𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam kayini lafiya Allah yakaro ilimi mlm tambayata yau ita
ce saurayi ne da budurwa suke tare yahana ta kula kowa ko da awayane ko chat
duk yahana ta ya ce inhar zatana yi tose su rabu duk tadena amma matsalar a nan
ita ce malam kullum tunaninsa tanayi a ɓoye kuma itake kiransa setamai miss calls 5 inkuma
yakira baya kusa inyamata miss calls a waya seyayi fushi kuma ita taka sa gane
wannan lamarin shi ne take Neman shawara da mufita. mun gode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salaam. Shawara ta a nan ta yi hakuri ta rabu dashi, shi ne
zaifi mata Alkairi.
Abin da ya sa na ce idan za ta iya yin hakurin shi ne, da alama ita ce ta
na ce masa, shi ya sa ma yake mata irin wannan, abin da aka San namiji fa, shi
ne zaike lallaɓa mace,
ba mace bace zatake lallaɓa
namiji ba, duk da dai Allah ya kawo mu wani zamani.
Kalli yadda soja ya je da kwarjini a idon mutane, amma idan ya je gida sai
ya lallaɓa
matarsa, amma in ban da mace ba wanda soja zai lallaɓa, kawai hukunci yakeyi daidai da yadda ya
gadama.
Haka Sarki yana da kwarjini a cikin fadawansa da mutanen gari, amma idan ya
shiga wajen matarsa, sai ya kaskantar da kansa.
Haka gwamna ana masa jiniya da sojoji da yan-sanda da sauransu amma idan ya
shiga wajen matarsa sai ya risina, Kai kowanene ma haka ne.
Amma ke namiji yana hanaki yadda ya gadama. Sabida haka mace tana da kima a
musulunci, ki duba yadda manzon Allah ﷺ ana cikin tafiya tare da ayarin sahabbansa MAZA
da MATA kamar yadda imamu maliku ya fitar a cikin muwadda, babin da yake magana
a kan sallar kasaru. Da sarkar ummuna Aisha ta tsinke ta faɗi, sai da manzon Allah ﷺ ya tsaya aka kwana a wurin tare da
sahabbai ana neman wannan sarkar ba’a sameta ba sai daga baya, har sai da
manzon Allah ﷺ ya yi
barci a wurin, mutane suka ce da sayyadina Abubakar, Kayiwa Aisha magana ta
hakura da wannan sarkar, ta tsayar damu, Sabida ita ce ta tsayar da tafiyar
gabaki ɗaya.
Ni banga Dalilin da zaisa namiji yana baiwa mace wahala ba ita kuma ta na
ce masa, ta rabu da shi kawai, Sabida wallahi na sani wannan kuma kamar a
rubuce yake a wurinki, ko da bayan Ya aureki ya dinga azabtar dake ke nan, sai
dai idan kin ga ba za ki iyaba ki ce ya sakeki, nan da nan zai mayar dake ba zawara,
ko kuma ki yi ta zama tare da shi 'yan uwanki mata suna kallonki a matsayin yar
kwawa da naci.
Sabida haka Ni banga Dalilin da zaisa ki na ce masa ba, kullum ke ce mai
bashi hakuri, ke ce mai lallabinsa, ke ce Mai nemansa sai ya gadama zai dauki
kiranki ba, idan kuma ya kiraki idan kina da wani uzurin da ya sa baki daga
wayar ba, ba zai yi miki uzuri ba, zai dinga miki fada ko yana miki fushi.
Ba mamaki ko kina Addu'ah ne a kan Allah ya zaɓa miki Alkairi, sai Allah yake nuna miki
cewar wannan ɗin ba
Alkairi ba ne, aka fitar miki da mummunan halinsa da irin zaman da zaku yi
bayan ya aureki, amma kuma ke baki gane ba.
Da yawa mutane suna Addu'ah Allah yana karɓa musu yana zaɓa musu Alkairi amma basa ganewa. Sai dai
kuma ban sani ba ko kina ganin kamar idan bai aureki ba, ba za ki sami mijin
aure ba, Wannna kuma wani abu ne na daban. Allah ya sa mu dace. 🤲
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.