Na Cancanta (Kashi na 9)

    Ƙofar babban falon gidan Mama Atika muka buɗe da sallama dauke da bakinmu, babu kowa falon sai ƙarar Tv da tashar Africa TV ce ake kallo zama mukayi nida Halima a kujera mai 2seater muka fara kallon film episode na Iyalina da shi ake haskawa tashar Africa TV ɗin muka tarar, ba mu jima da zama ba Mama Atika ta shigo falon da sallama gami da fara'arta muka amsa mata ta zauna kujera mai kallon tamu

    Gaisheta muka yi ta amsa murya sake ta kalle ni

    "Lale marhabin da manyan baƙi, Yanzu Ina kitchen na ji kamar anyi sallama shi ne na leƙo ashema kune, amma kuka tsaya daganan kamar gidan baƙonki ne Sumayyah"

    Mama Atika ta ƙarasa zancen fuskarta sake

    Na kalli Mama Atikar na ce

    "Yanzu nake shirin shigowa sai gaki”

    "Mama Atikar ta ce

    "Ya mutanan gidan, kwanaki Khalifa ya yi anguwar taku har na ce ya biya yaji lafiya kwana biyu, Auntyn tasu bata turoku, to sai ya kirani waya ya ce dare ya yi ba zai samu biyawa ba, ni ɗinma naso zuwa to hidimar yau da kullum idan ba ka ya ki cewa saita hanaka zumun cin na”

    Na jinjina kai na ce

    "Haka ne Mama, muma makaranta ta ɓoye mu ba mu zuwa”

    Ta ce

    "Haka ne yanzu a jikinki nawa ne”

    Na ɗan yi murmushi

    "Wannan shekarar mukayi ƙualifying"

    Mama Atika ta ce

    "Allah ya taimaka ya ba da sa'a”

    Na amsa da

    "Amin"

    "wannan fa banganeta ba”

    Tayi maganar tana nuna Halima

    Na ce

    "Ƙawata ce, sunanta Halima, ai mun taɓa zuwa nan da ita”

    Mama Atika ta ce

    "Aiko bangane taba, sai yanzu. . . . "

    Ba mu ƙarasa zancen ba, Aunty Abida ta ƙaraso cikin falon ta nufi gurin Mama tana magana a shagwaɓe, ko gaisuwar da muke mata bata saurara ba ta fara magana

    "Mami yunwa nake jii”

    Tsaki Mama Atika ta yi ta kalleta

    "Zoki daukeni ki cinye, tun da baki san hanyar kitchen ba sakarai kawai, Kuma baki ga su Sumayyah ba ne, har gaisheki suka yi”

    "Yi hakuri Mami ban ji ba ne” ta ƙarasa zancen tana kallonmu

    Mama Atika ta ce

    "Kyaji ai”

    "Sannunku"Aunty Abida ta ce Mana

    Muka amsa cikin haɗa baki "yawwa, Aunty Abida ina yini”

    Ta amsa da

    "Lafiya lau"

    Daga nan ta yi gaba a girme Aunty Abida ba wani girmemin ta yi da yawa ba kawai matsayinm ƙanwar uwa gare ni nake girmama ta, amma ban da haka mai zai ja min gaidata, kawai matsayin ta gareni ya ja haka.

    Maganar Mama Atika ta katse min tunanina

    "Ina Rumaisa ne, ba ku zo da ita ba”

    Na ce

    "Eh amma Mama ta ce za su so da ita da Ahmad da Khadija, ni ma saboda zan tafi Katsina na zo yau"

    Mama Atika ta kalle ni

    "Katsina Kuma gurin wa?"

    Na ce” gidan Abba Hashim (Baban Katsina”

    Mama Atika ta kalle ni ba tare da ta ce komai ba ta ce

    "Allah ya kaimu lafiya”

    Na amsa da "Amin" na san Mama Atika ta yi niyyar magana sai dai ganin Halima nafi tunanin ya sata yin shiru domin tunaninta bai bata Halima tasan abubuwa da dama a rayuwata ba

    Sai la'asar bayan mun yi sallah muka baro gidan Mama Atika bayan mun ci abinci mun ƙoshi da duk da na ce mata mun ci abinci sai da ta tilasta muka ƙara ci, Kaya masu yawa ta ba mu da kuɗi dan Mama Atika akwai san kyautatawa 'yan uwanta yaranta ne dai ba su da kirki, zan iya cewa kaf dangin Mamanmu babu mai san Mama kamar Mama Atika kodan ka sancewar kusan tare suka taso kuma gidansu ɗaya sai dai matsala guda Mama Atika bata zuwa gidanmu sosai bakomai na halin da muke ciki ta sani ba, ita kuma Mama bata fiye kai ƙorafin yanayin rayuwarta ba takan ce” Ubangiji ya kamata mu kaiwa kukanmu, shi ne yake son mai roƙarsa amma ɗan adam bayansa roƙo, ta kance shi ma korafi kamar roƙo ne, ita bata fatan tayi” hakan ya sa bakomai 'yan uwan Mama suka sani game da rayuwar da take ciki ba sai inhar sunzo su gani da idonsu su yi ta faɗa bata faɗamusu, duk da suma ɗin ba wani ƙarfi garesu ba, Mama Atika ce dai dukta fi su hutawa, ita kuma ba wani zuwa dangi take ba, wasu sunce mijin tane bai fiye bari ba

    Yau ta kama Asabar ranar da Yaya Samir zaizo tun asubar fari na gama shirina wanda inayi ina tunanin makomata idan naje gidan Baban Katsina ya rayuwata za ta ka sance.

    Mama ce ta kalle ni da na fara hawaye jin Yaya Samir ya faɗawa Abba ya tawo yana hanya, hakan ya sa Abba ya fita waje, da tun zamansa gidan yau faɗa da Nasiha yakemin kamar wadda za a yi wa aure ko na tafi ke nan ba zan dawo gidanmu ba

    "Sumayyaha kukan mai kikeyi kamar wata yarinya ya kamata ki samawa kanki lafiya, ko ni da aka tura boarding tun daga JS1 ban taɓa kuka haka ba, bare ke ɗin da girmanki kuma cikin 'yan uwanki za ki tafi”

    Maganar da Mama ta yi ta katse min tunanin da nake da na san dauriya kawai ta yi amma dai kowa yasan ba rayuwar 'yanci zan yi ba gwara a ce ma rayuwar boarding ɗin, kamar ba zan magana ba na dai daure nace

    "Mama ina tsoron mai zaije ya dawo bayan zuwana kina ganin dangi Abba babu mai sonmu"

    Ta dafani

    "Haba Sumayyah ki tuna Allah a ko da yaushe yana tare dake kuma shi ne yake ƙaddara komai duk yadda akaso cutar dake ki tuna Allah baya zalinci kuma zai miki sakayya a gurin Mai ƙoƙarin zalintarki fatana dai dake duk wuya kada ki taɓa tunanin zalintar wanda ya zalinceki ki sakawa mai zalunci da alkhairi a ko da yaushe, sai kiga alkhairi da albarka ya lulluɓe ki, zan riƙa miki addu'a insha Allah babu abin da zai faru dake koma ya faru ki ƙaddara a ranki ƙaddarar ki ce”

    Na share hawaye na, na ɗagama Mama kai tare da ce wa

    "Mama kinason ki kwantarmin da hankali bayan ke naki ba kwance yake ba, kawai kina daurewa ne”

    Mama ta riƙe hannuna

    "Karki ce haka, Habiba hankalina a kwance yake saboda inada Allah, kuma ma komai za su miki karki manta kansu za su yiwa, kuma ba za su canza ki ba 'yar uwar su ce ke dole, idan Kuma sun hana wasu su faɗa ba bazssu hana wasu faɗi ba, Kuma komai sukayi na munana miki karki manta haka Allah ya ƙaddaro miki”

    Kai na ɗagawa Mama, bankai ga cewa komai ba na ji sallamar su Halima da Batul amsa musu mukayi da murmushi cike da fuskata Mama suka gaisar daganan suka maida kallonsu gareni na hararesu

    "Malama hararar mai kike mana” faɗin Batul tana ita ma hararata

    Na ce” kunfi kowa sani, yanzu a ce sai yanzu da ina gaf da tafiya za ku zomin sallama”

    Tsaki Batul ta yi

    "Dama kika samu muka zo"

    Na ce” ai na san ko baki zo ba Halima za ta zo"

    "Kin manta Kalima ce za ta zo ba Halima ba, ai ni yanzu da Halima munfi tip da taya, tun da gashi za ki gudu ki bar Halima” faɗin Batul da ta bini da muguwar harara

    Mama ta fara magana

    "Kai Batul da Sumayyah sababbu kun fara fa ke nan, ni ku tashi ku barmin ɗaki”

    Halima da sai yanzu tasa baki ta ce

    "Wallahi Mama korasu"

    Batul ta ce

    "Ai harda ke”

    Haka muka koma ɗakinmu muka zube saman tabarma muka ci gaba da fira da yi min nasiha ko waccensu da idea ɗin da za ta kawomin kuma kowacce shawararta abar dubawa ce bayan sun game min nasihar na kallesu

    "Gaskiya na gode sosai, na kuma ƙara godewa Allah da ya haɗa ni da ƙawaye kamarku, ko ba’a faɗa ba na san na san zan yi rashin masoya”

    Murmushi Halima tayi

    Batul ta goge hawayenta

    "Sumayyah ban taɓa haɗuwa da ƙawar da nake jinta raina ba sama da ke, sai kuma Halima, kin CANCANTA da mu yi miki komai ba ma nasiha ba”

    Halima ta dafani

    "Sumayyah kin cancanta da komai garemu ke ƙawa ce”

    Na goge hawayena da ni ma suka tararmin

    "NA CANCANTA!NA CANCANTA!haka kowa ke faɗa amman har yau na kasa fahimtar hakan"

    Halima ta ce

    "Dama ke ba za ki fahimta ba, amma ke ƙawace, ta kwarai, baki taɓa yin wani abu na rashin dai-dai gabanmu ba saima idan mukayi mu ki nuna mana bai kamata ba, mu shaidane a bayanki akwai uwa ta gari Mama ta miki tarbiyyar daba wanda ba zai so ki da ita ba, muddin yasan kansa”

    Nayi murmushi na ce

    "Kuma bayanki akwai iyaye na gari kamar Mama na na gode Allah da na ka sance na samu ƙawaye na gari waɗanda su kayi dacen uwaye na gari”

    Dariya mu kayi da dariyar tamu ta yi dai-dai da sallamar Abba da kuma baƙon murya wadda na san ta ya Samir ce, da mintina ba su fi biyu ba na ji Abba ya fito tsakar gidan yana cewa

    "Ina Sumayyan ne?"

    Na jiyo muryar Mama tana cewa

    "Tana ɗakinsu Batul da Halima ne suka so"

    Sallamar Abban na ji ɗakinmu muka amsa masa su Batul suka gaishesa ya amsa da fara'arta ya ƙara da cewa

    "Wato an zo rakiya, Allah ya sa ƙawartaku karta mantaku idan taje Katsina?"

    Na ce cikin muryar tausayi

    "Kai Abba karkamin addu'ar haka”

    Yayi dariya ya ce

    "Ba addu'a bace, kunsan mene”

    Duk muka girgiza kai

    Ya ce” haka Mama da Mama Atika suka yi da suka je boarding suka dawo hutu"

    Na ce” Mama” da ƙarfina

    Abba ya ce

    "Yi hakuri, tashi kuje ku gaisa da Samir, karki haɗamin tanbotse da Mamanku, ke ɗiyar Mama”

    Gaba ɗaya muka yj dariya muka miƙe inasan Abbanmu saboda yadda yake mu'amala damu tamkar abokansa, danma baida lokaci sosai a gida, amma hakan baisa mun raina sa ba, haka muka miƙe ba wai dan naso gaisuwar ba da sallama muka shiga ɗakin Mama da shi kaɗai muka samu ɗakin yana zaune saman Carpet ɗin sallah ya ki shigiɗa da jikin bango da gorar faro kusa da shi yana danna waya babu laifi Yaya Samir yana da kyawunsa iya nasa Kuma ya iya kwalliya gaisuwar da na ji su Halima sun fara masa ya dawo dani tunanin da na tafi ba tare da gama ba na yi saurin bin gaisuwar da sukeyi muka ƙarasa tare cikin murmushi ya amsa mana

    Yana kallan su Halima dani kaina ya ce

    "Habiba ban gane su ba”

    Na ce

    "Kawaye nane, tare muke Day dasu"

    Na nuna Halima na ce masa "wannan Halima” na nuna Batul na ce” wannan Batul"

    Yayi murmushi ya kalle ni

    "Idan kika barni, ku fa 'yan uku ne, ashe ƙawaye ne, Allah ya raya ku musha biki”

    Nayi murmushi kawai a raina na amsa da Amin

    Kallonmu da Yaya Samir keyi ya sani saurin miƙewa na ce

    "Yaya bari muje”

    Ya kalle ni ina tafiya fa zamuyi yanzunnan"

    Na ce” to ɗakinmu zamuje”

    Muna shiga ɗakinmu na yi saurin cewa

    "Kai Yaya Samir ba dai kallo ba, kunga yadda yake kallonmu"

    Batul ta kalle ni sheƙe ƙe

    "Kin ji yarinya da rainin wayau, ki ce dai Yana kallanki shi ya sa ma muka miƙe za mu ba ku guri ke Kuma kika biyo mu"

    Halima ta ce

    "Faɗa mata dai, ashe shi ya sa taƙi Yaya Hakim da Malam Hamid ashe zumun ci za a haɗa”

    Batul tasa dariya ta ce

    "Sosai kuwa, mu dai Allah ya sa kar ana wanna tafiyar muji labarin ɗaurin aure babu gayyata”

    Tsaki na yi na ce

    "Ku fa daɗina da ku yarinta”

    Batul tasa dariya ta ce

    Au ban da ke, ko da ke ba sabanba anyi saurayi Mai mota”

    Duk muka yi dariya, rayuwarmu da ƙawayena tana burgeni idan muna hira ba za ka ba mu ƙananun shekaru ba

    Haka cikin mintina da ba su fi goma da zuwan Yaya Samir ba muka fito tafiya gaba ɗaya gidanmu dasu Rumaisa suka ƙi zuwa Tahfiz saboda tafiyata da ƙawayena suka rakomu har wajen motar Yaya Samir muna kukan rabuwa da ba musan ranar sake haɗuwa ba danma ina da number ɗinsu a kaina sai dai babu batun yin wayar tun da ba ni da waya Mama Rumaisa, Ahmad, Khalil hawaye suke zubarwa da ni ma haka ne gurina ana saka kayana a boot Yaya Samir ya shiga motar ni ma na shiga gidan gaba ya ja motar da addu'o'in iyayena da 'yan uwana dasu Batul muka bar kofar gidanmu da ni dai tun da nake ban taɓa zuwa guri na kwana ba, fuskata na rufe cikin hijabi ina hawaye ganin muna ƙoƙari ficewa unguwarmu.

     **** **** 

    Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
    Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
    Lambar Waya: 08124915604
    Na Cancanta

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.