Ticker

Na Cancanta (Kashi na 43)

Gwaggo na cikin ba wa Mama Yoghurt ɗin aka turo ƙofar haɗe da sallama aka shigo Abbah Zaid ne da su Jabir sai Abbah

Abbah Zaid da Murmushi fuskarsa yake ƙara sowa

"Alhamdulillah ta samu ashe”

Dukka murmushi aka yi Abbah ya ƙaraso yana miƙa wa Gwaggo magani

"Oh ni Abdulllahi sai kaje kayi zamanka kuma” Gwaggo ta yi maganar tana ansar maganin

Abbah kansa ya mayar ƙasa ya ce” Wallahi Gwaggo sai chemist na cikin unguwa aka sameshi, ina hanyar dawowa na haɗu da Zaid ma, shi ne muka ƙara so tare a mota”

Gwaggo da ta ciro maganin a leda ta riƙe shi hannunta ta ce” Oh ni yanzu wannan ɗan abun shi ne ya yi wuyar samu haka”

Aunty Maryam ta kalli maganin ta yi dariya kaɗan"To ai Gwaggo haka magungunan suke fa kana rainasu haka sai kaji su da wuyar samu"

"Ai na ga alama Maryama Allah ya rufa asiri” cewar Gwaggo ta ƙara sa maganar tana cire maganin akwalinshi

"Gwaggo ina yini ba’a gaisa ba” Abbah Zaid ne mai maganar yana murmushi

Gwaggo ta maida kallonta ga Abbah Zaid ta yi murmushi

"Lafiya ƙalau zancen maganin nan yaɗauke min hankali”

Ya ɗaga kai "Haka ne ya mai jiki?, aina ga ta samu sosai Allah ya ƙara lafiya”

Gwaggo ta ce” Amin dai Zaidu Allah ya saka muku da alkhairi ya bar tare”

Yayi murmushi "Amin Gwaggo ai yiwa kaine duk wanda ya taimaki wani ai ba wanin ya taimaka ba kansa ya taimaka, Allah dai ya karɓi ayyukanmu"

"Amin"dukka ɗakin muka ce, Cikin haɗin baki muma muka gaisheda Abbah Zaid cikin sakin fuska ya karɓa gaisuwar tamu da tambayarmu ya mai jiki muka amsa da Alhamdulillah

Aunty na ga ta wurgawa su Jabir harara sannan na ji ta ce

"Baku iya gaisuwa ba ku?, Sannan Ummin taku fa ba za ku gaishe ta ba?"

Gwaggo ta yi murmushi” Kyalesu Rumaisah baki ga yanzu aka gama gaisawa da Abbahnsu ba?"

Aunty ta yi murmushi kaɗan"Allah Gwaggo ba suda niyyar hakan baki gani ba sun tsaya sai kallon mutane sukeyi kawai”

Gwaggo cikin murmushi ta juya ta kalli Jabir da Muhammad da tun da Aunty ta fara magana ransu ke haɗe alamun ba su so faɗanba

"Kunji Ummanku ta ce ba kuda niyyar gaida mutane haka ne”

Aunty ta hararesu hakan ya sa sukayi ƙasa da kansu Sannan suka ɗago suka furta cikin haɗa baki

"Ina yininku?"

"Ya mai jiki”

Murmushi su Aunty Jamila suka yi suma cikin haɗin baki suka amsa da

"Lafiya ƙalau"

"Mai jiki Alhamdulillah"

Inda Mama take kwance suka ƙara sa

"Ummi Ina yini?"

"Ya jikin naki”

Mama da murmushi ta kallesu a hankali kuma na ji ta furta

"Alhamdulillah"

Gwaggo cikin sigar zolaya ta ce” Waye ɗan nawa Jabirun a cikinku?"

Murmushi Jabir ya yi ya ce "Nine Gwaggo"

Gwaggo ta dafa shi” To mezan samu, na ga hannunka bakomai kar na ce nafasa auren"

Murmushi Jabir yayi” Aini dama Gwaggo kinyi min tsufa”

Ido ta zaro"Lallai Jabir to ai anfisan irinmu"

Murmushi duka mukeyi muna jin dramar Gwaggo da Jabir hatta Mama ita ma murmushi take yi, da alamu ita ma firar na mata daɗi

Turo ƙofar da aka yi yasamu maida hankalin mu ga ƙofar Uncle Jabir ne ya shigo bakinshi ɗauke da sallama ya ƙaraso ciki gaisawa ya yi dasu Abbah sannan ya tambayi ya mai jiki, Sannan muma muka gaidasa

"Wai ina Sumayyah ne?"Cewar Uncle Jabir

Aunty Asiya ta kalli inda nake tsaye ta ce” Gata nan tsaye tana kallanka harma gaisawa ai kun yi” ta ƙara sa maganar tana nuna masa ni

Uncle Jabir ya kalli inda Aunty Asiya ta nuna masa ya kalle ni” Oho Yaya Asiya ido ke gani ai ban ganta ba da farko"

Yayi maganar yana sake kallona fuskarsa babu alamun wasa ya ce” Yawwa ki je Nasir da Juraid na waje ki shigo dasu na ce suzo mu shi ga tare sunce a'a na dai miki magana”

"Toh"na iya furtawa dan ba ƙaramin kunya na ji ba gashi yadda idan kowa ya sauka akaina da hanzari na maida idanuna ƙasa na fara tafiya

Aunty na ji ta ce” Su Waye kuma haka Jabir?"

Uncle Jabir na ji yana cewa” Ɗaya makwabcinsu ne ɗaya kuma saurayinta”

Da wannan maganar na ƙara sa fita Ina fitowa idanuna ya sauka a kan na Juraid ka sancewar da hasken nefa a asibitin suna tsaye daidai inda muka zauna ɗazu, Kaina na mayar ƙasa ganin su duka ni hankalinsu ya karkata gareni haka na ƙara so inda suke

"Assalamu alaikum"Na fitar a hankali na sake ƙasa da kaina

"Wa'alaikumussalam"suka haɗa baki gurin amsamin, Gaisawa mukayi

Daganan muka ɗan yi shiru hakan ya sa na ɗago fuskata muka haɗa ido Juraid ɗan murmushi ya yi min

"Muje ciki to ki mana iso, duk da ba ma ke yadace mu kira ki shigo damu ba, kawai saboda Nasir ya ce na kiraki ne”

Na ɗan ɓata fuska alamun banji daɗi ba na kalleshi ni ma kallona ya yi ya ce "Sosai kuwa tun da bakya taɓa faɗa min komai hatta zuwa asibitin nan na Mama ko flashing ki yi kifaɗamin bansamu arziƙin hakan ba na gode”

Na buɗe baki da niyyar magana ya katseni” Kin ga ya wuce muje ciki”

Ina ƙoƙarin wucewa gaba na fara tafiya na ji Muryar Yaya Nasir"Yawwah Sumayyah ɗan dawo ki ɗauki wannan ledar"yayi maganar yana nuna min ledar

Inda ledar take na kalla da take kusa da Yaya Nasir ledar babbace sosai "Allah yasan irin kayan da Juraid ya lodo a ciki gaba ɗaya baya gajiya shi da yi min hidima” na faɗa a raina

Dawowa na yi na ɗauki ledar mai ɗan nauyi ba laifi danma ledar mai ƙarfi ce danasan sai ta iya yagewa ina gaba suna bin bayana har muka ƙara sa ƙofar ɗakin na murɗa handling ɗin muka tura su Rumaisa idona ya sauka kansu ba a tsaye suke ba yadda na fita na barsu yanzu sun shimfiɗa tabarma duk sun zauna sun zauna

Sallama mukayi idon kowa na falon ya koma kanmu, idona na yi hanzarin saukewa ƙasa saboda kunyar danaji ta dabaibayeni, A haka naƙarasa inda su Rumaisah suke na aje ƙatuwar ledar

 Sannan na ɗan iya ɗago kaina a lokacin su Juraid sun tsugunna suna gaishe da su Abbah da tambayar ya mai jiki

Dai Dai lokacin na ji an turo ƙofar da ƙarfi gabana na ji ya faɗi musamman maganar da na ji ta biyo baya

"Yawwa ka gansunan"na kasa tantance muryar wanene saboda yadda aka yi maganar cikin alamun faɗa da zafin rai, Hakan ya sani saurin ɗaga idona na kalli su waɗannan

"Innalillah wa'inna ilaihir raji'un"na yi hanzarin ambata a cikin raina da banida tabbacin bata fito fili ba

Mai kuma muka sake aikatawa kuma mai karo na biyu ba Abbah ya kawo Mama asibiti ba bare na ce da kuɗinsu ya kawota me Abbah Hashim yakeso rayuwar mu takoma bayan wadda muke ciki, indai ba gizo idona ke min ba Abbah Hashim ne ya shigo tare da wani jami'in ɗan sanda ga shaidar hakanne da baƙin kaya a jikinsa

"Yallaɓai ga Abdullahi ɗin nan a tafi da shi kawai a haɗa da ƴar tashi” Maganar Abbah Hashim da na ji a alamun harzuƙe a karo na biyu ya sani saurin dawowa daga gajeren tunanin da na tafi na kuma sauke idanuna kan Abbah Hashim da ɗan sandan na kuma sake tabbatarwa sune

"Kamar ya a tafi Abdullahi kun shigo guri babu sallama kun kuma razanar da mutane a kan abin da ba kuma mana bayani ba” Abbah Zaid ya yi maganar yana ƙara kafesu da ido

Abbah Hashim ya ɗan saki ƙaramin tsaki "Dan Allah yallaɓai ka komosu ka taho mu tafi”

Abbah Zaid cikin muryar ɓacin rai ya ƙara kallan Abbah Hashim

"Babu wanda za a kama a nan sai dai kai aka kamaka mara imani mara tausayi wallahi daga ganinka ka raba hanya da waɗannan ababen da na zayyano maka ko tantama babu idan ban wawanci a asibiti zakazo ka ɗaukowa wanda yake fama da jinyar matarshi ɗan sanda bashinka yaci kome koma me ya yi ma akace ma yana asibiti ai ka san tun da ba aiki yake ba ba zuwa daɗi ya yi ba”

"Kai ta shafa a kan wannan mai ƙashin tsiyar kake jin zan ragwantawa Abdullahi ne ba asibiti aka kawota ba jiya ko yanzu aka kawota tana suma tana farfaɗowa sai an tafi da shi kuma kaɗan ya gani muddin bai rabu da wannan matar ba mai ƙashin tsiya a haka rayuwarshi za ta ci gaba da ɗaiɗaicewa” Abbah Hashim ne yake maganar yana yi yana nuna Mama yana nuna Abbah

Ɗan sandan baiyi ƙoƙarin hanashi ba da alama kuɗi ya ba su masu yawa dan indai a Gwarzo ɗan sandan yake to an daɗe da kashe case ɗin mu, sai dai kuma tun da da kuɗi

Abbah Zaid ya ja dogon tsaki” Da alama kai jahil. . . "

Uncle Jabir ya yi saurin tarar Abbah Zaid da cewa

"Dan Allah ka kyalesa duk abin da ya yi niyya yayi, amma su fita can waje su bar mu da ƴar uwarmu mu bata rigima muke ba duk abin da zai faɗa kansa, ko na ce suke faɗa”

Abbah Zaid ya kalli Uncle Jabir"A kyalesa fa kace Jabir ba ka jin abin da yake faɗa ne?, kuma shi Abdullahi me ya musu kuma wacce ƴarsa yake tunanin a haɗa da ita?"

Uncle Jabir ya jinjina kai ya maida kanshi ga Abbah Hashim da yake hura hanci yana zaro ido ya ce” Ina jinsa mana to ya zamuyi tun da ƙaddarar aure ta haɗamu dasu, shi kuma Abdulllahi uwa ɗaya uba ɗaya suke da shi ai ƴarsa ƴarshi ce”

Abbah Zaid Abbah Hashim ya kallah sannan ya kawar da kai "Amma dai akwai alamun taɓewa a wannan lamarin wannan halittar sam ba za ka kalleta kayi marmarin ƙara wa ba a haka bare ka mata kallo na tsanaki a matsayin ɗan uwa abokin kuka”

A harzuƙe Abbah Hashim ya nuna Abbah Zaid"Malam ka shiga taitayinka ba dakai nake ba idan so kake abun ya shafeka bismillah"

Gwaggo da alamun ɓacin rai ga idanunta ya yi ja ta dubi Abbah Zaid"Dan Allah kayi shiru ka kyalesa”

Sannan ta juyar da idanunta ga Abbah ta furta

"Abdullahi”

Abbah da tun da Abbah Hashim ya fara cin mutuncinsa idansa ke ƙasa jin kiransa da Gwaggo ta yi yasashi ɗagowa da jajayen idanunsa da rawar murya ya ce

"Na'am Gwaggo"

Gwaggo ta sake kallon Abbah cikin dakewa ta ce” Dan Allah ka bi su kawai mu muna jin da abin da ke damunmu ne idan ma takardar saki ne Hauwa'u tana jira”

Abbah ya buɗe baki da niyyar sake magana Gwaggo ta ɗaga masa hannu ta ce” Na fahimci komai dan Allah ka bisu kar a ƙara sa ƴata a wani baƙin cikin ga ciwo tana fama dashi”

Ƙarar waya da na ji ya sani ɗagowa na kalli inda kunnena ya juyo min ƙara Abbah Hashim na ga yana ƙoƙarin saka hannunsa aljihu ya ciro ƙaramar waya mai madanne ya danna ya saka a kunne banji mai aka ce a wayar ba saboda ba ta speaker sai amsar da Abbah Hashim ya bayar da

"Toh shike nan"daganan ya cire wayar a kunnenshi yana ƙoƙarin maidata aljihu ya kalli Abbah da murmushi wanda kana gani ka san ba mai fassara mai kyau ba ne sannan ya yi ƙoƙarin juyawa har ya fara tafiya yana ƙoƙarin saka hannunsa a murfin ƙofar sai kuma ya juyo ya sake kallon Abbah

"Ba dai ɗana kake ƙoƙarin ya yi rayuwa kalar taka ba kake ƙoƙarin kusantashi da ƴarka shi ma kana so na yafeshi yadda iyayenmu suka yafewa mace kai, Mu zuba ni da kai wallahi ko ɗana ya janye aurennan saina gama ƙara sa wulaƙantaka harta rigar sakawa sai taso gagararka sannan zan ji zuciyata ta wuce daga abin da kayi min kuma ba kai kaɗai ba har ƴarka abun sai ya shafa” daganan Abbah Hashim ya tura murfin da ƙarfi ya fice ɗan sandan ma yabi bayanshi, babu wanda ya sake magana har suka fice gaba ɗaya

Jin ficewarsu ya sani kife kaina a cinyoyina na fashe da kuka mai ban tausayi sai yanzu na tuna a gaban su Juraid komai ya faru shin za su fahimceni ko kuwa abaibai zai kalli rayuwar tawa ne wanne hali Mama za ta sake ka sancewa idan ina kuka shi Abbah da ya kasa kukan ya yakejin zuciyarsa. . . . . . . 

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments