𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Mutum ne yake fama da
matsalar aikata wani abin da ya saɓa
wa shari’a. Yakan samu damuwa sosai bayan ya aikata laifin, yakan tuba, ya yi
sallar dare, ya ɗauki
alƙawarin
cewa ba zai sake ba har abada. Akwai ma lokacin da ya yi alwashin idan ya sake
zai yi azumi guda sittin! Amma kuma bayan tsawon lokaci sai ya sake komawa! To,
wai menene hukuncin wannan? Me ya kamata ya yi a kan wannan matsalar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Babu shakka saɓon Allah abune da ke
haifarwa da bawa matsaloli masu yawa, amma kuma Allah mai yalwar falalane
matukar mutum ya yi nadama yagane kuskuren sa ya tuba to lallai Allah mai yawan
gafarta zunubaine, Allah maɗaukakin
sarki ya ce:
وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Kutuba zuwa ga
Allah gaba dayanku yaku muminai Zaku samu tsira da rabauta. (Suratul Nuur : 31)
Yasake cewa:
قُلْ يَٰعِبَادِىَ ٱلَّذِينَ أَسْرَفُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُواْ مِن رَّحْمَةِ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ
يَغْفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُۥ هُوَ
ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Kace dasu yaku
bayin Allah wadanda kukayi Laifukawa kawunan ku kada kuɗebe zaton tunanin Allah bazai iya yafe muku
ba, lallai Allah yana gafarta zunubai gaba ɗaya
kuma shi Allah mai yawan gafara ne dajinkai ga bayinsa. (Suratul Zumar 53)
Kalmar tuba
tana da girma da dalililai masu zurfi, bakamar yanda wasu dayawa suke ɗauka ba, kawai kafurta da
harshe kuma kaci gaba da aikata laifuka, ka lura ka kula dafadar Allah maɗaukakin sarki:
وَأَنِ ٱسْتَغْفِرُواْ رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيْهِ
Kunemi gafarar
ubangijinku sannan kutuba zuwa gareshi (Suratul Hud : 3)
Haka ɗin dai zai yi ta bin
matakan da malamai suka shimfiɗa
a duk lokacin da yi zunubin kuma yake son samun ingantacciyar tuba, karɓaɓɓiya a wurin Ubangijinmu Tabaaraka Wa
Ta’aala.
Matakan da za
ki ɗauka domin neman
gafarar Allaah da samun tubansa da yafewarsa a kan kowane irin zunubi su ne
kamar haka:
Ki daina yin
aikin saɓon a daidai
lokacin da hankalinki ya dawo jikinki, kika fahimci kin saɓa wa Allaah Ubangijinki.
Ki yi ƙoƙari
tuban naki ya zama saboda Allaah Maɗaukakin
Sarki ne kaɗai, ba
domin wani dalili daga cikin dalilai na dabam ba.
Ki ji a cikin
zuciyarki da jikinki cewa, wannan abin da kika aikata mummunan aiki ne, wanda
kuma zai iya haifar miki da mummunan sakamako a Duniya da Barzahu da Lahira,
idan Allaah Ta’aala bai tausaya miki ya yafe miki ba!
Ki yi nadama
da baƙin
ciki a kan abin da ya auku na wannan mummunan sakacin da kika yi har wata gaɓa daga cikin gaɓoɓinki ta karkace ta faɗa cikin saɓon.
Ki faɗa wa Allaah Ubangijinki
Masanin ciki da wajen al’amuranki cewa: ‘Ya Allaah! Na tuba kuma na komo gare
ka. Don haka ka yafe mini saɓon
nan da na tafka.’
Ki ɗaura niyyar cewa ba za ki
sake komawa ga yin irin wannan sakacin ba, balle har a samu wata gaɓarki ta sake aikata laifi
mai kama da wannan a iya tsawon rayuwarki.
Ki yi amfani
da wani kyakkyawan aikin imani da kika taɓa
aikatawa ko wani mummunan aikin sharri da kika nisance shi saboda Allaah kaɗai, ki yi tawassuli da
hakan ga Allaah a wannan lokacin.
Watau, ki roƙi
Allaah Ta’aala da
wannan aikin.
Ki yi ƙoƙarin
gyara abubuwan da kike iya gyarawa na ayyukan da sakacinki ya sa suka lalace,
ko waɗanda kika ɓarnata ta dalilin wannan
saɓon, idan suna iya
gyaruwa.
Ki rabu da
wuri, ko duk wanda ya zuga ki ko ya yaudare ki ko kuma ya taimaka miki har kika
tafka wannan zunubin.
Ki yi ƙoƙarin
kusanta ko haɗuwa da
sababbin ƙawaye
da sauran mutanen kirki, waɗanda
za su iya taimaka miki su zuga ki ga ci gaba da aikata alhairan da za su iya
zama gyara ko masu kankarewa ga abin da ya gabata na ɓarna.
Idan kuma
laifin ya haɗa da haƙƙin
waɗansu bayin Allaah
ne, to a nan sai kin mayar musu da haƙƙoƙin nasu, ko kuma kin nemo amincewarsu da
yafewarsu.
Lalata duk
kayan da ake amfani da su wurin aikata laifin, kamar misali kwalaben giya ko ƙwayoyin
daskarar da ƙwaƙwalwa ga masu shaye-shaye, ko kuma hotunan tsiraici ga masu
kallon fima-fimai da sauran makamantansu.
Waɗannan su ne matakan da za
ki riƙa
ɗauka a duk lokacin
da waɗannan maƙiyan
suka sa kika zame kuma kika afka cikin aikata dukkan wani zunubi ko saɓo. Allaah Ta’aala nake roƙo ya
tsare mu, ya taimake mu gaba ɗaya,
kuma ya sa mu fi ƙarfin shaiɗanunmu
da zukatanmu. Allaah ya shiryar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.