Ranar Indifenda (63)

Tunda yau aka ba da 'yanci,
Ya kamata mu bibiye shi. 

Tunda an ce wai da 'yanci,
To kamata yai mu gan shi. 

Tunda yau aka ba da mulki,
Yaushe zai daɗi mu ji shi?

Tunda yau take Indifenda,
Ya kamata a waiwaye shi. 

Tunda sun ce sun sake mu,
Ya kamata fa duk mu tashi. 

Ya kamata mu hau ta turba,
Cigabanmu mu ƙarfafe shi. 

Ya kamata sahun ya miƙa,
Duk rashi fatara a bar shi. 

Yanzu yau dai babu 'yanci,
'Yan kaɗan ke moriyar shi. 

'Yan kaɗan ne ke bishasha,
'Yan kaɗan ne ba su nishi. 

'Yan kaɗan sun sace naira,
Mu muna fatara da bashi. 

Yau tsaron ma ba a samu,
Fargaba kowa ka gan shi. 

Yau wuni aka yi da yunwa,
Yau abinci wuya gare shi.
 
Yau ina shakkar da 'yanci,
Sun bugai sun taka kanshi. 

Ya yi sixty three a coma, 
Yaudara ce wai akwai shi. 

Babu 'yanci babu 'yanci,
Babu shi balle a gan shi. 

©
Murtala Uba Mohammed
01/10/2022
10:17 nd

Post a Comment

0 Comments