Rayuwarmu A Bodin - (Labarin Gaskiya) - [Complete Book]

    💦💦 Rayuwarmu A Boarding  - (A True Life Story)💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa
    (Rukee Sauwa)

    Page 1-5

    Rayuwar Boarding
    Photo Credit: BBC

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    Garin kebbi, gari ne mai ɗauke da yarukka kala-kala da kuma unguwanni.

    Shiyar sarakuna wata makaranta na hango, shiga na yi domin na ɗauko muku rahoto, da alama makarantar ta kwana ce wato (Boarding school) ga wani symbol na ga an rubuta GGC Unity, sai yanzu na gane Unity domin kuwa makaranta ce da ta yi fice a cikin kebbi even outside kebbi ma, makaranta ce mai ɗauke da ƙabila kala-kala tun daga Hausa, Fulani, Yoruba, Naijan, Christians etc.

    Wasu yara na gani su biyu sai wani dattijo amma ba sosaiba, ƙare musu kallo na yi, suna kama sosai sai dai ɗayar tafi ɗayar ƙiba dukanninsu ba farare ba ni sosai sai dai a kirasu da chocolate colour ne kyawawa ne.

    "Rukayyat please ku yi karatu ba ruwanku da rashin ji domin na san kece mai matsala na san Hafsat ba ruwanta” wadda aka kira da Rukayya ce ta ɗago tare da shagwaɓe fuska "haba Abba to ni mina yi, ke nan ita bata bata laifi sai ni " na san halinta ne shi ya sa” cewar Abba yana sa hannu cikin aljihun rigarshi, kuɗi ta ke Rukayya ta washe baki domin tasan zataji daɗi da kwalama.

    Dubu biyar Abba yabasu ya ce gashi su riƙe ba’a rasa abin saye ba amsa sukayi tare da godiya, dai dai nan wata matashiyar budurwa ta isu wurin doƙawa ta yi tare da cewa " Abba ina wuni ya gida " lafiya ƙlau Hadiza ya karatu "Alhamdulillah" masha'allah to ga ƙannenki nan ki kula dasu hardai Rukayya "to Abba insha'Allah " yauwa Hadiza "dubi biyu yabata amsa ta yi tana mai godiya tare suka rakashi har motarshi kirar matrix (4+) sunanan tsaye har ya bar makarantar se alokacin na ƙara ƙare musu kallo sosai.

    Rukayya kyakyawa ce chocolate mai ƙiba tanada dogon hanci kuma ga manyan idanu iya karta shekaru goma sha biyar (15) tanada manyan hip's sosai sai dai batada breast, Hafsat fara ce amma ba sosai ba domin da kaɗan ta ɗara Rukayya tanada manyan idanu hancinta siriri mai tsayi gata da breast ammfa Rukayya ta gita hip's iya karta shekaru goma sha shidda(16) amma za a ce years ɗinsu ɗaya da Rukayya domin girman jikinta.

    Hadiza kyakyawa ce ajin farko ga diri ga tsayi baƙa ce amma baƙinta mai haske ne da kyau idanunta ƙanana ne masu lumshewa hancinta ƙarami ne hakan ya sa ya yi chir a fuskarta ya yi kyau sosai sanye take da wasu chess blue wando mai faɗi ne sosai domin ku su huɗu za su shiga ciki, ka san cewar tanada jiki ya sa wandin yimata kyau domin daga sama kamar an matseshi yadda bombom ɗinta suka cikashi sai dai haka halittata ta ke ƙaramin hijab ne iya karshi ƙirjinta hakan yaba rigar damar fitowa fili, mai digon fari da blue.

    "Mine yan ƙanen " harararta Rukayya ta yi domin ta tsani sunan "wai yan ƙanne nifa bana son wannan sunan ki kirani da sunana” cewar Rukayya tana kama ƙugu kamar mai shirin faɗa, sai alokacin Hafsat ta yi magana ka sancewarta ba mai son hayaniya ba " to uwar masifa daga zuwanki sai faɗa ai sai ki yi nan dai ba gida ne ba” eh ina ruwanki wallahi bana son raini sai in zaneki yanzu wurinnan " dukansu dariya sukayi dai dai nan Hadiza ta kira wasu students su biyar ta ce su ɗaukumata kaya kamar uwarsu jiki na rawa suka kwasa, har suka isa hostels ba mai cewa komai wata budurwa ce sanyi ta ke da ƙani yulolun ɗankwali wanda iya duwawunta kawai ya rufe rabin breast ɗinta duk waje suke rungume Hadiza tare da faɗin. . . . .

    Comments ɗinku shi zai ba ni damar ci gaba da rubuta wannan littafin rashin comments na nufin bai muku ba nikuma bana son abin da bai muku ba fans🥰🥰🥰.

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa

    (Rukee Sauwa)

    Page 6-10

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . "Dijee Bala ina kika samomana yarannan " su Hafsat ne ta faɗa a taƙaice " ki ce ƙanenmu ne sanunku" ina wuni” suka faɗa a tare "lafiya yakuke ya gida " lafiya lau" juyuwa Dijee Bala ta yi ta kalli junior's ɗin ta ce " ke kukai kayannan room 2 Fati kamba " tsaye sukayi domin sun san abu mai wuya ne su iya bi ku bayan room ɗin .

    "Ku bukuji ba ne " ta faɗa da ƙarfi "Anty Lola ba za abarmu ba " suka faɗa jikinsu na karkarwa " shin ɗakin mallakin su waye "naku " suka faɗa a tare " to ki je kukai "tafiya sukayi sukuma suka bi bayansu.

    Mamakine ya kama su Rukayya ganin duk inda saka bi anata ba su hanya, wani dogon room suka shiga " wow ai wannan kamar gida Rukayya ta ce ta na shiga ɗakin, ɗakin yasha gyara dogon room ne kamar dai na boarding schools, gadaje ne jere har gado shida irin gadajen yan boarding masu hawa ukku gefen dama ukku haggu ma ukku.

    Ku wane na tsakiya ansa matras (katifa) an shimfiɗa beed sheet ga fankuna da gloves sai ƙamshin air freshner ke tashi, can ƙarshe kuma toilet ne mai abun zama da kuma shower, wani lungu kuma an aje gas guda ɗaya sai risho ƙarami kuda ga kuma tower's ƙanana kuda biyu ga kuma basket mai ɗauke da duk wani abin buƙata aje gefe, ledar kasa ce mai kyau aka shimfiɗe ɗakin da ita "ku ina tsaf " cewar Hafsat bayan sun gama kallon ɗakin.

    Bura'uba wasu shegonan Juniors ne a ɗakin nan" cewar wata budurwa da ta shigo room ɗin dubansu suka kai gareta a tsora ce ban da Dijee Bala da kuma Lola da suka shiga kwanarsu, sanye ta ke da wani yolulun gyale da ta ɗaura rabin nononta duk a waje gashi har fant ɗinta ana gani kanan bako ɗankwali, sai wata bulala a hannunta wadda ta yi tsawonta biyu.

    Isuwa ta yi inda suke tare da cewa "ku dan ubanku wani tsautsayi ne ya kawoku room ɗinnan dan ubanku ku rage tsawonku ku haɗa tsawo za ku yi dani” dasauri suka rage tsawonsu ban da Rukayya da ke mata kallon up and down " ke dan ubanku ba za ki rage tsawon ba " ta faɗa tare da kallon Rukayya " dan ubanki dai kuma anƙi ɗin " kanta ta yi gadan -gadan. . . . . .

    Share fisabilillah

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa

    (Rukee Sauwa)

     Page 11-15

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . kanta ta yi gadan gadan duk da Rukayya ta tsorata haka ta dake ta na ƙara riƙe kogo.

    Ɗaga santaleliyar bulalarta ta yi daniyar zuba mata amma sai taji an riƙe bulalar ta baya, Rukayya ta gama tsorata domin tasan idan wannan sandar tahau banta ta gama yawi ku dama bakin ɗaine ba wani ƙarfi(🤣🤣🤣🤣)

    "Ƙull Kaza karki kuskura hannunki yasauka akanta, kokuma ku wuce” da sauri suka fita " haba Dijee Bala wannan wane irin abune haka " ke su Hafsat ne fa da Rukayya "cewar Lola da ta leƙo kanta daga kwancen da ta ke, murmushi ne ya subce mata domin ta daɗe ta na jin labarinsu abakin Dijee Bala " da yau na tabka abin kunya” ah to" cewar Lola " amma dai kece Rukayya ko" tafaɗa tana nuna Rukayya " eh ni ce " tafaɗa cike da tsiwa " ke kuma Hafsat ko" eh " Hafsat tafaɗa cikin sanyi domin gaskiya ta tsorata .

    "Ku shigo ku huta " cewar Dijee Bala shiga sukayi ka sancewar yau asabar kuma magrib ta gabato hakan ya sa sukayi wanka tare da al'wala zane suka ɗaura iri ɗaya yayinda Hafsat tasa hula Rukayya kam bata saba kallonta Hafsat ta yi kafin ta ce " waike ba za ki daina zama haka ba ne wallahi ki kiyayeni” sannu uwata Anty ku ita ta gaji ta bari " Rukayya ta faɗa cike da tsiwa " to ya yi Rukayya kufara tun yanzu za ku zo kuci abinci ku sai na iskeku ne” to ke Anty Hadiza bikiji mai ta ke cemin ba kamar wata uwata "Rukayya tafaɗa tana tura baki gaba " eh kuma wallahi sai kinsa hular " tafaɗa tana samata hular akanta zama ta yi suka fara cin indomie wacce tasha kayan kamshi sai tururi ta ke .

    Kaza da Lola ne suka shigo kwanar suna ɗan jansu da fira sosai ku suka saki jiki dasu harda kyalkyalewa.

    "Wainiku yau ina Wasila ta shiga ne” Dijee Bala tafaɗa tana kallonsu"hmmmm tana kanta wurin loverta Nana "Lola ta ce” aisaidai muhaɗu da ita Raka wajen bajewa " ok " kawai ta ce bayan sungama cin abincinne sukayi sallahi suka kwanta sai bacci su Dijee Bala kuwa wanka sukayi suka ɗaura zani iri ɗaya ɗaurin talli ɓaris rabin nono duk waje sai ture ka ga tsiya da sukayi suka fice a ɗakin tare da kullewa.

     Wani wurine mai faɗi yasha cement yan'mata ne sai kiɗan long da jarka ke tashi suna isa wurin yaɗauki shewa, fillin ko wacce ke shiga tana baje ukkunta basudawo ba har 10pm suka dawo harda Wasila Naija tasu ta tada su Rukayya amma Kaza ta hana wai ba za ta tada mata babe's ba suna baccin gajiya tabari sai gobe tun da gobe lahadi sai suhaɗu su zaga dasu badon tasuba ta haƙura suka kwanta.

    Asubar fari

    Wash wallahi na gaji ku yi hakuri da wannan azumi ya yi beating bana son ɓata muku shi ya sa na yi wannan ina fatan za ku fahimceni😍😍😍😍😍.

    Comment and Share fisabilillah

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    ✍️Alƙalami ya fi takubi🗡️

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Page 16-20

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . . . Bugun Raka da aka yi ne ya tadda su Rukayya a firgice salati suka fara a tsorace Rukayya ce ta yi ƙarfin halin kiran Anty Hadiza amma shiro fitowa ta yi waje nan ta ga su Kaza kowaccensu da bulala a hannunta suna zaune saman long " har kun tashi” cewar Kaza da ta lura da Rukayya alokacin su Wasila suka lura da ita daidai nan kuma Dijee Bala tafito wani lungu riƙe da bulala da torchlight.

    "Ƙanwa kun tashi " eh" hafsat da ta fito yanzu ta faɗa, Rukayya ko inbanda tura baki ba abin da ta ke " waya taɓa mana Ƙanwa " cewar Wasila Naija tana rungumu Rukayya jikinta, ƙara shigewa jikinta ta yi, " ai saiku yi ta yi indai wannan ce " Dijee Bala ta ce ta na kama hannun Hafsat suka shige ciki.

    "Kin ga kyalesu zumuje ki yi Al'wala da brush" cewar Kaza tanajan hannunta buta ta bata da brush, sallah sukayi tea mai kauri da bread suka haɗa musu Kaza ce keba Rukayya abaki ita kuma sai karɓa take yi tana shagwaɓe fuska " baby tashi ki yi wanka” Kaza ta faɗa tana duban Rukayya shagwaɓe fuska ta yi kafin ta ce " uhm nidai a'a” zaro ido Kaza ta yi kafin ta yi magana Hafsat da ke ƙoƙarin ɗaura towel tafara dariya kafin ta ce " ɗaya wallahi yar'luku ta ta batason wanka musamman na safe” ta ci gaba da dariya suma su Lola dariya suka sa, haushi ne ya kama Rukayya ta ɗauki cream ɗinda ke gefenta tana jefama Hafsat itaku tana ƙaucewa” baby ki barta muje " to bikiga tana mun dariya ba " Rukayya ta faɗa hawaye na wanke mata fuska.

    Asanyaye Hafsat ta zo durƙusawa ta yi ta kama hannunta tana masifar ƙaunar yar'uwarta kawar dakanta ta yi gefe " please dear ki yi haƙuri kin ji” ta faɗa tana share mata hawayenta " anƙi naƙi hakura ɗin" to karki haƙura inba bura'uba ba ya tana baki haƙuri kina mata iskanci " cewar Dijee Bala ta na kama hannun Hafsat dama already su Wasila na waje suna jiransu suka fice.

    Kuka tafashe da shi kafin tafara magana " aidama na san bakwa sona duk na ƙarya ne, munafukan banza nafi ƙarfinku ba dai ta mutum ba saidai Allah nan gani nan bari dukiyar uban wani ce” ( to Rukayya irin wannan kirarin haka nidai na yi nan kafin Rukayya Fan's su sani gaba💃💃💃💃💃💃💃💃💃) " mtsss aikin banza "ta ƙarashe maganar tana faɗawa kan bed ta ci gaba da kukanta. . . . .

    Asha kuka lafiya🤣🤣🤣🤣🤣

    Comments

    Vote and

    Share fisabilillah

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    ✍️Alƙalami ya fi takubi🗡️

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa

    (Rukee Sauwa)

     

    *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

    _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa

    https://m. facebook. com/story. php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

       💪🏻J. A. W 💪🏻

    Page 21-25

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . . Kaza ce ta ƙaraso inda ta ke batason wannan kukan sa Rukayya keyi Allah yasamata ƙaunar yarinyar har cikin zuciyarta, hawa kan bed ɗin ta yi tare da rungumuta jikinta, ajiyar zuciya suka sauke tare, ta rage sutin kukanta sai sauke ajiyar zuciya ta ke, can ka san zuciya Kaza ta ce " please is ok dear stop crying " naƙi bayan kowa baya sona duk kun tsaneni” shiiii waya gaya miki ba ma sonki ba haka ba ne gaskiya ne, kin ga Hafsat ta girmeki bai kamata ta na duƙawa ta na baki haƙuri kina mata walakanci ba” ta faɗa tana shafa gashin kanta " ok harda ke wai ta girme ni " dariya ta yi domin ta fahimci cewa Rukayya nada son girma sosai” nifa ba haka nake nufi ba, to ni nabaki haƙuri instead of her " uhm" ta ce ataƙaice " to please am sorry for" kafin ta ƙarasa Rukayya ta sa hannunta ta rufe mata baki " na haƙura " kawai ta ce tare da juya mata baya " to kina sona " tasake jefomin tambaya ɗan jim nati kafin na ce " sai na yi shawara da hafsat tukunna” ok nibanmakai ki soni ba harsai kin yi shawara ko " a'a ba haka ba ne to ki yi haƙuri "inasonki " ta faɗa tana juyu fuskarta suna fuskantar juna " and promise me ba za ki yi secret love ba " eh" kawai na ce mata kiss tabani mai kyau a kumatu ƙara shigewa jikinta ta yi " kuma yau ba zamu yimusu magana ba " eh " dahaka mukayi bacci.

    Ɓangaren Hafsat sun zagaya ko ina acikin hostels ɗin inda ta haɗu da wata matashiyar budurwa sa'arta Balkisu, Balki yarinya ce maikyau fara ce amma ba sosaiba tanada tsayi kaɗan sun haɗu ne bakin kanta kawai Hafsat ta burgeta sukayi magana sama sama domin hankalin Hafsat duk baya kanta sakamakon tabar rabin jikinta na fushi da ita, haka suka dawo daidai lokacin mungama Sallah.

    Da sallama suka shigo ku kallonsu ba muyiba maka fara cin gwaben garin da mukayi yaji kaya sosai, suma sharemu sukayi sallah sukayi suka faracin abinci, mukuma mungama shiryawa na yi cikin zane iya guiwa santala santalan ƙafafunta suka bayyana fauda tashafa sai lipstick mai wal wali ta yi kyau sosai sai dai bata sanya ɗankwali ba domin ɗabi'arta ce tun gida.

    Har lokacin Hafsat ta kasa cin abinci kawai motsa shi take yi nikuma ina satan kallonta ta gefen ido domin na ƙware a satar kallo, duk nadamo ganin taka sa cin abinci jinake kamar na rungumeta na lallaɓata ta ci abincin amma ina dole sai na nuna mata na yi fushi koma abani haƙuri.

    Dama haka muke ku gida idan muka yi faɗa bata iya cin abinci harsai munshirya, saɓanin ni da ba ruwana ko na hannunta sai na karɓe na ci idan na gama sai muci gaba da faɗan, maganar Kaza ce ta dawo da ni daga tunanin da na fara " sweet muje ko" eh muje” saida muka kai bakin ƙofa na juyu na kalli Hafsat har yanzu ko loma ɗaya bata kai bakinta ba na ce " gwandama mutum yaci abinci don wallahi idan ƙwalsa ta kama mutum, hmmm ko nafishi kiɓa ɗaukarshi zan yi na nunama Allah na buga da ƙasa " gaba ɗayansu dariya sukayi harda hafsat sai lokacin hankalinta ya kwanta tafara cin abinci saida na tabbata tafara cin abinci sannan muka fita. .

    Comments

    Vote and

    Share fisabilillah

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    ✍️Alƙalami ya fi takubi🗡️

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa

    (Rukee Sauwa)

     

    *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

    _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa

    https://m. facebook. com/story. php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

       💪🏻J. A. W 💪🏻

    Page 26-30

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . . . Munzaga sosai har dare sannan muka dawo wanka kawai mukayi sai cornflakes da mukasha muka kwanta domin gube akwai class, tun asuba muka tashi already munada ruwa a Flaƙs wanka mukayi sukasha tea nikuma na ci bread haka muka shirya cikin wando poppul wanda yaɗan kama ƙugunmu sai white riga har cinyarmu hijjabinmu ƙarami bai ida rufemuna hannu ba schools back ɗinmu da shoe's duk black mun yi kyau sosai haka muka jera duk inda mukabi sai an kallemu kallon rashin sani kamar twins banbancin kawai shi ne ɗaya tafi ɗaya ƙiba kuma ɗaya tafi haske ana gama Assembly har class ɗinmu su Kaza suka kaimu Js3¹.

    Kuda muka shiga Hafsat ta hango Balki wurinta muka nufa Hafsat na gabatar dani muna zama ba jimawa wasu yan'mata ba za su wuce sa'armuba suka shigo su biyu kana ganinsu ka san za suyi rawar kai.

    Ɗayar ce ta ɗanama ɗayar duka a baya tana faɗin " bura'uba ke kin ga wasu twins "tafaɗa tana nunamu murtuƙe fuska mukayi domin ku Hafsat ba bayaba wurin rashin son raini wurinmu suka nufa suna zuwa ɗayar ta miƙomin hannu .

    " Am by name is Rukayya Abubakar Masama and she's my best friend Nazba Abubakar and you " Am my name is Rukayya Muhammad Waziri and she's my blood sister and my best friend Hafsat Idris Waziri " shaking hand mukayi jafin wadda aka kira da Nazba ta yi magana " wow wai dama ku ba twins ba ne na yarda da akecewa blood is fast then water" dai dainan malaminmu ya shigo class ɗinmu "

    Sai 2:00pm sannan muka tashi a gajiye muka kama hanyar hostel mu biyar niya Hafsat, Balki, Nazba, And Masama fira mukeyi a hankali har muka kai bakin mosƙue dazai rabamu dasu sannan Hafsat ta ce " a wane house kuke "Kanta room 8kufa” Room 2 Fati kamba " me " suka faɗa suna zaro idanu " meye wai duk kunwani tsorata haka " Hafsat ta faɗa tana kallonsu " kai ina kundai manta room ɗinku amma room ɗinau Kaza ai bawasa ba” dariya mukayi kafin muce " OK to kuzu bakin MA'inna Haruna sai kujiramu bayan isha” ok haka muka rabu muna shiga room muka iske su Kaza faɗawa na yi kan jikinta ina faɗin " wash my na gaji wallahi " ayya sorry kin ji” ta faɗa cikin nuna damuwarta akai na "yanzu muje ki yi wanka da sallah saimuci abinci " tashi na yi na yi duk yadda ta ce kafin na kwanta 4 aka tadani wai mutafi Rav class haka ba dan naso ba muka je ba mu muka dawo ba sai 6 agajiye na yi Magrib da isha mukaci abinci sai bacci. . . . . .

    Asuba tagari🥰🥰🥰

    Comments

    Vote and

    Share fisabilillah

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    🏻Alƙalami ya fi takubi🗡️

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa

    (Rukee Sauwa)

     

    *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

    _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa

    https://m. facebook. com/story. php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mos

       💪🏻J. A. W 💪🏻

    Page 31-35

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . . Da misalin ƙarfe takwas na daren ranar Friday muna bakin raka mu dukkanmu kowacce da kalar shigarta mun yi shiga ta ban tsoro manyan hijjabai farare da baƙaƙe muka baɗa farar fauda duƙawa mukayi muka fara rerafe muna kukan dabbobi iri iri su deeje bala nata kwasar rawarsu kawai sukaji magana da ƙauƙausar murya nece.

    "Nikesun hanjin biyuncan " Hafsat ta ce " nikuma tun da ni ce tsofuwa zan ɗauki hanjin ukku " wani kukan akuya Nazba ta yi nan fa suka hau gudo kowa yana gudun ceton rai saida mukaga sun watse sannan da sauri muka je Rizab muka wanke fuskarmu kowa ya yi ɗaki da gudu.

    Haka rayuwa ta ci gaba da gudana damu a cikin Unity cikin jindaɗi da walwala yayinda wata Christan Yar' Ss2 ta samun ido haka kawai ta tsaneni, ɓangaren soyayyata da Kaza sai abin da yaci gaba inda nafara secret love dawata Feedo tana aji biyar tana matuƙar sona haka muke zuwa secret room na Fati kamba musha love mun yi suna cikin GGC kuwa yasanmu Biyun Deeje Bala haka ake kiranmu muna jindaɗinmu sosai.

    Munfara Exam ta first term Alhamdulillah komai yana tafiya lafiya ƙlau kusan kullum rigima muke da Hafsat yauma muna zaune muna sanye da chess bansa hula ba tashi ta yi ta ɗaukomin kafin tasami harararta na yi nacire cikin masifa nace.

    "Wallahi kika kuma samun hularnan saina ci ubanki” ban ƙarasa ba ta bugemin baki domin tun da muka zo makarantarnan na kware a zagi, ramawa na yi kallona ta yi cikin fushi da nuna bacin rai ta ce " Sabida ina gaya miki gaskiya shi ne kike mun haka karki damu wata rana za ki duba kudu, Arewa, Gabas, Yamma, amma ba za ki ganniba za ki nemi mai baki shawara irin wadda nake baki ba za ki samuba kowa zai juya miki baya sabida za ki za mu musu abin jidali mutum biyar kawai za su tsaya dake wato ƙawayenki amma akwai wani haske dazai shigo rayuwarki ba da jimawaba” tana gama faɗar haka ta wuce zugum na yi ina tunanin waɗannan kalaman summin tsauri amma idan na chanka dai dai tana nufin ke nan za ta tafi ta barni 'ina ba zan taɓa bari kibarniba” nafaɗa ina share hawayena.

    Yau za mu tafi gida hutun mako ukku sosai muke kuka nida Kaza dakyar' aka rabamu tarigamu wucewa hakan ya sa muka haɗa kai nida su Nazba muna yi haka kawai na ji bana mararin zuwa hutun kamar wani Abune zai faru nan kusa gabana sai faɗuwa yake haka muka wuce gida.

    Mun yi hotu lafiya komai ya yi yadda akeso mundawo babu abin da muka fasa harsai yau da dubunmu ta cika kamar kullum munshirya zuwa raka muka fara ba su tsoro ashe Amira na ganinmu tsawa ta daka mana ai dasauri muka juya hakan yajawo hankalin su Kaza dake rawa kuwa yataru kufaɗi abin da nakamaku kuna yi tsaf dama Gb ce matsoraciya tafara faɗin har abin da ba’a tambayeta kuka nafashe da shi ina faɗin "wallahi haram nibaruwana dama saida na muku wa'azi kuka ƙiji yanzu gashinan ankamamu Anty ustaziyya ki yi min rai wallahi Allah ba da niba” ( to akwai matsala Rukayya daga magana 🤣🤣🤣🤣)

    "Karya kike ki cema mai tsara yadda komai zai ka sance ai ina jinku" aikuwa kamar jakkai haka suka dinga dukanmu da fashion kamar kura taga nama kuka muke da ruƙun yafiya amma saida sukamana lis kafin subarmu daƙyar mkaje ɗaki ba wanda ya ce mana komai sai harararsu nake ina faɗin " nidai ya Allah kana ganin duk wanda yama bawanka mugunta ka saka mishi” shareni sukayi haka har mukayi bacci tun da asubah aka tadamu wai muje punishment kuka nasaka haka suka tunkuɗa keyarmu gaba sai Raka muka kama kunne muna tsallan gwado idan suka wuce na tashi inna gansu nakuma ina kuka Allah sarki su Hafsat kusauɗaya ba su ɗaguba wata senior ce taji tausayina ta ce na tashi duk na fisu wahala aikuwa nafara mata godiya harda duƙawa .

    Haka rayuwa ta ci gaba inda yanzu su Kaza na yin Neco sungama Weac tuni mun yi faɗa da Kaza saboda ta kamamu nida Feedo muna kessing juna dafe zuciyarta ta yi ta zube wurin sumammiya a firgice nayo kanata sai dispensary kwananta biyu ta murmure inda akace zuciyarta tafara samun matsala tun daga ranar idan naje kusa da ita za ta tashi ta ba ni wuri idan ina mata magana za ta shareni.

    Yaukan snaɗau Alƙawarin saina shawo kanta wanka na yi nashirya kwanarsu Balki nabarau can ka sancewar yau batada Exam ita kaɗaice zaune a ɗakin sallama na yi ta amsa tana shiga kwanarta iskuta na yi nafara magana ina kuka.

    "Haba my yaza kimin haka bayan na faɗa miki kuskurene bantaɓa aikatawa ba sai ranar da kikagan mu dan Allah ki yi haƙuri idan ba su kike zuciyata ta buga ba kirasa niba kiji yadda zuciyata take bugu da ƙaunarki jinin jikina hawayena komai nawa da kwaunarki nake yi " naƙarashe faɗa ina ɗaura hannunta saman kirjina daya tsananta bugu.

    Rungumeni ta yi ita ma tana kuka take faɗin " meyasa za kimin haka wallahi ina kaunarki ina kishinki kada kikuma yin secret love kin ji” na ji ba zan sakeba tun daga ranar muka shirya ka sancewar muma muna yin jarabawar shiga aji biyar wato zango na uku a Ss1 rana ɗaya muka gama su sukayi signing out muna kuka suna kuka ranar nida Kaza munsuma ba adadi har ƙaramar hauka mukayi magana take mun cikin wani irin mawuyacin hali da kuma sarƙewar zuciya.

    " ba zan rayu idan babukeba akusa dani ke ɗin haskece fitila wayooni wayyo kaina Rukee ki'agazamin fuskar Kaza ta jiƙe da ruwan hawayen sonki inkika tafi zanmutu nifa " kamar waƙa tana yi muna dariya da kuka har muka durƙusa hannunta na cikin nawa idanunta na cikin nawa jinin na na gudana a jikinta hawayenmu heart beat ɗinmu lokaci guda yake gudana magana nake yimata ni ma kamar waƙa.

    "Nima inkika tafi zanmutu wallah rayuwata dake ta dace kinsace zuciyata nabarmiki amma ba zan lamun ci nisanta daga gareki ba” mutanen dake wurin kowa kuka yake mana babu wanda yataɓa ganin irin wannan soyayyar jinsi mai ƙarfi babu lesbian a ciki.

    Tafin alalo su Nazba ki yimana suma suna kuka tashi mukayi muana buga ƙafa inkasa ta hagu saika buga ta dama ka tuma ka dire biyu lokaci ɗaya haka muka dingayi muna waƙokin Alalo na soyyaya sabuwar waƙa muka fara intayi ni ma na yi ban ma san minake cewa ba " wayyo ƙaunata " wayyo Rayuwata zuciyata lafazin ne tafiso" arayuwata banmata ruwarshi” . . .

    Haka har aka sanyani mutan baba kuka nake kamar na shiɗe leƙo kaina na yi ta glass ganin ansata cikin mota ya sa na kalli cikin idonta kawai alama nake da bakina na furta” I LOVE YOU I WILL NEVER FORGET YOU IN MY LIFE I WILL ALWAYS REMAINED YOU IN MY HEART I WILL NEVER EVERY TRY OR THINK TO FALL IN LOVE AGAIN " Ahankali ita ma alamar tagane menace tafara motsi da bakinta yadda zangane "I LOVE YOU THE WAY YOU I WILL NOT STOP LOVING YOU SHOW ME WHAT'S LOVE YOU HELP ME YOU I DON'T EVEN KNOW HOW TO THANKS YOU BUT I PROMISED YOU I WILL KEEP LOVE YOU AND I WILL KEEP YOUR PROMISED I WILL GIVE YOU A BIG SUPPRESSED YOU ARE MY EVERYTHING" Tafaɗa dai dai muka fita get ɗin GGC wanda bai barmin kuda ɗigo na farin cikin ba komai yatafi da shi mundawo da sati biyu Hafsat tafara wata irin rashin lafiya aka kwantarsheta asibiti yau na kaimata ziyara ta riƙe hannuna tana faɗin. . . . . .

    Pls pray for my Hafsat😭😭😭

    Comments

    Vote and

    Share fisabilillah

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    🏻Alƙalami ya fi takubi🗡️

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa

    (Rukee Sauwa)

     

    *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

    _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa

    https://m. facebook. com/story. php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

      💪🏻J. A. W 💪🏻

    Page 36-40

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    Hannuna ta kama ta ce " Rukayya ta " dasauri nakalleta domin abu mai muhimmanci kawai zakaji takira sunana hankalina nabata ina mai tsareta da idanu, ahankali cikin muryar marasa lafiya ta ce " Yar'lukuta ta ki saurareni dakyau inaso kicire komai a ranki ki fuskanci rayuwa kada rasa wani jigo a rayuwa ya sa ki gaza yanzu ne lokacin daza ki nuna iyawarki ki nuna Ku ba kowa a tare dake za ki iya rayuwa " dakatawa ta yi tana maida numfashi alamar ta gaji.

    Wasu hawaye na ji naka sa gane na miye " kin ga kidena magana kina ƙarama kanki ciwo ke kike nan kwance but ni ma I will fell the pain" hmmm inaso mugana ne domin ina jin ajikina this is Our last meet in" banbari taƙarasa ba nakulle bakinta da tafin hannuna kuka na kufcemin.

    Wani murmushi ta yi wanda ya fi kuka ciwo tana cire hannuna ta ci gaba da cewa " ki yi min alƙawari cewa kamar yadda muka tsara za ki yi and you will win it zamuyi suna a GGC zamuyi muƙami mutaka kowa yasan da zamanmu zamuyi passing da kyaututtuka kala kala ki yi min alƙawari kubani you will not give up" kuka nafashe da shi ina girgiza mata kai domin na gane wasiyya ta ke barmin " kidena cewa haka za mu rayu tare mu mutu tare” ana haka baba ya ce nayashi mutafi gida muna kuka aka rabamu .

    Washe gari ina ɗakin zaune bayan juma'a ba kowa ta ɗaura kanta saman cinyata tana lumshe idanunta takalle ni ta ce " kidinga karantamin kalmar shahada ina amsawa harsai kin ji bana amsawa alamun bacci yaɗaukeni kin ji” kyaɗamata kai na yi nafara karanta mata tana amsawa munjima a haka na ga tana tamin murmushi kawai idanunta suka lumshe kiranta nake yi ina jijjigata na ji shiru.

    Dasauri natashi nakira likita ganin na yi yana cire kanula dake hannunta ya rufe mata fuska, kallonshi na yi na ce " me hakan yake nufi dan girman Allah ka tadamin ita " nafaɗa wani kuka na kufcemin kallona ya yi cikin tausayawa ya ce” tarigamu gidan gaskiya Allah daya fimu sonta ya amshi abun" baigama ƙarashe zancenshiba na sume, saida na yi sati ɗaya na farfaɗo ba da wani kalan kuka na tashi ina faɗin " Baba kanajin abin da ya ce wai yana nufin Hafsata ta tafi wai za ta barni kana jinsa Masoyiyar tawa yar'uwata” kuka ne yaci ƙarfinta rungumeta Baba ya yi yana yimata nasiha kala kala daƙyar tafara dawowa dai dai haka har anfara tunanin a maidata day school amma ta kafe kan lallai saita kuma Unity za ta ci gaba da abin da suka fara harsukai matakin nasara haka ta dawo inda ta cinma sabuwar rayuwa a unity domin Docars tasata a gaba idan wanki tabayar ita ce idan ruwa takeso ita za ta ɗebo mata duk wata wahala bata take amma fa haryanzu rashin ji bata bar ku ɗayaba haka za ta yi komai aka sakata ba musu ammafa za ta rama ta bayan fage yanzu duk Unity bawanda bai san biyun Deejeh Bala ba saboda rashin ji.

    Nazba taƙarashe ba Little Hafsat dake zaune fuska duk hawaye da majina labarin "RAYUWARMU A BOARDING " Tana nuna Rukayya data tsare fuskanta da kallo cikin mirror Little Hafsat kyakyawa ce sosai tun da tashigo Unity Allah yaɗauramata ƙaunar Rukayya haka ta dinga binta harauka kulla abota yanzu tana Ss1 while Rukayya kuma Ss2, numfasawa ta yi kafin ta ce ina yawana ganin maso na kallon kanta cikin mirror " hmm fuskan Hafsat take kalla acikin tata domin suna mahaukacin kama da juna shi ya sa idan taji kewar Hafsat haka ta ke.

    Ba komai haka rayuwa ta ci gaba da gudu yau daɗi gobe ba dadi ta kama yau za su fara ƙualified sunfara a sa'a saura 1 weeks a gama . . . .

    Kudinga bin marubuciya da abin da ta rubuta domin ni banajan labari idan kuna karatun novel ɗina za ku gani banga fa'idar jan labariba idan ka'isar da abin da kakeso agani.

    Comments

    Vote and

    Share fisabillilah

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    🏻Alƙalami ya fi takubi🗡️

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa

    (Rukee Sauwa)

     

    *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

    _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa

    https://m. facebook. com/story. php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

       💪🏻J. W. A 💪🏻

    Page 41-45

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . . Duƙe ta ke tana wankin kayanta tana tuna rayuwa ita da akema wanki ayimata komai wai yau ita ke wankin kayanta hawaye masu zafi suka zubo mata ahankali takai bayan hannunta tana gogewa magana ta ke cikin ƙunar rai dakuma kewa” tabbas yau na tabbata banida masoyi a duniya sama dake Hafsat I really love you may your soul rest in peace, yau naduba gabas, yamma, kudu, Arewa bangankiba ba I miss you " wani kuka ne yaci ƙarfinta a hankali ta durƙushe a wurin ji kawai ta yi an dafa kafaɗarta ta baya juyawa ta yi taga su Nazba, Balki, Gb, Masama rungumeso ta yi tana kallan wani irin kuka domin sukaɗaine last hope ɗinta rungumeta sukayi kafin sufara mata magana cikin taushi” ki yi haƙuri duk tsanani na tare da sauƙi wata rana sai labari” cewar Balki.

    Nazba ma ta ce " tabbas and we will never leave you mune nan naki kin ji Ku ba haka ba " haka ne” Masama da Gb sukace.

    Ana haka suka fara jin saukar bulalai a jikinsu Docars ce da mutanenta dukansu take kamar hauka Rukayya batata ta ke ba ƙoƙari ta ke takare dukan ita kaɗai saida ta da kesu sosai kafin ta kalli Rukayya ido cikin ido ta ce " I hate you " murmushi mai ciwo Rukayya ta yi kafin ta ce " and nikuma I love you " wani kalan kallo tamata kafin ta wuce.

    Ɗagasu ta yi tana ba su haƙuri domin ta yi tayi sudaina binta saboda duk inda suka tafi basa dawowa Normal kowa ya tsaneta da wa'inda ta ke tare dasu, haka suka gama exam lafiya ba’a sallamesu ba domin sai su Docars sun yi handing over garesu next week da wannan Docars ta samu ta buɗe sabon muzguna musu saida ta yi kwana biyu bata barsu sunfita daga ɗakinsuba wato Room two Fati Kamba inda Rukayya ku'a jikinta tana kallon ɗakin tana tuna rayuwa da sukayi aciki tana kuka domin tun da su Dejeeh Bala suka gama Docars ta kuresu daga ɗakin kwanansu biyu basici abinciba duk sun galabaita ba abin da sukeyi sai kuka dakuma tuna baya yanzuma suna kukansu kawai idanunta suka fara ganin kamar inuwar Hafsat.

    Inuwar daku a mafarki ba za ta manta da itaba inuwar da kuda babu ruhi ajikintaba ba za ta gushe a kwakwalwartaba Hafsat ce ta bayyana tana mata murmushi ta ce " be brave my yar'lukuta saura kiris you will win and you will fulfilled our promised dama na gaya miki and yanzu kin ga masoyanki na gaskiya” Magana take yi kuka na kwace mata " meyasa za kimun haka meyasa za ki gujeni a lokacin da kika san ina matukar buƙatarki meyasa za kimun haka meyasa " rungumeta ta yi kafin ta ce " bangujeki da son rainaba na gujeki ne domin haka Ubangiji ya ƙudurta ki jajirce kada kitaɓa buɗewa makiyi hannu " tana faɗin haka ta ɓace bat, wani kuka ne Rukayya ta kyace da shi ana haka Docars ta zo ta ce su Masama duk su wuce amma Rukayya ta tsaya haka ba dan ransu yasuba suka tafi jan Rukayya ta yi kamar karya har Raka duk SS3 ananan ciki harda Feedo tsohuwar lover Rukayya wadda tun abin da kaza tayimata ta tsani Rukayya alalo suke bugawa suna dukanta da fashion duk wani mai imani zai tausaya mata haka suka daketa saida numfashinta yafara ɗaukewa ba imani suka tafi suka barta.

    Little Hafsat dasu Nazba da ke laɓe suna kuka haka sukayi saurin ɗaukanta sai dispensary aka bata gado emagency anyi tambayarsu kamar me sai suce ba su saniba kwananta ukku da murmure ta dawo dai dai aka sallameta ana gobe za su amshi muƙami, washegari taro ya yi taro inda aka fara raba prefect inda duk wanda za aba matsayi saije kun tsohun prefect ya amsa ana kawowa kan Rukayya aka bata head girls inda Docars za ta yi mata handing over kamar ta mutu ta cire ɗankwali ta bata fuskarnan ba annuri ahankali yadda ba maijinsu ta ce " I hate you " and I love you " Rukayya ta ce tana murmushi harzata tafi aka tsyar da ita inda aka sake bata muƙamin Hostels captain, kowa na taya ta murna ban da yan baƙin ciki ranar sunsha kashi domin kunsan ɗabi'a ce ta yan' boarding idan sukayi handing over sudinga dukan wa'inda sukaba to haka ce taka sance dan sundako musamman Rukayya data amshi manyan muƙamai har biyu haka dai kowa ya watse,

    Rukayya ta yi kuka sosai domin tasu a ce Hafsat nanan taga wannan girma data samu su rungume juna suyi murna amma kash muriwa tayimata sauri na rabata da "IDENTITICAL TWINS" (my next novel littafin akwai chakwakiya kudai kubiyuni) ɗinta haka suka kuma hida hutun 1 months suka dawo komai yakuma muhallinsa su Rukayya suka koma Room two Fati Kamba suka gyara ɗakin yadda yake haka suka dinga zuba mulki cikin Unity inda ku ɗan Js1 da yashigo yau indai yakwana a unity yasan labarinsu domin sun shimfiɗa mulki dayafi na Deejeh Bala dan ita har mate ɗinta bata bariba yauma suna shiri za su tafi Raka daganan su wuce dukan let out.

    Shiryawa sukayi cikin zane iya cinya ɗaurin talli bari wanda rabin nonowansu duk a waje yake suka fita Raka cike ta ke da mutane haka sukadinga rawa abinsu saida suka gaji suka fara Round duk wanda Allah ya sa suka kama su duka har suka gaji suka wuce. . . .

    Comment

    Vote and

    Share fisabilillah

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    🏻Alƙalami ya fi takubi🗡️

    💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦RAYUWARMU A BOARDING

    (True life story)💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦

    Free Book

    Mallakar Rukayya Buhari Sauwa

    (Rukee Sauwa)

     

    *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

    _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa

    https://m. facebook. com/story. php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo  

       💪🏻J. W. A 💪🏻

    Page 46-50

    Bismillahir Rahmanir Rahim.

    . . . . . . Haka Rayuwa ta ci gaba da zuwa inda su Rukayya suke zuba mulki sun ransu har suka fara Weac basajin daɗin tafiya subar unity suna tuna rayuwar da sukayi amma ina dama haka rayuwa take dole subar unity wasu su shigo haka har suka gama exam lafiya komai sun amshi kyaututtuka da dama ind a gwamnan kebbi ya ba Rukayya kyauta dakuma bata damar ta zaɓi abin da takeso in Allah ya yarda kafin yabar mulki zai yi mata kallonshi ta yi kafin ta ce " sunake yi a gina sabon house a hostel mai suna Biyun Deejeh Bala " kallonta ya yi yadda take maganar za ka tabbatar tanason abin murmushi ya yi ya ce "shi kaɗai kike so" kyaɗa mishi mai ta yi kallon mutanen dake wurin ya yi ya ce " insha'Allah nanda 1 months zan kammala ginin kuma ita za ta buɗeshi.

    Haka Rukayya tabar Unity bayan sunsha kukansu dasu Nazba duk da gari ɗaya suke ta tafi gida da kewa da kuma tunani.

    Kewar Rayuwar da sukayi a makarantar da kuma tunani Hafsat ta, bayan wata ɗaya cike Unity ta ke da mutane ba msaka tsinke su Rukayya dasu Nazba duk sun yi wanka cikin ankonsu na materials pink mai kyau sun yi kyau sosai kafin taji andafa ta juyuwar da za ta yi wazata gani Kaza ce sanye cikin kaya na alfarma ta yi masifar kyau da jiki alamar hutu yazauna wata irin runguma ta yi mata wanda saida taji zafi ta ce” ohchhhhh" sakinta ta yi tana murmushi wani mahaukacin kiss tafara sauke mata a fuska mutane kallonsu kawai suke magana taji da muryar da ba za ta taɓa mantawa da itaba tana faɗin " oh mu kuma aisai mukoma tun da ba’a son dakuma ƙaunar ganinmu " Anty Hadiza tafaɗa da ƙafi dayaja hankalin mutane kanso bakinta yaƙi rufuwa ganin harda su Lola da Wasila dake har Naija ai a kan farin ciki ya yi mata yawa kawai tasa kuka suka haɗu suna tayi.

    Mutane sai nuna Deejeh Bala sukeyi suna faɗin gatacan ita ce ainahin Deejeh Bala ana haka sai kawai wata yar'yarinya yar' kimanin shekara ukku ta zo tana faɗin "Momy kince za ki nuna min takwarana ina ta ke " cikin maganarta ta yara " kana ganin ta ka ga Kaza domin suna mahaukacin kama duƙawa Rukayya ta yi ta kama hannun yarinyar tana kallon Kaza, tun kafin Rukayya ta yi magana Kazan tarigata da faɗin " ya'tace” wata runguma tayiwa yarinyar tana murmushi ta ce " ya sunanki” Rukayya amma Ammyna tana cemun Baby wai sunan wata masoyiyarta ta samun kuma ta ce za ta kaini na ganta” ɗago idanunta ta yi da suka yi jaa sosai tana kallon kaza kafin taƙara rungume yarinyar tana faɗin " na gode na gode dayi min takwara da kikayi tabbas keɗin masoyiyata ce ta haƙiƙa ina matuƙar masifar ƙaunarki " kafin kaza ta yi magana aka fara kiran sunanta kan tazu ta buɗe house, kallonsu ta yi tana kuka kwarin guiwa suka bata ta hanyar gyaɗa mata kai tafiya take yi ahankali har ta isa kafin ta amshi sexul ta yanke Jan zaren dake wurin kowa tafi akemata Mike aka bata akace ku miye abin da idan tana wurinnan ta tunashi takanji baƙin ciki amsa ta yi wani murmushi ta yi kafin ta ce.

    " My soul Hafsat idan na buɗe idanuna na ga nasarar da nasamu a rayuwa ta nakanji hawaye na zuba kuma zujiyata takanyi zafi saboda ita ce mafarin komai tare da ita muka fara komai kuma ita ce silar zamuwata abin da nazama” taƙarashe wani kuka na zu mata duk wanda ke wurin saida ya zub da hawayen tausayinta kafi aka sake cewa” kuza ki iya faɗin wani abu agameda rayuwarku" magana ta ci gaba da yi tsaf tabada labarin "RAYUWARMU A BOARDING" Kowa kuka yake yi kafin ta ci gaba da cewa” ita ce rayuwa ta kuma na ji daɗi daya ka sance nabada "RAINA FANSA” ( My next novel) ga burinta banida abin da zance sai Alhamdulillah haka kowa yadinga tufa albarkacin bakinsa inda taƙara samun kyaututtuka suka shiga cikin Biyun Deejeh Bala house wanda aka yi gini mai kyau da kuma Coulities zama suka yiakan wani bonk cikin wani ɗaki suduka Deejeh Bala, Kaza, Lola, Wasila Naija, Nazba, Balki, Gb, Masama and Rukayya suka haɗe kai suna kuka mai taɓa zuciya ahankali aukace " ALHAMDULILLAH " Wanda ni ma na ajiye alƙalami na ina mai cewa

    "ALHAMDULILLAH!ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!!

    Anan nakwo ƙarshen wannan labarin mai taken RAYUWARMU A BOARDING kuskuren dana yi Allah yay yafemun abin amfani a ciki Allah yabaku ikun aiki da shi kubiyuni domin samun ƙayataccen labarina dazan fara mai taken " IDENTITICAL TWINS "nan ba da jimawaba.

    Wannan littafi tun farkonsa har ƙarshensa sadaukarwa ne gareku my two Hafsat Allah yaji ƙanki my first Hafsat yar'uwata aminiyata abokiyar ahawara Allah ya yi miki Rahama ya sadamu a Aljannah my Alive Hafsat Allah yayiwa rayuwarki Albarka.

    Ma'assalam

    Comment and Share fisabilillah

    Taku har kullum

    Rukee Sauwa

    Domin magana da marubuciya kai tsaye 0703044691

    🏻Alƙalami ya fi takubi🗡️

    *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

    _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen Hausa

    https://m. facebook. com/story. php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

       💪🏻J. A. W 💪🏻

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.