Ticker

Na Yi Wankan Janaba Da Sabulu Shin Alwala Ta Tananan

TAMBAYA (40)

Assalamu alaikum Dan Allah Ina tambaya a kan yayinda nakammala wankan janaba Kuma nasake yin wanka da sabulu alokacin shin alwalata Tananan kokuma Sena canja???

AMSA

Waalaikumus, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

Hukuncin yana damfare da tambaya, shin sabulu najasa ne ?

Dukkan malamai sun hadu a kan cewar sabulu ba najasa ba ne ba

Anfison a gabatarda alwalar a cikin wankan da aka yi shi da zallar ruwa mai tsarki ko kuma da soso da sabulu a maimakon ayi shi da farko kamar yanda kayi

Wankan janaba na kamala yana dauke matsayin alwalarne ko da kuwan anyi wankan da sabulu

A takaicedai alwalarka ta yi in sha Allahu indai har babu abin da ya faru dakai wanda yake warware alwalar

Sannan kuma anason mutum ya sa a ransa cewar zai yi niyyar bawai don gaggawar ya yi ya gama ba ko kuma don nuna gazawa a ibada saidai anaso ya yi hakanne da kyakkyawar zuciya da kuma niyyar tsarkake jikin domin bautawa Allah SWT saboda hadisin da Abu Hurairah RTA ya rawaito cewar Annabi SAW ya ce: "Ayyuka suna karbuwane da niyya, kowanne mutum zai samu abin da ya yi niyya ne”

Hadisan suna cikin Sahih Bukhari 1:1 (Babin Ilimi), da kuma Sahih Muslim 1:19 (Babin Imani)

Sannan ita niyya bawai firtawa ake ba ko kuma karanta wata addu'a saidai ana yin niyya ne a zuciya

Subhanakallahumma, wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

✍️Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments