Ticker

Rataye 1: Wasan Girjim

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Wannan wata wasa ce dangin dara. Sau da dama akan yi caca da ita. Wato a sanya kuɗi kan cewa duk wanda ya yi nasara a wasar, to zai mallake kuɗin. Wani lokaci akan sanya wani bu daban da ba kuɗi ba, kamar tufafi da makamantansu. Maza manya ne suka fi gudanar da wannan wasa. Sai dai akan samu wasu lokuta da yara ke yi, musamman waɗanda suka gani daga manya. Mutane biyu ne suke gudanar da ita, sai dai za su iya fin yawan haka yayin da aka yi taron dangi.

Wuri Da Lokacin Wasa

i.                        Akan gudar da wannan wasa a filayen caca, da keɓaɓɓun wurare cikin kasuwanni. Yara sukan yi a gindin inuwowin bishiyoyi a cikin unguwanni.

ii.                        Ana gudanar da wannan wasa da hantsi ko rana ko ma da yamma. Sai dai ba a faye yin ta da dare ba.

 

Kayan Aiki

i.                        Ƙodagon goruba ko taura ko ƙwallon mangwaro ko duwatsu ko makamantansu.

 

Yadda Ake Wasa

Akan zana gidajen dara kimanin talatin da shida (36) ko a yi ‘yan gurabu yawan wannan adadi. Akan yi gidajen daran shiɗa a tsaye, shida kuma a kwance, jere da juna reras. Daga nan kowa daga cikin ɓangarori biyu na masu wasa zai zaɓi nau’in ‘ya’yan da zai yi amfani da su (ko dai tsinke ko dutse ko ƙwallon mangwaro ko na taura ko ƙwadagon goruba da makamantansu). Kowa zai ɗauki ‘ya’ya goma sha biyu ya zuba su ta hanyar jerewa a layuka biyu na farko da ke gabansa. A wani lokaci akan yi taron dangi, wato mutane biyu ko sama da haka su kasance suna tafiya a tare. Wato su yi shawara kafin ɗayansu ya yi tafiya. Wani lokaci kuma za a samu wani mutum da ba ya cikin wasa amma yana sanya baki a wasan. A irin haka, abokin wasan wanda ake sa wa baki zai iya ƙin yarda, musamman idan wasar ba ta buqatar wani ya sa baki.

 

Daga nan mai tafiyar farko zai fara tafiya ta hanyar tura ɗa zuwa gidan da ke gaba da shi. Za su ci gaba da tafiya karɓa-karɓa. Akan tura ɗa zuwa gidan gaba ko baya ko gefe. Yayin da ‘ya’ya biyu na ‘yan wasa daban-daban suka mannu da juna, mai tafiya zai cinye wannan ɗa da ke jikin ɗansa (idan akwai gidan da zai iya sauka a bayan ɗan). Idan kuwa mai wasa ya kai ga shiga ɗaya daga cikin gidaje biyu da ke kusurwa a gaban abokin karawarsa, to ya shiga Sarki. Saboda haka, za a naɗa shi Sarki ta hanyar ƙara ɗa ɗaya a kan wannan ɗa da ya shiga Sarki da shi. Sarki yana da ikon yin  doguwar tafiya. Saboda haka zai iya cin ɗa da ke nesa da shi. Amma Sarki ba zai iya cin wani Sarkin daga nesa ba. Ɗa kuwa ba zai iya cin Sarki ba, ko da suna kusa da juna, sai dai idan ya rage ɗa ɗaya ne kacal ga mai wasa.

 

Wasu lokuta mai wasa kan ambaci: “girjim” daidai lokacin da ya ɗaga ɗa daga wani gida zuwa wani gida, musamman domin zolaya. Hakan na faruwa yayin da ya sunsuni/shinshini ƙamshin nasara kan abokin karawarsa, wato domin zolaya. Yayin da aka cinye ‘ya’ya mai wasa ko aka kulle shi gaba ɗaya, to an kore shi ke nan daga wasan a wannan turmin.

 

Wasu Daga Cikin Dokokin Wasa

Duk da akan samu bambance-bambancen dokokin wasar daga wuri zuwa wuri, an yi ƙoƙarin kalato wasau daga cikinsu kamar haka:

i.                    Sanya baki a wasar da ba ta sa baki laifi ne.

ii.                  Idan ɗan wasa ya samu damar ci, sai bai ci ba a wasar da take tsakar ci, to za a ɗauke wannan ɗan da ya ƙi ci da shi.

iii.                Yayin da mai wasa ya dace ya ɗauki akalar wasan da ke ci sai ya yi wata tafiya daban, to damar lokacin was an/kakar was an wannan lokaci ta huce/wuce.

iv.                Duk wanda aka shiga ɗaya daga cikin kusurwowin gabansa biyu, dole ya naɗa wa abokin wasansa Sarki.

v.                  Sarki yana fawar doguwar tafiya.

vi.                Ɗa ba ya iya cin Sarki sai ya kasance shi kaɗai ne ya saura a gidan mai wasa.

vii.              Sarki zai iya cin ɗa daga nesa.

viii.            Sarki ba zai iya cin Sarki daga nesa ba.

 

Post a Comment

0 Comments