Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
460. Dole mu je mu gai da Sani ɗan Belɗo,
A yi waƙa da kwaikwayo sai ɗan Belɗo,
A bi icce a hau
saman nai sai yaɗo,
Dole ka dole don
ruwan sama sai kwaɗo,
Gafiya ba fita
garai sai ɓoyewa.
461. Lura da kyau idan ka tashi rubutawa,
Masu karatu su
lura nan ga karantawa,
An yi alamar cikin
rubutun Hausawa,
Lura ruwa biyun ɗigo biyu aka sawa,
Ɗaya zai hau saman ɗayan gun zanawa.
462. In ka gan shi an rubuta a rubuce,
Kai ko ka zo kana
karatu a karance,
Sai ka bi ƙa’idar rubutun
Hausance,
Amfaninsu sai wurin buɗe zance,
Don a ruwaito yadda mai shi ke cewa.
463. In aka sa shi sai alamar buɗewa,
Ita ce ƙa’idar rubutun
Hausawa,
Sauƙi za ya zo ga masu
karantawa,
Don haka zan kula
gabanin zanawa,
Su biyu za su zo
ga kalmar farawa.
464. Can ƙarshensa sai alamar rufe zance,
In ka sa ta duk
wuya an magance,
An cika ƙa’idar rubutu a
rubuce,
Za ka gane su can
a ƙarshen rufe zance,
Su biyu za su
sake zowa ga rufewa.
465. Makaɗi shi ka tanadin ‘yan turaye,
Dubi abin da zan
faɗa don ka kiyaye,
Don ka taho da ‘yan ɗigagganmu tagwaye,
Sai ka saka su, don ka huta kai
waye,
Yadda ake ganin
abin zai dacewa.
466. Na ji Alu yana faɗin wannan zance,
Ya ce: “In ka zo
da hankali ka yo dace,
Za mu tsaya mu ba ka
saƙo a rubuce,”
Malam ne ya ce: “Haramun tarko ce,
Duk mai cin ta
tabbata bai morewa”.
467. Ai nassi ya ce: “Jikin duk da ka cin ta,
Matuƙar ya sani ya ƙyale don wauta,
Ko kuma don yana
ganin wai riba ta,
Bai more ma alƙiyama, ku rubuta,
Za a saka shi gun
wuta mai ƙonewa”.
468. Ba ka ganin yawan mutanen da ka cin ta,
Su ke yin
hada-hada don sun manta,
In aka ce ga haram
a nan su ka kiranta,
Ba su gudun wai a
ce da su, su ka jiranta,
Nan duniya
cikinmu su ke holewa?
469. A yi kaurin wuya, da faɗi, ga tunbi,
Su ci daɗi cikin miyarsu akwai zabbi,
A shigo manya-manya motoci sabbi,
Manyan riguna, agogo da madubi,
Ko tafiya sukai
jiɓi na karyowa.
470. Ranar lahira idan an tara mu,
Za a yi bincike a
gano aikinmu,
Wasu ko za a ƙwace ladar su a ba mu,
Sannan wasu za a
gan su duk sun damu,
Sai sun ce: “Ina wurin don ɓoyewa”.
471. Rabbu ya ce: “Zabaniyawa ku tsare su,
Ku riƙe kar ku bar su yanzu
a ɗaure su,
An masu tanadin
wuri don a saka su,
Zaluncin da sun ka
yo da ]ai an kama su.”
Ga sarƙa a ba su domin ɗaurewa.
472. Duk a wurin da mun ka ce, “an ce” lura,
Za mu taho da ‘yar
alamar ga ku lura,
Mun saka ɗan ɗigo-ɗigo biyu mun ƙara,
Haka nan inda mun
ka sa “sun ce” lura,
Ko “ya ce” a nan ruwan za su tahowa.
473. In kuma mun saka su sai buɗe zance,
Domin wanda yaf faɗa shi ya kasance,
Ya yo zantukan da an sa a rubuce,
Don haka mun ka sa alamar a rubuce,
Can ƙarshen mu sa makullin kublewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.