Sa'adatu Sa'ar Mata

    In ka kusan jama'a ta bayan ƙauyuka,
    To babu shakka za ka hango dala.

    So ya fatattaki zuciya har ta dake,
    Na É—au takobi kansa yau zan falla.

    Na kauda tsoro zuciyata ta tsike,
    Ba na gudun tsawa bare bulala.

    Ƙarfi na so shi ne ya sa ni sadautaka,
    Ƙarfen digar jirgi da hannu na ɓalla.

    Ban ma tunanin nai hakan ko ban yi ba,
    Tamkar biredi na yi shi sala-sala.

    Ba na jiran barci bare neman tuwo,
    Don sun sani a cikinsu ba mai shalla.

    In na tuno rabuwarmu ni da Sa'adatu,
    Sai in ji tamkar zuciya tai shela.

    Ta faÉ—awa al'umma abin da ya ke ciki,
    Ƙunci na ruhi zuciya tai talla.

    Wataran idan na tuna ta sai nai murmushi,
    Wataran da nai kewarta sai nai ƙwalla.

    Ta nuna so tamkar É—iya a wurin Uwa,
    Adu'a take kullum idan tai salla.

    Ta faÉ—a tana "Rai zuciya na bar maka"
    Don sonka ya zarce kuÉ—i da tagulla,

    Ya mamaye min zuciya ya sarƙafe,
    Koginsa ya cika babu hanyar É“ulla.

    Don duk samari sun gaza kan tsaida ni,
    Ni kai kaÉ—ai ne zuciya ta walla.

    Nima a zuciya ke kaÉ—ai ce zahiri,
    Ko da a kan hanya na gansu kala-kala.

    Mun farraƙe kowanmu na goge ido,
    So ya rufe kan zuci yai mana illa.

    Allah ya ban madadinta zan daÉ—a godiya,
    Haskenta ya taɓa zuci tamkar cocila.

    Hotonta ne a saman waya ta lokaci-
    Kan lokaci sai na É—aga shi na kalla.

    Ita ce kaÉ—ai mai sanya raina yai fari
    Yau gashi ba ta nan ta ya zan sam kula

    Ita ce Sa'a, Sa'a ta matan duniya,
    Kowa ya samu kamarta ya sam daula 

    Maisugar Ringim ✍️ ✍️
    12/10/2023
    ringimmaisugar@gmail.com
    09123098967
    Soyayya

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.