanin da nake na
ɗago na kalleta na yi
murmushi
Gwaggo ta kalli Aunty Asiya ta ce”
Wanne irin soja kuma Asiya”
Aunty Asiya ta kalle ni ta maida
kanta ga Gwaggo"Eh mana Gwaggo tun fa da suka zo take tsaye a nan kamar
soja ko body guard shi ya sa kikaji na tambayeta”
Aunty Maryam ta kalle ni” To ai
goyon A'isha ne bayanta ina jin za ta tashi ne tana zama”
Aunty Jamila ta ce” Ai fah za ta iya
tashi yarinya abu ba abu ba ko girma batayi amma sai rigimar tsiya, ƙyaleta
ki zauna abinki in ta yi kuka a kaiwa uwarta”
"A kaiwa wacce uwar tata
nufinki kin san dai Hauwa'u bata ɗaukar
ta yanzu ina ma tagama dawowa hayyacinta saidai a baki ita”
Aunty Maryam ta yi maganar tana
hararar Aunty Jamila
Ina ƙoƙarin zama kusa da Gwaggo
ba tare da na ce komai ba dan haka nan na ji inasan tsaiwar dan A'isha ta yi barci
tuni
Aunty na ji ta ce” A'a fah ai ni
ce uwartata, sai nake ji ina ma Hauwa'u ta barmin ita wallahi Aunty
Maryam"
Aunty Maryam ta yi murmushi” Anya
kuwa ai dama ta yayeta ne yanzu kuwa ai ba zai yiyu ba”
Fitowar su Abbah daga ɗakin shi da likita ya katse
firar da akeyi likitan ne ya wuce yabar Abbah hankalin su Gwaggo ya dawo kan
Abbah suka haɗa baki
gurin cewa
"Ya jikin Hauwa'u ɗin"
Abbah da yana yin damuwa kaɗan ya ce
"Alhamdulillah amma an sake jona mata jinin ma yanzu allurar barcin ma an
sake mata, sunce suna buƙatar ta riƙa samun barci”
Sake haɗa baki suka yi da cewa” Toh Allah ya ƙara
sauƙi”
Abbah ya kalli Aunty"Yaushe
kuka dawo?"
Aunty ta ce” Yanzu babu daɗewa, amma daga wannan ai ina
jin an gama saka jinin, inda buƙata za su sake ɗibar jinin nata duba iya adadinsa kafin su ƙara tun
da ansa uku ke nan"
Abbah ya girgiza kai ya ce
"Wallahi ban sani ba, baiyi min bayani ba”
Aunty ta ɗaga kai” Eh dama ba tambaya ba ne na ji suna
ma Daddynsu Jabir bayani ne jiyan, Allah ya bata lafiya”
Abbah ya ce "Amin Allah ya
saka muku da alkhairi”
Duka muka amsa da Amin, Gwaggo ce
ta kalli Abbah
"Yawwa bari a zubo maka
abincin gama na Rumaisah na san da zafinshi”
Aunty Asiya ta kalli
Gwaggo"wai dama baici abincin ba Gwaggo?"
Gwaggo ta ce” Eh mana kin manta, zai
ci Hauwa'u ta tashi ya tafi kiran likita”
Aunty Asiya ta ɗaga kai sannan ta kalle ni”
Sumayyah zuba wa Abbahnku abinci mana”
Miƙewa na yi jiki a sanyaye kamar ƙwai ya
fashemin haka na fara zubawa Abbah abinci, tun da na ji ana sake ƙara wa
Mama jini ga wata allurar barcin jikina ya sake sanyi ina jin kamar muna gaf da
zama marayu duk da bawai a nan take ba ita mutuwa saita ɗauki mai lafiya tabar wanda yake buƙatar
mutuwarma idan kwana ya ƙare dole ne ba makawa ka tafi, Hakan na ci gaba da tunanina
har na gama zubawa Abbah abinci na ƙara sa inda yake ina ƙoƙarin
miƙa
masa na ji muryar Gwaggo
"Bari Sumayyah Ahmad ya ɗauko kujera a ciki ya sa
masa acan wajen" Juyowa na yi ina kallan inda Gwaggo ke nunawa da hannu
gefen inda muke ne kaɗan,
Dawowa na yi na rufe abincin da wani plat ɗin
sannan na koma na zauna inda nake, Ahmad ne ya miƙe ya ɗauko
kujerar ya sawa Abbah ya dawo ya ɗauki
plate ɗin ya kai ma sa
Kamar jira Aunty Asiya take ya
bar gurin ta fara magana
"Allah Gwaggo dan kince abar
tuna bayane kika ji na yi shiru ni ma amma ba abin da ke damun Yaya Hauwa'u sai
yunwa wallahi haba ni na rasa abin da ke damun wancen mutumin"
Aunty Jamila ta amshe zancen"Kema
dai kin faɗa Asiya
abun na cikin tuwo a kwarya kamar wanda aka yiwa asiri haba rayuwar dai gaba ɗaya sai a hankali”
Aunty Maryam harara ta auna
musu"Zaku fara halin naku ko?, gaban ƴaƴanshi su yi muku fitsara kuce basuda kunya”
Aunty Jamila ta ɓata fuska "Wanne halin
namu kuma mufa gaskiya ce sai mun faɗa
indai mun ganta, Dangin ubansu za su yiwa rashin kunya idan ma ita ce, wa ma ya
sa ni ko saboda ƙiyayyar da suke yiwa Yaya Hauwa'u suka asirceshi, ya zauna ba
a tsiya ba arziƙi ba”
Gwaggo ta kalli Aunty Jamila ta
harareta” Yi ta yi Jamila tun da ba kyajin magana sai ki yi ke kaɗai ko idan ƙannanki
su Zainab masu biye miki sunzo ku yi zancenku tare, mu dai ta lafiyarta muke yi”
Aunty sai yanzu tasa baki” Ni
Gwaggo ma maganar asirin da tayine bata yi min daɗi
ba, inma shi sukayi ai ɗan
su ne kuma komai ya samu bawa rubuce yake wani sila kawai yake zama dan Allah
Jamila ki iya bakinki dai”
Aunty Jamila ta ɗaga kai "Haka ne Yaya
Rumaisah"
Gwaggo ta harareta "Watoh
Maryamu kin rainata kina ganin ta kullum ko?"
Aunty bata bawa Gwaggo amsa ba
saima tashin da tayi” Bari naje dubo wani yaro ɗan
makwabciyata an kawoshi nan"
Aunty Asiya ta harareta” Wa toh
ba za ki ce na zo muje tare ba?"
Aunty Jamila ta ce” Yanzu fa
zance kin cika ƙorafi wallahi”
Gwaggo ta kallesu"In madai abin
da ya fi ɗan
makwabciyane kun yi gulmarku ku gama”
"Haba Gwaggo maimakon ki
yimasa addu'a amma kina neman ma ƙaryata wa” suka haɗa baki gurin bawa Gwaggo amsa da haka
Aunty Maryam ta yi dariya kaɗan"Ai Gwaggo ta hardace
halinku ne”
Dariya suka ƙunshe
suka bar wajen kallon bayansu Gwaggo ta yi ta ce "Allah dai ya shirya
yarannan kawai”
Su Aunty suka amsa da
"Amin"
A raina ni ma da "Amin"ɗin na amsa ina murmushi na
bisu da kallo, suna burgeni Aunty Jamila da Aunty Asiya bakinsu kusan a haɗe yake ka sancewarsu
sakwanni da halinsu ya zo ɗaya
kuma gidajensu babu nisa da na juna
Maganar Aunty ta katse min dogon
tunanin da nake shirin faɗawa”
Kin haɗawa Abbanku da
ruwa ne?"
Kai na girgiza” A'a Aunty ai
kamar mun manta ruwan ma a mota” na ƙarasa maganar ina juyar da kaina inda
muka aje kayan
Aunty ta ce” Kwarai kuwa kayan ne
sun yi mana yawa, Ahmad tashi ka buɗe
Boot ka ɗauko za ka iya?"
Ahmad ya ɗaga kai” Eh Aunty"
Aunty ta yi murmushi” Au na fa manta
karambaninka kaida Jabir"
Ahmad amsar key ɗin ya yi ya bar wajen, Aunty
ta shiga ba da labarin ƙinjin da Ahmad ke mata lokacin yana zuwa gidan nata Gwaggo na
sake ƙara
mata wani labarin na rashin jin Ahmad. . . . . . .
Na Cancanta (Kashi na 42)
Ina ɗago idona ya sauka kan Malika da take ta
aikamin saƙon
harara har ta ƙaraso inda muke zaune da sallama sannan ta gaishe dasu Gwaggo
Aunty da batasan Malika ba na ji tana cewa Gwaggo
"Gwaggo wace ce Malika ko ɗiyar Yaya Maryam ce?"
Gwaggo ta girgiza kai” A'a wannan
ƙawar
Sumayya ce makwabtansu ne kuma, Amma ɗiyar
Maryama ko Nasiba tafi su Sumayyah girman jiki bare Abida kamar Maryama jikinta
yake da girmanta, kuma Abidah ta girmi Sumayyah da a ƙallah shekara uku ma ƙanwarta
kuma Nasiba ma ta girmi Sumayyah, duk suna makaranta da tuni kin gansu
sunzo"
Aunty ta yi murmushi
"Alhamdulillah ai karatun na da anfani indai da halin yi ɗin tun da zaman ma ba auran
ba ne sai Allah ya kawo, Allah ya taimaka ya ba su sa'a ya kawo miji na gari”
Gwaggo tace” Uhmm ke dai Rumaisah
to Amin dai amma ƙoƙartawa kawai akeyi dai haka nan, gashi a haka har Abida ta kusa
gamawa, sai bautar ƙasa ita kuma ƙanwarta Nusiba tana Shekara ta biyu ne da
shiga ita ce ta ba Sumayya kusan shekara”
Aunty ta ce "To ya za ayi
Gwaggo haka za a ci gaba da ƙoƙartawa, Allah ya ƙara horewa ai ilmi
makarine indai da shi ko ya yake za kiga banbanci da wanda baiyi ba a dai
wannan zamanin da muke ciki bare su kuma ai za ki ƙara ganin rayuwarsu ta ƙara
canzawa da abubuwa masu kyau insha Allah addu'ar ku dai ita ce makaminsu a ko
ina”
Ni ko da hankalina na ga hirarsu
Aunty da Gwaggo da har nama manta da zuwan wata Malika ma dukan da na ji a
cinyata ya sani maido da hankali na zuwa ga inda aka dokeni Malika ce da take
zaune kusa dani da ban san ma ta kai ga zama ba
Cikin haɗe fuska na juyo gaba ɗaya ina kallan Malika ita ma haɗe fuskar ta yi ta kuma ƙimin
magana ni ce na katse shirunmu
"Haba Malika me na yi
miki?"Duk da na san laifin nawa amma inason sake jin ba'asi
Hararata Malika ta yi "Bansa
ni ba Sumayyah, tsabar wulaƙanci na zo gaishe da mamarku ki juyamin baya ma ni ce ma na zo
ai tun da baki iya faɗa
min ba”
Ganin na yi laifi inji Hausawa
sunce gaishe da mai gaisheka ko ba zai amsaba hakan ya sa na sassauta da murya
na ce” Haba mana ƙawata shi ne to na dukan hankalina yana wajen maganar su Aunty
ne fa, kuma wallahi da wuri muka taho asibitin ne, waye ya miki bayanin
asibitin"
"Uhmm kin gama daɗin bakinki ba buƙata
kisan waye ya faɗa min
ai bari na tashi saiki fi sauraron labarin da kyau"Malika ta yi maganar
tana miƙewa,
ni ma miƙewar
na yi ganin ta fara tafiya ya sa ni ma na bi bayanta
"Toh sai kizo ki gaishe da
Mama tun da kinƙi yarda ki haƙura”
Kallona ta yi "Rakani to
wajen Mama ɗin"
Murmushi na yi” dan Allah kiya haƙuri
Malika ita Mama ba a fara ganin ta ba ma kin san private Hospital sunce batasan
hayaniya ne”
Daƙyar na lallashi Malika ta dawo ta zauna, Aunty
ta dube ni
"Ya na ga ɗazu ta tashi?"
Na yi murmushi na kalli Malika
sannan na ce” Ai da ta yi fushi ne Aunty"Murmushi Aunty ta yi ba tare da
ta ce komai ba suka ci gaba da fira da Aunty Maryam
Har Yamma sosai Malika takai a
asibitin sannan ta ce za ta tafi za ta yi suyar dankali, dama ta jira ko za a bari
a ga Mama amma har lokacin ba su ba riba, sallama ta yiwa su Gwaggo sannan na
biyota na ɗan rakata
hanya muna tafe muna ɗan
fira
"Juraid kuwa ya san Mama
bata da lafiya?"Malika ta jefomin tambayar a lokacin muna ƙoƙarin
rabuwa
Kaina girgiza mata Sannan na ce” A'a
gaskiya ban faɗa masa
ba”
"To wai maiyasa ne?, kin san
ba zaiji daɗi ba idan
baki faɗa masa da wuri
ba”
Cikin sassauta murya na ce
"zan fa faɗamasa
amma kin san me Malika banasan wannan hidimar tashi tana yin yawa gashi Abbah
ma bayaso duk ya kawo saiya yi min faɗa
Malika ta ɗan taɓe
baki” Haka nan za ki daure ki faɗa
masa, ai hidima ta zama wajibi indai kanasan mutum shi ma duk ciki soyayya ne
ko mai ƙantarta
musamman ma ke kuma ai kin cancanta ayi miki saima a samu lada”
"Haka ne dan Allah toh kifaɗamasa idan kin koma gida na
san zaizo ai wajen dankalinki”
Ɗan rausayar dakai tayi” Eh ƙila
suzo, idan madai ba su zoba Yaya Nasir zan faɗa
masa, kin ga dasu Zainab sunzo tare”
"Ai Gwaggo ta ce sunzo da
rana kafin muzo saidai ƙila Uncle Jabir ya zo da wata cikinsu"
"Toh shike nan sai kun taho
zance” cewar Malika
Kai na ɗaga mata "Toh shike nan mun gode sosai a
gaidamin Na'im"
Murmushi Malika tayi” wato iya
Na'im ko?Yawwa Sumayyah ban gane wannan Aunty taku ba na ji Gwaggo ta ce mata
Rumaisah sister ɗin
waye?"
Murmushi na yi” Oh wai ba kisan
Aunty Rumaisah ba ƙawar Mama ce baki ji Rumaisah da sunanta ba?, zan iya ce miki
ta mafi ƙawarta
ma, duk itafa ta yi komai na asibitin nan"
Jinjina Malika ta yi "Masha
Allah ban ɗauka da ƙawa
irin wannan a yanzu ba Allah na yi zaton sister ɗin
Mama ce ta jini ko wannan zaman asibitinma da ta yi batayi komai ba ai ta yi ƙoƙari
matuƙa,
amma ba mu taɓa zuwa
gidan ta da keba ko?"
Ɗaga mata kai na yi na ce” Eh mana mu
kanmu ba mu jima da saninta ba, mu muna kano ita kuma sunfi zaman Abuja karatun
yaranta ya zaunar dasu gida yanzu, kuma ko bakin Mama banma san sunan Aunty ba kin
san Mama batasan shiga cikin ƙawayenta yanzu sai taga kamar za a nuna
mata ko in kula tun da ita bata da shi yanzuma Ahmad ya sake haɗa mu aikinnan da ya fara
toh a gidanta ne”
"Allah sarki amma na ga tana
da kirki sosai namaga A'isha hannunta, Mama fa nada gaskiya Sumayyah yanzu ɗan uwanka ma sai kanadashi
kake nashi shi ya sa nesa nesa ko Ummanmu haka take”
Kai na ɗaga alamun gamsuwa da zancen Malika Sannan na
ce "Haka ne Malika ni ma daga kan Aunty na ƙara tabbatar ba duka masu kuɗi suke haka ba wasu
talakawa suka fi ƙaunama tun da Mama fa jiya aka kawota asibiti A'isha ke
hannunta, kin ga bari dai sai mun haɗu
gida sai muyi labarin sosai kar magriba tayi”
Malika sama ta kalla sannan ta kalle
ni
"Haka ne kuwa kin ga har
rana ta gama rufewa ma”
Harta fara tafiya ta
juyo"Yawwah ki gaida min Mama idanta tashi”
Kai na ɗaga mata ita kuma ta juya ta ci gaba da tafiya
Bayanta na bi da kallo Malika
akwai kirki sosai ita ma tana cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata da wannan
tunanin naja ƙafafuna na koma cikin asubitin inda muke
***********************************
Ƙarfe takwas da mintina Mama ta tashi
likita ya ba mu damar shiga mu dubata
Kallon Mama nake cike da tausayi
haka ita ma idanta na kanmu har muka ƙara so gefen gadonta muna jera mata sannu
Gwaggo zama ta yi gefen gadon
"Sannu Hauwa'u Allah ya ƙara kiyaye gaba kawo muku mafita ta
Alkhairi, yanzu meke miki ciwo?"Gwaggo ta ƙara sa maganar tana goge hawaye
Mama cikin muryar ciwo ta ce” Gwaggo
ta yardani na gaji da kwanciyar"
Gwaggo da Aunty da suka fi kusa
da ita suka tayar da Mama, sai sannan Khalil ya ƙara sa inda Mama take Aunty ta ɗaurasa kan gadon
Mama da ta fara waige waige ta
maida dubenta ga Gwaggo
"Mama ya banga A'isha ba?ko
ta mutu ne?"
Gwaggo ta girgiza kai ta yi murmushi
kaɗan"A'isha na
wajen Rumaisah tun jiya madara ma ta siya mata ana bata yanzu ta yi barci, Hauwa'u
Rumaisa ta gama zama ƙawar arziƙi ba wajenki kaɗai
ba har wajenmu ma ba dan ita ba da ƙila zancen wasu akeyi yau ba naki ba ita
ta tsaya kan komai itada mijinta”
Mama kai ta ɗago ta maida dubenta ga
Aunty, da tun da Gwaggo ta fara magana idan Aunty ya koma kallan ƙasa
kasa magana Mama ta yi ita ma
Gwaggo ta ci gaba da cewa” Tun da
na zo na ga jikinki na fita nemo kuɗi
ni ma yarda mijinki ya fita nemo wa haka muka dinga cigitawa babu ba’a samu
komai ba kafin mu dawo gidan kuma Ahmad ya kira Rumaisah sai ji mukayi ankaiki
asibiti ba ma na gwamnati ba na kuɗi,
da da ƙawaye
kamar Rumaisah na tabbatar da babu wanda rashin shaƙiƙin ɗan uwan da dan babu shi ko
yana da shi ya ƙiyi ko bashi da shi damuwar hakan za ta dameka tun da aka
kawoki nan ɗin daga
jiya zuwa yau ita da mijinta ke hidima da. . . . "
"Habah!Gwaggo kin san bata
gama jin sauƙi
ba kuma ba komai cikinta dan Allah ki kyale maganar nan haka” Aunty Maryam ce
ta yi hanzarin katse Gwaggo da cewa hakan
Gwaggo ta goge hawayenta ta kalli
Aunty Maryam tare da harararta” Na ƙi na yi shiru abin da ba mu da halin yi
muka samu mutane masu arziƙin da suka fiyewa Hauwa'u dangin mijinta da ta tara ƴaƴa ɗaya ɗaya har shidda da su dan na yi zancen shi ne
abun laifina kome?"
Aunty Jamila jin Gwaggo ba za ta bar
maganar ba ya sa sauri matsawa gadon da Maman take a hankali na ji tana cewa” Sannu
Yaya Hauwa'u, me kike son ci yanzu?"
Mama ta girgiza kai a hankali ta
furta "Babu komai”
Aunty Mama ta ɗago ta kalla” A'a ba zai
yiyu ba likita ya ce lallai kici abinci sannan kisha magani, Sumayyah bare
ayabar can ki miƙo mata”
Da saurina na ƙara sa
inda ledar ayabar take ajiye da Uncle Sha'aban na ji Gwaggo ta ce shi ne ya
kawo ɗazu buɗe ledar na yi na ciro
ayabar na ɓare na miƙa wa
Mama tas ta cinyeta
Aunty ta dube ni” Ƙaro
mata wata tun da ta cinye "
Ƙara ɗauka
na yi na ɓare na miƙa mata
na koma na tsaya inda nake
Gwaggo ta dubi Rumaisah "Wai
ina kujerar da muka fita da ita ɗazu,
miƙowa
Auntynku takwararki ta zauna mana”
Aunty na kalla da sai yanzu na
fahimci ashe tsaye take Aunty Asiya take zaune a kujera tana baiwa Adil Mama
Aunty Maryam ta yi murmushi kaɗan"Ai Gwagg da
Sumayyah ki kace kawai ita ce ƴar wajen Rumaisah bata yi da takwararta ɗin"
Gwaggo ta yi murmushi ita ma” Haka
ne kuwa Maryama ina lura da ita gashi ma Rumaisah ma ita ce ta ɗebo Hauwa'u sosai ita
wannan Sumayyah ai tafi kwaso dangin ubannata marasa kirki”
Aunty Jamila ta kalle ni sannan
ta ce” Sosai kuwa Gwaggo kina kallonta kin ga ƙanwar ubanta Asma'u Khalil ko Asma'u
Halil take nema na manta kin san ƴar ajinmu ce”
Ita dai Rumaisah kujerar ta
janyowa Aunty inda take Aunty ta zauna sannan ta fara magana
"Toh nidai Gwaggo duk bahaka
ba ne kawai dai saboda Sumayyah ce babba shi yas sa”
Aunty Maryam ta kalli
Gwaggo"To kin ji dai Gwaggo ko, zancenmu na bayyana”
Murmushi Aunty ta yi jin su Aunty
Maryam tsokana suke ji gurin Gwaggo Aunty ta maida kanta” Kin ga shiru magani ɗaya ya yi wuya”
Gwaggo ta mai da kanta kallan
window"Wallahi kuwa ko ɓurɓushin Abdullahi kin ga ban
hangaba ko aɗan bata
Yoghurt ɗin can kafin
ya dawo?"
Aunty ta ɗaga kai "Eh haka ne da an bari sai
zatasha maganin tun da ɗaya
ne amma Rumaisah ɗauko
abata rabi, Kar su Auntynku su ci gaba da yi min tsiyar komai nafi kiran
Sumayyah"Ta ƙara sa maganar tana murmushi
Su Aunty Maryam murmushi suka yi
haɗin bakin cewa” Ai
gaskiya muka gani ne”
Aunty bata sake cewa komai ba sai
murmushin da ta sake yi
Rumaisah da bata ce komai ba
cikin sanyinta ta fara tafiya aiwatar da saƙon Aunty inda Yoghurt ɗin yake ta ƙara sa
ta ciro Rufaidah Yoghurt da shi ma yana cikin ledar da Uncle Sha'aban ya kawo, miƙa wa
Gwaggo haɗe da cokalin
jikin Yoghurt ɗin, Gwaggo
ta maido mata da cokalin "Ungo ki ɗaurayeshi”
Aunty Maryam ce ta kalli Rumaisa ɗin "Ɗauki
wancen ruwan kisa a ciki kular can sai ki ɗaurayeshi”
Yadda Aunty Maryam ta ce haka
Rumaisah ta yi nidai da ido nake bin Rumaisah duk abin da take yi Rumaisah tana
da natsuwa sosai komai nata cikin sanyi da taushi take yi dan halin Mama kaf
Rumaisah tafi kowa cikinmu kwashewa ban da kamanninta da Mama ɗin kuma da take yi. . . . .
. . . . . .
**** ****
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.