Ticker

6/recent/ticker-posts

Nijeriya Ranar Indifenda - Hausa Haiku 21

1.
Yau Najeriya
ta cika shekaru har
Sittin da uku.

2.
'Daya ga watan
goma alif d'ari tara
da sittin daidai.

3.
Turawan mulkin
mallaka suka sauka
daga karaga.

4.
Samun y'ancin kai
ya tabbata gare mu
'Yan Najeriya.

5.
Akai ta murna
ga biki har budiri
kowa da buri.

6.
Saboda kwance
mana talala, yau mun
samu walwala.

7.
Sai dai fa kash!
An gudu ba'a tsira
ba, jiya iyau.

8.
Yan k'asar babu
mai nuna farin ciki
Illa k'alilan.

9.
Don k'asar tamu
ta yi rashin dace an
rasa shugaba.

10.
Kwaya d'aya tal
da ke da hangen nesa
tun juyin mulki.

11.
Ga mu da k'asa
mai jama'a mai komai
mun kasa seti.

12.
'Yan k'asar ga Ilm
amma amfani da shi
ya gagare mu.

13.
Bangaranci da
k'abilanci sun hana 
mu cimma buri.

14.
Ina matsalar 
ta samo asali ne?
Babu masani.

15
Da farko manyan
sun samu ilm kyauta sai
suka so kansu.

16.
Rowa da 'Kyashi
suka hana su kishi.
Kowa bakinsa.

17.
Maimakon gina
mutum ya zamo gina
k'asa, suka k'i.

18.
Kowa ya ci ya
bai y'ay'ansa salwa sai
ya toshe kofar.

19.
Har ta kai kowa
ya zama tururuwa
mai tara hatsi.

20.
Ba don ki ci ba
sai don ki san rumbunki
a cike yake.

21.
Najeriya yau 
indifenda. Su k'oshe
mu kwana yunwa.

 Daga Taskar

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960

A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments